Header Ads
Showing 204001 words to 207000 words out of 287659 words

Chapter 69 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1826

Ads at the middle of Article



tsakar dare Angel tafarka, ta dinga addu'a tana roƙon Allah akan yabata abun arzikin nan wanda yafi na Unaiza, hada ƴar ƙwallarta, itafa bilhaƙƙi so take itama su fito mata, ko dan saboda Danish ya daina kallon na ƴar gidan daddy, ya koma kallon nata,

ƙuruci dangin hauka🤣

tun lokacin da Danish ya ɗaukar mata alƙawari bai ƙara kula Unaiza ba, gashi ta nace mashi, ko toilet ya shiga sai ta bishi, idan yana bacci sai dai yajita a jikinshi tana lalubarshi, ta zamar mashi masifa, Da angel ta lura da hakan saita koma tana bashi kulawa ta musamman, Ta sanya mishi ido sosai, Idan suna cin abinci unaiza tana kashe mashi ido, sai angel tace mishi ya tashi ya koma saman gado zata kawo mishi abincin shi yaci acan, da yake yana son farin cikin ta, ga kuma alƙawari da aka yi mishi na abubuwa idan sunfito, shiyasa yake bin umarninta sau da ƙafa, idan dare ya yi zasu kwanta bacci, Angel bata runtsawa gefen gadonshi take zama tana bashi labarai masu daɗi har sai bacci ya ɗauke shi, kafin ta koma tana Yin addu'o'inta na dare da saba yi, Idan ya tashi zuwa toilet da kanta take raka shi ta tsaya abakin ƙopar har sai ya kammala ya fito tukunna su ke komawa ɗaki atare, hakan ba ƙaramin ƙona ma Unaiza rai yake yi ba, angel ta toshe duk wata ƙopa da zata haɗa ta da Danish, taƙi samun yarda take so kamar tayi hauka, yarinyar ba ƙaramar jarababbiya bace, Idan abun ya motsa da kanta take Amfani, Saboda tsabar shaiɗanci, hatta su Haris saida taso su bata haɗin kai, a ƙarshe taci ubanta hannun Naufal, saboda bai ɗaukar raini, Ta addabi rayuwarsu, Wani sabon shaiɗancin saita koma tana binsu Azeeza tsakar dare saman gadajesu, tun arana tafarko data fara yi musu hakan suka tarar mata, dama angel ta faɗi musu cewa mayyace kuma idan suka bari ta ta6a jikinsu to zata shanye musu Jinine har sai sun mutu, tsoro ya kamasu, shiyasa aranar su kayi mata bugun mutuwa, a ƙarshe suka kulleta Cikin toilet, Ta dinga kuka tana faɗin su buɗe mata ƙopa bazata ƙara ba, amma suka ƙi buɗe ta, babu ci babu sha Yinin ranar, sai tsakar dare ne suka je suka buɗe mata ƙopa, a ƙasa suka sameta kwance tana fitar da numfashi sama sama, Angel ta ciko bokiti da ruwa suka sheƙa mata shi a jikinta, sharkaf su ka jiƙa ta, ta dai ci baƙar wahala awurinsu, dama masu lallashinta haris da Danish ne to duk sun fita sabgarta, shiyasa su angel suka samu damar koya mata hankali, Sai gashi tafara yin hankali ta koma tana jin shakkarsu, bata ƙara gigin ta6a wani acikinsu ba, Sai dai har yanzu bata daina yi musu gorin ƙirji ba, idan rashin kunyar ta motsa haka zata dinga yada musu habaici acikin ɗaki babu mai tanka mata, kuma duk da haka bata hakura da Danish ba, dama kawai take jira da zata ke6e dashi.

