Showing 159001 words to 162000 words out of 287659 words
Chapter 54 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
ɗaɗɗago da glass ɗin, Ta dure shi ƙasa, Tana yunƙurin hawa bisa tagar, Taji ya damƙi ƙafafuwanta daƙarfi, a ƙoƙarin ya janyota ta faɗo Cikin rashin sa'a ya zame wandon Jikinta gaba ɗaya ya sabule ƴan fararen cinyoyinta santala santala suka bayyana a suffarsu, saboda tsabar jaraba ko waiwayon wandonta bata yi ba, A haka ta dire tagar ta faɗa ta baya.................."
Ta tafi tabar danish a tsaye hannun shi ruƙe da wandonta, don ma Allah yasa rigar uniform ɗinsu tana da ɗan tsayi ta rufe ass ɗinta duka,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Tun da ta dure tagar nan , danish ya kasa motsawa tamkar an ruƙe ƙafafuwan shi, Jikin shi yai mugun sanyi tamkar wanda aka zarewa laka, idanuwan shi na akan wandonta data bar mishi ruƙe a hannun shi, Kallon shi yake yi batare da ƙyaftawar ido ba, tsabar tashin hankali ne ƙarara akan fuskarshi , babban abunda yake jima tsoro Hannun da Angel zata faɗa, ba lallai ta Iya ganewa Ginin kurkukun ba. Domin kuwa a birkice yake. Idan har ba ka da ilmi akan shi, har ta6in hankali zaka iya samu saboda ruɗanin da zaka shiga,
Muryar shi na rawa ya furta"bazan ƙyale ta ba, why angel? Dole na bi bayanki, " Yana yunƙurin haura tagar, kunnuwan shi suka jiyo mishi sautin muryar haris dake ta ƙwala ma shi kira daga can cikin ɗakin su, Aikuwa a matuƙar ruɗe Ya fasa Yunƙurin dura tagar, da sauri Ya nannaɗe wandon angel. Ya wurga shi saman tukunyar fulawar nan ta Cikin toilet ɗin, kafin ya miƙa hannu ya ɗauki fitilar da angel ta ajiye acikin toilet ɗin, Ya juya ya nufi hanyar fita, buɗe ƙopar shi keda wuya, Sai ga haris ya faɗo sashen toilet ɗin hannun shi ruƙe da fitila, Haska fuskar danish yai, ganin shi ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, sam ya gaza runtsawa saboda tunanin mutun biyun nan batool da kuma danish, fargabar Halin da suke aciki Ya hana shi sakat.
danish ya yi mamaki zuwan haris nemanshi , bai ta6a tsammanin wani daga Cikin su zai waiwaye shi ba. Duba da irin aika aikar da ya yi musu.
Sun ɗauki tsawon mintuna suna kallon Juna, sai daga bisani haris ya jefa mashi harara tare da cewa"Ya jikin naka"? daƙyar danish ya samu ya dai daita natsuwarshi, Cikin sanyin murya yace"Da sauƙi" ta6e baki haris yae kafin ya kuma cewa"ka zo mu koma ɗaki, naga baka ci breakfast ɗinka dana ajiye maka ba, kuma nasan kana jin yunwa, tun safe har dare ko ruwa baka sha ba," yana magana yana wurga mashi harara dake nuni da cewa ba don yaso yake yi mishi maganar ba, har yanzu akwai sauran haushin shi da yake ji acikin zuciyar shi,
Danish bai motsa ba, kallon haris kawai yake yi, shi damuwarshi akan angel ne, Baya jin zai Iya bin haris su koma ɗaki,
Jin yayi shiru yasa haris sake cewa"magana fa nake yi maka"? Fuskarshi a yamutse ya soma magana,
"Meyasa ka damu da ni? Duk irin abunda na aikata mu ku? Rai a6ace haris yace"ba wannan na tambaye ka ba, abinci nake magana, kazo muje ka ci" girgixa kai danish yai alamar a'a yace"Na ƙoshi, ka ƙyale ni koda yunwa zata kashe ni, bai shafe ka ba, lokacin dana buƙaci taimako awurinku, akan ku bani ruwa in sha, ka tuna abunda ka yi mani?
A fusace haris yaja dogon tsoki tare da matsawa ciki ya ruƙo hannun danish da niyar ya fusgoshi su tafi, da sauri danish ya ƙwace hannun shi, cikin kakkausar murya yace"Nace maka bazanci ba! Ka rabu dani! Babu ruwan kowa da rayuwata, tun da kun nuna cewa bani da amfani acikin ku," wani irin kallo haris yake bin shi da shi, kowannan su sai faman huci yake yi,
Shi burin shi haris ya tafi ya bashi wuri ko ya samu yaje ya taimaki angel, don yasan yanzu haka tana can tana neman ɗauki ta gama furgicewa,
Haris Na ƙoƙarin buɗe baki don Ya mayar mishi da martani, Muryar Deeja Ta katse mishi Hanzarin shi, daga can cikin ɗaki Ya jiyota tana ƙwala mishi Kira, don dole ya saki hannun Danish Ya juya da gudu ya koma Cikin ɗakin,
Shigar shi ke da wuya, Ya yi arba dasu deeja gaba ɗayansu agaban gadon Azeeza, tunkafin ma ya ƙarasa shiga hankalin shi yai matuƙar tashi, Ganin azeeza rungume jikin deeja, babu numfashi, kamar matatta, Su parveen sun tasa ta gaba sai kuka suke Yi,
A bunda ya faru, Tun lokacin da azeeza ta 6oye ƙarƙashin gado ta 6oye don kada giant ya ɗauke ta, gaba ɗaya sun manta da azeeza, da ta 6oye a ƙarƙashin gadon ta, Har suka kwanta basu tuna da ita ba, sai daga baya ne deeja tana kwance saman gadonta, ta yi zurfi acikin tunaninta, kwakwalwata ta soma tariyo mata abunda ya faru kafin atafi da Batool, Nan take ta dafe ƙirji, ta miƙe zaune tana Ambaton sunan azeeza, Koda sauran ƴan uwan nasu suka ji tana kiran sunan azeeza, suma sai suka wartsake kowa Ya sauko daga saman gadon shi, A gaggauce Deeja ta ɗauko dayar fitilar data rage a ɗakin, Ta ajiye ta daga ƙasa gefen gadon Azeeza, Ta zuƙunna tana leƙa kanta ciki, Anan ne taganta xaune Kamar gunki babu abunda ke motsi ajikinta, Ta fashe da kuka Tare da kai hannu ta 6an6arota daga Jikin bangon data jingina, ta janyota wajen gadon, ta kwantar da ita saman jikinta, Su Hanna duk suka kewayesu, kowa ya zuƙunna suna ta kuka suna ambaton Sunan Azeeza, Zuciyoyinsu duk sun karaya, ganin yadda jikinta ya sandare, Cikin shessheƙar kuka hibba tace su jira ta dauko ruwa a yayyafa mata wata'ƙil su samu ta farka, tana karasa yin maganar ta miƙe ta ɗauki fitilar ta nufi gadon batool, tana laluban robobin ruwan da suka ajiye, sai dai bata samu ko ɗaya ba, duk sun ƙare, Jiki amace hibba ta dawo tana haska su da fitilar hannunta tace babu ruwa, bari naje toilet na ɗebo, har ta juya zata nufi toilet ɗin, Muryar deeja ta katse ta da cewa"Ina haris yake? Naji motsin shi ɗazu, Ya sauko daga saman gadon shi, ina tunanin toilet ya shiga, Bari na kwala mishi kira yazo," Batare da6ata lokaci ba, deeja ta shiga kwala mishi kira, Sai gashi ya faɗo Cikin ɗaki,
Haris na ƙarasawa kusa dasu, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunan azeeza tare da cewa Meya faru da ita? Nan suka sanar dashi komai, tun daga zuwan Giant, dafe kanshi yai da hannu ɗaya, idanuwanshi sunyi jajur, zuciyarshi duk ba daɗi, Yau dai gaba ɗaya basu ji daɗin ranar ba, sun yini da baƙin Ciki acikin ransu,
Kallonsu parveen yae ganin yadda suke ta yin kuka babu ƙaƙƙautawa, Cikin sigar lallashi yace"Ku kwantar da hankalin ku, azeeza zata farka suma ne tayi, bari naje na ɗebo ruwa a yayyafa mata" yakai karshen maganar tare da juyawa Ya nufi cikin ɗakin, Yana laluban Inda ya jefar da robar ruwan daya watsa ma danish ɗazu, Cikin sa'a yaci karo da ita can gefen dining carpet ɗinsu, Da azama ya je ya ɗauko bottle water ɗin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin su.
Lokacin daya shiga, baiga danish ba, babu shi babu alamarshi, Sai dai bai kawo komai aranshi ba, ganin ɗaya daga Cikin ƙopar toilets ɗin nasu a garƙame, sai yayi tsammanin ko yana aciki ne, ɗayan toilet ɗin ya shiga ya kunna fanfo ya tarba robar ruwan, sai da ta Cika tab, kafin Ya kashe fanfon Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya koma inda su deeja suke a zazzaune, Zuƙunnawa yai, bayan ya ajiye fitilar hannunshi, Ya tarba ruwan a tafin hannun shi ɗaya, Ya watsa ma azeeza saman fuskarta, Kowa ya baza ido yana jiran ganin ta farka, amma shiru ko motsi bata Yi ba, Nan fa hankulan su suka ƙara tashi matuƙa,
Cikin shessheƙar kuka suka haɗa baki suna roƙon azeeza akan ta taimaka musu ta farka, Haris dasu Javed sai lallashinsu suke Yi, ganin yadda duk suka shiga damuwa, parveen na kuka tace"tun da muke arayuwar mu ba mu ta6a fuskantar tashin hankali, irin na yau ba, An ɗauke mana batool, ga azeeza kuma taƙi farkawa, Ni tsorona ma kada ace ta mutu....." kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, ta kifa kanta saman gwiwarta, muryar deeja adisashe tace"dan Allah ku daina maganar mutuwa, wlh bana sonji, in sha Allah azeezan mu zata farka, babu abunda zai same ta, addu'a ya kamata muyi mata," Haris yace"wace irin addu'a? Babu abunda zata yi mana, kawai dai mu jira zuwa lokacin da zata farka," idanuwanta cike tab take ƙwalla take kallon shi,
Tsananin tausayinsu ne ya kamata haris, bayin Allah, tun safe hankalin su ba'a kwance yake ba, ga shi har dare ya ratsa basu runtsa ba,
Kusan sau uku haris yana yayyafa ma azeeza ruwa akan fuskarta amma taƙi farkawa, Jikinsu duk yai sanyi, haka suka zauna a kewaye da ita, suna kallonta yayin da hawaye ke cigaba da sauka a kan fuskar kowannan su.
"To ko dai mu yi ma tsohuwa magana tazo ta duba ta kada ta mutu" acewar yasmin, har suna haɗa baki wurin cewa"Taje ta kirawo ta," Da sauri yasmin ta miƙe ta dauki fitila ta wuce ɗakin tsohuwa, lokacin da yasmin ta bubbuga ƙopar ɗakin tsohuwa bata buɗe mata ba, kusan sau takwas tana yin knocking kamar zata 6alle ƙopar har saida haris yace mata ta dawo zai iyayiyuwa bata nan,Tukunna ta ƙyale ƙopar ta dawo wurinsu ta zuƙunna,
Magiya suka soma Yi mata akan tafarka
"Azeezan mu ki tashi dan Allah, Badan halin mu ba, wlh ba mu gaji dake ba Muna matuƙar ƙaunarki ƙaramar mu kuma babbar mu, pls wake up, kome kike so zamuyi maki, bazamu ƙara 6ata maki rai ba, kuma ba zamu bari giants su ɗaukar mana ke ba" kamar wasu sabbin mahaukata haka suka dinga yi mata sambatu akan tafarka, tun sunayin maganar da ƙwarinsu har ta kai ga muryoyinsu sun disashe, kowa yaja gefe suna matsar ƙwalla, idanuwansu duk sun kumbura saboda tsabar kukan da suka sha,
"Wai ina angel take ne!? Nifa banganta acikin mu ba? Yakamata wani yayi mata magana tazo taga halin da azeezan mu take aciki, tayi mata addu'a ko mun samu tafarka" Kallo kallo suka shiga yi a tsakaninsu, Jin abunda deeja tace, gaba ɗaya sun manta da babu angel acikinsu sai da tayi wannan maganar su ka tuna da ita, Hanna tace"ɗazu acan nabarta zaune bakin ƙopar shiga sashen toilets dinmu," tayi maganar tare da juyawa tana nuna musu wurin, Basu ga komai ba, naufal yace"kodai tayi bacci ne"? Haris ya bashi amsa da cewa"ae bata a saman gadonta, ɗazu da zan shiga toilet na duba naga babu ita" a matuƙar ruɗe suke kallon juna, Eve tace"kodai ta shiga toilet ne? Bari inje in dubo ta"
da sauri haris ya dakatar da ita tare da cewa"Ni zan dubo ta" Ya miƙe tare da kai hannu ya ɗauki fitila Ya juya ya nufi sashen toilet ɗinsu, yana gab da zai shiga, ba zato ba tsammani sai ga danish Ya faɗo hannayenshi biyu suna rungume da angel, ya tallabota a jikinshi, babu alamun tana motsi, A wani irin yanayi Su Hanna suka mimmiƙe tsaye suna kallon shi, mamaki ƙarara akan fuskokinsu, Yayin da zuciyoyinsu ke acunkushe da tambayoyi dangane da abunda ya faru da ita da har ta sume bata motsi,
An rasa me buɗe baki yayi mishi magana A cikinsu, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye Ya wuce da ita saman gadonta Ya kwantar da ita, sumar kanta duk ta hargitse, Fuskarta tayi jawur, musamman tsinin hancinta, hada ɗigon Jini, daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba, hawayene ta ko'ina akan fuskarta, kayan Jikinta sunyi uban squeezing, Hada wandonta Daya maida mata ajikinta, Da gudu Su Hanna suka Tunkaro gadon suna tambayarshi Meya faru da angel a ina ya ɗaukota? bai tanka musu ba, Domin kuwa A yanzu baya atare dasu, itace A gabanshi, zuciyarshi sai harbawa take yi da sauri sauri, numfashin sa da hucin zafi yake fita, a wani irin yanayi yake bin fuskarta da kallo...................."
"Shin meya faru da angel Bayan ta dura tagar nan"?
Lokacin da Angel ta haura tagar nan, ta faɗo ta baya wani irin duhu ne ya mamaye idanuwanta, kanta ya soma juyawa, Ta sanya hannayenta bibbiyu ta dafe kanta, Jikinta ya soma kerma a hanzarce ta fara ƙoƙarin kamo sunan Allah acikin bakinta, sai dai abun ya faskara, sautin shessheƙar kuka ta dinga Ji acikin kunnuwanta, ranta ya dinga bata cewar batool ce take kuka, Cikin duhunnan, ta miƙi hanya gudu gudu sauri sauri hada tuntu6e, ita kanta batasan ina zata dosa ba, domin kuwa notikan kwanta sun kwance, bata ji bata gani, a makance take tafiya burinta takai ga inda take jiyo sautin shessheƙar kukan nan, Haske ta fara hangowa a ƙarshen hanyar data biyo, da gudu ta nufi inda take hango hasken nan, tana faɗowa cikin wurin, Idanuwanta suka sauka akan katafaren filin dake da manya manyan benaye, a ƙalla sun kai Shida benayen kuma kowane matakalarshi ta haura goma sha, don akwai wanda matattakalarshi takai talatin shine wanda idan ka hau zai kai ka har third floor na ginin, Ginin yana da tsayi da faɗi, Daga sama wasu irin manya manyan fitilune da suke haskaka wurin, idan ka kalli kowani hawa na benan zakaga Wasu Tagogi wadanda glass din Jikinsu launin Ja ne, Masu girma, Babu ƙofofin ɗakuna Sai dai da alama za'a Iya samun ƙofofinsu ta can cikin hanyoyin dake akwai, wani irin kurman Ginine, Mai matuƙar ruɗarwa, wani irin fargaba ne ya ɗarsu acikin zuciyarta lokacin da tafara Jin wani irin gurnani, Ginin Ya dinga juya mata, benayen suka dinga motsi Suna Yin ƙasa da sama, Waro ido waje angel tayi Jikinta na 6ari, Ta zabura zata Juya ta koma Inda ta fito, sai dai ina babu hanya, tama rasa gane ta inda ta faɗo Cikin wurin, Tsabar ruɗi yasa ta baza da gudu ta faɗa tsakiyar wurin, hannayenta dafe da kanta saboda wani irin firgici da take aciki, tuni zufa ta wanke Jikinta sharkaf, Bata gama rikicewa ba, Daga can saman hawa na uku ta soma Jin muryar mahaifinta tajudden Yana kuka yana kwala mata gira, A matuƙar ruɗe ta juya ta baya tare da ɗaga kanta saman benan, A tsaye ta hango shi, tare da Wasu irin haluttu masu gashi gashi ajikinsu, Jibga jigba, Sun kewaye shi, Sai Cuzgar naman Jikin shi suke yi, Wata irin gigitacciyar ƙara angel tasaki, mai kuwar gaske, Ta fashe da matsanancin Kuka tana fadin"Daddy! wayyo Allah na daddyna! Shikenan sun kashe mini daddyna!! nashiga uku, Dan Allah ku ƙyale mini daddyna" Tana kuka ta watsa da gudu ta nufi ɗaya daga Cikin benayen da nufin taje ta taimaki daddynta, tana gudu ana maida ta baya, Da zarar takusa kaiwa saman benan sai taga Sun juya mata, Benan yaja da baya, Ya koma can Ciki, Haka ta dinga bin benayen tana ƙoƙarin hawa samansu, Amma wani abun ruɗarwa benayen tamkar masu Rai, sosai suke motsawa wurin yin ƙasa da sama, Jikinta duk zufa ta galabaita sosai, idanuwanta sunyi jawur, Jijiyoyin wuyanta duk sun fito ruɗu ruɗu Jikin fatarta, Muryarta har ta disashe, Duk da mawuyacin halin da tashiga na tsoro da firgici hakan baisa ta fasa yunƙurin hawa benan ba, Bakomai take ji ba face mahaifinta da take hangowa can saman waɗannan halittun suna Cin naman jikinshi, sai kuka yake Yi yana miƙa mata hannu akan tazo ta taimake shi, Akan idonta halittun suka gutsire ƙafafuwanshi, Jini ya dinga tartsatsi yana gangarowa ta saman benan, Angel tashiga ruɗani, addu'a ta kubce mata, gaba ɗaya tunanin ta ya gushe, Tun tana yin kuka har ta koma tana yin na zuci, Ƙafafuwanta sai zogin azaba suke yi mata, saboda zarya da tadinga Yi, Lokacin da benayen suka gama yi mata wasa da hankali, Suka koma yadda suke, waɗannan halittun suka 6ace ma ganinta, sai dai gangar jikin mahaifin ta dake a yashe saman hawa na uku, Da gudu ta haura saman dogon benan nan wanda ya ke da matattakala Talatin, Tana tafiya tana zamewa, a haka harta samu ta haura saman shi, Tana ƙarasawa inda gangar jikin tajudden take, ta zuƙunna saman gwiwowinta, ta dinga kuka hada majina tana ambaton sunan shi tana faɗin sun kashe mini daddyna, sun rabani da farin Cikina, Wayyo Allah na, Ya Allah ka ɗauki raina nima in huta, yatsun hannunta na kerma ta ɗaga su da nufin ta shafa gangar jikinshi, nan take gangar jikin ta 6ace 6aat, a matuƙar gigice ta zazzare idanuwanta eye lashes ɗinta suka bubbuɗe, tsigar jikinta ta dinga tashi, zufa ta ko'ina, kwakwalwarta ta burkice, kafin ta yi wani yunƙurin motsawa ta soma Jin motsin tafiyar wasu abubuwa ta ko'ina, a firgice ta ɗan juya baya tana kallon Jikin wata taga dake a datse, Ras taji gabanta yai wani irin mugin bugu, Bakomai bane angel ta gani face wasu irin manyan kunamu sun ɗaga ƙarin su, Yayin da suke gangarowa daga Jikin bangon suna tunkaro inda take zuƙunne, wa'iyazubillah, ƙiris ya rage zuciyarta ta buga, saboda tsabar razanar da ta yi, ga shi jikinta babu ƙwarin da zata Iya saukowa daga saman benan, Jikinta na 6ari ta soma rarrafawa tana tunkarar banen dan ta sauko ƙasa, tana kuka tana waiwayon kunamun dake tunkarota, a wannan lokaci ta dinga kwala ma danish kira na fitar hayyaci tana faɗin yazo ya taimake ta, zasu kashe ta, ta mutu ta bani ta lalace ƙarshenta yazo,
Adai dai wannan Lokacin Danish Ya faɗo Cikin wurin, Hannun shi ruƙe da wandonta, sai faman waige waige yake yi, karaf idanuwanshi suka sauko akan angel da ke yin rarrafe tana saukowa daga saman benan, Hankalinshi yai matuƙar tashi, da ƙarfi ya ambaci sunanta yana faɗin ta tsaya kada ta motsa ba abunda zasuyi mata, sai dai kash angel bata Iya fahimtar maganar shi, saboda bata acikin hayyacinta, Da gudu ya nufi benan da niyar yaje ya taimaka mata, kafin ya ƙarasa gwiwowin ƙafarta suka sage, Tun daga kan matattakalan farko Angel ta burki ce ta dinga mirginowa tana gangarowa ƙarshen stair ɗin, kanta da hancinta duk suka fashe