Header Ads
Showing 207001 words to 210000 words out of 287659 words

Chapter 70 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1835

Ads at the middle of Article

mishi amma ko ajikin shi.

tsotai ne yakai Majnun gadon Unaiza ƴar gidan daddy, Ya sanya hannu yana bubbuga ƙafafuwanta don ta farka yaga ita kaɗai ce bata tashi ba, can cikin bacci ta dinga jin bugun da akeyi mata, a hautsine ta farka tare da miƙewa fuskar nan tayi jawur da ita babu annuri, suna haɗa ido da majnun Ya washe mata baki, ranta ya 6aci sosai dama ta tsani yaron, zabura tayi ta damƙo wuyan rigarshi, Haris da Danish har suna haɗa Baki wurin ƙoƙarin dakatar da ita akan karta ta6a lafiyar jikin shi, ko kallo basu isheta ba, ta daddaga ta kwakkwasa mashi zafafan maruka saman fuskarshi, azabar zafi yasa yaron ya dafe kuncinsa ya fashe da kuka, parveen hada cewa"Allah shi ƙara maka, Ae kaine da shegen jan faɗan tsiya," duk sun yi tunanin za ta sake shi ne tun da ta mare shi, amma sai suka ga ta sanya hannu ta shaƙe wuyanshi da ƙarfi kamar zata kashe shi, idanuwanshi suka firfiro waje, A gigice Danish ya yunƙura tare da angel hada deeja suka nufi gadonta, Suna ƙoƙarin ƙwace shi daga hannunta amma taƙi sakin shi, rai a6ace Danish ya daddage ya watsa yatsun hannayenshi biyar saman kuncinta, ji kake tass! Abun da bata ta6a tsammani ba, Da sauri ta saki Wuyan majnun idanuwanta akan fuskar Danish, tun da take arayuwarta bata ta6a jin azabar mari irin wanda Danish yayi mata ba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta da suka cicciko tab da ƙwalla, hannayenta bibbiyu dafe kuncinta.

Su azeeza dake kallonta, dariya ce ƙumshe acikin bakunansu, Musamman da ta dinga binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, kamar tana tunzurasu ne akan su yi dariya, Angel ce ta rungume majnun ajikinta, tana lallashinshi, Sai kuka yake yi, Wuyan shi hada sahun akaifar Unaiza wurin yayi ja sosai jini ya kwanta abunka ga zabayyana dama ya lafiyar giwa.

"Wani ya samo min ruwa in bashi" angel ce tae musu maganar, da sauri parven ta sauko daga saman gadonta, ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko bottle water cikin wanda suka ajiye taje ta miƙa ma Angel tasa hannu ta kar6a tare da cire murfin ta kwafa mishi abaki, sosai yasha ruwan har yana shaƙewa, kusan rabin robar ya shanye, kafin ya janye bakin shi, Yana faman tatta6e fuska ya kalli unaiza a lokacin ta dawo da kallonta kan Danish, da alama bakinta ya gama mutuwa saboda marin da yayi mata ba.

Cikin shessheƙar kuka Chinonso Ya nuna ta da yatsa yana faɗin"I hate u, mai idon dodo, bana son ki," Dama ranta a6ace yake, azabure ta yunƙura ta sauko daga saman gadon da niyar ta sake bugun chinonso, a tsorace yaron Ya yi saurin faɗawa jikin angel ya ƙanƙameta, Wata irin gigitacciyar tsawa Danish Ya daka mata, wadda tayi silar dakatar da ita, Da kakkausar murya yace mata"kada ki kuskura kice zaki ƙara ta6a shi, ke baki da hankali ne baki ga yaro bane? Ko so kike ki kashe shi ne shiyasa kika shaƙe mishi wuya" yae maganar idonshi akan fuskarta, wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, la66anta har kerme suke yi wurin faɗin"Ni ka mara? Sannan ka rufe ni da faɗa sai kace wata ƴar cikin ka, To ni ko ubana bai ta6a ɗaga min murya ba, balle har yayi gigin ta6a lafiyar jikina, rana ta farko da mahaifiyata ta fara yi min tsawa akan idona daddyna ya kwashe ta da mari, Amma zuwana Cikin ku, kun maidani kamar wata jaka, Wai me kuke nufi dani ne? Na kasa ganewa........" daƙyar ta ƙarasa maganar, hawaye ta ko'ina saman fuskarta, Still idonta akan fuskar Danish, su Deeja sun kasa kunne suna sauraronta babu wanda ya tanka mata, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yai ba.

tana magana jijiyoyin wuyanta duk sun firfito ruɗu ruɗu saman fatarta, Sautin muryar ma daƙyar yake fita

"Ni bazan cigaba da zama acikin wannan Munafukin Ginin ba, nafara kokwanto akan ku, Kun ƙi ku sanar dani ina ne nan, wai me ake nufi dani ne? So ake dole sai nayi rayuwa kamar dabba! to nagaji! nagaji!! bazan Iya cigaba da zama acikin Ƙuntataccen dakin nan ba, wlh ban yarda da kowa ba, so ake akashe ni, Ni ku faɗa min me ake aikatawa acikin ginin nan? Kowa ya maidani jaka, Ni da nazo ɗaukar karatu? Ance min school ce but why har yau ba'a kai mu class room ba? Na yi shiru ne don inga ko akwai wani shiri da ake yi mana amma naji shiru har yau, babu zancen zuwa aji mu ɗauki karatu, nayi expecting ɗin zan samu abunda nake so shima kun hanani saima neman kassara rayuwata da ku ke yi, ta ko'ina kun ƙuntata min, Nifa ban saba da irin wannan rayuwar kullen ba, Ni school din ma na fasa amaidani gidan daddy na, wlh bazan zauna ba!!! " tana magana tana matsar hancinta, fuskar tayi jaga jaga da hawaye,.

Da alama marin Danish ba ƙaramin zaburar da ita yayi ba, sai sambatu take yi tana zazzaga masu masifa ta inda ta shiga bata nan take fita ba.

"magana fa nake yi maku, duk kunyi min shiru sai kace kurame, Ku faɗa min ina ne nan? Kuna ƙara jefa ni cikin ruɗani! Abubuwa dayawa suna neman rikita min lissafin ƙwaƙwalwata! meyasa tun da nazo babu wani sauyi, ni fa ba haka daddyna ya faɗamin ba, yace min school ɗin akwai wuraren shaƙatawa acikinta, amma ni bangani ba, shi fa ya faɗamin hada lunch room da garden da swimming pools ga zoo irin na gidan mu, hada cinema but why are we always locked in the same room like an animal? Nifa na saba agidan mu, Ina yin duk abunda nakeso, ban saba da wahala ba, duk rana saina fita yawon buɗe ido, Har night club ina zuwa sometimes a hotel nake kwana tare da friends ɗina, Taya rana ɗaya za'a kawo ni wannan gurin me kama da Gidan Yari!"

a hargitse ta ƙarasa maganar, Cikin raunin murya da sagewar gwiwa ta zube saman ƙasa tana ci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita, basu ta6a jin tausayinta ba irin na yau, ganin yadda duk tabi ta burkice, tsawon lokaci babu wanda Ya tanka mata, da zarar angel ta yi yuƙurin buɗe baki ta yi mata magana, da sauri Danish ke dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kan shi alamar karta fada mata, tuntuni take son faɗa mata gaskiyar zance akan daddynta mugune sadaukar da ita yayi kuma nan ɗin kurkukun ƙaddara ne, da komai da suka sani dangane dashi wata'ƙil ta dawo hayyacinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne! Sai dai Danish yaƙi bari a sanar da ita.

Sosai take yin kuka babu mai lallashinta, Gefen fuskarta inda Danish ya mara hada sahun yatsun hannun shi ruɗu ruɗu, Tamkar da bulala aka shafi wurin, shi kanshi sai daga baya ya yi danasanin marinta da yayi duk da laifinta ne itace taja ma kanta,.

Saukowa gabriel yae daga saman gadon shi, gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan shi, Bai nufi ko'ina ba sai wurin da Unaiza take zuƙunne tana kuka, Zuƙunnawa yayi tare da sanya hayyanshi biyu ya rungumota jikin shi yana lallashinta, sai ya dinga ganin kamar twin sister ɗin shi ce take kuka, muryar shi ƙasa ƙasa yake faɗin"its okey unaiza, Stop shedding ur tears, ina atare da ke" kallon kallon sauran ƴan uwan nasu suka somayi atsakaninsu, sun yi mamaki ganin yana lallashinta, bayan shima yasan halinta na dabbanci da rashin kamun kai, dakatawa tayi da yin kukan tayi lamo ajikin shi, dama Gabriel akwai ƙira, Ta samu wurin zama, kamar zata shige cikin shi, jin tayi shiru yasa shi ɗagowa ya kalli su Danish dake atsaye suna kallon su, Magana ya soma yi musu

"Nima na jima ina so in tambaye ku game da kurkukun nan amma nakasa, Mu tamkar baƙi ne acikinsa, ina so insan komai agame da shi, Tsawon kwanaki, Banga an dawo min da ƴar uwata ba, kuma ni banga ana fidda mu waje ba, kullum muna kulle a room ɗaya, sannan waɗannan mutanan dake zuwa wanda ku ke kira da giants sam basu kwanta min araina ba, meyasa koda yaushe suke zuwa cikin shiga ta baƙaƙen kaya? Suna 6oye kan su don kada mu gansu, na fara zargin wani abu, it seems like something strange is going on in this prison. I wonder what they're hiding from us."

Shiru suka yi babu wanda ya tanka mashi, A ƙagare yace

"Na yi magana anyi shiru ba'a tanka mini ba, hakan na nufin hasashe na ya zama gaskiya kenan? Akwai wani abu dake faruwa wanda ba'a so mu sani, pls ku faɗa mana abunda ku ka sani tattare da gidan kurkukun ƙaddara, ku wayar mana da kanmu Ni da Unaiza! ni ƴar uwata ma itace damuwata, bansan Ina aka kaimin ita ba, awani hali take! Idan naci gaba da 6ata lokaci za'a iya cutar min da ita batare da sanina ba,"

Wani irin mugun bugu zuciyoyinsu su ka yi bakomai ne ya faɗo musu aransu ba, fa ce Ƴar uwarsu batool, haƙiƙa Gabriel Yayi wata magana da su ba suyi tinaninta ba, lokacin da suke 6atawa na rashin ta6uka komai akan adawo musu da ƴar uwa, kamar suna ƙara jefa ta cikin matsala ne, idan ma mutuwa ce ae yanzu ya isa ace batul ta mutu saboda azabtarwar da su ke yi musu idan su ka ɗauke su.

Shessheƙar kukan su Azeeza ne ya karaɗe cikin ɗakin, Jikin su yae mugun sanyi, ita kanta angel hawaye ne suka cicciko mata acikin idanuwanta, a marairaice take kallon Danish.

kukan su parveen ya ƙara dasa tsoro da firgici acikin zuciyar Gabriel, Yana ƙoƙarin Tambayarsu meyasa su ke ku ka, Danish yae saurin dakatar dashi ta hanyar yi mishi magana

"Gabriel, is enough! Maganarka bata da amsa, kamar yarda ka tsinci kanka acikin kurkukun nan ba tare da kasan komai dangane dashi ba, mu ma haka muka tsainci kan mu, Ƴar uwarka da aka ɗauka ba'a ita kaɗai ba ce, ka tuna su goma ne aka juya dasu, so ka kwantar da hankalin ka, Su ma suna acikin kurkukun nan kuma suna rayuwa kamar yarda muke yi". Cikin karyayyiyar murya gabriel yace"Bana tunanin haka, Saboda ina ji acikin zuciyata wani abu yana faruwa da ita, ya za'ae na tabbatar da cewa tana Lafi......." bai ƙarasa maganar ba, sakamakon ganin angel da ya yi ta miƙe da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu tana kuka,

Da sauri gabriel Ya janye unaiza daga jikin shi ya miƙe Ya nufi hanyar shiga sashen toilet ɗin da niyar yabi bayan angel, sai dai kafin yakai ga ƙarasawa Danish yasha gabanshi, damƙar damtsen hannun shi yae tare da cewa"Kada ka yi gigin cewa zaka bi bayanta, Ka koma ka lallashi waɗanda ka fama ma ciwon dake acikin zuciyarsu, har sai sun yi shiru," Kamar wani ubanshi haka ya bashi umarni, ku ma abin mamaki gabriel bai musa mishi ba, Ya amsa mishi da toh, kafin ya juya ya nufi su azeeza, ɗaya bayan ɗaya ya dinga zuwa bakin gadonsu yana lallashin su, Har sai da ya samu su ka yi tsit Sannan Ya koma bakin nashi gadon ya zauna, Jikin shi duk ba daɗi kewar ƴar uwarshi ta addabe shi, tuni unaiza ta koma saman gadonta, chinonsa ma ya hau nashi gadon.


Sam bata ji alamar shigowar shi cikin toilet ɗin ba, tana zuƙunne gaban tukunyar furennin nan, Sai kuka take yi kamar marainiyar da ta rasa gata a duniya, Furen batool ya ƙara tayar mata da hankalin ta, ganin yadda Jikin shi ya bushe Ƙamas, Ganyayyakin jikinsa duk sun tsamure, Alamar babu lafiya atattare da mamallakin furen, A gefen ta Danish ya zuƙunna Tare da ambaton sunanta, Angel kusan sau uku Yana kiranta bata ɗago ba, sai da ya ɗaura hannun shi ɗaya asaman kafaɗarta tukunna ta ɗago ta kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu, fuskar tai jaga jaga da hawaye wasu nabin wasu

Cikin shessheƙar kuka tace"Me zaka faɗa mini? Kai idan ma lallashina zaka yi to banso! Ko ka yi abanza tun da ba iya dawo min da batool za ka yi ba, Ku ma wlh rantsuwar ɗan musulmi, zanje na dawo da ƴar uwata ne, ko da zan rasa raina ne akan hanyar zuwa wurin ta...." bata ƙarasa maganar ba, Ta daura kanta saman gwiwowinta, gaba ɗaya ta kashe mishi baki, Ya rasa me zaice mata, don ya lura babu sassauci akan fuskarta, shiyasa tun farko bai so Gabriel Ya fara maganar ƴar uwarshi ba. Ga shi yanzu yaja mishi masifa,

Jim ya ɗan yi kafin cikin cool voice ya furta"Angel, nasan bazan iya dawo maki da ita ba, kamar yarda kika faɗa, ku ma kema haka koda ace kin ƙara dura tagar nan da niyar kije neman ta, ba lallai bane Ki iya tsira, ko kin manta abunda Ya faru dake ne a rana ta farko da kika haura....."? Daƙyar ya ƙarasa maganar saboda yadda ta ɗago tana wurga mishi harara gwanin ban tsoro launin idanuwanta kamar na zombie, masifa ta soma zazzaga mishi

"Bana son ganinka, sai iya daɗin baki, Danish idan har ni bazan iya shiga prison ba, kai zaka Iya, tun da har ka iya zuwa ka ɗauko ni, dan haka inaso kaje ka dawo mana da batul ɗin mu, Danish ka taimaki rayuwar batul, tsawon wata ɗaya da weeks babu ita, ka duba ka gani fa, ko su deeja 2 weeks ne aka dawo mana su, amma Jibi kaga yarda aka canza musu halittarsu to inaga ita da ta jima a hannunsu"

Baisan ya zaiyi ya fahimtar da angel ba, ya san koya lallashe ta abanza don ba jin shi zatayi ba, hakan ya sa shi miƙewa Ya fuce daga Cikin toilet din tabi bayan shi da kallo, Zuciyarta akarye ta miƙe, Tana sharar kwalla, Bata fito daga Cikin toilet din ba, Sai da ta goge bankinta, Tayi wanka,

Lokacin da ta fito, su hanna ta taras A cikin sashen toilet ɗin nasu, suna jiran wanda ke aciki su fito suma su shiga, kallon su kawai tai batare da tayi musu magana ba tasa kai ta fuce daga wurin, shigarta ɗaki keda Wuya, Sai ga Giants sunzo kawo musu abinci, nan take ta ɗaure fuskarta, su uku hannayensu ɗauke ta farantan kayan abincin su, ciki suka shiga tare da sauke trays ɗin saman dining carpet ɗin su, Atare suka ja baya kamar yadda suka sa6a ƙame wa,

Kaitsaye angel ta nufi inda suke, Danish na jin takun tafiyarta ya ɗan ɗago daga kishingiɗan da yake saman gadon shi, Hatta haris da Gabriel da suke acikin ɗakin hankalinsu na akanta


"Har yaushe ne zaku kammala amfani da ita ku dawo mata da ita? Nasan kun gane akan wa nake magana, Ƴar uwar mu batul tana ina"? Ranta a6ace take yi musu magana, babu wanda ya motsa, tsawa ta daka musu tare da cewa"Da ku fa nake magana? Nasan kuna ji na, mugaye kawai......" jiki na 6ari danish Ya sauko daga saman gadon shi ya nufi angel ya ruƙo hannunta yana ƙoƙarin janyeta baya, gudun kada su cutar da ita, fashewa tayi da matsancin kuka, Tana bugun Danish akan ya saketa, wlh sai sun fito musu da ƴar uwarsu, Wannan maganar tayi matuƙar ɗaure ma Gabriel, da Unaiza kai, don tuni ta miƙe zaune saman gadonta, idanuwanta luhu luhu take kallonsu, Saboda sautin kukan Angel har na cikin sashen toilet dinsu saida suka fito, hankalinsu yayi matuƙar tashi ganin yadda take kuka tana ƙoƙarin kwace kanta daga hannun danish donta kaima Giants hari, A ƙarshe da ta ga dagaske Danish bazai Ƙyale ba, ta daddage ta gartsa mishi ciwo a damtsen hannun shi tare da sanya hannayenta biyu ta ingije shi gefe ɗaya, taku ɗaya zuwa biyu takai ga farantan kayan abincin da aka kawo musu, Robar ruwa ta ɗauko ta buɗe murfin, Cikin zafin nama ta watsa ma giants ruwan ajikinsu kaf ta zazzage musu shi.

waro ido waje su Parveen su ka yi ganin irin bala'en da take so taja musu, kowa yasha jinin jikin shi, Tana haki tace"Dama nasan bazaku motsa ba, saboda ku ɗin dabbo bi ne, Marasa imani, Allah dai yana ganin ku mugaye, Wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har wani abu ya sami batul sai kun gane ba ku da wayau, domin kuwa saina addabi rayuwarku, inyaso ku kashe ni, kai bazan ma mutu ba bi'iznillahi har sai na ga bayan ku..." Bata kai ƙarshen maganar ba, Danish Ya sake damƙota, kamar ƴar dambe sai harba ƙafarta take yi, ahaka yaja ta har zuwa saman gadonta, Ya jefar da ita, Kafin ya juya ya kalli Sauran yace dasu su je su ci abinci," da sauri suka nufi kayan abincin nasu kowa ya zauna banda Gabriel da Unaiza, kalaman angel sun yi matuƙar ɗaga musu hankali, tunani suke yi wacece batul? Meyasa aka ɗauke ta?

A gefen gadon Angel Danish ya zauna yana gadinta, gudun kada ta ƙara zuwa ta 6allo musu aiki, Shi kaɗai yasan me yae mata, da har tagaza ɗagowa, hawaye sai bin fuskarta suke yi, ta ɗaura kanta saman pillow,

Bayan sun kammala cin abinci sauran da suka rage ma waɗanda basu samun damar xuwa suci ba, acikin kwando suka adana mu su nasu, Giants na fita daga Cikin dakin, Gabriel ya soma tambayarsu wacece batul? su azeeza suka bashi amsa da cewa ƴar uwarsu da aka ɗauka, yaso ya ƙara tambayarsu dalilin dayasa aka ɗauke ta amma Danish Ya hana shi, ta hanyar
Ƙura mishi ido yana kallon shi, nan take yaji maganar ta fita aranshi, bai ƙara tada ta ba.

Yinin ranar babu daɗi suka yi shi, Saboda halin da suka shiga na tunawa da ƴar uwarsu, Kowa jikin shi yae sanyi, Har marece ya yi babu wanda ya motsa acikin su, majnun ne kaɗai yake ta tsalle tsalle shi kaɗai atsakiyar ɗakin su.

Lokacin da marece ya nutsa, Gabriel ya bukaci yin wanka, Saukowa Yae daga saman gadon shi, Ya nufi toilet ɗinsu Ya shiga, bayan yasanya jamlock ya datse ƙopar Ya dan jingina bayanshi Jikin ƙopar, yayin da zuciyarshi ke acunkushe da tunanin abubuwan da suka faru ayau, Tabbas ya razana sosai da gidan kurkukun nan, duk da baisan komai adangane dashi ba

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads