Header Ads
Showing 135001 words to 138000 words out of 287659 words

Chapter 46 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1820

Ads at the middle of Article

ba,

Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan Suka fuce daga Cikin ɗakin,

Ganin suna yunkurin zuwa saman gado su kwanta ne, yasa angel ta dakatar dasu, tace su motsa jikinsu, Idan sun kammala su watsa ruwa ajikinsu, Sannan Sun kwanta su huta, babu musu suka amsa mata da toh, banda danish da haris, tuni sun haye saman gadajensu, Shi haris damuwar rashin deeja ne yasa shi ƙin ta6uka komai, tunanin abunda ya faru daren jiya kafin atafi da ita ya tsaya mashi arai, Yaji tausayinta sosai, su kansu sauran ƴan uwan nasu sun damu da deeja, Ba yadda zasu yi ne shiyasa suka barma Allah komai,

A tsakiyar ɗakin suka Jera layi suna yin exercise, kamar wasan ƴar tseral haka suka dinga zubawa da gudu idan suka kai ƙarshen bango sai su dawo su sake komawa, Sai da suka tara uwar zufa ajikinsu tukunna kowa Ya nufi toilet domin watsa ruwa, Bayan sun fito ne, parveen ta matsa ma angel akan tayi mata irin kalabar da tayi ma su azeeza, Dama tun ranar da ta ganta ta kwallafa rai akan tana so itama, kafin marece yayi angel tayi ma parveen kalaba biyu akanta, ba ita kaɗai ba hada rubina tayi mawa, Bayan ta kammala musu kitson, Kowa Ya koma saman gadonshi ya zauna, Fira suka soma yi atsakaninsu acikin firar ne, suka tambaye ta, wai da tace musu wata rana zasu fita idan suka fita ina zasu je? Su da basu san komai na wajen kurkuku ba, murmushi tayi tare da cewa su kwantar da hankalinsu, Gaba ɗayansu zasu yi rayuwa agidan daddynta, Tace daddyna yana da gida, kuma gidanmu ɗaki Shida ne, Akwai palour ɗaya, dani da azeeza da batool zamu ware ɗaki ɗaya, Parveen da deeja da hanna zasu ware nasu ɗakin ɗaya, sai Eve da hibba da rubina suma zasu ɗauki ɗaya, nawa kenan? Suka ce mata Uku, tace toh, sauran ɗakunan guda uku, Javed da Naufal tare da Mubeen zasu ɗauki ɗaya, sai Haris shi da wancan Maji daɗin gadon suma zasu ɗauki ɗaki ɗaya," da ta ambaci maji daɗin gado hada harara ta wurga ma danish, ya lumshe idanuwanshi tamkar baiji me tace ba,

Azeeza tace"Saura ɗaki ɗaya ya rage, wa za'a bamawa" angel tace"Na daddyna ne idan Allah yasa yana araye, ko ince daddynmu" gaba ɗaya suka saki murmushin farin ciki, parveen tace"amma kina ganin daddynki zai so mu," angel tace sosai ma, In ma daddyn nawa baya araye, zamu zauna wurin auntyna adama ne, Ko gidansu aunty aneelerh na, zasu ɗauki nauyin duk wani abu da zamu buƙata, Cin mu shan mu da suturarmu, kuma zamu yi rayuwar ƴanci, Zamu je inda muke so, Muje shan ice cream, muje cinema kallo, hada shopping mall zamu dinga zuwa kowa ya za6i abunda yake so, " parveen na murmushi tace"Zamu dinga samun abinci akai akai"? Dariya angel tayi tare da cewa"Sau uku arana, za'a bamu breakfast, lunch and dinner, Idan ma kinga dama tsakar dare kika farga da yunwa zaki Iya zuwa kitchen ki girka abunda ranki yayi maki, " Gaba ɗaya suka sanya ihu suna murna jin tace zasu Iya girki da kansu, Ga kuma abinci available, A lokacin jikin angel yayi mugun sanyi, ganin yadda suke ta farin Ciki, gani take kamar bazasu rayu ba, balle aje ga maganar fita daga Cikin wannan Kurman kurkukun ƙaddarar,

Batool tace"wlh angel baki ji irin daɗin da naji ba, sai naji dama ace yau mu fita daga kurkukun nan, muje gidanku, kinga shikenan mun rabu da giants, bazasu ƙara zuwa su ɗauki wani acikin mu ba, balle har su cutar dashi,"

Azeeza tace"Nima na ƙosa inga ranar da zamu fita daga prison ɗin nan, wlh Ina so inyi rayuwa irin wadda ki kayi tare da daddynki, ae kince mana zai so mu, muma zai maida mu kamar ya'yanshi, zai dinga zuwa damu yawo yakaimu wuraren da kika bamu labari ko"? Angel tace"Eh, kuma koda ace babu daddyna, akwai sauran dangina duk zasu so ku, kuma zasu gatanta ku kamar ya'yansu ku," acikin zuciyarta tace"sai dai fitar ce keda wuya, bansan ya zamuyi ba, gidan kurkukun nan yafi ƙarfi na, sai dai bai fi ƙarfin mahaliccin mu ba,

Har dare Yayi suna fira Gwanin ban sha'awa, ta faranta musu sosai, Bayin Allah sun ƙwallafa rai da son yin irin rayuwar da tayi, wato rayuwar ƴan ci, yanzu a shirye suke da zarar sun samu hanyar fita zasu bita ne, hmmmmmm


*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*



Saboda daɗin fira yasa suka dawo bakin gadon angel kowa ya samu wuri a gefe da gefen gadon suka zauna waɗanda basu samu wuri ba daga ƙasa suka zauna, Javed hada ƙoƙarin ɗauko fitilun ɗakin guda uku Ya kunna a ƙasa ya ajiye su, ɗakin ya yi haske, sun ɗauki tsawon lokaci, sai da angel taga sun fara gyangyaɗin bacci, ta Katse masu firar tare da cewa"its time to sleep, Kowa Yaje ya kwanta, gobe in Allah ya kai mu da rai da lafiya zan ƙarasa baku labarin" suka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya kowa Ya miƙe suna tafiya suna bangaje juna a haka suka nufi gadajen su, har sun kwakkwanta Muryar angel suka ji yo tana cewa"Su yi addu'a kafin su kwanta" suka amsa mata da toh,

Danish yana lafe saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, amma babu alamun bacci yake yi, Gyara kwanciyarta ta yi, yau bata ju ya ma shi baya ba, suna fuskantar Juna,

Ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi yasa tayi saurin Fuskantar ceilling, tare da rufe idanuwanta, Sam bata ji lokacin daya sauko daga saman gadonshi ba, sai dai taji hucin numfashin mutun yana kokawa da Nata numfashin, da sauri ta buɗe idanuwanta, Tsabar firgitar da ta yi ne yasa ta zare ido, Ganin fuskarshi a kusa da ta ta, Saman gadonta Ya hau Ya yi mata rumfa da ƙirjinshi, ƙiris Ya rage tsinin hancin shi ya gogi nata, Tsananin mamaki ne Ya kamata, Tuni ta shiga ruɗanin kome zai yi mata, Gashi ya tsareta da idanuwanshi ko ƙyaftawa babu, muryarta na inda inda tace"La..fi..ya"!? Yace"haƙuri nazo na baki, ki daina fushi dani, tun jiya baki yi mini magana ba, Idan muka haɗa ido sai ki ta harare na," daƙyar yakai ƙarshen maganar throat dinsa na moving kamar yana swallowing ɗin wani abu, yana ganin ta fara yunƙurin motsa la66anta alamar zata yi magana da sauri ya ɗaura dogon yatsan shi saman ƙaramin bakinta, Cikin sanyin murya yace"Pls don't shout at me, Idan kinsan ba me daɗi zaki faɗa mini ba, Kiyi shiru kawai, nafa baki haƙuri, Kuma na gane kuskure na,"

Hawayen da ta gani kwance a cikin fararen idanuwanshi ne yasa taji zuciyarta ta karaya, sai ma taji tausayin shi yakamata, Shi dai haka rayuwarshi take, Yana da matuƙar saukin kai, ga haƙuri matsalar shi ɗaya ragwanci, hannu tasa ta kawar da yatsanshi daga saman bakinta,

Sai da ta fara jefa mashi harara, kafin tace"Zan yafe maka amma sai ka yi mini alƙawarin wani abu" yace"komene ne zanyi" ɗan ta6a baki tayi tare da cewa"kada ka ƙara bari a ɗauki wani daga Cikin mu, Saboda nasan kana da ƙarfin da zaka Iya hana wa" tunkafin ta karasa maganar, Yae saurin girgiza kai yana faɗin"That's impossible, ki fahimce ni, Ni ba kowa bane face prisoner, bani da ƙarfin da zan Iya yin fighting da giants, sunfi ƙarfina, idan ba so kike in rasa raina ba"

tsoki taja"hmmm dama nasan haka zaka ce, Idan har dagaske baka da ƙarfi, to ta ya akai ka ke Iya shiga toilet bayan na datse ƙopa ta Ciki? Kuma ya akai ka iya 6a66ako glass door ɗin dake acikin toilet, tun daga tushen shi, taya zan yarda da maganganunka? Ta yi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi, Har lokacin yana a yadda yake bai ɗago ba,

Runtse idanuwanshi ya yi, tare da biting lower lip ɗinshi, A hankali ya ɗan ware su akan fuskarta, Muryar shi arauna ce ya soma magana"Bansan ya zanyi in fahimtar dake ba Angel, Ni kaina bansan Ya akai nake iya shiga wurin dake a rufe ba, Also ƙarfin da yazo mini time dana cire glashin nan yanzu babu shi ajikinta...." kawar da kanta gefe tayi tare da cewa"Ban yarda dakai ba, danish Ina zargin kai ma Giant ne, kamai da mu shashasha kana 6oye mana ainihin wanene kai, Sannan kuma kasan Komai game da kurkukun nan, Amma kaƙi ka sanar damu, kafi so mu yi ta shan wahala har mu rasa rayukan mu, Kana ji kana gani ana cutar da rayuwar ƴan uwan mu amma kai hankalin ka kwance, Ko ajikinka.....' Kafin ta rufe bakinta, Taji saukar ɗigon ruwan acikinsu, da sauri ta kalle shi, Hawayen shi ne suka sauka cikin bakin ta, Yana girgiza kai yace"angel stop accusing me, am not a giant, Bana jin daɗin maganganun da kike gaya mini, its hurting my heart," Daƙyar Ya kai karshen maganar, wani irin raɗadi zuciyarshi ke Yi mishi, idan akwai abunda ya tsana Ya biyo bayan Giant, Yaji zafin Kalaman angel fiye da zafin marin da ta yi mi shi, ita kanta angel da ta yi maganar sai daga baya ta yi danasanin furta mashi zargin da take yi akanshi, bata ta6a ganin fushi akan fuskar danish ba, sai yau, Jikin shi har kerma yake Yi, wurin saukowa daga saman gadonta, da sauri ta mike xaune tana kallon shi, Ji take kamar ta kira shi ta lallashe shi, girman kai ya hana tayi hakan, Ta yi tsammanin zai kwanta asaman gadon shi ne, amma sai taga ya ɗauki pillown shi tare da bargonshi, bai nufi ko'ina ba sai cikin toilet area ɗinsu, duk sai taji ba daɗi, Ya rasa ina zai kwanta sai cikin toilet, In da madaddalar shaiɗanu suke? Dama Ya lafiyar giwa, har ta koma ta kwanta da niyar tayi bacci amma sai ta gaza runtsawa, Damuwa duk ta cika ta, a ƙarshe dai ta ji bazata Iya jurewa ba, ta miƙe Ta sauko daga saman gadonta, sai da ta fara zuwa gaban table ta ɗauko fitila ta nufi cikin sashen toilet ɗin, Tana zura ƙafarta Ciki, ta same shi a kwance saman shimfidar da yayi, hawaye ta ko'ina asaman face ɗinshi, ya lumshe idanuwan shi jin motsin mutun yasa shi ɗan buɗe idanuwan da suka canza launi, koda ya yi arba da ita sai ya ju ya mata baya, A ƙasa ta ajiye fitilar ta zauna gefen shimfiɗar tashi, Kusan mintuna tana kallon gefen fuskarshi, Daƙyar ta iya buɗe baki ta soma magana,

"Danish fushi ka ke yi dani? nayi nadama, da nasan kalamaina zasu 6ata maka ranka, da ban furta maka su ba, nima na faɗi ne kawai badan ina nufin hakan ba, " Babu irin lallashin da bata yi mishi ba, amma ɗan tahalikin nan yaƙi tanka mata, Muryarta a karye tace"Nagaji da lallashinka, Kaga Idan ma bazaka haƙura ba, to ka tashi mu koma ɗaki ka kwanta, Amma kwana a wurin toilet ɗin nan sam bai dace ba, Akwai shaiɗanun aljanu zasu iya cutar dakai,' sai lokacin yace"Meye damuwarki idan sun cutar dani? Jikin ki ko nawa"? Ta bashi amsa da cewa"Namu, saboda na damu dakai, dani dakai abu ɗaya ne, jinin dake yawo ajikin ka shi yake yawo ajikina, taya ɗan uwa zai share ɗan uwansa? Duk da nasan laifina ne amma na gane kuskure na na yin fushi dakai bazan ƙara ba," Bai ƙara tanka mata ba,

"Pls danish, mu koma ɗaki, " magiya ta dinga yi mashi amma yaƙi tanka mata, har ta fara tunanin ko ya yi bacci ne jin shiru, matsawa ta yi sosai kusa dashi, ta ɗan kwanto saman jikin shi tana leƙen fuskarshi, ya rufe eyes ɗinshi, kamar ya fara bacci, yanke shawarar ɗaukar shi ta yi kamar yarda ya ɗauketa jiya da ta yi fushi ta kwanta a ƙasa tsakiyar ɗakin su, Murmushi ta saki yayin da take nannaɗe hannun rigarta, tana kammalawa, ta soma kiciniyar ɗaukar shi, duk yana jin motsin hannayenta a bayanshi, wani irin nauyi ne dashi yadda kasan dutse, Ta tattara Iya ƙarfinta na ƙarshe ta ɗaɗɗago dashi, ta samu ta raba shi da saman bargon, tana ƙoƙarin Juyawa don ta nufi ɗaki dashi, wani irin nauyi Ya fisgeta, ba arziƙi ta sake shi ta rubza saman jikinshi, tana faman haki hana nishi kamar wadda tayi uban gudu, bawan Allah, kanshi ya bugu sosai, ba yadda ya iya, Jarabar angel tafi ƙarfin shi, har time ɗin bai buɗe idanuwanshi ba, bai kuma motsa ba, saboda nauyin jikinta dake asaman nashi, Babu alamun zata ɗaga shi, ta kifa kanta saman kirjinshi, sumar kanta duk ta tarwatse, slowly ya ɗan ware idanuwan shi, ya ɗaurasu akan sumar kanta, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta""An..gel" Ƙasa ƙasa ya furta sunan, bata amsa mashi ba. Kuma bata ɗago ba, ranshi ne ya bashi cewar kodai tayi bacci ne

Zagayo da hannayen shi yae saman bayanta, a wannan yanayin bacci ya yi awon gaba su, manne da juna,

A washe gari

Haris ne ya fara farkawa daga Bacci, Cikin buƙatar zuwa toilet, Saukowa Ya yi daga saman gadonshi ya nufi toilet yana hamma tare da yin miƙa duk a lokaci ɗaya, Zura ƙafar shi keda wuya ya yi arba da su angel dake a kwance saman bargon danish, sun ƙanƙame juna suna bacci, Yadda kasan tip da tyre, Tsabar mamaki ne ya kama dashi, har wani leƙen su yake yi don ya gane ma idonshi da kyau, hada sanya hannu ya ruƙe ha6arshi, can kuma sai ya saki murmushi, Mutumin da ke jin fitsari maimakon ya shiga toilet, Sai ya juya saboda gulmar data ciyo shi, Jikin shi har rawa yake Yi, wurin komawa cikin ɗakin, agaban gadajensu Javed, Yaje yana tashin su daga bacci, ɗaya baya ɗaya ya dinga tada su, Kowa Ya mike yana miƙa da hamma tare da tambayar shi lafiya? Yace musu Su zo suga wani abun ban mamaki, Koda jin haka jiki na rawa, Kusan atare suka sauko daga saman beds ɗinsu, lokacin da su batool suka shiga, Suna Yin arba dasu Danish manne da juna, Kowa Ya buɗe baki haɗi da zare ido, Kamar sun samu tv, A kewaye da shimfidar Suka zuƙunna suna kallonsu, Yayin da su masu baccin basu san wainar da ake toya ba,

Angel ce ta fara farkawa, A hankali ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, ras taji gaban ta ya faɗi ganinta ajikin danish, sam ta manta meya faru jiya, waro ido ta ɗanyi tare da sanya tafin hannunta ta rufe bakinta, Gyaran miryar Da haris yai mata ne yasa tayi wuff ta sauka daga saman jikin danish ta koma gefe ɗaya, Ta yi tunanin zata ga haris shi kaɗai amma sai ta gansu kaf ɗinsu kewaye dasu, Tawaga guda, sun baza na mazurinsu suna kallon Ikon Allah, Muryarta na in ina tace"Am..kun..gane..jiya..um" bata ƙarasa maganar ba, Batool tace"Ai mun riga mun gane komai ba sai kin yi mana bayani ba," azeeza tace"ƙwarai kuwa, Aljanu ne suka kawo ku nan, koba haka ba"? Ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu Hannah, har suna haɗa baki wurin cewa eh, wani kallon rainin wayau taga suna Yi mata, Kafin ta ƙara furta wani abu, danish ya farka yana kokarin buɗe idanuwanshi, Biji biji yake iya ganinsu, Haris yakai hannu ya bugi ƙafarshi"tashi ka yi mana bayani, meya faru a daren jiya," gaba ɗaya jikin shi kasala yake Ji, Yunƙurawa Yayi tare da miƙe wa zaune, a lokacin idanuwan nashi sun washe yana ganinsu, One by one ya dinga binsu da kallo, sai wani sakin murmushi suke Yi kamar sabbin mahaukata, ɗauke eyes ɗinshi yae daga kan fuskokinsu, Ya mayar dasu kan angel da tayi wuƙi wuƙi da ido, Suna haɗa ido dashi, ta fara zazzaga mashi masifa"Duk kai kaja mini ina zaman zaman lafiyata, Tun farko basai da nace Ka koma ɗaki ka kwanta ba amma saboda kafiya irin naka kaƙi jin maganata, Ka nace saika kwana anan, Ni banma yarda dakai ba, kaine ka janyo ni jikinka, har bacci ya ɗauke ni, saboda rashin tsoron Allah, gashi kaja min zunubi," tun da tafara faɗa suka zuba mata ido suna kallonta, Ita fa gani take kamar suna zargin wani abu, yayin da su kuma basu kawo komai aransu ba, saboda ilminsu bai kai nan ba, Abun ma burgesu Yayi, don su a wurinsu ba wani bane don mace ta haɗa jikinta dana namiji, sun saba ba tun yanzu ba, saboda haka suka taso suna rungumar junansu, abu ɗaya ne basu yi neman junansu, shima saboda basu da shauƙin sha'awa kwata kwata, an cire masu shi, amma fa suna ƙaunar junansu sosai, sai ma mutun ya yi tsammanin akwai soyayya asakaninsu, Alhalin nan kowa babu wannan aransu, Kawai ƙaunar juna ce,

"Angel ki daina ƴan kame kame, Mun riga mun san komai," harara ta jefa ma hanna da ta yi maganar tace"Me kuka sani? Idan ma wani abu ku ke zargi to shine ke da laifi ku tambaye shi ku ji,"a ƙule tayi maganar, shi dai baice komai ba, idonshi na akan fuskarta,

Parveen tace"danish ka faɗa mana gaskiyar abunda ya faru? Dagaske ne Kaine silar komai? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, saboda gudun jarabar angel,

Javed yace"Ni ban yarda ba, Nafi zargin Angel, Cos danish bazai ta6a kawo ki nan ba, sai dai ko kece kika biyo shi, wama ya sani ko faɗa ne ya haɗa ku, " miƙewa tsaye angel tayi"Ni kun ga tafiya, Ina da abun yi" Takai karshen maganar tare da Juyawa ta Nufi toilet ta buɗe ta shige, Jamlock ta sanya ta datse ƙopar, kafin ta le6e tana sauraron me suke cewa,

"Danish faɗa mana gaskiya, Meya faru daren Jiya a tsakaninku? Ya akai kuka baro ɗaki kuka dawo nan"? Batool ce ta jera mashi tambayoyin, angel dake la6e ta yatsina fuska aranta tace"Wannan batool ɗin sai kace ƴar jarida, ko ina ruwansu da abunda ya faru adaren jiya in ban da gulma da son jin kwakwaf mtsww"taja tsaki daga ƙarshe,

Tana Jinsu suna ta tambayarshi ya faɗa musu, Amma yaƙi basu amsa sai dai ce musu ya yi, ya manta komai, bazai iya tunawa ba, dole suka haƙura da tambayarshi, Ajiyar zuciya angel ta sauke, a fili

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads