Showing 87001 words to 90000 words out of 287659 words
Chapter 30 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
da waɗannan kwartayen idanuwan nata,
"A'uzubillahi minasshaiɗanirra'jim, Aniyarki ta biki, Kuma ina nan ina zuba ido, Gobe adawo mana da ɗan uwan mu danish, idan ba haka ba komai zan iya aikatawa wlh, zan nuna maki hatsabibanci na, zan addabi rayuwarki,
"takai ƙarshen maganar tare da jefa mata harara ta murguɗa mata baki, gyaɗa kai tsohuwa tayi Batare da ta furta wata kalma ba, ta dogara sandarta zuwa kopar ɗakinta, ta buɗe ta shige tare da jan ƙopa, tafiyarta keda wuya angel tabi kowani sashe na ɗakin ta tottofe shi da addu'o'in neman tsari kamar yadda ta saba, ta kuma bi kowani gado tun daga kan gadon su Hanna duk ta wanke su da addu'a, bayan ta kammata ta koma saman gadonta, A tsakiyar gadon ta zauna tare da ɗaga hannayenta tana addu'a, akan Allah yabata Ikon yin nasara akan miyagun mutanan nan, Allah kuma Ya tsare mata daddynta aduk inda yake, idan kuma Ya mutu Allah ya kai rahama ƙabarinshi, Hatta danish sai da ta yi ma shi addu'a, Ta kuma roƙi Allah daya kawo masu ɗaukin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Ta jima tana yin addu'o'i kafin daga ƙarshen ta janyo bargonta, ta lullu6a ma Jikinta,
Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci Yayi awon gaba da ita, can cikin dare wata irin zufa ta soma wanke fuskarta, wani irin matsanancin zafi ta ko'ina ajikinta, mutsu mutsu ta dinga yi tana matse idanuwanta, yayin da ta dunƙule hannayenta, tamkar ƴar dabbe, duk ta hargitsa shimfiɗarta, da alama mafarki take yi, ciccije la66anta tayi har sai da ta fasa su, ƙasa ƙasa take karanta duk wata addu'a da tazo mata a cikin kanta, a daren ranar bata yi bacci mai daɗi ba,
Tun daga saman gado Ta mirgino ta ƙundumo ƙasa ta daki floor ɗin sosai, har cikin kanta taji zafin buguwar da ta yi, Lokaci ɗaya ta farka kamar wadda Aka tsakura ta ware manyan gray eyes ɗinta tana kallon ceilling, Sai faman haki take yi kamar wadda ta yi gudun famfalaƙi,
Ƙoƙarin tariyo abunda tayi mafarki akanshi tayi, A cikin mafarkinta wasu baƙaƙen Maguna Guda uku sun farmake ta asaman gadonta, Faɗa ya kaure a tsakaninsu, Ta dinga yakushinsu tana kai masu cizo suma suna kokarin yakushinta sai dai Allah bai basu nasara ba, a ƙarshen itace taci galaba akansu ta yi masu jina jina sukai ta kuka, har suka sauko daga saman gadonta suka watsa aguje,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta saki murmushi har dimples ɗinta suka lotsa, da alama taji daɗin damben da tayi acikin mafarkinta, bata motsa daga kwancen da take a ƙasa ba, hada bargonta da pillow ɗinta duka suna rungume a hannuwanta, Suma hadasu akayi artabun,
"Gidan kurkukun ƙaddara Ba gidan marayu bane Gidan Matsafa ne" yanzu ta ƙara tabbatar da zarginta akan cewa Gidan Mallakin Matsafa ne, Sai dai batasan wasu kalar matsafa bane, masu shan Jini, ko kuwa masu Cin naman mutun, akwai sauran rina akaba, dole sai ta bi asannu tukunna zata gano ainihin me waɗannan matsafan suke aiwatarwa da mutane ,
Ta yi zurfin acikin tunaninta muryar batool ta katse ta"Sister lafiya? Me kike yi a ƙasa"? Wurga idonta tayi akan batool dake A zuƙunne gabanta, ba tasan Lokacin da tazo wurinta ba,
"Sai faman sakin murmushi kike Yi kamar wadda akayiwa albishir da mukullin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara" fashewa angel tayi da dariya Jin abunda batool tace, haƙiƙa maganarta ba ƙaramin daɗi tayi mata ba, wannan babban albishiri ne kuwa mutun ya mallaki mukullin fita daga kurkukun ƙaddara, Har tafara ayyana irin shagalin da zatayi aranar da tabar gidan kurkukun nan, zatayi farin Cikin da bazata Iya misalta shi ba,
"Faɗamun me kike ma dariya? Wata'ƙil nima ya sanya ni farin Ciki"acewar batool fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar,
Mikewa zaune angel tayi still pillown ta na rungume a hannunta, sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, hada side by side na fuskarta, hannu batool takai tare da ruƙo gashin kanta tana fadin"yakamata In rage maki sumar kannan naki, idan ba haka ba nan gaba idan kina tafiya sumar zata dinga taɗiyo ƙafarki ne," dariya suka saki atare,
Angel tace"baki lura gashin ki yafi nawa yawa ba? Kalli Fa yadda sumar kanki ta Cika ko'ina kamar kin kifa kwando asaman kan naki, Gashin duk ya nannaɗe kamar taliyar indomie,"
Ta6e Baki batool tayi ta ɗan kai idonta kan sumar kannata, ita kanta tsoron kallon yawan sumar ta take Yi, saboda yadda take ha66aka,
"Kwanan nan zan samu abunda zan datse ta, Don ni banga amfani gashin kaina ba," acewar batool,
Angel tace"da ace a waje kike rayuwa da baki faɗi hakan ba, saboda gashi abun ado ne ga ƴa mace, yana ƙara ƙawata kyan mace sosai, kuma yana jan hankali mutane, idan Allah yasa muna da rabon fita daga Cikin kurkukun nan, ke da kanki zaki shaida abunda nake faɗa maki, mutane ma rububinki zasu dinga yi saboda kyanki,"
Duk wannan maganganun da angel ke yi batool fa bata fahimtarta, domin kuwa batasan Ya kyan fuskarta ya ke ba, tun da Allah ya halicce ta Bata ta6a kallon madubi ba, tadai san kyau a fuskar danish da kuma fuskokin su Azeeza, Amma Ita batasan Ya kamanninta suke ba, kamar yarda suma su Azeezan basu ta6a kallon madubi ba, Basusan Ya suffarsu take ba, Sai an kwatanta masu,
"Angel nifa bansan Ya ake ganin kyau na ba, Saboda bansan ta wace hanya zan ga fuska ta ba," tayi maganar tana kallon angel,
Tuntsirewa angel tayi da dariya Hada dafe Ciki, Batool ta daure fuska"stop laughing at me bana son wasa fa " daƙyar angel ta samu ta dakata da yin dariyar, A tsanake Ta kalli batool tana zayyana mata kyawun fuskarta,
"Farko dai ke doguwace, fara sol son kowa ƙin wanda ya rasa, idanuwanki Dara dara dasu manya farare ƙyal launin su brown colour, ga dogon hanci, tausasan la66anki brownish colour ne yadda kasan yankan tumatur saboda tsabar kyansu, ke fa ɗin kyakkyawa ce ajin farko, tun da angel ta soma magana batool ta saki baki galala tana kallonta, Tsabar farin Ciki ya hana ta furta komai, Daɗi take Ji ana zayyana mata irin kyanta,
Wani abu da angel bata sani ba, tun lokacin da Ta soma zayyana kyan fuskar Batool, Gaba ɗaya su Hanna dasu azeeza, rubina Hibba, eve, yasmin, da deeja da parveen Kaf ɗinsu Suna a zuƙunna kewaye dasu, Jira suke ta kammala Zayyana ma Batool kyawun fuskarta suma ta faɗa masu Ya nasu Kyan yake, Tofa angel ta zama Mirror,
Baƙaramin wahalar da ita su ka yi ba, Sai da tagama da matan sai ga Javed da mubeen, hada naufal suma suka tasa ta gaba sai ta faɗa masu Ya kyawun fuskarsu yake, har wani jiri take gani acikin idanuwanta saboda tsabar gajiya, Ga gunwa tana ji sunƙi bari ko toilet ta shiga ta watsa ruwa ajikinta, sai daɗi suke ji an faɗa masu cewa su kyawawane, Sai da ta kammala Javed Yace"Yanzu ki faɗa mana waye yafi kowa kyau acikin mu"? Suka tsareta da ido suna jira su ji amsar da zata basu, Kowa sai gyara sumar kanshi yake yi don ta ce shine yafi kyau,
"Zan fada maku tsakani da Allah, wanda yafi kowa kyau acikin ku, Baya atare daku yanzu haka," gaba ɗaya taga sun kwashe da dariya, Da mamaki akan fuskarta tace"meya baku dariya" Mubeen yace"saboda Kin canka dai dai, Wannan wanda baya atare damu shine yafi kowa kyau acikin mu,"
Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da ɗaura idonta kan batool tace"Amma duk da kyanshi, Batool itace zata zo na ɗaya saboda Ita macace, bayan batool kuma sai Azeeza kodan saboda wannan kyakkyawan murmushin nata, Daga azeeza kuma sai Javed...." duk wanda ta ambaci sunanshi sai taga yanata washe baki
"To ki faɗa mana wanene Yafi kowa muni Acikin mu"?
Batare data yanke shawara da zuciyarta ta basu amsa da cewa"Haris ne, Cikin mata Kuma deeja ce"
Deeja dake atsaye Ta ruƙe qugu tuni ta tur6une fuska, jin an kirata da mummuna, dama a ƙule take da angel ganin yadda sauran Ƴan uwanta duk suka Saki jiki da ita, bayan irin Ƙarairakin da tayi masu, ita kanta angel tayi mamakin zuwan da su ka yi wurinta, bayan Irin juya mata bayan da su kayi amma yau sai gashi sun sake da ita, duk da tasan Zaiyi wuya ayanzu su yarda da ita, kamar yadda suka yarda da ita a lokacin Baya,
Duk wannan abun dake faruwa Haris Baya acikin ɗakin bai jima da farkawa ba, Ya wuce Toilet, baisan wainar da suke toyawa ba,
"Kowa ya ta shi yaje ya shiga wanka, ya tsarkake jikin shi, kafin giants su kawo mana breakfast ɗin mu," batool ce tayi masu magana, ɗaya bayan ɗaya kowa ya mike Ya nufi Toilet,
Lokacin da suka kammala Yin wanka, bada jimawa ba, Giants Suka kawo masu Abinci, Yau Hada Chocolate Cake aka kawo masu Kowa ɗaya, ba ƙaramin dadi suka ji ba, Saboda suna matuƙar son cake,
Yanzu sun saba da zarar Sun kammala Cin abinci, Sai a haɗu a motsa Jiki, Bayan sun gama, Kowa zai zauna ya huta ne, Yau fa tun da aka ta shi basu ga walwalar haris ba, Hatta angel tayi mamakin halin daya shiga yau, ya saba kullum sai ya ƙunsa mata baƙin Ciki, amma Yau kota kanta baibi ba, ko abincin shi bai ci ba, kamar wanda ɗan kanoma Ya kama haka ya dinga yi masu safa da marwa acikin ɗakin, idan ya gaji da yin zarya ƙafafuwanshi suka soma yi ma shi raɗaɗi sai ya koma saman gadonshi ya kwanta ya kalli ceilling, damuwace ta ishe shi ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, Ya gaza samun kwanciyar hankali, kowa ya kasa gane kanshi,
A lokacin suna zazzaune Saman gadajen su suna hutawa, Haris Ya sauko daga saman nashi gadon, Buguzun buguzun yake tafiya har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa yaci burki ya tsaya tare da kai hannu ya kwankwasa ƙopar, Duk suka zuba mashi ido suna kallon shi, kusan sau uku yana buga kopar kafin, Ya soma jin alamun ana buɗe kopar ta Ciki,
Tsohuwa Ce ta fito hannu ruƙe da sanda, tun daga kan yanayin yadda ta ganshi ta tabbatar da cewar ba a hayyacin shi yake ba, ya haɗe rai zuciyarshi har wani tafarfasa take Yi,
"Harisu Lafiya ka ke buga mun ƙopa"? Yana huci yace"Nagaji da jiran dawowar danish, So nake naganshi, ko bai warke ba adawo mana shi cikin mu mu cigaba da yin jinyarshi, hankalin mu sai yafi kwanciya," tunkan haris yakai ƙarshen maganarshi, Sauran ƴan uwan nashi duk suka sauko daga sama beds ɗinsu suka nufi inda tsohuwa da haris suke atsaye, banda angel dake hakimce saman gadonta, tana kallonsu,
Marairaice mata fuska Azeeza ta yi, Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace"Idan har dagaske Kina son Mu, adawo mana da danish ɗinmu mu cigaba da yin jinyarshi acikin mu, mun yi maraicin rashin shi acikin mu,"
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga Yi mata magiya akan adawo masu da danish ɗinsu, Su suke Yi mata magana amma idonta na akan angel, dake kallonta fuskarta ɗauke da kayataccen murmushi, aranta tace"nasan yanzu zata ƙara jin haushina saboda sun fara tuhumarta akan bazata dawo masu da ɗan uwansu ba, Yanzu ya rage naki tsohuwa kodai ki dawo da danish ko kuwa sufara zarginki,"
Gyaɗa kai tsohuwa tayi fuskarta a tur6une tace"Ku kwantar da hankalin ku, Yau danish zai dawo Cikin ku, Kuje ku xauna," Takai ƙarshen Maganar tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta,
A bakin ƙopar ɗakinta, suka Zazzauna don yau sunci alwashin indai Danish bai dawo ba anan zasu kwana, angel dai na can kwance daman gadonta bata motsa ba, ta zuba ido tana jira taga ta wace ƙopa za'a shigo masu da danish, Dagaske zai dawo yau ko kuwa? Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tana jin bacci sama sama,
Har wuraren marece ba'a dawo masu da ɗan uwansu danish ba, sai da kowa ya fidda rai da dawowarshi aranar
Kwatsam Ba zato ba tsammani, suna zazaune a bakin kopar ɗakin tsohuwa wasu har sun fara gyangyaɗin Bacci, Suka soma Jin motsi buɗe ƙopa, zumbur kowan nan su Ya miƙe Cike da sa ran Ganin danish, sun tabbatar shi ne saboda yanzu ba lokacin kawo masu abinci bane sun riga sunci tun ɗazu da safe,
takun Tafiyar Giant suka Jiyo daga Can kusurwar Benan, Jiki na Rawa suka Watsa da gudu Xuwa bakin stairs ɗin Kowa Ya ci burki yana faman Baza Idanuwanshi, Tuni Giant ɗin daya kawo shi Ya juya ya fuce Ya datse door,
Tun daga ƙasa suka soma Kallon shi, doguwar ƙafarshi sai kerma take yatsun ƙafar duk sun manne ma juna, jikin shi sai rawa yake yi idanuwanshi sun zazzaro tamkar ƙwayar idonshi zata faɗo ƙasa, jijiyoyin wuyanshi duk sun fito ruɗu ruɗu saman farar fatarshi,
Kayan jikinshi duk sunyi uban squeezing, sumar kanshi ta hargitse duk ta cukuikuiye
Lamarin ya yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Duk sun gaza yi mashi magana, haris ne ya yi ƙoƙarin furta sunan shi"DANISH lafiyarka kuwa? Ko har yanzu jikin ne"? Ya yi tambayar yana ƙoƙarin matsawa kusa danish,
Dafe kai suka ga yayi da hannuwanshi, Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda ta razanar dasu, Angel dake niyar nutsawa Cikin baccin ta, Sautin ƙarar danish ya farkar da ita, a firgice ta ware idanuwanta tare da kallon inda suke a tsaitsaye Cirko cirko abakin Benan, Da sauri ta sauko daga saman gadon Jikinta har 6ari yake yi, ta cikinsu ta ratsa ta tsaya Dab dashi tana kallon shi,
Ya ƙanƙame Jikinshi yana Girgiza masu kai, la66anshi na kerma ya soma faɗin kada su matso kusa da shi, baison ganin kowa, ya tsani kowa" yana kai ƙarshe maganar shi, da gudun gaske ya bi ta tsakiyarsu ya bangaje su bai nufi ko'ina ba sai Cikin toilet area ɗinsu Ya shige ɗaya daga Cikin toilet ɗin Yaja ƙopa ya datse yadda baza su iya shiga ba,
Fashewa da kuka Aziza tayi saboda tsoran da taji,
Da gudu suka ɗunguma zuwa bakin ƙopar ta farko, Haris ne ya shiga bin ƙofofin toilets ɗin yana kwala mashi kira"Danish! danish! Baka ji ina kiran ka? Wai meke faru ne? Pls ka buɗe mana ƙopa, Munyi kewarka sosai," a ƙopar toilet na ƙarshe yaje ya bubbuga ta yaji ta a garƙame alamar Nan ciki danish ya shiga,
A ruɗe rubina tace"Bari naje na faɗa ma tsohuwa tazo taga halin da ɗan uwanmu yake ciki, kada mu rasa shi" ta yi maganar tare da juyawa da gudu ta fuce,
Cikin shessheƙar kuka aziza tace"Wayyo Allah danish meya ke faru dakai ne? Dan Allah ka buɗe ƙopar,"
Hawaye ne acike da idanuwansu Javed, Eve tace"Ban ta6a ganin shi cikin wannan mawuyacin halin ba, sam danish baya a hayyacin shi," tana rufe baki deeja tace"Ai duk laifin Angel ne, itace sila da ace bata ta6a lafiyar jikin shi ba, da duk hakanbata faru ba,"
Cike da takaici Angel tace"Nifa bani ce silar shigar shi cikin halin nan ba, koda ace ni ce amma ae an kai shi treatment room ko? meyasa daya dawo babu sauƙi ajikin shi? Kenan ba duba lafiyar jikin shi akayi ba, Wani abunne daban su ka yi mashi........"tsawa Haris ya daka mata"Idan har Danish ya rasa ranshi, ke ma ki shirya binshi, ƙafarshi kafarki, muguwa kawai,"
Fashewa angel tayi da matsanancin kuka tana faɗin ita ba ita bace sila,
Faɗo wa cikin wurin rubina tayi har suna haɗa baki wurin tambayarta ina tsohuwar take, idonta cike tab da kwalla tace"Na kwankwasa ƙofar ɗakinta, bata buɗe ba"
Guntun tsoki Haris yaja, Yaci gaba da bugun ƙopar yana kiran sunan danish amma shiru bai amsa masu ba,
Gaba ɗaya sun taru agaban toilet ɗin Sai faman ƙwala mashi kira suke yi ya yi shiru babu magana,
"Me zai hana mu sanya ƙarfi mu buge ƙopar wata'ƙil ta buɗe," batool ce ta kawo wannan shawarar, gaba ɗaya suka shiga bugun ƙopar, idan wannan yayi ya gaji sai wannan ya jaraba, duk anan ƙarfinsu ya ƙare dama ya lafiyar gwiwa, abinci sau ɗaya arana,
Gaba ɗaya sun fidda rai da fitowar danish, duk jikin su ya yi sanyi, ransu yana basu cewar danish ya mutu acikin kewayan,
Ransu duk a jagule suka fito daga wurin toilet din, suka koma cikin ɗakinsu a ƙasa kowa ya zauna, angel tana a tsaye bakin ƙofar farko ta shiga toilets ɗinsu,
Idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla, zuciyarta acike take fal da tunanin Meya faru da danish? Yau 5 days kenan Yana a treatment room meyasa baiji sauƙi ba? Anya kuwa duba lafiyar jikin shi akayi ko kuwa ƙara mashi ciwon akayi? Duk yadda ta ƙagara ta yi toxali da danish sai da taji ƙuncin halin da ta ganshi aciki, kwata kwata Baya a hayyacinshi tamkar an canza shi, runtse idanuwanta tayi tana tuna Yanayin da tayi arba dashi, gwanin ban tsauyi kamar wanda aka zaƙulo daga bakin kura,
"Yanzu ya zamuyi? Munbar shi acan ciki, Allah kaɗai yasan halin da yake Ciki" mubeen ne ya yi maganar fuskarshi jaga jaga da hawaye,
Naufal yace"muna ji muna gani zamu rasa ɗan uwanmu, Wai meke faruwa da danish? tsohuwa tace an kaishi treatment room, ana duba lafiyar jikin shi but why danish baiji sauƙi ba"? Ya yi ma kanshi tambayar da baida amsarta,
hibba tace" ga shi tsohuwa bata nan, nasan da ita zata ceto rayuwarshi" daga inda angel take tana iya juyo maganganun su, ta tsani taji sun ambaci sunan tsohuwa, kuma har suna da yaƙinin itace kaɗai zata iya ceton rayuwarshi,
Aziza sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, shi haris Yama rasa ta cewa saboda tsabar ƙululun baƙin Cikin daya tokare mashi maƙoshin shi, zuciyoyinsu sun karaya, ba haka su kayi tsammanin zasu ga ɗan uwansu ba, ba ƙaramin sage masu gwiwa akayi ba, sun rasa yadda zasu yi danish Ya buɗe masu ƙopa, Ko magana baiyi balle ma su sanya ran yana araye,
Gaza jurewa angel