Header Ads
Showing 174001 words to 177000 words out of 287659 words

Chapter 59 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1830

Ads at the middle of Article

sai suka ga kamar ruwan hawayene kwance acikinsu.

Kafin su yi yunkurin yi mata magana ta riga su cewa"Ku ɗauko mini akwatin nan da aka kawo muku" da sauri naufal da haris suka je suka janyosu agabanta suka kwantar da akwatin nan,

"Kunsan menene aciki"? Suka haɗa baki wurin cewa a'a, murmushi ta saki tare da cewa"Sabbin Uniform ɗinku ne masu kyan gaske, tare da takalma, da sauran abubuwan da nasan zaku buƙata, Zaku Iya buɗewa ku gani"

Wani irin farin Ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu, Jiki na rawa suka zuƙunna agaban akwatunan haris ne jagaba wurin buɗe akwatin farko, Kaya ne danƙare acikinshi, A ninke suke an jera su, uniform ɗin farko Launin baƙaƙe ne sun sha banban da kalar style din na jikinsu,

"Mutun Uku, Su fiddo da kayan a hankali sai ku dudduba a tsanake" acewar tsohuwa,

Suka amsa mata da toh, haris da deeja ne sai angel suka sanya hannayensu cikin akwatin suna zaro kayan tare da ɗago dasu suna warware ninkin da aka yi musu, haɗaɗɗun riguna ne masu kyan gaske, basu da banbanci da Wrap coat, suna da igiyoyi guda biyu a jikinsu, tsayin su zai kai har gwiwowinsu, sannan suna da dogon hannu, gefe da gefe akwai aljihu ajikin rigunan, yadin jikinsu mai matuƙar kyau da ɗaukar ido, kowace shirt tana da ƴar vest launin red acikinta, Uniform ɗin farko masu launin Black, Mallakin angel da batool ne tare da Danish, Numbobinsu ne akai no 1 no 2 zuwa 3, A bayan rigunan, wani abun mamaki daga ƙasan numbers na jikin uniform ɗinsu, Kowa da sunan da aka sanya mishi su ukun nan, da turanci aka rubuta sunayen anyi amfani da launin Ja, A bayan rigar Batool an rubuta


*HEART BEAT*(Bugun Zuciya) rigar danish an rubuta *PRISON SHIELD* (Garkuwar kurkuku) yayin da ita kuma Angel abayan rigarta aka rubuta *DESTINY* Wannan suna dai ya ɗaure musu kai, Har tsohuwa su ka tambaya menene ma'anar sunayen tace masu kada su damu, suna ne kawai, Angel bata yadda da sunayen ba, basu kwanta mata aranta ba, tabbas akwai dalilin dayasa aka rubuta musu sunayen abayan rigunansu, su ukun nan, Ita dai fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane.

kowace riga tana da dogon wadonta masu kyan gaske, Uniform dinsu azeeza sunyi kyau sosai launin Ja, iri ɗaya ne dana su Danish banbancin kala ne kawai, Sai kuma rubutun dake abayan rigunansu Angel, babu anasu rigunan sai dai numbobinsu, abun burgewa kowace riga tana da cotton scarves, Irin ɗan mayafin nan da mazan indiya suke ɗaurawa asaman wuyan su.





*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*




Launin ja, tun daga kan fuskokinsu zaka shaida irin tsantsar farin cikin da suke aciki, tun kafin ma su sanya kayan ajikinsu har sun fara Imagining irin kyan da zasu yi musu, tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, daga ƙasan Uniform ɗin nasu, wasu haɗaɗɗun rigunan sanyi ne masu dan banzan kyau, launin bright rust red da kuma dark brown, sai faman ɗaɗɗaga rigunan suke yi suna kallonsu, sun rasa bakin magana saboda tsabar murna, ga wasu hats haɗaɗɗun hulunan gayu na mata dana maza masu kyan gaske, Ƙasan akwatin gaba ɗaya sabbin takalmansu ne kala bibbiyu, zubin anckle boots da kuma slippers, Yara fa sun zama ƴan gayu, kaf saida suka zazzage kayan akwatin suna ta kallonsu suna yaba kyawunsu haɗi da nuna irin farin cikin da su ka yi.

Tsohuwa tace su buɗe ɗayan kwatin su duba kayan dake acikin shi, tasan zasu Yi farin ciki, akwai wata ƴar kyauta data sanya musu aciki, taban mamaki, Jin wannan maganar yasa suka tattara uniforms din da komai na akwatin farko suka maidasu ciki suka datse shi, cike da zumuɗi Angel ta buɗe musu akwati na biyu, a danƙare yake da kaya, abu na farko da suka fara Cin karo dashi, hankys ne launin ja da baƙi, mai ɗauke da sunayen kowannan su, sun yi matuƙar Yi musu kyau, Hada mayukan gyaran Jiki dana gyaran gashi, da Set na kayan gyaran akaifa, ga wasu ribboms na ɗaure gashi, Yawanci duk basu san yadda zasu yi amfani dasu ba, amma tunda ga angel sunsan zata Yi musu bayanin komai.

"Tsohuwa, kince akwai gift da kika sanya mana, Ta na ina? Ko su ne waɗannan kayan"? Angel ce tai mata tambayar tana kallonta,

Tsohuwa tace"Ku duba daga can ƙasan akwatin zaku same ta" Jiki na rawa suka ɗaɗɗaga kayan har suka taddo wrapping sheet ɗin dake nannade da wani abu, wanda shape ɗinshi daga sama round ne mai faɗi, ƙasa kuma ya ɗan tsuke, kallon juna suka yi cikin ƙagara da son ganin menene aka nannaɗe haka, kowa ya baza ido suna jiran ganin menene, A tsanake angel ta soma warware wrapping sheet ɗin awani slow, Sai da ta taddo ƙarshen shi ta yakice paper ɗin da aka nannaɗe shi, A hankali take bin shi da kallo, Su azeeza duk suka zazzaro idanuwansu ganin wani abun ban mamaki da basu ta6a gani ba, shin kunsan menene? Nasan Kun ƙosa kuji, To ba komai bane face*MADUBI,*

wani irin farin Cikine ya bayyana akan fuskar angel da ƙarfi ta ambaci sunanshi MIRROR, yayin da take kallon kyakkyawar fuskarta wadda yaushe rabon da taga suffar face dinta tun tana atare da daddynta tsawon shekara huɗu da watanni yama kusa ci ka 5yrs,

Ya burge ta sosai, madubin Round shaped ne mai matuƙar ɗaukar ido, Yadda kasan ƴan ƙauyen ido sama, Haka suka kewaye madubin Suna Kallon fuskokinsu, sun saki baki kamar lehen sakarai, In ka cire mutun ɗaya wanda Yaja gefe ɗaya kamar baya maraba da ganin sabon abunda basu ta6a gani ba, su kuwa sai ihu suke Yi suna Murnar ganin fuskokinsu kamar suyi hauka, Ɗakin nasu ya cika da Hayaniyar su, abun nema ya samu, Tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, Sun tasa madubin gaba Na tsawon lokaci, sai faɗi suke wai dama haka fuskokinmu suke? azeeza tace Wai Allah na, dama haka nake da kyau? Komai na fuskata ɗan ƙarami mai kyau, Hanna tace"Nima fa kyakkyawace, Idanuwana farare ƙyal, ga dogon hanci, " deeja tace"duk da ban kai ku kyau ba, amma Nima ba daga baya ba, Manyan kyau ne dani," tana rufe baki yasmin tace"ni matsalata idanuwana ƴan mitsi mitsi kamar zasu shige ciki, hancina luluyayye, har ƙwara bakina ma, " gaba ɗaya suka kwashe da dariya hada tsohuwa, parveen dai ta ƙura wa madubin ido ita da Rubina sai kallon fuskokinsu suke yi kamar zasu lashe su, har sai da haris Yakai hannu ya danƙwashi kawunansu tukunna suka zabura, suna faman wurga mashi harara,

"Idan kun gama kallon ƙurallan ku bamu abun muma mu duba kyawun fuskokinmu" Wani irin kallo parveen tai mishi tare da cewa"shawara kyauta haris, Ka haƙura da duba abun nan, saboda Ina jiye maka tsoron munin fuskarka da zaka gani, zai iya sawa zuciyarka ta buga" kafin haris ya bata amsa deeja ta riga shi cewa"Ki Iya bakin ki Parveen, Ƙarya kike kice wai haris bai da kyau, don kawai yana da duhun fata ne, kuma ahakan Ba ƙaramin kyakkyawa bane, kawai kina yi mishi baƙin Ciki ne," takai ƙarshen maganar tana jifarta da harara, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma haris ba, koba komai deeja ta yabe shi, abunda ma ya ƙara burgeshi, da kanta ta ruƙo madubin daga hannun angel ta kanga mashi saitin fuskarshi, Atare suka haɗa faces ɗinsu suna kallon juna ta cikin madubin sai dariya suke saki,

Satar kallon danish angel tai don taga a wani yanayi yake ciki, Yana zuƙunne a tsakaninsu javed da mubeen, yaɗan duƙar da kanshi ƙas, Yayin da idanuwanshi suke akan yatsun hannun shi, Aranta tace Shi kuma haka zai ƙare! Kowa Yana kallon fuskarshi acikin mirror, banda shi, wama ya sani ko aljani ne, shiyasa yake tsoron Ya haska fuskar shi Cikin madubi, Amma dai zanso Ya kar6i mirror ɗin nan kodan yaga irin baiwar kyan da Allah yae mishi......." kasa ƙarasa maganar tai ganin yana ƙoƙarin ɗago da kanshi da alama yaji ajikinshi ana kallonshi,

da sauri ta duƙar da nata kan ƙasa tana faman tsuke baki, koda ya ɗago Bai ci sa'ar haɗa ido da ita ba, Sai suka haɗa ido da Haris Ya sakar mishi murmushi yana faɗin" Deeja bani abun nan in haska ma Sarkin kyau fuskarshi, Nasan yau danish ko bacci bazai iya yi ba idan har yayi tozali da kyakkyawar fuskarshi," Ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu Ya ruƙo madubin, Ya ɗan yunƙura ya miƙe ya nufi danish, sai dai kafin ya ƙarasa danish yae saurin kifa kanshi saman gwiwarshi, bubbuga bayanshi haris yae tare da cewa

"Kar ka bani kunya mana, Kowa ya share ka sai ni na damu dakai, pls bro Ka ɗago ka kalli fuskarka," batare daya ɗago da kanshi ba yace"Haris i can't bana son ganin shi, pls ka janye shi daga saiti na, zai iya affecting lafiyata,"

jin wannan maganar ta Danish yasa duk suka ɗago da idanuwansu suna kallon shi, Lamarin ya ɗaure musu kai,

Deeja tace"But why danish? Kowa fa ya duba fuskarshi Kuma lafiya lou ba wani abu daya cutar damu, sai kai zaka ƙi kallon fuskarka? Javed yace "Haba danish idan ma saboda abunda ya faru a tsakanin mu dakai ne yasa kace ba za ka duba abun nan ba, Ina mai baka haƙuri just for today a matsayin mu na ƴan uwa mu kalli fuskokinmu acikin baƙon abun nan,"


Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, sai roƙonshi suke yi suna yi mishi magiya akan ya kalli madubi amma ɗan tahalikin nan yaƙi ɗagowa, rai aɗan 6ace Haris Ya damƙi sumar kanshi da niyar ya ɗago da kanshi Ya tursasa mishi akan ya kalli madubin, aikuwa rai a6ace danish ya bangaje haris Madubin dake hannun shi ya kubce zai kife ƙasa, Jiki Na kerma Ƴan matan su kayi sauri ruƙo shi, Ran haris ya ƙara 6aci ya shiga zazzaga mishi masifa, deeja tace"Su rabu da shi, dama baya atare dasu, Shi kaɗai yasan dalilin shi na ƙin kallon madubin, danish ba abun yarda bane, Tsohuwa dai tana atsaye tana binsu da kallo bata tanka musu ba, duk wanda yai magana idonta na akan la66ansa.

Naufal yace" Ku ku ka damu da shi, ae gaya nan ya baku kunya, Kar Allah yasa ya kalli madubin, don ma ya samu ana lalla6a shi ne, Kuma wlh da ace Madubin nan ya fashe silar hankaɗe haris da kayi, Da ka ji ajikinka, shashasha" yana huci yai maganar,

"Ni dai A iya sani na, Aljanu ne basu son kallon madubi ko su gifta Ta wurin da aka ajiye shi, idan su ka yi suffar mutane saboda baya 6oye ainihin suffarsu ta jinni, na ta6a kallon wani film da irin hakan ta faru, ina da tabbacin cewa danish Ba cikakken mutun bane, Yana da alaƙa da aljanu," Angel ce tai wannan tunanin acikin ranta,

Gyaran muryar da tsohuwa tayi musu ne yasa suka ɗago suna kallonta, Banda Danish daya kifa kanshi saman gwiwowinsa.

"Ku ƙyale shi, Idan ya nu na baya son abu to ku daina ƙoƙarin tursasa shi, kuma kada hakan yasa ku zarge shi, Danish ɗan uwan ku ne, tamkar uba yake agare ku shi da Haris, Tun ɗazu Na lura da irin wariyar da ku ke ɗan nuna mishi, shin meya faru atsakaninku ne? Ko wani zai iya faɗa mini"? Tai tambayar tana bin faces ɗinsu da kallo, Deeja ce ta kwashe duk abunda ya faru tsakaninsu tun daga kan batool daya bi cikin toilet ya ruƙo hannunta ya damƙa ma giant ita, har izuwa irin bugun da suka yi mishi, da kuma yanke alaƙar da suka yi da shi" tun kafin deeja takai ƙarshen maganarta, tsohuwa ta soma girgiza kanta, Yayin da idanuwanta ke akan Danish daya kifa kanshi, duk sun lura da irin damuwar dake akan fuskar tsohuwa, magana ta soma yi cikin nuna 6acin ranta ga abunda suka yi mishi

"Kada ku kuskura ku ƙara ɗaga hannu kuce zaku ta6a lafiyar jikin shi, bama shi kaɗai ba, Kowa ma, Nayi mamakin jin cewa kun haɗa kai kun bugeshi sai kace wani jaki, ko a shekaru Danish Ya ɗare maku amma ahaka kuka rufe ido kuka jibge shi kamar bawan ku, ina hankalin ku ya tafi ne? Musamman ke angel," tai maganar tana nuna angel da sandar hannunta, Yatsina fuska angel tae tare da cewa"Ae ni ban ta6a shi ba, lokacin da suka jibge shi, Na suma bana ahayyacina kuma da ace idona biyu saina 6alla hannun shi daya ruƙe batool, saboda baida tausayi mugu ne shi, inaji ina gani Ya raba ni da batool ɗita, tana kuka ina kuka" daƙyar angel ta karasa maganar tare da ɗaura kanta saman laps ɗinta tana shessheƙar kuka tunawa da irin abunda ya faru aranar, gashi har yau babu alamun za'a dawo musu da ƴar uwarsu,

Deeja tace"Har ga Allah danish ya ƙona mana rai, yayi mana abunda bazamu ta6a mantawa ba, tabbas shi dan uwanmu ne amma baya atare damu, akwai wata mummunar manufa atare dashi, In ba haka ba meyasa duk irin shaƙuwar dake a tsakanin shi da batool bai duba wannan ba, ya rasa dame zai saka mata saida sharri, ae wlh duk abunda ya faru da batool alhakinta na akan wuyanshi, Kuma jira muke ta dawo muga awani hali take aciki, kafin mu ƙarasa yanke mishi hukunci" Daga cikin zuciyarta take magana, fuskarta babu alamun wasa, tsohuwa sai jinjina kai take yi, Tana kallonta, sai da takai ƙarshen maganarta tukunna tace"Aikuwa indai kuka ce zaku Cigaba da ta6a lafiyar jikin shi da rabon wata rana ku rasa madafarku, nayi mamaki da Danish ya ƙyale ku har kuka jibgeshi, bayan yana da ƙarfin da zai Iya rama abunda ku ka yi mishi, amma saboda ƙaunar da yake yi maku sai baiyi hakan ba, Saboda baya son wani acikin ku ya cutu, baku da masoyi a duniyar nan daya wuce Danish, shi tamkar jagora ne acikin rayuwarku, ku daina raina shi, akwai ranar da zaiyi maku amfani, amma muddin kuka ce zaku cigaba da nuna mashi wariya acikunku, to tabbas kuwa xakuyi danasani mara amfani......." Tunda tsohuwa ta soma kora musu jawabi, suka kasa kunne suna sauraronta, batare da suna fahimtar taƙameman abunda take son ganar dasu ba, donsu ana su tunanin basu ga amfanin da zai iya yi musu ba, in banda ya hau gado ya naɗe kamar wani basarake,

"Ba lallai ne ku fahimce ni ba, saboda na karanci hakan akan fuskokinku, Shawarace nake baku kyauta, Bana so ku yi danasani Anan gaba, " har suna haɗa baki wurin furta Kalmar danasani, deeja tace akan me zamu yi danasani? Bata bata amsa ba, tace"Ku tattara kayayyakin nan ku maidasu cikin akwatin, Ku rufe shi, sannan Ku kawar dasu gefe inaso muyi magana daku kafin in tafi" da sauri Su haris suka mayar da kayan da suka curo cikin akwatin suka datse shi, tare da jansu gefe ɗaya suka jingine su jikin table ɗin dakinsu,

bayan sun dawo Tsohuwa ta basu umarnin su miƙe tsaye, Gaba ɗayansu suka yunƙura tare da miƙewa suna kallonta, duk sun ƙagara da suji me take son faɗa musu,

Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo na ɗan wani lokaci kafin ta soma magana cikin muryarta ta tsoffi,

"Tsawon shekara da shekaru Ina Rainon Yara agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a samun Yaran da suka kwanta min araina ba naji ina ƙaunarsu har cikin zuciyata irin ku ɗin nan ba, Kun ciri tuta, domin kuwa kun kafa tarihi acikin rayuwar tsohuwa tamira......." murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Inka cire mutun huɗu, Angel, deeja, Haris da Danish, Babu walwala attare dasu,

"Naso ace ina da hanyar da zan Iya taimaka maku, saboda ƙaunarku da nake yi sai dai kash bani da damar yin hakan, Amma ina fatan nan gaba idan muna da tsawaicin kwana mu sake haɗuwa daku, duk da nasan zaiyi wuya ........." Kallon kallo suka shiga yiwa junansu, Kamar sun fara fahimtar inda zancenta ya dosa,

"Tsawon lokaci Ina atare daku, Duk da ban amfane ku da komai ba, Amma nafi waɗanda su ka yi silar zuwan ku kurkukun nan, Na raini wasunku tun suna ƙanana tun basusan kansu ba, har suka fara tasawa suna rarrafawa yanzu gasunan sun girma gwanin ban sha'awa, wannan abun farin Ciki ne kuma abun ayaba mini ne, ga wanda yasan ya dace" tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi, bayin Allah duk jikinsu yai sanyi, Sai kallon suke yi,

"Acikin ku akwai waɗanda suke Yi mini kallon muguwa maƙaryaciya, Mara amfani, Akwai ma wadda tace dani da tukunyar fulawar dake acikin toilet dinku bamu da banbanci, " duƙar da kai ƙasa angel tai, Cikin jin Nauyin maganar da tsohuwa tayi,

"Ba za ku ta6a sanin amfani na ba, sai ranar da bana atare daku, A ranar zaku tuna da irin mahimmancin da nake dashi acikin rayuwarku, kuma a wannan lokacin zaku yi danasanin rashina atare daku, Amma bana son hakan ya karya zuciyoyinku, Inaso ku ƙarfafa ma juna gwiwa kusanwa ranku cewa, ko babu ni, ko babu wani acikin ƴan uwanku xaku Iya rayuwa! Domin kuwa ba'a halicci duniya don mu dawwama acikinta ba, dole ne akwai ranar da kowa zai barta, ko muna so ko bama so......." dakatawa ta ɗanyi da yin maganar idanuwanta sunyi jawur a yayin da take kallonsu.

"Abunda yasa na buƙaci abaku waɗannan sabbin kayan saboda Inaso nima wata rana ku tuna dani acikin rayuwarku, A ƙalla dai nayi muku abun kirki........" bata ƙarasa maganar ba, sakamakon shessheƙar kukan da suka fara, Batasan ya akai suka ɗagota ba tunkafin ma takarasa zance, girgiza kai ta ɗanyi tana murmushi tace"Jikokina kenan, meyasa zaku karaya tun yanzu? Haba Kar muyi haka daku, kada ku bari hawayen ku su xuba, akwai ranar da zasu yi maku amfani,"

"Dan Allah ki fahimtar damu me kike son faɗa mana? Gaba ɗaya kin jefa mu acikin ruɗani" azeeza ce tayi magana,

"Bankwana nake Yi muku! " wani irin bugu zuciyarsu tayi, Tsabar tashin hankali ne ya bayyana akan fuskokinsu, Sam sun kasa furta komai,

"Dama na faɗa maku cewa, Ni mai raino ce, a ƙa'idar aikin masu raino na gidan kurkukun ƙaddara, da zarar yaran da yake raino sun mallakin hankalinsu, to za'a canza wanda zai dinga kula da su ne,"

A

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads