Showing 63001 words to 66000 words out of 287659 words
Chapter 22 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
dai ba wani abunne ya faru da shi ba," haris ne yai maganar, gaba ɗaya sauran dake asaman gadajen su duk sun sauko, sai zagaye cikin ɗakin suke yi suna neman Danish, Saƙo da lungu ko'ina suka shiga dubawa amma babu shi, lamarin yayi matuƙar ɗaure masu kai,
"Yakamata mu sanar ma tsohuwa halin da ake ciku" Acewar Mubeen,
Deeja tace"bari naje na kirata," tana kokarin zuwa taje ta sanar da ita, Batool tayi saurin cewa"ku dakata" gaba ɗaya suka Juyo suna kallonta,
Haris yace"kin gano inda ya ke ne?
Girgiza kai tayi"a'a, " kafin ta kalli angel da ke a tsaye tace"lokacin da kika saki ƙarar nan, baki ga gifcin mutun ba"?
Shiru angel tayi tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru,
"Gaskiya ni banga gifcin kowa ba, amma meyasa kika tambaye ni"?
"Saboda danish baya son tsawa, zai iyayiyuwa lokacin da kika saki ƙarar nan. Har muka farka daga bacci, a wannan lokacin danish ya rikice ya sauko daga saman gadon shi ya faɗa wani wurin"
Sakin baki angel tayi galala tana kallon batool, da mamaki akan fuskarta tace"saboda kawai nayi ihu sai ya 6ace a neme shi arasa, ko dai yana da ta6in hankali ne"? Tayi tambayar tana kallon batool,
Kafin batool ta bata amsa, Haris yace "yanzu ba lokacin yin magana bane, bamusan awani hali ɗan uwanmu yake ciki ba, yamakata muyi hanzarin nemo shi"
Ya kai ƙarshen maganar, tare da kai hannu ya kar6e fitilar dake a hannun batool, ya yi gaba suma suka bi bayan shi,
Ko'ina kaf sai da suka duba, Basu ga danish ba, a gajiye suka koma saman gadajensu, kowa ya zauna cike da jimamin rashin ganin danish,
Deeja tace"ni dai bari naje na kira tsohuwa," haris ya dakatar da ita" dare yayi sosai, kada mu takura mata, mu jira zuwa gobe da safe, nasan kafin lokacin duk inda yaje zai dawo ne"
Angel dai duk ta rasa sukuni, aranta tace No wonder dama ni nasani, ba cikakken hankali gare shi ba, "
Bacci ne ya fara ɗaukar wasu daga Cikin su, Mutun uku ne suka gaza runtsawa, Haris da Batool sai Angel, kuma dukansu idanuwansu acike suke da bacci,
Fitsari ne ya matse ta, da sauri ta sauko daga saman gadonta, hannunta ruƙe da fitila, ta nufi first door ta toilets ɗinsu,
Bayan ta buɗe ƙopar ta shiga ɗaya daga cikin toilet ɗin, ajiye fitilar ta yi a ƙasa, ta sanya hannu ta tu6e wandon jikinta ta zuƙunna tana fitsari, har wani lumshe ido take yi, saboda daɗin da taji, sai da ta kammala yin fitsarin tayi tsarki, tana ƙoƙarin mayar da wandonta, taji mutsu mutsun mutun, Hankalin ta yayi matuƙar ta shi, Kasa juyawa tayi la66anta sai kerma su ke yi, tsananin tsoro ne bayyane acikin idanuwanta, Ta wutsiyar idonta take hangen shi biji biji, koma wanene dai a zaune yake, ya jingina bayan shi jikin bango, Gefen tukunyar fulawar dake ajiye cikin toilet ɗin su,
Tafi ƙarfin minti goma a tsaye batare da ta juya ba, zuciyarta a cunkushe da tunanin wanene Acikin toilet ɗin? Mutun ko Aljan? Kenan koma wanene ya gama ganin budurcin ta," ta ambaci hakan acikin zuciyarta, tunma kafin taga wanene Ranta ya 6aci ta harzuƙa sosai, ko aljani ne wannan ɗan tahalikin sai ya ɗanɗani kuɗarsa,
Daurewa ta yi ta cije, a wani slow ta ɗan juya tana kallon wurin,
Har saida ta zabura lokacin da tayi arba da Danish, a matuƙar ruɗe take kallon shi,
Ya ƙanƙame Jikin shi da ke ta kerma, ya saki dogayen ƙafafuwanshi ƙasa, ya jingina bayan shi jikin bango, Gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi,
Runtse ido ta ɗanyi tare da biting lower lip ɗinta, Har ta kai hannu zata rarumi bucket ta kwaɗa ma shi akai, sai kuma ta fasa ganin da alama bai ganin ta, saboda sumar kanshi data lullu6e eyes ɗinshi,
cikin sanɗa ta soma tafiya tana tunkararshi, a saitin inda yake zaune ta zuƙunna, tana kallon shi,
Abunda ya faru lokacin da angel takwatsa ƙarar nan, ya farka a firgice ya duro daga saman gadonshi tamkar walƙiya yabar cikin ɗakin saboda tsabar rikitar da ya yi ashe cikin toilet ya faɗo,
Tagumi ta zabga tana kallon ikon Allah, ta sauke ajiyar zuciya yafi sau uku, da ace yau ta kama shi yana kallonta lokacin da take Cikin yin fitsarin nan, da kuwa ya gane kuransa, Allah ne ya taimake shi saboda sam baya a hayyacinsa, baisan ma ta shigo cikin toilet ɗin ba,
Miƙa hannu tayi da niyar ta janye sumar dake akan fuskarshi, sai kuma ta fasa ta miƙe, taje ta ɗauki fitilarta, kafin ta kama hanyar fita daga cikin toilet ɗin, Bayan ta fito ta nufi cikin ɗakin kamar yadda ta tafi tabar batool da haris xaune saman beds ɗinsu a haka ta same su,
Gefen gadon batool ta tsaya tare da ɗan ranƙwafawa saitin kunnanta tace"Danish yana a toilet, ki faɗa ma haris kuje ku ɗauko shi, Amma kada ki ce ni na faɗa maki"
Buɗe ido batool tayi jin maganar Angel a cikin kunnanta"are u serious danish yana acikin toilet"
"Eh, yanzu na ganshi aciki, amma kamar baya a hayyacinsa"
Jiki na rawa Batool ta sauko daga saman gadonta, Sai da tafara gaya ma Haris cewa Danish Yana acikin toilet, tukunna tayi gaba shima yabi bayanta,
Ajiyar zuciya angel ta sauke, tare da ajiye fitilar ƙasan gadonta, Ta haura daman gadon ta kwanta, tana jiran taga sun shigo da shi, Zuciyarta a cike take da tunanin meke damun shi? yanayin abubuwan da yake yi kamar akwai wani abu dake damun shi, ' can kuma saita ja guntun tsoki aranta tace"Ko ina ruwana da shi, matsalar shi ce,"
Jin takun tafiyarsu yasa ta ɗan saci kallonsu, Batool ce da haris sun ruƙoshi daƙyar yake tafiya, A saman gadonshi suka sake shi, ya haye saman mattress ɗinshi ya kwanta, Haris ya janyo mashi duvet ɗinsa ya lullu6a mashi har zuwa chest ɗinsa,
Kafin suka koma saman beds ɗinsu domin yin bacci,
Juyowa tayi da niyar ta saci kallon shi, karaf suka haɗa ido da shi, Harara ta jefa mashi, tare da juya ma shi baya ta kalli 6angaren hagu,
Tunani ta shiga yi acikin zuciyarta, anya kuwa ɗazu bai kalle ta ba, lokacin da take yin fitsarin nan ba? Idan kuwa haka ne tabbas ya gama da ita, shikenan Ya gama ganin tsiraicinta, ranta ne ya bata cewa ta ƙara juya taga idan ya yi bacci, a hankali ta sake waiwayowa, karaf suka haɗa ido da shi, Ɗaure mashi fuska tayi tare da zare ma shi gray eyes ɗinta"Kallon ya isa, Ka juya ka kalli can mana, bakasan ba'a son ana bacci ta 6angaren Hagu ba,"
Yadda kasan tayi magana da gunki, Ko motsa lips ɗinsa, baiyi ba balle ma tayi tunanin zai tanka mata,
"Can't u hear me"? a ɗan tsawace tayi ma shi maganar, jin yaƙi tanka mata kuma yaƙi daina kallon nata, yasa ta ruƙo pillownta, Ta daddage ta jefa ma shi saman fuskarshi, Salon Jan faɗa,
A hankali ya ɗaura dogayen yatsun hannunshi saman pillown ya janye shi daga kan fuskarshi, Ya ɗaura shi saman nashi pillow ɗin ya haɗa biyu kenan, ya ɗaura kan shi asama,
Rai a6ace tace"ka dawo mun da pillow ɗina, ko ranka ya 6aci," banza ya yi mata,
"Magana fa nake maka"
Sai lokacin ya ɗan buɗe baki yace"Zo ki ɗauka, ae bani na kawo shi nan ba" shiru ta yi tana cigaba da kallon shi, ganin ta tsare shi da ido, yasa shi juya mata ƙeya,
Cike da takaici ta koma ta kwanta, tare da jan bargo ta lullu6e fuskarta, sai da tayi addu'a tukunna ta samu bacci ya yi awon gaba da ita,
In the morning,
Kasancewar Jiya basu samu isasshen bacci ba, Babu wanda ya farka,
Cikin bacci angel ta yi Kakkauran Juyi da niyar ta gyara kwanciyarta, kwatsam idanuwanta suka sauka akan fuskar tsohuwa dake a tsaye bakin gadon ta, hannunta na ruƙe da sanda, mamaki ne ya kamata har ta soma tunanin kodai mafarki take yi, ƙura mata ta yi tana kallonta, itama kuma tsohuwar ita take kallon,
Ƙasa ƙasa da murya angel ta ambaci"A'uzu billahi minasshaiɗanin Rajim"
Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Ni ce shaiɗanin"?
Bata amsa mata tambayarta ba, har saida ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta jikin bango, tukunna tace "Ai kin wuce nan, idan akwai na gaba da shaiɗan to ke ce tsohuwa"
Baki asake tsohuwa ke kallonta,
"Meyasa kika zo kika tsaya a bakin gado na"? Ta yi tambayar fuska a ɗaure take kallonta,
"Zuwa nayi don in tashe ku daga bacci, naga har gari ya waye baku farka ba......" tunkan takai ƙarshen maganarta, Angel ta katse ta da cewa"Ƙarya kike yi, Idan tashin mu kika zo yi daga bacci why baki bi kowani gado ba, Sai kika zo kan gadona kika tsaya kina kallo na, wlh kiji tsoron Allah, tsofe tsofe dake kina ƙarya," ta ƙarasa maganar tana sakar mata harara,
Jinjina kai tsohuwa tayi"Ke wai baki jin tsoro na? Meyasa baki jin shakkar yi mini magana ne?
"Inji tsorin ki akan me? Ni da nake neman hanyar da zan tarwatsa shirin ku taya kike tunanin zan ji tsorin ki? Idan ma kina tunanin hakan acikin ranki to ki daina, suma waɗanda suke jin shakkar taki don kin juya masu tunaninsu ne, Amma asannu zan dawo da su Cikin hayyacin su, "
Shiru tsohuwa tayi tana kallonta batare data ce komai ba.
Angel taci gaba da cewa" ina zargin jiya ke ce kika kwaɗe mun kaina da sandar hannun ki, Saboda kinga ina ƙoƙarin kwance shirinki, wato so ki kayi nima ki ɗaure mun kaina ta yadda zan manta da komai, tabbas kinso ki yi nasara sai dai Allah bai baki ikon yin hakan ba, farkawar dana yi daga bacci komai dana manta sai da ya dawo cikin kaina, Kuma bazan fasa faɗa masu Allah ba, har sai na fargar da su,
"Taya kenan zaki iya aiwatar da hakan? Ko kina tunanin zaki iya sarrafa tunaninsu ne? Yaran da ni na raine su da hannu na, na gatanta su, tun da suke basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, komai suna samu ba'a abunda ban yi masu ba, matsayin uwa nake a wurinsu, a haka kike tunanin zasu ji maganarki fiye da tawa"? Tsohuce ta yi maganar yayin da take sakin wani irin bazawarin murmushi,
Wani irin kallon rainin wayau angel tayi mata"Wlh tun da nake arayuwata ban ta6a ganin Muguwar maca ba, Azzaluma kuma macuciya irin ki ba!"
Yadda tayi magana batare da jin ɗar ba, ya yi matuƙar girgiza tsohuwa,
"Wai ke baki jin tsoron Allah? Ki tuna fa komai kike yi Allah yana kallon ki, har kina da bakin da zakice kin basu gata? Kin raine su? Kuma har kike kiran kanki a matsayin uwarsu? Tirr wlh ji nake kamar inyi kakin majina in watsa maki akan fuskarki saboda natsane ki, Wlh nafi son mutuwa ta so dubu dake!" Zuba mata ido tsohuwa tayi tana kallon Ikon Allah,
Sassauta murya angel tayi Idanuwanta cike tab da ƙwalla tace"Kin cuci rayuwarsu, kin gama dasu, ni banmasan ya zan kwatanta irin cin zalinsu da ki kayi ba, kuma ga dukkan alamu kin sani kike take sani, dan baki yi kama da jahila ba, Kawai salon tsabar mugunta ne, Yaran nan ko nonon raƙuma suka sha iya abunda zasu yi kenan, Ga sunan Wasu kala da su they don't even know anything about the one who created them because you never told them, cos of your wickedness Kin barsu a cikin duhu, sun zo duniya a wahalce kuma zasu koma a wahalce, Idan yau ɗayansu ya faɗi ya mutu menene makomarshi dan Allah meyasa ki ka yi musu haka? Meyasa?.........." kasa ƙarasa maganar angel tayi saboda wani irin ƙuntataccen kuka daya kubce mata, kuka sosai ta fashe da shi,
Tsohuwa kuwa ta kafe ta da waɗannan Kwala kwalan idanuwanta nata, masu kama dana ƴan ƙwaya,
Cigaba da magana ta yi"Idan wani zunubi suka aikata maki, bai kamata ki ɗauki fansa ta wannan hanyar ba, balle ma nasan basu aikata maki komai ba, To kodai cikin danginsu wani ya yi maki badaidai ba, shiyasa kike ɗaukar fansa akansu" ta yi tambayar idanuwanta jawur hawaye duk sun wanke fuskarta,
Tun da suka soma magana babu wanda ya farka daga cikin masu yin baccin, tamkar wasu matattu,
Jinjina kai angel tayi"dama nasani bazaki bani amsar tambayata ba, sai dai ki kafe ni da ido kina kallo," ta yi maganar cikin sanyin murya tare da sanya hannunta da dama tana share hawayen dake silalowa,
Kafin ta ɗaura da cewa"Allah ba azzalimin bawansa bane, Allah zai bi masu haƙƙinsu, inda na gode ma Allah, Mutuwa tana akan kowa, Walau mutun walau aljan, akwai kwanciyar ƙabari akwai kuma hisabi, Ina fata duk kin shirya ma wannan........" Muryar Batool ce ta katse ta ta hanyar kiran sunanta"ANGEL" koda tsohuwa taji muryar batool, Sai ta juya da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar shiga ɗakinta,
Har ta kusa shiga ciki muryar angel ta sake katse ta da cewa"Baki san Su ji me muke tattaunawa ne shiyasa kika nemi hanyar guduwa? Allah dai yana a madakata yana jiranmu, kuma inaso ki sani Zanyi amfani da ilmin da nake da shi, da kaifin basirar da nake da shi wurin Sarrafa tunaninsu, Kuma zansa su kar6i addinin musulunci, after that I will fight for our freedom, because no one deserves to live a locked up life!
Tsawon mintuna tsohuwa bata motsa ba, kuma bata juyo ta kalli inda angel take ba, can dai taci gaba da dogara sandar, har samu ta shige cikin ɗakinta taja ƙopa ta rufe,
Fashewa da wani sabon kukan angel ta yi, da sauri batool ta sauko daga saman gadonta, tazo gaban gadon angel ta zauna daga gefenta,
Muryarta aruɗe take faɗin"Sister what's wrong with u? and why are u crying"? Kallonta angel tayi da idanuwanta da suka rune, muryarta a karye tace"Batool ina kuka ne saboda ku"
"But why"?
"it will be hard for you to understand me, even if i tell you, so just forget about it," cikin shessheƙar kuka ta yi maganar,
Dafa shoulder ɗinta batool tayi"Pls ki faɗa mun meyasa kike kuka sabo da mu"?
"Baki ga tsohuwa ba"? Angel ce ta yi mata tambayar, girgixa kai batool ta yi"Banganta ba, tazo ne? Ita ce ta saki kuka"?
Girgiza kai tayi"A'a, Mubar maganar, inaso zan shiga toilet," daga haka ta zuro da ƙafarta daga saman gadon ta sauko, ta nufi toilet ɗinsu, Ta tafi tabar batool da tunanin dalilin kukanta, meyasa ta ke yin kuka saboda mu? ta yi ma kanta tambayar da bata da amsarta,
Tunda ta shiga Cikin toilet ɗin taci burki ta tsaya Idonta na akan Window nan dake a jikin bango, wadda ta ƙwallafa ma rai akan son Fasa glass ɗin jikinta, don ta samu damar dura wa Cikin kurkukun.
Hannu tasa ta share hawayen dake akan fuskarta, Cikin zuciyarta ta soma yin magana"rana ta farko dana tsinci kaina cikin gidan kurkukun nan, A ƙagare nake dana nemi hanyar da zan fita daga Cikinsa, Amma Ayanzu bana sha'awar Barinsa batare da waɗannan bayin Allahn ba, Kuma batare da ƙwaƙƙwarar hujja da zan yin amfani ba, wurin ganin na tarwatsa duk wani shirinsu, Zanbi komai asannu domin Cimma nasara, Bi'iznillahi,'
Angel yarinya ce mai kaifin basira Fiye da tunanin mai tunani, wayan dake gare ta yafi ƙarfin shekarunta, wasu ɗabi'un nata da halayanta sam ba irin na yara bane, she's genius"
Lokacin da ta fito daga wankan, A tsaye ta samu Batool tana jiran na ciki ya fito ta samu ta shiga itama tayi wankan" Kallon juna su ka yi,
Murmushi Batool ta sakar mata tare da cewa"tun ɗazu nake jira na ciki ya fito in samu nima in shiga in yi wanka,
Angel tace"Wani ya shiga sauran toilets ɗinne"?
Jinjina kai batool tayi"Eh, Hanna ce ta shiga ɗaya, ɗayan kuma Danish ne da deeja suka shiga Ciki," Har wata zabura angel ta yi jin abunda batool tace"What! danish da deeja ne suka shiga atare? Saboda me"?
Fuskar batool asake tace"Dama idan babu wuri kuma uziri ya kama mu, mutun biyu suna amfani da toilet ɗaya......."
tunkafin Batool takai ƙarshen maganarta, Angel ta yi gaba zuwa ƙopar sauran makewayin, Rai a matuƙar 6ace takai hannu tana Bubbuga ƙofofin tamkar zata Fasa su,
"zaku fito ko saina 6alle ƙopar"? Tana huci ta yi maganar, Bama tasan wanne suke a ciki ba,
Kusan atare suka buɗe ƙofofin toilets ɗin, na biyun Hanna ce ta leƙo kai, Na ƙarshen ne Deeja da danish suka fito, wani matsiyacin kallo Angel ta shiga binsu da shi from head to toe, hannun shi na a ruƙe da rigarshi, ita kuma iya rigarce har guiwarta, wandonta na hannunta,
"lafiya kike bubbuga mana ƙopa"? Fuska aɗaure deeja ta yi mata tambayar"
Dakuwa angel ta sakar mata"Ungo nan, Ku dukanku ku kar6a ku raba,"
Kallon juna su ka yi don basu fahimci me take nufi ba, Runtse ido tayi zuciyarta na tafarfasa ta ambaci"Allahu ajirni fil musibati......
Batool sai faman tamyarta take yi lafiya? Meya faru"? Ware idanuwanta ta yi akan fuskar deeja da ta danish, sae faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, da alama bacci bai ishe shi ba, Sam tarasa ta ina zata fara, wato su awurinsu ba laifi bane idan mace da namiji sun shiga toilet ɗaya, tun zuwanta bata ta6a sanin suna yin hakan ba, Sai yau da take ji awurin batool ta kuma gani da idanuwanta,
Cizon lips ɗinta tayi tamkar zata fasa su, Cikin fusata ta