idan muka koma 6angaren Majnun, Babu abunda ya sauya, Mahaukaci ne na gaske, 6arnar daya ƙara yi musu wadda ta gigitasu, Aranar sun taru aɗaki Gabriel Yana koya musu rawa, da yake ya iya sosai, Ba ƙaramin daɗi suke Ji ba, sun dage suna ta tiƙar rawa iri iri, Ashe Yaron nan Ya gudu Zuwa toilet ɗinsu bai nufi ko'ina ba, Sai Wurin tukunyar fulawar nan, Yasa Hannu Ya tsige furen Batool dana daddynta, Hada Na aneelerh, ba zato ba tsammani sai gashi ya faɗo ɗakin hannun shi ruƙe da su Yana Faɗin Wai su kalli Ya curo musu shukokinsu, hankalin su yae matuƙar tashi, musamman angel, gani suke kamar ya kashe rayukan masu Furennin ne, ransu ya 6aci sosai, da gudu suka nufe shi da niyar su buge shi, da sauri ya juya shima ya watsa a guje Ya shige Cikin toilet ɗin, da yake mahaukaci ne, Ya buɗe murfin trash can ɗinsu, Ya faɗa ciki ya 6oye yana haki, gudun kada su buge shi, koda su ka shigo basu same shi ba, kuma ba su yi tsammanin ya 6uya acikin abun zuba sharar ba, Kaf suka bincika kowani sashe na toilet basu gan shi ba, Danish ya basu haƙuri akan su ƙyale shi, yace musu ae ba wani abu bane don ya cire furen zai iya fitar da wani tsiran, jin hakan yasa hankalinsu ya kwanta aranar saida ya sake tsuro wasu flowers ɗin masu kyau, sak irin wanda Majnun ya cire musu, sukai ta murna sam sun manta da yaron nan, Ashe bayan ya shige cikin trash can ɗin Bacci ya ɗauke shi, ga bola duk da babu wani abun datti sosai 6awon kayan marmarin da suke sha ne wani harya fara ru6ewa, Har dare yayi babu chinonso, Hankalinsu yaƙi kwanciya, Suka soma nemanshi saƙo da lungu har ƙarƙashin gado, har toilet suka koma neman shi tsakar dare amma basu ganshi ba, saboda su ba son cewa ana Iya cire murfin abun zubda sharar ba, shiyasa ba su yi tunanin yana aciki ba, Arufe saman shi yake sai dai ƴar ƙopar da za'a zubar da shara ciki, da suka gaji da neman shi ɗaki suka koma kowa ya kwanta, tsakar dare Chinonso Ya farka daga bacci, ya ganshi acikin trash can, Yasa hannu zai ɗage murfin yaƙi curuwa, Ya dinga kurma ihu yana faɗin su zo su taimake shi, dodonni zasu cinye shi, babu wanda ya iya jinshi saboda sun nutsa cikin baccinsu, Tun yana kuka da ƙarfi har muryarshi ta disashe, Hada fitsari ya saki aciki, Jikin shi duk zufa, sai kerma yake yi, wani irin tsoro ne ya mamaye shi, saboda bai ƙaunar duhu, saboda sun manta basu kunna ƙaramar fitilar dake acikin toilet ɗin ba.

bari dai in taƙaice mu ku zance sai da Chinonso yae kwana biyu acikin Abun zuba sharar nan, basu san dashi ba, ba komai yajawo hakan ba face rashin kawo musu fruit, dama shine ke kaisu zubda shara acikin trash can ɗin, Aranar da zai Cika kwana Uku cuf aka kawo musu fruit, Bayan sun gama Cin abinci Parveen ta tattara 6awon taje zata zubda, sai da ta tsaya ta lashe na lashewa, Don har 6awon wani lokaci tana Ci, Bayan ta gama ɗan kingin da ta rage irinsu 6awon lemu da bata sha, ta buɗe murfin zata zubda nan take idonta suka sauka akan hurhurar gashin kan Majnun, Ya sandare aciki Ya ƙame, babu alamun yana motsi, wata irin gigitacciyar ƙara tasaki saboda ta tsorata sosai, Da gudun gaske su Angel suka faɗo ɗakin suna tambayarta lafiya hannunta na kerma tadinga nuna musu abun zuba sharar tsoro yasa kowa yaƙi zuwa ya duba, Sai da Azeeza taje ta kira Danish Ya taso daga saman gadon shi, ya shigo toilet ɗin Ya buɗe murfin trash can ɗin, yayin mamakin ganin yaron nan, Hannu biyu yasanya ya tsamo shi daga Ciki ya sauke shi ƙasa, yaji jiki kuma idonshi biyu amma baya motsi, ko magana ya kasa, Jikin shi sai wari yake yi, gefen bakin shi hada 6allin ganyen furennin daya cinye lokacin da yunwa ta addabe shi, ' Su parveen sun sha mamaki, Wai harya iya buɗe murfin gaba ɗaya ya shige, kuma ya maida murfin Ya datse amma Ya kasa fitowa daga Ciki.

Ba tare da 6ata Lokaci ba, Hanna da hibba suka taimaka wurin cire mashi kaya, Yasmin ta kar6a tasa abokiti ta wanke mishi su, Wankan tsarki su kayi ma jikinshi, da sosa da sabulu suka wake shi, Bayan sun gama Aka ɗauko bargo ɗaki suka ƙudundune shi aciki, suka kaishi ɗaki saman gadon shi, Allah yaso sun rage sauran abincinsu da aka kawo musu, Yana daga kwance suka dunga cusa mashi abaki daƙyar yake wuce wa, Sai da yaci ya ƙoshi cikin shi yae ƙato, tukunna ya dawo hayyacin shi, ya fashe musu da kuka yana faɗin wai basu ƙaunarshi yana ta kiran sunansu akan suzo su taimake shi amma suka ƙi zuwa,' dariya kamar zata kashe su, parveen tace ashe kasan sunayen mu? Nayi tunanin baka sani ba, Cikin shessheƙar kuka yace"nasani mana, ba wanda bankira ba, hada Angel da danish da hanna, amma kuka ƙi zuwa, dodo yae ta tsorata ni" saboda tsabar dariya hada dafe ciki, Tun da suke dashi bai ta6a nuna yasan fuskokinsu ba balle sunayensu, Amma yau ya zaƙe yana zazzaga musu masifa, tass saida ya lissafa musu sunayensu, Sun sha mamaki, Angel hada yi mishi nasiha akan ya daina rashin ji da 6arna, ya dinga kwanciya saman gadon shi yana bacci, kamar mutumin kirki ya amsa mata da toh, suka ce to ya kwanta, yanzu, Batare da yayi musa ba, Ya gyara kwanciyarshi, sai gashi bacci ya ɗauke shi, hakan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba, duk da sunsan zaiyi wuya ya daina 6arna tunda abun daga kwakwalwarsa ne.


💋PRISONERS💋


Kwakkwance suke saman gadajensu, Sarah kaɗai ce kwance a ƙasa ta shimfiɗa bargonta kamar yarda ta saba.

Mutun ɗaya ce ta rage acikin ɗakin idonta biyu, sam ta kasa runtsawa sai juyi take yi saman gadonta, tarasa meke mata daɗi acikin duniyar nan, komai ya tsaya mata cak, babu alamun zata runtsa a daren yau, Yayin da take fuskantar ceilling, Jikin ta na asanye da tsoffin uniform ɗinta da suka maida kayan baccin su, ɗakin nasu yayi tsit sai sautin minsharin masu bacci, basu kashe hasken floor lamps ɗinsu ba, Saboda yau majnun bai yi musu haukan dare ba, tun da suka tsamo shi daga cikin trash can suka lalla6a shi ya kwanta bacci ya ɗauke shi, Har dare bai sauko daga saman gadon shi ba, Ya ji jiki da alama.

Kamar an tsunkule ta, ta zabura ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa da sauri sauri, sakamakon tunawa da ƴar uwarsu batool da ta yi, zuciyarta sam ba daɗi, sai yanzu ma take jin haushin damuwa da tayi akan ƴar gidan daddy, Sun saki jiki suna ta rayuwarsu batare da sun ta6uka komai ba, akan ƴar uwarsu.

Saukowa ta yi daga saman gadonta, ta ɗaura eyes ɗinta akan shimfiɗar Danish, Ya rungume pillow abun shi sai sharar baccin sa yake yi, Cikin sanɗa ta nufi tsakiyar ɗakin tana tunkarar sabbin gadajen da su parveen suka gaje, don har yanzu basu daina kwana saman su ba, tun ranar da aka kawo su Jamima, aka koma da mutun goma, su ka ci gaba da kwana saman su, Mutun biyar ne ba su kwana saman tsaffin gadajensu, Ita da Danish sai haris da Deeja, da kuma naufal, Amma sauran kowa ya samu sabon gado.

Agaban gadon Unaiza ta tsaya tana kallon wani sabon salon kwanciya, ta tura hannayenta cikin short ɗin jikinta, saboda jaraba Cikin bacci tayi wurga da bargonta ƙasa, Tana numfashi boobs ɗin ta na yin sama da ƙasa, Ta6e baki angel ta yi, Ji take kamar ta sanya hannu ta maida su cikin ƙirjinta su shafe, A nemesu arasa, ko sun huta da guyabarta, " Guntun tsoki taja tunawa da abunda ya taso da ita daga saman gadonta, da sauri ta nufi ƙopar shiga sashen toilet ɗin su, bakomai take son gani ba face furen batool tana so taga awani hali yake ciki, Tana ƙoƙarin shiga toilet ɗin taji motsin shigowar mutun ta bayanta, a firgice ta juya don taga wanene, lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya ganin Danish ko me ya tada shi daga bacci, rayawa tayi aranta may be yayi tsamanin zata ƙara dura tagar ne shiyasa yabiyo bayanta.

Harara ta shiga jefa mashi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi, red vest ɗin Jikin shi ta fiddo mashi da hasken fatarshi sosai, Idanuwanshi da alamun bacci acikinsu,


"Halan Ka biyo ni ne don kaga me zan yi acikin toilet? in banda sa ido, mutun na jin bacci amma ya kafe sai ya takura rayuwar wani, ni nasan saboda ni kazo nan" ta yi maganar tana murgaɗa mishi ƙaramin bakinta.

Bai tanka mata ba har sai da ya tako zuwa gabanta ya tsaya ya ɗan duƙo da kanshi saitin fuskarta, Cikin Cool voice ya furta mata"abunda kika faɗa gaskiya ne, Saboda ke nazo nan" ta6e mashi tausasa la66anta tayi tare da cewa"Kasan dai baka isa ka hana ni yin abunda na yi niya ba, zaifi ka daina wahalar da kanka akaina" ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, ganin yadda take mishi magana tana jifar shi da harara hadi da murguɗa mishi baki, a ƙarshe ma taja mishi tsoki ta juya zata shige toilet, da sauri ya damƙo damtsen hannunta ya dawo da ita jikin bango yayi mata rumfa, mamaki ne ya kama ta, Ta zuba mishi ido tana jiran ganin me zai yi mata.


"Saboda na damu dake ne shiyasa na biyo bayan ki ba don wani abu ba" yatsina fuska tayi tare da cewa"Ni ban damu da kai ba don haka kaima ka daina damuwa dani, pls ka koma ka kwanta ni ka bani hanya in wuce ka na 6aramin lokaci" Hada bubbuga ƙafa irin ya takura ta ɗin nan,

Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba,
"Kince ba ki damu dani ba, but why kike hana idonki bacci don ki roƙi Allah akan ya baki abunda zai faranta min raina"! Har saida gabanta ya faɗi jin abunda yace, wani irin kallo ta soma binshi dashi, gaba ɗaya ya kashe mata ba."

Daƙyar ta iya buɗe baki tace "Danish kana nufin duk time da nake farkawa tsakar dare ina addu'a idon ka biyu? why ka sanya min ido, ko time dana ɗaukar maka alƙawarin na faɗi ne kawai don in kawar maka da tunaninka akan wancen yarinyar, kuma ni nayi hakanne gudun kada ta 6ata maka tarbiyar ka, saboda Nifa basa burgeni, bata su nake ba" tana magana tana hura hanci, Hannu yasa yaja tsinin hancinta tare da cewa"Nafa san me nake yi angel, ki daina ƙoƙarin nuna kamar ba donni kike yi ba, kina 6oye min irin ƙaunar da ki ke yi min," ranta a6ace tace"waya ce maka ina ƙaunarka ni? To wai ni akan me ma xan yi addu'ar Allah ya bani su...." ya bata amsa da cewa"Saboda inaso" fuskarshi a ɗaure ya bata amsa, kamar tasa hannu ta shaƙe wuyanshi haka take ji, muryarta a fusace tace"Dallah ni bani wuri na wuce, kunnuwana ba zasu juri sauraran waɗannan kalaman naka ba,"

tana ƙoƙarin janye shi don ta wuce yae saurin cewa"Its okey, kin bani damar in cigaba da kallon nata kenan"? Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a,

"nifa bance bazanyi bane, maganarce ke bana so," ta faɗi hakan tare da sanya hannayenta ta ture shi gefe, Ta nufi ƙopar shiga toilet, har ta kusa shiga sai kuma ta ɗan dakata da alama wani abu take tunani ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace"Ni abunda ban fahimta ba, me zakai dasu da kake son su fito min? Ka san dai bana manya bane, Na jarirai ne, don haka ka daina murna, iya kallo ne shima ba koda yaushe zan bari kana kallan min abuna ba, da zarar Mun rabu da unaiza, zan haramta maka ganinsu," ta ƙarasa maganar tare da faɗawa cikin toilet din hada sanya jamlock ta datse ƙopa, ta kifa kanta jikin ƙopar tana

Kanga kunnuwanta ta yi ajikin ƙopar don taji idan yana nan ko ya tafi, ba zato ba tsammani taji saukar hannun shi saman bayanta, a firgice ta juyo tana kallon shi, Yayin da shima yake kallonta, Ba ta yi mamakin ganin shi acikin toilet din ba tun da ba yau bane rana tafarko da ya fara Yi mata irin hakan ba, runtse idanuwanta tayi tare da bubbuga ƙafa tace"Nashiga uku! Wai meye ruwanka dani ne eye? Ba mun shirya ba, kuma nace maka nima zanyi irin nata to me kuma kake so"? Fuskarta a hautsine tayi mishi maganar, wani irin kallo yake binta dashi idanuwanshi kamar zasu lumshe saboda baccin da yaje ji,

"Angel, kin ɗaga min hankalina why zaki ce wai na jarirai ne, menene haka ba daɗin ji, kuma kince da zarar mun rabu da unaiza shikenan ko kallon su ma bazan ƙara yi ba, Ni na yi tsammanin duka zaki mallaka min su, tun da donni zakiyi su, idan kika min hakan baki min adalci ba," muryarshi asanyaye sautinta ke fita, Lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, har wani zazzare mashi ido take yi don ma yasan cewa ba wasa take yi ba, a cikin zuciyarta kuwa tunani take yi Anya Danish bai da ta6in hankali? Taya zai tsareta akan abunda ma basu da tabbacin zasu fito ko ba zasu fito ba.

"Kin yi shiru baki ce komai ba"? Muryarshi ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, Ganin yana ƙoƙarin dagula mata lissafi yasa ta ruƙo hannun shi acikin nata, Tace mishi"muje mu kwanta," bata jira amsar shi ba, ta buɗe ƙopar toilet ɗin, taja shi suka fuce har zuwa cikin dakinsu, Abakin gadon shi ta tsaya tare da kallon shi tace"nasan damuwarka, yanzu mu kwanta mu yi bacci, zamuyi magana zuwa gobe" ba don yaso ba ya ƙyale ta ya hau saman gadon shi ya kwanta itama ta wuce nata gadon ta haye, tana faman sauke ajiyar zuciya, ganin yana kallonta yasa ta janyo bargo ta rufe har kanta, lumshe idanuwanshi yae tare dajan nashi bargon ya lullube jikinshi, kowannansu da abunda yake saƙawa acikin ranshi, gani take kamar akwai shaiɗanu ajikin danish, waɗanda ke sanya shi yana yin abubuwa, Da farko yace yana son yi mata wanka yasa naci taƙi amincewa yanzu kuma so yake ƙirjinta sun fito ko uban me zaiyi dasu, Anya kuwa Danish bada biyu yake yi mata wasu abubuwan ba? Ta fara kokwanto akanshi, da wannan tunanin bacci yae awon gaba da su.

A washe garin ranar, majnun ne ya farkar dasu daga bacci, Tun da ya farka daga bacci ya sauko daga saman gadonshi yana miƙa da hamma, ya nufi gadajensu ɗaya bayan ɗaya ya dinga bubbuga ƙafafuwansu, yana faɗin su tashi ayi wasa, One by one su ka soma farkawa idanuwansu a kumbure fuskokin su duk a yamutse an sha bacci, su parveen hada miyan bacci a gefen baki, sun ji haushin tada su da ya yi, sai faɗa su ke yi

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads