Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 287659 words

Chapter 32 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1817

Ads at the middle of Article

very fast, ƙasa ƙasa da murya yake furta mata, kada tadaina, taci gaba yi mashi yana samun sauƙi," kamar yadda ya buƙata haka taci gaba dayi mashi karatun, har sai da taji tempreture ɗin jikin shi ya dawo normal, numfashinsa da natsuwarshi sun daidaita tukunna ta dakata da yi mashi karatun acikin kunnuwanshi, zame jikinta ta yi daga nashi, tare da sanya hannayenta ta dafa shoulders ɗinshi, eyes ɗinta na kallon Fuskarshi, idanuwanshi tamkar na mashayin giya,

"Danish can u see my face" tayi maganar tana nuna mashi fuskarta, jinjina mata kai yayi alamar eh, ɗagowa ta yi tare da kallon su Haris dake a tsaitaye, Yadda kasan ƙerarrun gumaka, tsabar mamaki yasa sun kasa rufe bakunansu, Kowa zuciyarshi acike take fal da tunanin menene angel ta karantawa ɗan uwansu danish harya dawo cikin hayyacin shi,

"Angel kinyi matuƙar bamu mamaki" batool ce tayi maganar a lokacin ta dawo inda suke.

"Duk da bamusan menene kika karanta ma danish a kunnanshi ba, amma nayi matuƙar jin wani irin sanyi da daɗi acikin zuciyata, sai naji dama baki daina ba, kin cigaba da yi,"

Batool nakai ƙarshen maganarta, Javed yace"Nikaina naji wani irin daɗi mara misaltuwa, nayi mamaki kuma ganin yadda danish ya samu natsuwa yadaina haukan da yake yi," yakai ƙarshen maganar idonshi akan danish,

Hanna tace"i feel the same, zanso nasan menene angel kika karanta mashi me daɗi," tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,

"Zanyi maku bayani, amma yanzu danish yana buƙatar kulawarmu," tayi maganar tana kallonsu,

Haris dai yayi shiru shi da deeja kowa na tofa albarkacin bakinsa kan irin dadin da suka ji amma banda su, saboda tsabar kunyar da suka ji,

"Ga abincinsa kar ya lalace, aba shi yaci" parveen ce tayi maganar, tare da rankwafawa ta ɗauko tray din ta miƙa ma Angel, hannu biyu angel tasa ta ruƙe handle ɗin tray ɗin a tsakiyarsu ta sanya tray din, ta cire jan ƙyallen, waro ido parveen tayi ganin Roasted Chicken guda ɗaya sai maiƙo take yi ga wani irin ƙamshi, gefe kuma Milk ce a cikin bottle me sanyi, sai wooden bowl mai ɗauke da Fruits salad,'

"Zaka iya ci"? Ta yi tambayar tana kallon danish, wata irin narkakkiyar zufa ta gani tana gangarowa ta cikin yalwatacciyar suman kanshi, bai iya bata amsa ba, sai dai kallon ta da yake yi,

Sai lokacin harisun tsohuwa ya samu damar buɗe baki yace"Bari na taimaka ma shi ya watsa ruwa ajikin shi," yakai ƙarshen maganar, Tare da ruƙo danish, Javed ya taimaka shi suka yi mashi jagora zuwa Cikin toilet ɗinsu,

Bayan tafiyarsu batool ta kalli sauran ƴan uwan nasu"tun da jikin nashi da sauƙi, ku je ku kwanta," Yadda kasan ƴan gudun hijra haka suka tafi sharaf sharaf kowa Ya hau saman gadonshi Ya kwanta,

Ganin parveen taƙi tafiya yasa tace"ke fa" Hannu tasa tana ɗan sosa keyarta "Jira nake Su haris su dawo da danish yaci abincin shi, idan ya rage nima in samu in ɗan ci....." wani kallon rainin wayau batool tayi mata wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar,

"Sai kace kinfi kowa Jin yunwa, Allah yasa idan ya fito ya cinye abincin duka sai muga ya za ki yi" angel dake zaune saman gadon danish ta yi zurfi Cikin tunaninta, bakomai ya ɗaure mata kai ba, face yadda ta iya yin karatun qur'ani tiryan tiryan tun zuwanta gidan kurkukun tasha Yin attempting karatun qur'ani tana gazawa, sai ta dinga jin raɗaɗi a maƙoshinta, A yau dai kamar umarni aka bata tayi karatun haka tadinga ji, Kuma taji kwarin guiwar yin qira'ar, kenan nan gaba zata Iya samun damar yin ibada, mamaki take yi ya akai take samun nasara akan wasu abubuwan? Tabbas Allah yana atare da ita saboda kyakkyawar niyar dake gareta, kuma tana ji aranta cewa Akwai masu yi mata addu'a, fatanta Allah yasa dadynta idan yana araye ya kasance ɗaya daga Cikin masu Yi mata addu'a, Saboda ita addu'ar Iyaye kar6a66iyace akan ƴa'ƴansu kamar yadda hadisa ya tabbatar da hakan,

Shigowarsu haris Cikin ɗakin ne ya katse mata zancen zucin nata, ta ɗago tana kallonsu, Hannayensu ruƙe dana danish, jikin shi duk lemar ruwa, Hada sumar kanshi suka wanke mashi, duk ta manne mashi saman fatar wuyanshi, Lokacin da suka ƙaraso, Saman gadon ya haye ya ɗan kishingiɗa kan shi saman pillow, jikin shi duk ya saki babu ƙwari, idanuwanshi na a lumshe,

"Abincin fa"? Angel ce tayi ma shi maganar, slowly ya dan buɗe idonshi akan fuskarta, in a throaty voice ya furta mata"I can't eat anything now, u can share it," voice ɗinshi yayi low sosai, daƙyar ta iya jin me yake cewa,'

Cikin rashin jin ɗaɗin maganar shi haris yace"Ko madarar ce ka ɗaure ka sha, nasan kana jin yunwa," girgiza ma shi kai ya yi"bazan iya ba, kada ku damu kanku am ok,"

Babu wanda yaji daɗi Acikinsu, Sun so koda milk ɗin ce yasha, amma ya nuna masu cewa babu yunwa attare dashi, Su parveen abun nema ya samu, zama su kayi a kasa Kowa Ya shiga kai hannu yana yagar naman kazar yana Ci, Komai saida suka Bi suka lamushe, bayan sun kammala, Haris Ya zauna gefen gadon Danish, sauran suka wuce saman beds ɗinsu suka kwanta, Angel ma tuni ta koma nata gadon, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, danish ya dawo Cikin su, sai da dare ya nutsa, tukunna haris yabar gefen gadon danish ya koma nashi gadon ya kwanta,

Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan ta juya ta saci kallon shimfiɗarshi, yayi bacci ko baiyi bacci ba?, kasa jurewa tayi a hankali ta dan mirgina ta juya ta 6angaren da yake fuskanta, bayan shi kaɗai take iya gani, jikinshi na lulu6e da bargon da haris ya rufa mashi har zuwa kafaɗarshi,

tana kokari rufe idanuwanta, taga yana mutsu mutsu, ƙoƙarin juyowa ya yi, da sauri ta rufe idanuwanta, don kar ya gane shi take kallo, natsuwa ya yi a yayin da yake kallonta, zuciyarshi cike fal da mamakin canza mashi da tayi, yafi tunanin taji tausayin shi ne saboda halin daya shiga, wata zuciyar kuma tana saƙa mashi cewa kada ka yarda da ita, so take ka saki jiki da ita, ta samu damar kashe ka cikin sauƙi, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin sanyi yaji ba, tun da ta karanta mashi wannan abun da baisan menene ba, Sai yaji duk duniya babu abunda yake kwaɗayin ya kasance yana sauraro acikin kunnanshi idan ba shi ba,

Tunani tayi ko yayi bacci yanzu, tana mutsu mutsun buɗe idanuwanta, yayi saurin rufe nashi eyes, shima baiso ta gane cewa Ita yake Kallo, ta jima tana kallon shi, da zarar taga xai buɗe ido sai ta rufe nata idon, shima haka idon yaga zata buɗe idonta sai yayi saurin rufe nashi, Sai da suka raba da dare suna wannan wasan, Kafin Allah ya kawo bacci 6arawo yayi awon gaba dasu


*ANEELERH*

A tsaye Take saman darduma ta kabbara sallah, Jikinta sanye da dogon Hijabi maroon colour har ƙasa ta sauko, tana ƙoƙarin yin sujjada Taji mutun saman bayanta Ya haye, Kasa ɗagowa tayi saboda gudun kada ya faɗo tasan bai wuci junaid bane, ba yau ya saba yi mata haka ba, a bedroom ɗin Mami ya kwana, har yasan ya tako daga ɗakin mami zuwa ɗakinta, a duk inda ya kwanta bacci ya ɗauke shi ko mun tsakiyar dare ne idan ya farka sai ya nemota duk inda ta shiga, Yadda kasan malamin duba,


Bubbuga bayanta taji yana yi tare da ambaton "Doki sukuta sukuta, doki sukuta sukuta!, yana magana yana sukuwa hada cewa Mommy, Ki tashi mu tafi yawo,' a hankali ta miƙa hannu ta ruƙo shi tare da janye shi daga saman bayanta, Ya faɗo daga gefe saman dardumar, bubbuga ƙafafunshi ya shiga yi, yana raira mata kuka, daurewa kawai take yi sam bata so taji yaron yana kuka, Tsananin tausayin shi taje ji,

Hannu ya miƙa ya ruko cazbaharta dake ajiye saman darduman, Ya miƙe zaune ya zura cazbahar saman wuyanshi, Allah Allah take ta kammala sallar kafin yayi tunanin ɗaukar qur'aninta da ta ajiye wurin daya ɗauki cazbahar, kura mata ido yayi jin taƙi tanka mashi ashagwa6e yake kiran sunanta"mommy! Ni ki tashi muyi wasan doki" yayi maganar da hausarshi da bata ƙarasa nuna ba, ya hanata sakat, daƙyar ta samu ta kammala yin sallar ta zauna zaman tahiya, Ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, Yana cigaba da yi mata shagwa6a, bayan sallame sallar ne ta samu damar kallon shi,

"Bansan meyasa kake yi mini haka ba junaid why? Bakaga sallah nake yi ba, bana hanaka in ina sallah kana hawar min bayana ba"? Wani kallo taga yana binta dashi, kamar wani mai hankali, a yanzu fa shekararshi biyu da rabi,

Sai daga baya ma ta lura da rigar dake ajikinshi, Singlet ce ta abie ya sanya, ta yi mashi yawa har ƙasan ƙafafun shi takai, cike da mamaki tace"kai! Waya sanya maka rigar abie"? Fuskarshi a tur6une yace"Ni na ta" hararar shi tayi"you're lying, ina kaga wayan da zaka iya ɗauko rigarshi ka sanya? tayi maganar tare da kai hannu tana jan kumatun shi,

"Faɗa mun gaskiya My baby boy, ko mamie ce ta sanya maka ita"? Girgiza mata kai yayi"kintan Allah wlh ni nata, in na miki ƙarya Allah ya ƙona......" bata bari yakai ƙarshen maganr ba, ta ɗan hambare bakinshi" Bana haka irin wannan rantsuwar ba?ba'ajin magana ta ko"? ashagwa6e yace"Ae ae nima musha naji yana yi," tsoki taja, shiyasa batason Junaid Yana zuwa wurin shi, duk a wurin shi yake koyan wannan rantse rantsen marasa kan gado, dole sai ta ja mashi kunne, Ya daina Yi agaban ɗanta, tun da yaron wayau ne dashi komai ɗauka yake yi acikin kanshi,

"Kadaina kaji babu kyau," amsa mata yae"Toh, in na daina zaki kai ni wurin Angela"? Murmushi tasaki tare da cewa"Da alama kana son ƴar uwar nan taka junaid, sai dai bansan ya za'ae in kaika wurinta ba, Nima nemanta nake yi...." cikin sanyin murya takai ƙarshen maganar, duk inta tuna su sai taji zuciyarta ta karaya, Almost 4 years kenan babu su babu labarinsu, '

Ɗaukar Junaid ta yi a hannunta ta miƙe ta ɗaura shi saman gadonsu, tana fadin"ka koma bacci dan Allah my baby boy, bana so kayi ta 6arna pls," amsa mata yayi"to" ya lumshe idanuwanshi alamar bacci zaiyi, ƙura mashi ido tayi tana kallonshi batare da ƙyaftawa ba,

Shafa fuskarshi tayi da hannunta, kafin ta zauna daga gefen gadon, takai hannu ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,

Gallery ta shiga, ta lalubo tsoffin hotunansu tana kallo, Wani hoto ta buɗo wanda suka yi su uku, Ranar graduation ɗinsu akayi masu hoton a University of Hagen, dake a ƙasar germany, su uku su kayi hoton kowannasu yana asanye Cikin Graduation gown sunyi matuƙar yin kyau, Allah yayi halitta ta farko Aneelerh ce, A tsakiyarsu Benazir ce kyakkyawar balarabiya, Ta ƙarshe kuma wata aminiyarsu ce masha Allah, Matar akwai diri kamar ita ta ƙera kanta, kowacce da irin baiwar kyan da Allah yayi masu, sai dai kash gaba ɗayansu a halin yanzu ƙaddarar rayuwa tayi silar tarwatsewarsu,

A tsanake take kallon hotunan nasu, tayi matuƙar yin kewar aminnanta, bazata ta6a manta irin shaƙuwar da su kayi da juna ba, runtse idanuwanta tayi tana tuna wasu maganganun da suka jima suna yi mata yawo acikin kanta, ɗaya daga Cikin aminnan nata ne ta furta su a cikin text message da ta ta6a tura mata lokacin da take Cikin tashin hankali tace"Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu........"

Sosai aneelerh ta fashe da kuka, lokacin da ta kammala tariyo abunda ya faru, A fili tace"Allah sarki Aisha! Bansan A ina zan ƙara ganinta ba, Allah ya kare ki aduk inda kike, ni shaida ce akanki, Ke mutuniyar kirkice, bana fata, ƙaddarar rayuwa tayi silar canzaki daga yadda nasanki, '

Cikin shessheƙar kuka aneelerh tace"Narasa Aisha saboda korar karan da mahaifinta yayi mata, na kuma zo narasa Benazir, duk da ita don san ranta ta gudu, daga baya kuma Narasa Mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata, " jefar da wayarta tayi saman mattress, Ta kifa kanta Jikin pillow, junaid tuni ya jima da komawa bacci,

Tasha kuka kafin bacci yayi awon gaba da ita, Wuraren ƙarfe 9 na safe, Mami ta shigo ɗakin Jikinta sanye da atampa , murmushi ta saki ganin yadda uwa da ɗanta suke ta sharar bacci, Girgiza kai ta ɗanyi "Jikana mai abun ban mamaki, dama nasan bai wuci nan ka gudo ba, wurin mommyn taka, bayan ka sace mun rigar mijina, Allah dai ya shirya mun kai,' Takai ƙarshen maganar, tare da ƙarasawa Cikin ɗakin agaban gadon aneeleerh ta tsaya tare dakai hannu tana ɗan bubbuga kafarta" Daughter baccin ya isa haka, Ki tashi muje muyi breakfast,"

Buɗe ido aneelerh tayi sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, koda ganin busassun hawaye akan fuskarta, sai mami ta ɗaure fuska"aneelerh when zaki daina kuka? Sai kace wata ƙaramar yarinya? Abu kaɗan sai kuka duk kin maida kanki wata sauna," rai aɗan 6ace tayi maganar, yayin da take zama gefen gadon idonta akan fuskar aneelerh,

Miƙewa zaune aneelerh ta yi, batare da tace komai ba,

"Fada mun me kuma ya saki kuka"? Muryarta a disashe tace"Mami kiyi hakuri idan kukana ya 6ata maki rai, nasan bakya son ganin zubar hawaye na, nima ba so nake yi ba, sai dai wani abunne ko nayi kokarin na danne saina kasa, idan ba hawayen na zubar ba, bana jin daɗi," yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin kashe ma mami jiki tayi ba ,

Ruƙo hannayen aneelerh tayi acikin nata"Aneelerh, kodai zaki ɗauki shawarar mahaifinki ne, ki koma abuja gidan Uncle ɗinki da zama? ina ganin kamar in kina acan zaki fi samun sauƙi acikin zuciyarki, amma zamanki anan sam babu cigaba," girgiza kai aneelerh tayi yi"Mami dan Allah kudaina yi mun maganar komawa gidan uncle da zama, ya kuke so nayi da rai na? A halin da nake Ciki, ku kaɗai nake gani inji sanyi acikin raina, indai nayi nesa da ku, bazan ta6a samun natsuwa ba" takai karshen maganar fuskarta a yamutse,

Mami ta fahimci halin da aneelerh take Ciki, dama tasan zaiyi wuya ta amince tayi nesa da su,

"Shikenan, bazan ƙara yi maki zancen komawa can ɗin ba, ina fata hakan yayi maki" jinjina kai aneelerh tayi alamar eh,

"Yanzu ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki sarkin kuka, Allah idan baki daina ba sai yaronki ya raina ki, ga shi nan yanzu shima ya fara zama irin ki, ko kallon banza mutun yayi mashi sai ya fara ta6e baki zaiyi ma mutane kuka," murmushi gefen fuska aneelerh ta saki, tare da juyawa tana kallon junaid dake kwance, har lokacin wuyanshi na sanye da cazbaharta daya sanya,

Dariya mami tayi don ita sai lokacin ta lura da cazbahar da ke sanye a wuyan junaid,
"Wayaga ɗan Sarkin malamai," dariya sukayi atare, gwanin ban sha'awa,

Miƙewa mommy tayi"xan koma dining ki same ni acan ina jiranku,"

Amsa mata tayi da toh mami, kafin ta sauko daga saman gadon ta shige toilet, after some minutes ta fito tana gyara doguwar rigar material ɗin dake ajikinta,'

Har lokacin Junaid Bai farka ba, tasan dole yana jin yunwa, hannu takai tare da ɗauko shi, aikuwa kamar ta tsunkule shi, Yaita kuka yana fadin shi bai gaji da baccin ba, tana dariya tace"Am sorry My baby Boy, breakfast zamuyi da zarar mun kammala, Sai ka koma baccin ka, daƙyar ta samu ta shawo kanshi Ya daina kuka, Toilet ta shiga da shi, ta yi mashi wanka, ta fito dashi sa6e saman kafaɗarta, ta nado shi Cikin towel, Gyara mashi Jikin shi tayi kafin ta sanya mashi riga da wando, rungume dashi ta fito ta nufi dining table, Mami ta hango a zaune tana Shan tea, Kujera taja ta zauna suna fuskantar juna da mami tace"ɗazu ban gaishe ki ba, My first love, Ina kwana mamina, ina fata kin tashi cikin koshin lpy," fuskar mami dauke da murmushi ta amsa mata da cewa"Alhamdulillah, my lovely daughter, Ya grand son ɗin nawa naga yana ta tur6une fuska uwa alkubus, halan tashinsa ki kayi daga bacci"? Takai ƙarshen maganar idonta akan junaid, dake zaune saman cinyar mommynsa, sai shan mur yake yi, yana hura hanci, Shi an takura mashi,

"Mami saboda fa ya ci abinci na tada shi, amma da yake shi baisan abun arziki ba, shine yake ta hura mun hanci,"

Mami tace"kwantar da hankalin ki, ae da zarar yayi arba da noodles zai wartsake" hannu mami takai tare da ruƙo plate ɗin dake shaƙe da noodles ta tura ma aneelerh agabanta,

Hannunshi har kerma yake yi wurin kokarin tsoma shi Cikin taliyar, da sauri aneeleerh ta damƙi hannun nashi tare da cewa"Baka ga akwai zafi ba? So kake bakin ka ya ƙone"? ta6e baki ya soma yi alamar zaiyi kuka, lallashin shi ta shiga yi"haba my baby boy, Fushi ba naka bane bari na baka da hannu na" hannu ta sanya ta soma ɗibowa tana bashi abaki yana Ci,

"Mami Ina abie? Ko har sun tafi"? Jinjina kai mamie tayi"tun yaushe kuma, tun bayan sallar asuba yace mun bazai dawo gida ba, daga can zasu wuce, "

"Shi ne ko ya jira muyi sallama dashi" rai adan 6ace tayi maganar, mami tace"sauri yake yi ne, idan mun kammala cin abinci sai ki kira shi awaya ki yi mashi Allah ya kiyaye hanya," amsa mata tayi da toh, daga haka suka Cigaba da cin abincin su,


*south korea🌹*

Seoul City,

Hajiya adama ce zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, A cikin katafaren Palourn gidansu, jikinta na sanye da doguwar cord

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads