Header Ads
Showing 105001 words to 108000 words out of 287659 words

Chapter 36 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1822

Ads at the middle of Article

ta murza shi kamar tace shine sai kuma ranta ya bata cewar bashi bane, ƙasa ƙasa da murya yake ce mata ke ni ne, ki ce ni ne,' amma ina batool sai ta tsalleke shi ta ruƙo hannun Parveen, wadda tuni fitsari ya kamata, motsa lips ɗinta tayi tare da cewa"He is the one"

Hanna tace"you're wrong" tayi maganar tare da zame hannunta daga kan fuskar batool,

Waro ido tayi ganin parveen, gaba ɗaya suka fashe da dariya, Cikin shessheƙar kuka parveen tace"Ban yafe ba, Kinja min bala'e, "

Janyo kwalar rigarta batool tayi'hakuri zakiyi, dama kinfi kowa Cin abinci yau, Kizo kawai mu basu baya suyi mana dunduna, ba yadda ta iya haka suka duƙa, kowa yayi masu dundu abaya, parveen tasha kuka, ita kanta batool saida ta matse ƴar kwalla, don da mugunta suke yin dundun,

Komawa su kayi Cikin layi, next person da aka kirawo, Azeeza ce aka ce ta Canko masu Naufal, hanna ta rufe mata idanuwanta, Da yake Allah yayi mata baiwa, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita shinshina kamar mayya, wai da ƙamshin jikinsu take amfani, tana zuwa kan hannun naufal ta shinshina, sai ce wa tayi"Shi ne" gaba ɗaya suka sanya sowa, " tsohuwa fa yau ta samu abun nishaɗi, sai faman murmushi take yi, har lokacin basu son cewa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta ba, tana kallonsu,

Babu rabon azeeza tasha dundu, angel dai sai fargaba take yi, ta ƙosa layi yazo kanta taji wa za'ace ta canko, Har Allah Allah take Yi acikin zuciyarta,

Mutane na gaba da aka kira, Deeja ce akace ta gano Danish!!, hanna ta rufe mata idanuwanta suka tafi suna bin layi, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita saki tace bashi bane, hankalin angel yayi matuƙar tashi, fargabarta kada Deeja ta cankota, taja mata bugu, aikuwa dai deeja tana zuwa gaban angel ta damƙi hannunta, har kusan fitsari saida angel tayi, aruɗe take girgiza mata kai kamar tana ganinta, har ta buɗe baki zatace shi ne, sai kuma ta saki hannun angel ta ƙara gaba, nauyayiyar ajiyar zuciya angel ta sauke hada sanya hannu ta shafa ƙirjinta, taji daɗi,

Cikin rashin sa'a deeja ta canko Rubina tace shi ne" rubina taji haushi, shaƙo wuyan Deeja tayi tana jijjigata tace"saboda ke shashasha ce, ta ina hannuna yakai na danish tsayi? Ba ki ga yatsun hannayena guntaye bane? Ke baki banbancewa ne? Gaba ɗaya suka fashe da dariya, hatta danish dake a tsaye saida ya ɗan saki murmushin gefen fuska,

Hanna tana dariya tace"Ba faɗa bane wasa ne, Kuyi haƙuri kuzo ku xuƙunna, Ku kar6i la'adarku" rai a6ace Rubina ta fito daga Cikin layi, takai hannu ta jan yo wuyan rigar Deeja, suka shiga tsakiya, Suka duƙa, ɗaya bayan ɗaya kowa yazo yana yi masu dundu abaya, koda aka zo kan angel, saida ta naɗe hannun rigarta, dama haushin deeja take ji, ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta Buga mata dundu abaya, har saida deeja ta kife ƙasa tana kuka,

Girgiza kai tsohuwa tayi ganin irin muguntar da angel ke yi masu wurin Yin dundu, ta kosa layi yazo kanta taga idan ita zata Iya tsira🤣

"Tun da naga mutane sun ragu, saura mutun huɗu suka rage, bazai yiyu abaku za6i ku canka ba, Sabo da za ku yi nasara Cikin sauki, don haka gaba ɗaya ƴan wasa su dawo Kan layi," hanna ce tayi maganar idonta akan su Haris dake zuƙunne suna jinyar bayansu,

Miƙewa su kayi kowa yana hura hanci, Suka Koma Kan Layi, Tofa su angel murna ta koma Ciki, ganin sun koma su goma sha huɗu,

"Adai dai ta natsuwa, Last 4 person da suka rage, zan fadi sunayensu, akwai Eve, Angel, danish and hibba, sai kuma Ni hanna cikon ta Biyar, Yanzu Zan koma Cikin ƴan wasa, Batool ke ce zaki wakilce ni, A matsayin alƙalin wasa, a dokar wasan Sabon alƙali zai Iya faɗin nashi sabbin dokokin,"

murmushin mugunta batool tasaki, harta hango haɗin da za ta yi, Fitowa ta yi daga kan layi, Ta koma ta tsaya a inda hanna take, Ita kuma hanna ta koma Kan layi ta jera da sauran ƴan wasa

Idon kowa ya koma kan alƙalin wasa Wato batool, a tsanake ta soma magana" A matsayina na sabon alƙalin wasa, Ina da tawa sabuwar dokar, Mutane biyar da suka rage idan har na canko ɗaya daga Cikinsu, na bashi sunan wanda zai za6o mini, idan ya kuskura ya canko ba dai dai ba, dashi da wanda aka bashi sunan shi ya gano kowa Zai yi masu dundu A bayansu, Sa'an nan babu su babu Cin sauran abincin da muka rage, kason su za'a raba ma sauran Ƴan wasa ne su Cinye" tun da batool ta soma kora jawabi, hankalin angel ya ɗunguzuma, ba ita kadai ba hatta hibba da eve da hanna sai da hankalinsu ya tashi, Jin wannan Dokar ta batool, taya za'a raba ma sauran ƴan wasa abincinsu idan suka yi failing, akwai matsala babba,

Idon batool akan Na Angel data cika ta batse, murmushi ɗauke akan fuskar batoo tace"Next person Is......." Gaba ɗaya sun baza ido suna sauraronta, hatta tsohuwa a ƙagare take da taji wa batool zata Canko,

"Danish! " a hankali ya ɗago da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu kan batool, Yana jiran Jin wa zata ce ya canko,

Tunkafin batool ta ƙarasa maganarta, angel ta shiga girgiza mata kai daga inda take a tsaye Cikin layi, Alamar kada tace ya gano ta, don tasan halin danish zaiyi wuya ya iya canko ta, ita da take da tarin maƙiya acikin wasan kowa so yake tayi failing don tasha dundun, expecially haris da Deeja, a ƙule suke da ita, don har yanzu basu daina jin raɗadin dundun da tayi masu ba,

"Danish zaka Canko mana ANGEL, kafin mu fara zan ƙara tunasar dakai dokar wasa, idan har kayi kuskuran canko wadda ba ita ba, Kowa zaiyi maku dundu, sa'annan babu ku babu Cin abinci an jima, za'a raba ma sauran ƴan wasa naku" wani irin murmushin mugunta haris da deeja suke saki, daɗi kamar ya kashe su, don sunsan cewa Danish bazai iya canko daidai ba, saboda halinshi da suka sani,


Cike da shaƙiyanci deeja tace"Ina fata Danish Ya gaza canko ki, Na rantse hatta spinal cord ɗinki sai ya amsa idan nayi maki wani mugun ƙulli" tayi maganar tana kwatanta yadda zata bugu bayan angel da hannunta, gaba ɗaya suka sanya dariya, angel kuwa ta ɗaure fuska babu walwala kwata kwata, duk tasha jinin jikinta,

Haris yace"ni kuwa Da gwiwar hannuna zan daki bayanta har sai ya 6urma, In yaso su Giants sunyi jinyarta a treatment room," gaba ɗaya suka sanya dariya cikin nishaɗi, idanuwan angel tuni sun cicciko tab da kwalla, tabbas ta gama karaya domin kuwa tasan danish bazai ta6a iya gano ta ba acikinsu,

"Danish come forward" Batool ce ta yi maganar tana nuna shi, fitowa yayi daga Cikin layi, ya ƙarasa gaban Batool ya tsaya, saboda tsabar mugunta haris hada cewa ajira ya cire rigarshi, a ɗaure ma danish fuska da ita, don yasan tsayin Batool bazai kai na danish ba, hakan na nufin bazata Iya datse mashi ido da tafin hannayenta ba, batare daya samu ƙofar da zai iya kallonsu ba, jama'a kowa fa yaci burin bugun angela,

Hannu haris ya sanya tare da tu6e rigarshi, Ya wurga ma batool ta sanya hannu biyu ta ca6eta, idon danish akan na angel da tabi ta kame kanta, kamar ta fashe da kuka,

Ɗaure mashi fuska batool tayi da rigar haris, ta matse mashi ido sosai har saida yaji zafi,

"U can Start" ta ambaci hakan tana kallon shi, tafiya ya soma Yi yana lalubansu, ya ruƙo hannun rubina ya saki, ya ruko na azeeza ya saki, ya ruƙo na eve ya saki, ya kuma ruƙo na parveen ya saki, Kowa ya zuba ido yana kallon shi, ya cafko hannun javed ya murza shi, Kowa yayi tunanin shi zai canka amma sai suka ga ya saki hannun,

"A ƙa'idar wasan, Ba'a magana, idan na kama mutun yayi magana, kowa zaiyi mashi dunduna Biyu, sannan ya rasa abincin shi, Bayan wannan kuma Zai wanke mana uniform ɗinmu idan su ka yi ɗauɗa, zai kuma wanke toilets ɗinmu, Bayan wannan kuma ɗan wasa yana da damar da zai iya ta6a ko'ina ajikin sauran ƴan wasa domin ya samu damar canko wanda akace ya za6a, wannan ba laifi bane" alƙaliyar wasa ce ta kora masu wannan jawabin, tayi hakanne don tasan halin angel da shegen wayau, tana iya cewa zata yi ma danish raɗa don ya gano ta,

Cigaba da tafiya Danish Yayi yana ruƙo hannayensu, yana zuwa kan saitin angel ƴan hanjin cikinta suka kaɗa, kowa ya tsaresu da ido, jira kawai suke su ga idan danish zai iya gano ta,

Ruƙo hannunta na dama yayi da hannayenshi biyu, ya shafa su ya matsasu sosai, runtse idanuwanta ta yi jikinta na kerma, ba halin tace mashi itace, saboda idon kowa dake akansu,

Sakin hannunta ya yi, nan take su deeja suka soma Sakin murmushin mugunta, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, A wani slow danish Ya ɗaga ƙafarshi har zai wuce sai kuma ya ɗan dakata, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah,

Komawa ya yi gabanta ya tsaya tare da miƙa hannu tamkar zai kamo hannunta, sai kuma ya kauce hannunshi ya cafko sumar kanta, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, cikin sanyin murya yace"she's the one, am i right? Gaba ɗaya su Azeeza suka Daka sowa suna Tafa mashi hannu, hatta tsohuwa saida Ta ɗanyi murmushi duk da ba haka taso ba, amma Abunda ya burgeta kaifin basira irin na danish, yayi wayau, saboda yayi amfani da yanayin kakarwar da jikinta keyi, da ya ruƙo hannunta da farko ya fuskanci hakan, shiyasa ya sake dawowa ya kai hannu kamar zai damƙi hannunta, sai yayi wayan kaucewa ya damƙi gashin kanta, saboda yasan idan itace, zai samu gashin kanta har wurin qugunta, wato danish yayi amfani da kwakwalwarshi,

Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya angel ta sauke, lokaci ɗaya kuma ta fashe da wata irin mahaukaciyar dariya hada dafe ciki, Taji daɗi data tsalleke tarkonsu Haris da deeja, kamar su fashe da kuka saboda tsabar 6acin rai da takaici, plan ɗinsu ya rushe,

Sai da ta kammala shan dariyar, tukunna ta sanya hannayenta biyu ta warware ma danish ɗaurin da akayi mashi akan fuska, bayan ta kammala ta xame rigar tare da wurga ma haris ita saman fuskarshi, rai a6ace haris ya ca6e rigarshi yana faman kumbura baki

Natsuwa tayi tana kallon danish dake ta faman ƙoƙarin bude idanuwanshi, eyes lashes ɗinshi sun cukurkuɗe sun hana shi buɗe ido, matsawa tayi kusa dashi sosai, ta sanya yatsun hannunta wurin buɗe mashi idanuwan, yadda zai gani da kawai,

Fuskarta ɗauke da murmushi tace mashi"thank u so much danish, ka taimake ni, da yau an karya mini spinal cord ɗi na, gaba ɗaya suka saki dariya, banda haris da deeja,

Ruƙo hannunta danish yayi acikin na shi, ya jata suka koma gefe ɗaya, aka cigaba da buga wasa, juyawa tsohuwa tayi batare da kowa ya ganta ba, ta koma Cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe,

Lokacin da suka kammala wasan, Saman gadajensu suka koma, waɗanda suka sha bugu sai faman jinyar kansu suke yi, rabi da kwatarsu ba'a ɗauko tsawon lokaci ba suka kama baccin wahala,

In the night 🌌

Lokacin da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke, suka ɗauko fitilun ɗakin suka kunna su Saman Dining carpet ɗin su, Dakin yayi haske sosai, Kowa ya samu wuri saman Carpet ɗin ya zauna, Batool taje ƙarƙashin gadonta ta ɗauko masu Kingin Tsiren namansu, Ta rarraba masu Kowa Ya kar6a Yana ci, da suka kammala Suka ci snacks ɗinsu da Sauran kayan marmarinsu, Suna Ci suna fira gwanin ban sha'awa,

Bayan sun kammala Ci, Kowa ya kasa runtsawa, dama angel tayi tunanin daƙyar su iya yin bacci saboda baccin da suka sha A jiya, idanuwansu sunyi wuƙi wuƙi, babu alamun bacci,

Duk suna a zaune saman gadajensu, Tunani ta soma yi kodai taje toilet ta ƙara jaraba fasa glass window ɗin nan? Wata'ƙil idan ta dage kullum tana zuwa tana Bugun jikinshi, Allah ya taimaketa ya fara tsagewa, juyawa ta ɗanyi tare da kallonsu, kowa ya kishingiɗa saman gadon shi, kallon shimfiɗar danish tayi ya kifa kanshi saman Pillow, Aranta tace Allah yasa yayi bacci, kada yayi mini irin na jiya, don na lura akwai almatsutsai akanshi, ba shi kaɗai bane,

Zuro ƙafarta ƙasa tayi daga saman gadon, ganin sun rufe idanuwansu yasa ta lalla6a cikin sanɗa taje gaban Carpet ta ɗauki fitila, da sauri ta wuce ta shiga sashen toilet ɗinsu, Taja ƙopa ta garƙame ta, ajiyar zuciya ta sauke yayin da bayanta ke ajingine da ƙopar,

Glass window ɗin ta ƙurawa ido daga inda take a tsaye, tana ƙoƙarin motsawa da nufin taje ta fara aiwatar da aikin fasa shi, kwatsam Tajiyo shessheƙar kuka tare da Iface iface daga Can Cikin ɗakinsu, A matuƙar kiɗime ta juya takai hannu ɗaya ta Zare jam lock ɗin kopar, da gudun gaske ta faɗo Cikin Ɗakin, Tunkafin ta ƙarasa Ciki, Ta hango su batool da hanna, agaban gadon Deeja, su javed kuma suna a tsaitsaye gaban gadon parveen, ga kuma haris da danish agaban gadon Rubina, Hankalinta yayi matuƙar tashi, Iskokai ne suka tashi Ko kuwa menene? Karasawa ciki ta yi da sauri taci burki agaban Gadon Parveen, Idonta akanta, Ta daddafe Cikinta sai juyi take yi tana kuka tana fadin Cikinta Ciwo zata mutu su taimaka mata,

Arude ta kalli fuskokinsu Batool, Bakomai ta gani ba face tsantsar tashin hankali, sun rasa ya zasu yi mata, da sauri angel ta matsa gadon Deeja dake ta ihu tana fadin Cikinta ciwo yake yi mata, wuce wa tayi zuwa gadon rubina ta tsaya tana kallonta itama ta daddafe Ciki sai kuka take yi tana matse idanuwanta, fuskarta tayi jaga jaga da kwalla,

Kallon Su haris Tayi muryarta na kerma tace"MEKE FARU WA NE'?_

Fuskar Haris a hargitse ya bata amsa da cewa"mu ma bamu sani ba, muna a kwance muka Ji sautin kukansu, mun rasa ya zamuyi da su"

Shiru angel ta ɗanyi ta ruɗe ta rasa madafa, Komawa Tayi bakin gadon Parveen, su batool duk suna a tsaitsaye cirko cirko, a ƙasa ta sauke fitilar hannunta, kafin ta ɗago takai hannu ta janyo Parveen zuwa Jikinta, ƙanƙameta praveen ta yi sosai tana kuka tana faɗin" angel ki taimaka mun ciki na, bana jin daɗi, xafi yake yi mini raɗaɗi nake ji,

Ƙura ido angel tayi tana kallon ɗigon Jinin dake ajikin wandon Parveen Nan take ta gane cewa Jinin al'ada ne, a karo na farko kenan da ta ta6a ganin sunyi jini, ta jima tana mamakin ya akai basu fara ba, saboda a shekarunsu ya isa ace sun fara Shi tuntuni saboda sun girmeta, abun ya ɗaure mata kai,' shessheƙar kukan Parveen ne Ya dawo da ita Cikin hayyacin ta,

Ɗago da kanta tayi daga Jikinta, ta dafa kafaɗunta"Kiyi haƙuri kiyi shiru parveen zanje in faɗa ma tsohuwa," takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon, ta kalli su batool dake atsaye Cikin yanayi na damuwa,

"Ku kula da su, Bari nayi mata magana tazo ta duba su, in yaso sai tayi maku bayanin Abunda ke damun su," amsa mata su kayi da toh, da sauri ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa takai hannu ta bubbuga ƙopar, almost 3 times tana knocking ƙopar, Kafin tajiyo motsinta,

Buɗe ƙopar tayi tare da fitowa Hannunta ruƙe da sanda,

"Meke faruwa ne nake Jin koke koke" tayi tambayar tana kallon Wurin gadajensu,

Muryar angel na rawa ta bata amsa da cewa"ciwon Ciki suke yi Ina tunanin menstruation ne, suna buƙatar magani da kuma pads ɗin da zasu sanya"

Maimakon taga damuwa akan fuskar tsohuwa sai taga ta duƙar dakai ƙasa tana sakin wani irin shu'umin murmushi, ran angel ya 6aci sosai,

"Magana fa nake yi maki akan lalurar dake damunsu, don me xaki 6uge da yi mun murmushi? Maimakon Inga damuwa akan fuskarki? Kina ji suna kuka suna ihu amma ke ko ajikin ki? Ba zaki je ki duba lafiyar Jikin su ba"?

Ɗagowa tsohuwa tayi tare da kallonta, da wannan Shaƙaƙƙiyar muryartata ta tsoffi ta soma magana

"I ave no responsibility to check their health, the giants will come and take them to the treatment room" har saida angel ta zabura jin abunda tace, Can kuma ta wurga mata harara,

"Amma dai baki da Tausayi kuma baki da Imani, taya zaki ce za'a zo a ɗauke su? bayan kina da halin da zaki iya duba su da kanki? Kenan Giants su zasu duba Lafiyar su, Ke fa yakamata ace Kin duba su, Ba wani ƙato ba," zuciyarta a harzuƙe takai ƙarshen maganar, Kafin tsohuwa ta mayar mata da martani, Suka Soma Jin motsi buɗe ƙopa daga can saman benan.........................



*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*




A matuƙar kiɗime angel ta juya tana kallon stairs ɗin, hatta su Batool a ruɗe suka kai idanuwansu kan benan, tunkafin ma su ƙarasa saukowa sautin takalmansu ya karaɗe kunnuwansu, Cikin takun nan nasu na majiya ƙarfi suke tafiya bakowa bane face GIANTS, a jere suka sauko daga saman Stair cases ɗin, haƙiƙa hankalin angel yayi matuƙar ta shi, Jikinta har tsuma yake yi, juyawa tayi tare da kallon tsohuwa, Cikin karyayyiyar murya tace" na roƙe ki dan Allah Ki taimaka, kada ki bari a tafi dasu parveen, abar mana su acikin mu, Ni nayi alƙawarin zan kula dasu," idanuwanta cike tab da ƙwalla takai ƙarshen maganar,

Girgiza kai tsohuwa ta yi babu alamun sassauci akan fuskarta tace"Ba hurumina bane shiga abunda ba ruwana, Dokar Prison ce, Wadda bani na tsarata ba, duk wani mara lafiya za'a zo a ɗauke shi akai shi inda za'a duba lafiyar shi, idan kinga na duba mutun to ciwon bai yi tsauri bane, Giants da ki ke gani basa sauraron kowa, Koda kuwa nice, saboda ba a ƙarƙashina suke ba, dukan mu Ma'akaita ne dake aiki gidan kurkukun ƙaddara, Kuma a ƙa'ida wani baya shiga hurumin wani........."

kalaman tsohuwa sunyi matuƙar girgiza angel, kafin ta yi yunƙurin buɗe baki ta furta wata kalma, tajiyo muryar parveen tana kuka tana faɗin Kada su bari a tafi da ita, mutuwa zata yi, ita bazata bi su ba ' a hargitse angel ta juya tana kallonsu, Kusan atare giants suka kai hannuwansu saman gadajensu Deeja da rubina da parveen, Wata irin ɗauka su kayi masu ta

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads