Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 287659 words

Chapter 4 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1761

Ads at the middle of Article

tadinga 6arna kenan kamar 6eran gida,

****Boss Bature******

A kwana atashi. Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea, Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya, duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure rabuwa da ita, Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi, Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki, ko 6ari bata ta6a yi ba a bun ya dame ta sosai, Shi kan shi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa, har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu, Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi, Lokacine baiyi ba ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalin su harya basu Labarin Iyayen shi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa, Tunda suka ji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu,

A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji, Ashe Yanzu wasan Ya fara,

Tun tana da shekara Uku Ya sanyata nursery, hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata, rana ta farko da ta fara zuwa makaranta, ta samu ƴa'ƴan mutane ta dinga gartsa masu Cizo, Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta, saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta Saboda baza su Iya Control ɗinta ba, ga shi ya hana a dukar mashi ƴa ko tsawa Baiso Ayi mata sai dai bayan idonshi.

Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa'ƴan mutane, tun da yayi mata faɗa abunda bai ta6a Yi mata ba a ranar har fushi tayi taƙi cin abinci, daƙyar Ya lallashe ta ya samu suka shirya da ita,

Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece, tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado, a tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba, bayan fitarshi Da rabin awa ta farka tana Jin yunwa gashi Sam bata da juriyar Yunwa,


Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar Ɗaura girki, Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din, Dama tasan Yadda yake kunneshi Saboda wasu lokuttan a tare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki, To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta.


Yana Wurin aiki Aka kira shi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi, Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan.


Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi, Duk yabi ya ruɗe babban tashin hankalin shi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta, da gudun gaske Ya fada Ciki gidan, Su uzair suka bi bayan shi dama sunzo hada aneelarh, A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo, Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi,

Sai da suka gama shan wahalar nemanta, Ba zato ba tsammani suka same ta a cikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha.

Da gudu suka nufe ta gaba ɗaya suka rungumeta, kowa ya na faman sauke ajiyar Zuciya,


Abunda Ya faru a she bayan ta kunna gass, ta sauko daga saman Chair ɗin, Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha, Sam ta manta da tabar gass a kunne, duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita ba ta ji ba, Baba maigadi ne Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Ciki don yaga me ke faruwa, koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi, Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman a gaji,

Angel tasha fada awurin Taj kuma duk da laifin da tayi ma shi ko dungurin ta bai yi ba, kadan daga Cikin munanan halin angel shine, Bata barinbshi yayi bacci muddin ta farka, to shima dole ya farka baccinshi Ya qare, Idan suka fita Yawan shakatawa komai ta gani tana so, koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi idan ba haka ba hmmm xa'aga tashin Hankali, Bayan wannan Ta iya jan faɗa idan suka Je anguwa, komai ta gani saita dauka ta jefar, Ayita nema tana ji bata faɗin ita ta dauka.

duk duniya babu wanda bata Jin tausayin shi Irin mahaifinta, azabtar da shi take Yi, Shi kuma Ya mutu akan sonta Bai iya rabuwa da ita ga shi ta tsani taga yana karatul Alqur'ani, da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun, kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba idan uziri ya hana shi zuwa masallaci, Kamar shaiɗaniya haka take, har malami aka dauko yayi mata addu'a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu, tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta, ta dinga buge mashi hannu tana faɗin dama ya daina wahalar dakanshi, Ita lafiyarta qalou

Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya, Ta sace takalmanshi ƴan madina, sai da ya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗauke su, su ka yi ta nema kasa ko sama babu su, bayan tafiyarshi ta fiddo takalman da ta 6oye a ƙarƙashin gadonsu taba Taj, wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta, haushi kamar Ya rufeta da bugu, yaji kunyar abun nan haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abun sa,


Babban abunda zai baka mamaki da ita sam bata da tsoro, yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon har ta Iya kunna kallo, tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta,


Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radion su, Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe, Tasa key ta rufeshi, dalilin da ya sa Ta yi ma shi haka shi ne, Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair, Ita kuma bata son zuwa gidan tafi son duk inda zai je ya tafi da ita, Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakin shi bayan ya shiga wanka, Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai, Ta murɗa mashi key ta datse ɗakin Ƙarfin Hali,

Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,


Saboda bala'in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daɗi, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa,

Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,


Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini,

Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi "Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,"

Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace"Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata" Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje"Kije ki nemi wani uban"


Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama'a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin "Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa"Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa'yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba


Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.

Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,


A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,
Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya'yan mutane,

A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,

Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.

Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,

Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.

Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,

Ba'a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.

Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin "Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin,"
Copral ne Ya bata amsa da cewa"Ana zargin su da sace Ƴa'ƴan mutane suna amfani da su"
Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace
"Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba....."bata kai ƙarshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta"Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu,"
Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin, Cikin sanyin murya ta furta"where's the evidence"?

Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office ɗin shi

A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,

Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baƙin zalunci," yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen,

Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami"You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce," muryarta a disashe takai ƙarshen maganar,

"Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi," acewar dpo,

Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel,
"Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne,"
Da buɗe bakin angel sai cewa"Ni ƙarya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae"

Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa"You are under arrest" ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa
Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa"Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani.
Girgiza kai Dpo yayi"Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne"
Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution"
Jinjina kai dpo "Good idea Copral"Dpo ne ya kira sunan shi
"Yes sir" ya amsa mashi.
"Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku,"
"Consider it done sir" Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi,

A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel,

Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men ɗin akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,

Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi,

Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,

Bin shi da kallo kawai aneelerh tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta ƙalou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou "

Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads