Header Ads
Showing 222001 words to 225000 words out of 287659 words

Chapter 75 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1785

Ads at the middle of Article

ni, ba gaskiya bane abunda ya gaya maki, bana so ne ku yi danasani,"

Harara Gabriel ya watsa mashi tare da cewa"idan har dagaske ƙarya na ke yi akan abunda na faɗa mata, to ka bari muje tare da ita mu duba, idan har bamu ganta ba, shi ne ka ke da damar da za ka iya ƙaryata ni,"

rai a6ace Danish ya nuna shi da yatsa

"Ka yi min shiru! Bana so na ƙara jin maganarka, wawa kawai, kaine silar komai, kuma bazan ƙyale ka ba,"

Gabriel ya daki ƙirjinshi da hannu tare da cewa nima bana so ka ƙyale ni, Ɗan rainin wayau, dama daga ganin fuskarka ba mutumin kirki bane, wama yasani ko ɗan leƙen asiri ne kai acikin mu......."

Ɗaya daga Cikin abunda Danish ya tsani Ya ji an faɗa mashi kenan, aiko ranshi yayi mugun 6aci har baisan time daya damƙi wuyan Gabriel da hannu biyu ba, ya tura shi zuwa jikin bango ya matse shi, Da gudu Angel ta nufe su da niyar ta dakatar dashi, sai dai kafin ta isa, tai tuntu6e ta kife ƙasa, Kafin ta yi wani yunƙurin ɗagowa

faɗa ya kaure a tsakanin Danish da Gabriel, Yadda kasan dawakai suna kokawa, dunƙule hannu Gabriel yai ya dinga naushin cikin Danish, Don ya sakar mashi wuyanshi daya shaƙe mashi amma yaƙi saki, duk da irin jahilin naushin da yake kaima Cikin shi, ko girgiza baiyi ba tamkar baisan ma ya na yi mata, ganin dagaske so yake ya kashe shi yasa Gabriel daddagewa Ya sauke mashi naushi saman idon shi na hagu, nan take Danish ya saki wuyan Gabriel Gaba ɗaya ya faɗi ƙasa hannun shi dafe da idonshi, kamar zaiyi hauka, shi kanshi Gabriel da ya yi silar jefa shi cikin halin da yake ciki sai da gabanshi ya faɗi, ganin Jini yana gangarowa ta cikin idon nashi daya nausa, wata irin gigitacciyar ƙara Angel ta saki, A matuƙar razane ta miƙe daga kwancen da take akasa ta watsa da gudu ta zube sama gwiwowinta agaban Danish, Hannu biyi ta sanya wurin ɗago dashi ta ƙanƙame shi ajikinta, Sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, Gaba ɗaya tabi ta gigice, ta ruɗe ganin yadda idon shi ke fitar da jini jawur dashi,

"INNALALLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN! Gabriel ka kashe mishi idonshi, Ka kashe min Danish ɗina! wayyo Allah na! nashiga uku na bani na lalace!!" Hankalin Gabriel idan yai dubu to ya tashi, Kamar ya ɗaura hannu akai ya fasa ihu haka yake ji, la66ansa sai kerma suke yi, ya haɗa uban gumi, Muryarshi aruɗe yake faɗin"Angel bada son raina na aikata mishi hakan ba, shine ya shaƙe min wuyana! sosai ta ƙanƙame Danish ajikinta, Jikinshi yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyacin, ko ina kerma yake yi, ga wani irin nishi da ya ke fitarwa.

hannunta data ɗaura saman nashi hannun daya rufe idon da ke bleeding dashi, tuni ya jima da jiƙewa sharkaf da jininsa, wa'iya zubillahi, Lamarin tamkar a mafarki yake faruwa, sun yi fatan ace mafarki ne su ke yi ba agaske ya faru ba, ta yi Danasanin Biye ma Gabriel da tai da duk hakan bata faru ba, da tasan Danish zai rasa idonshi silar yunƙurinsu na haura taga da bata yi gigin yin hakan ba, Yanzu gashi dare ɗaya sun ja mashi bala'e, Gabriel ya naƙasa shi, akan abunda bai taka kara ya karya shi ba, duk wannan koke koken da suke yi na cikin ɗaki basu farka daga baccin da suke yi ba, kamar waɗanda suka sha sleeping pills, tana kuka tana faɗin Gabriel ya zamuyi Dashi kada ya mutu, jinin shi sai zuba ya ke yi, Ya Allah kasa mafarki ne nake yi, bazan iya jure ganin danish cikin mawuyacin halin nan ba! Bazan ta6a yafe ma kaina ba, da kai kanka Gabriel kaine silar komai, Ga shi zan rasa ɗan uwana....

Da gudu Gabriel Ya nufi igiyar shanyarsu ganin mayafin azeeza da ta manta Tun ranar da akazo aka tafi ƴar gidan daddy, Angel ta shanya shi don ya bushe bayan ta kammala sanyaya mata jikin ta dashi, aranar suka barshi saman igiyar, ɗaukowa Gabriel yai jiki na 6ari garin sauri hada tuntu6e ya ƙarasa inda Angel take a zuƙunne ta ƙanƙame shi ajikinta, daƙyar Gabriel ya iya 6an6aro kanshi daga saman ƙirjin Angel, ya dawo dashi saman jikin shi, ya sanya mashi mayafin ya tamke mashi idanuwanshi dashi, sai nishi ya ke yi yana yarfa dogayen yatsun hannayenshi, Bawan Allah shi kaɗai yasan irin raɗaɗin azabar da yake ji acikin idonshi, jijiyoyin hannanyenshi dana wuyanshi shatunsu yafito ruɗu ruɗu saman fatarshi, hatta saman goshinsa jijiyoyinne, gwanin ban tsoro, sosai Gabriel ya ɗaure mashi mayafin duk don jinin ya dakata da zuba, haƙiƙa na yi baƙin Cikin ganin kakkyawar fuskar Danish da jini ya wanke ta, har saman wuyan shi, Gabriel na gama daure mashi idon nashi, angel ta sanya hannu biyu ta dawo dashi jikinta, ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka mai cin rai, tana faɗin"ɗan uwana rabin raina dan Allah kada ka mutu kabarni Danish ɗina, na gane kuskure na, ban da wayau, ga shi naja maka ka rasa idanuwanka, duk laifina ne, namanta cewa duk abunda ka ke yi kana yi ne don ka kare ni daga faɗawa halaka amma saboda taurin kai irin nawa nagaza fahimtar hakan, mun cuce ka Danish mune silar komai!!........ Sosai ta fashe da kuka, Shima Gabriel ɗin kukan yake yi tamkar ranshi zai fita, tashin hankalin da ba'a sama shi date!!

Mexai faru da danish? Ga ido yana ta bleeding zai mutune ko zai rayu a matsayin makaho mara ido ɗaya? Wani irin hukunci su haris zasu ɗauka idan suka gane cewa Gabriel ne silar da Danish ɗinsu Ya makance? Wani hali zasu tsinci kansu? Alƙamina Ya tsaya Cak! sai mun haɗu next page in Allah yakaimu da rai da lafiya, amma fa ga dukkan alamu Danish ɗinku saiya leƙa treatment room! Daga nan kuma.6arna zata auku, Don angel bazata juri zama babu shi ba, dama shine mai tsawatar mata akan karta haura taga, inaga idan babu shi........😳 hasashe na ne kawai🥱






💋PRISONERS💋



Saboda tsabar yadda jinin ke fita hatta Mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi idon nashi ya jiƙe sharkaf da jininsa, Lamarin ya yi matuƙar gigitasu, Sautin muryarta har ya fara disashe wa saboda tsabar kukan da tasha, Gabriel da ke a zuƙunne ƙasa gabanshi sai yarfa hannayen shi ya ke yi, Yarasa uwar ubanshi zuciyarshi sai bugawa ta ke da ƙarfi da ƙarfi duk ya firgice tsoranshi kada Danish ya rasa ranshi silar naushin da yai mashi.

Jikinta ba ƙaramin zafi yai ba, har time ɗin hannayenta biyu na ƙanƙame da kanshi a ƙirjinta, Jikin shi ya saki sosai shi kaɗai yasan zogin azabar da ya ke ji a cikin idon shi. Sama sama numfashin sa ke fita, maƙoshin shi ya bushe, ta ko'ina babu sauƙi a jikin shi, addu'oi ta dinga karantowa tana tottofa mashi samar sumar kanshi,

Cikin fitar hayyaci ya ke yamutsa vest ɗin jikinta da hannayenshi masu dogayen akaifu, duk ya faffasa mata fatar bayanta, amma ko kaɗan bata ji zafi ba, batasan ma yana yi ba, damuwarta gaba ɗaya akanshi ne, Da ace tana da halin da zata iya ɗauke mashi ciwon ta maida shi akanta da tuni ta yi hakan, Zaifi mata sauƙi akan taga Danish acikin mawuyacin hali.

la66anta na rawa ta soma ambaton sunan shi tana faɗin dan Allah Danish kada ka mutu kabarni, kada ka daina motsi, ni ko idona ne ma zan iya badawa asanya ma ka, Ya Allah ka kawo mishi ɗauki, Wannan wata irin baƙar rana ce, Sosai take kuka, idanuwanta sun yi jaga jaga da hawaye ta rasa ya zata yi dashi ga jinin yaƙi daina bleeding, Gabriel da ya gama rikicewa Sai magiya ya ke yi ma Angel akan ta cire idon shi ɗaya ta sanya ma Danish tun da shi ne silar rasa idon nashi.


Duk da halin da ya ke ciki hakan bai hana shi ƙoƙarin motsa red lips ɗinsa da su ka jiƙe sharkaf da jinin da ke ta gangarowa ta cikin ƙarƙashin mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi ido da shi, magana ya ke so yai mata amma ya kasa, la66ansa sun ƙi bashi haɗin kai, Jikin shi gaba ɗaya ba sauƙi, Yanke shawarar fita tai don ta sanar ma sauran ƴan uwansu ƙwara kowa ya sani, don su nemi mafita atare, Tana kuka tana ƙoƙarin 6an6are shi daga jikinta sai dai yaƙi bari ta raba jikinta da nashi, idanuwanta cike tab da ƙwalla ta kalli Gabriel muryarta na kerma tace

"Ka... ruƙe shi, Zan je na faɗa ma su haris," duk yadda gabriel yaso ya raba Angel da Danish abun ya faskara, mugun ruƙo yai mata bana wasa ba, Kallon Gabriel din tai"kaje ka yi musu magana kowa ya tashi su zo, " hawaye ta ko'ina a fuskarshi yace"Angel Pls kada ki faɗa musu cewa ni ne silar rasa idon shi......" tun kan ya ƙarasa maganar ta rufe ido tana zazzaga mashi masifa

"Har kana da bakin da za ka ce kada na faɗa mu su? Dole su san cewa kaine silar komai, mugu kawai ai bansan haka ka ke ba da tun farko ban biye maka ba.....hada zagi ta haɗa mashi, Jiki duk ba ƙwari Gabriel ya miƙe har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi ga ciwon mai raɗaɗi da ya addabe shi, a haka ya fuce daga Cikin toilet din, bai shiga ɗakin ba a bakin ƙopar ya tsaya yana matse kwalla.



Fitar Gabriel ke da wuya, ta soma jin muryarshi ƙasa ƙasa yana yi mata magana, da sauri ta ɗaura kunnanta saman la66ansa don ta samu damar jin me ya ke son faɗa mata.



Angel ki daina zubar da hawayen ki saboda ni, lafiyata qalou, ba abunda ya sami idona....."

Cikin muryar ku ka tace "ƙarya ka ke yi min Danish nasan ka faɗamin hakan ne don ka kwantar min da hankali na...." ku ka yaƙi bari ta ƙarasa maganar, Sassauta ruƙon da yai mata ya yi tare da ɗagowa da kanshi fuskar ta 6aci sosai da jiki, kasa tsayar da kan nashi yai, Sai dai ya kwantar da shi saman wuyanta, jikinta yai mugun sanyi, saboda ƙarfin hali irin nashi a haka ya cigaba da yi mata magana cikin raunin murya ta wanda ya gama galabaita.

_Angel, za'azo atafi dani, babu tabbacin zan dawo cikin ku, that doesn't mean that I'll die. Even if I'm not around, ki yi min alƙawarin ba za ki haura tagar nan ba_

cikin shessheƙar kuka tace"damuwar ka kenan Danish Ni yanzu bata wannan nake ba, lafiyarka nake so, kuma ni bazan juri rashin ka atare dani ba, wlh bazan iya zama babu batul sannan babu kai a tare dani ba....." kwantar da kanta tai gefen wuyanshi. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka sai shesseƙar ku ke ta ke yi, muryarshi ce ta ƙara katse mata kukan nata daƙyar yake iya furta maganar

"Angel, ki tashi mu shiga ɗaki, ki ruƙe ni mu tafi, inaso inga ƴan uwana kafin atafi dani, nasan yanzu haka suna akan hanyar zuwa ɗauka na" Jin wannan maganar tashi yasa ta ɗaga murya ta ƙwala ma Gabriel kira, Jin sautin muryarta yasa shi yin saurin buɗe ƙopa ya faɗo toilet ɗin

Muryarta asanyaye tace mashi

"Ka taimaka mini mu shiga da shi ɗaki"

jiki na 6ari ya ƙarasa ciki, atare da Angel su ka ruƙo Danish, daƙyar daƙyar suke jan shi saboda jikin nashi ba ƙwari, kamar lagwanin fitila, A haka suka janyo shi har zuwa bakin ƙopar fita daga cikin sashen toilet din nasu, duk inda suka taka sai jinin shi ya ɗiɗdiga

Kamar jira ake su dira ƙafafuwansu saman floor ɗin ɗakinsu, Ba zato ba tsammani, Su ka soma Jiyo motsin buɗe ƙopa, A matuƙar gigice Gabriel da Angel suka kalli ƙofar, Wata irin zufa ce ta shiga wanke fuskokinsu, damuwa ce ƙarara akan fuskar Angel.

Wani gabjejen Giant Ne ya shigo ɗakin Yana tafiya Tsokokin Jikin shi na motsawa, zazzafan gaske Star biyu ce a gaban rigar shi, a gaggauce yake taka staircases ɗin benan tsabar sauri kamar zai tashi sama, Da zafin shi Yake taka ƙafafuwan shi.

batasan lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, don tasan zuwa akai araba ta da Danish dinta, Sautin kukan Angel ne ya farkar dasu Haris, Hakalinsu a matuƙar tashe suka soma buɗe idanuwansu kusan atare Kowannansu ya yaye bargon da ya lullu6a da shi, sai dai kafin su yi yunƙurin saukowa daga saman gadonsu, Tuni wannan giant ɗin Ya jima da ƙarasowa ciki, tsabar tsoratar da Gabriel yai ne yasa shin Yin saurin sakin Danish yabar Angel da ruƙon shi, kamar amafarki su haris suke kallon Danish da Jini ya wanke ma fuska, ruɗu ya hana su gane wanene.

Yayin da wasu daga cikin su ke kallon Giant ɗin da ke tafiya yana tunkarar su Angel, Lamarin yai matuƙar ɗaure musu kai, Sun gaza yarda da abunda idanuwansu ke nuna masu, Tana ji tana gani, Giant ɗin nan ya sanya hannu biyu Duk irin tsayin Danish Kamar jinjiri Haka giant ɗin ya ɗauke shi tare da ɗaura shi saman kafadar shi, Cikin Zafin nama Ya juya dashi, Ya nufi Benan, Da gudun gaske Angel tabi bayan shi, tana kuka tamkar ranta zai fita tana ambaton sunan Danish, Adai dai bakin stair ɗin tai tuntu6e wurin taka staircases ɗin Gaba ɗaya ta kife kanta Ya daki ƙasa, ko motsi bata yi ba. Ga dukkan alamu ta sume ne, sai bayan da Giant ɗin Ya fuce daga Cikin ɗakin, Ƙopar na rufewa ta bada wanj irin sauti Garam!!

Shi ne silar dawowar su Cikin hayyacin su, Azeeza ta fashe da wani irin matsanancin kuka tun kafin ma taji meya faru, sautin rufe ƙopar ɗakin su ne yasa ta fahimci cewa Giants ne suka tafi da wani, shiyasa ta fashe da kuka, Jikin Haris har 6ari yake yi wurin saukowa daga saman gadon shi yana bin Fuskar Gabriel da kallo wanda Ya ƙame jikin bango tsabar tashin hankali ne akan fuskar shi, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya sauko daga saman gadon shi, Tun kafin ma su soma tambayar Gabriel a ruɗe yake girgiza musu kai hawaye nabin fuskarsa,

Muryar haris aruɗe ya furta"wanene aka fita dashi? Meya faru ne naga jini a jikin ka? Meyasa Angel ta ke kuka tana ambaton sunan Danish? Allah yasa mafarki nake yi ba gaske ba, zaifi min kwanciyar hankali na, akan ace wani abu ne ya faru da shi"!

tsabar ruɗanin da Gabriel ya shiga ne yasa shi Yin su6ul da baka wurin furta"Bada son raina na aikata mishi hakan ba, bansani ba, Ku ƙyale ni ku rabu dani inji da abunda ke damuna! ' zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa kamar ƙaramin yaro haka ya fashe da wani sabon kukan.


"Hakan na nufin wani abu ya samu Danish! Kada ka ce min Jinin shi ne wannan a jikin ka," haris ne yai maganar tare da sanya hannu biyu ya damƙi gaban rigar Gabriel ya ɗaɗɗago dashi Ya buga shi jikin bango, Idanuwanshi tuni sun rikiɗa sunyi jawur dasu

"ka faɗa min Me ka aikatawa Danish? Jinin wanene a jikin rigarka!

Yana magana tsokokin fuskarsa na motsawa, Kasa buɗe baki Gabriel yai duk yabi ya firgice,

Hankalin su Deeja ya tashi sosai, Har sun fara sharar ƙwalla Saboda sunji a jikin su wani abu ne ya faru da Danish ɗinsu, Da gudu Su hanna su ka nufi Angel da ke baje saman matakalar bene A saman laps ɗinsu suka kwanto da ita, Sai ku ka su ke yi suna ambaton sunanta haɗi da bubbuga jikinta akan ta tashi ta faɗa musu meya faru da su.

Kukan azeeza yafi na kowa sauti, Ta cika ɗakin nasu, Takaici biyu ga rashin ido, Ga takaicin halin da take tunanin waninsu ya shiga, Na tashin hankali, Abun ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, tana matuƙar jin zafin makantar daren da take fama da ita.

Takaicin duniya ya ishe su, kamar su yi hauka, Gabriel ya ƙi buɗe ba ki ya basu amsar tambayoyinsu, kuma shi kaɗai ne zai iya faɗa musu abunda ya faru.


Ga Angel taƙi farkawa, Har ruwa suka yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Babu wanda ya iya runtsawa acikin su, Zuciyoyinsu sun karaya sosai musamman Haris da ya gane cewa An tafi da Danish din shi Cikin mawuyacin hali, tuni zazza6i ya kama shi mai zafin gaske, Ciwon kai mai raɗaɗi ya kama Azeeza da ke ta ku ka, Babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, Bacci ya ƙaura ce wa idanuwansu, An rasa wanda zai lallashi wani acikin su, matan gaba ɗayan su asaman benan Suka kwana kewaye da Angel har ruwa suka ƙara yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Sun yi kuka har sun gaji sun gode ma Allah, Mazan cikin su A zuƙunne suka kwana, Yadda su ka rana haka su ka dare.

Kafin safiya ta yi kowannan su ya fita hayyacin sa, babu mai iya motsa la66ansa yai magana acikinsu, zazza6i duk ya lullu6e su, Don shi Gabriel ma suman zaune yai, bawan Allah duk ya damu kan shi, ga matsanancin ciwon kai da ya ke fama dashi.

A cikin su mutun ɗayane hankalin shi ya ke akwance, majnun dake ta sharar baccinsa, ko daren jiya da Angel ta ke ta kuka za'a tafi da Danish bai farka ba, hatta jamima da ta kasance autar cikin su saida ta tashi daga bacci hada ita cikin waɗanda suka kwana zaune saman benan ɗakin su.

Tsawon lokacin babu wanda ya iya buɗe baki ya furta wata kalma, Jamima ce tai ƙoƙarin cewa"Bari naje na ɗebo ruwa a ƙara yayyafa mata asaman fuskarta" ba wanda ya kalle ta, miƙewa tai da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu, tun da ta shiga hankalinta yai matuƙar tashi ganin jinin Danish daya ɗiɗɗiga a saman floor ɗin ya bushe ƙamas, ɗago wa tai da sauri tana kallon Jikin ƙopar toilets ɗin da suke a jere guda uku, kafin ta tsayar da idonta akan ƙopar toilet ɗin da A kayi badaƙalar nan jiya, Jikin ta na kerma ta ƙarasa tare da turo ƙopar shi ta faɗa ciki, gabanta yai wani irin mugun bugu ganin uban jinin da Danish ya zubar a inda

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads