Header Ads
Showing 81001 words to 84000 words out of 287659 words

Chapter 28 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1819

Ads at the middle of Article

zakuyi mun magana ba? wlh duk ranar da wani ya kuskura acikin ku, Ya furta koda kalmar A ce, zan gano ko wanene shi koda bansan shi ba, idan har naji muryarshi awani wuri zan shaida shi ne, saboda Allah yayi mun baiwar tantance muryar mutane," A zafafe takai karshen maganar, ga yunwa tana ji amma taƙi zuwa taje taci abinci,

Ruƙe qugu tayi"meyasa baku dawo mana da danish ɗin mu ba? ina kuka kai mana ɗan uwan mu? Tsohuwa tace kune kuka zo kuka ɗauke shi"? Tayi maganar tana faman haɗiyar yawu,

Aiki fa ya ga angel , ita kaɗai sai sambatu take yi kamar wata zautacciya,

Ganin taƙi zuwa taci abinci Yasa batool taje ƙarƙashin gadonta, ta ɗauko kwandonta, ta kwashe ragowar sauran abincin da suka Ci, da niyar ta ajiye ma angel da haris,

"Giants we are done," Javed ne ya sanar dasu, yayi hakan ne don su samu su tafi, kafin angel takaiga ƙure su, don in suka fusata, komai zasu iya aikatawa,

Ta gefen angel suka bi suka wuce, Tattara kayan Abincin su kayi a jera suka nufi benan, Ganin zasu tafi basu bata amsar tambayarta ba, yasa ta watsa da gudu ta riga su hayewa saman benen, a jikin ƙofar ta jingina bayanta tare da ware hannyenta, wato ta toshe masu hanyar sa zasu bi su fuce,

Tsayawa su ka yi a tsaye saman matattakalar benan, tunda suke aiki a prison ɗin, basu ta6a ganin hatsabibiyar yarinya irin wannan da take agabansu ba, da ace tasan irin hatsarin dake gare su da bata yi gigin shiga huruminsu ba,

Kallon kallon aka soma Yi atsakaninta angel dasu giants, Hankalin su Batool yayi matuƙar tashi, duk suna a tsaye bakin benan sai roƙon angel su ke yi akan ta matsa ta basu hanya su wuce, ba iri magiyar da basuyi mata ba, amma angel ta maƙe kafaɗa akan bazata matsa ta basu hanya ba, Ita so take taga ikon Allah Shin giants zasu Yi mata magana akan ta basu hanya su wuce ko kuwa"?

Cikin muryar fushi haris Yace"wai ke baki da hankali ne? Ba zaki matsa ki basu wuri su wuce ba? an faɗa maki basa magana, idan ma abunda kike ma hari kenan," rai a6ace tace"babu ruwan kowa dani, ku kama harkar gaban......."

bata kai ƙarshen maganar ba, Taga ɗaya daga Cikin giants ɗin ya miƙa ma na gefenshi Kayan abincin dake a hannunshi, Ya kar6a ya haɗa dana hannunshi, Zuba ido tayi tana jira taga me zasu Yi mata, wani irin zazzafan taku giant ɗin yayi yadda kasan Zaki Ya nufi abun harinsa, tuni jikin angel ya soma kerma, ta ƙanƙame jikinta tana girgiza mashi kai, muryarta na kerme ta shiga faɗin"wlh kada ka kuskura ka ta6a....."bata kai ƙarshen maganar ba, Taji ya damƙi qugunta ya ɗaga ta sama, yadda kasan ƴar tsana, ta dinga ihu tana kuka tamkar ranta zai fita, saukowa da iya yayi daga saman benan, Su batool duk sunyi tsuru tsuru suna kallon shi,

Daga inda yake yayi wurgi da angel Wani iko na Allah, Saboda tsabar iya saitinsu, bata faɗa ko'ina ba sai saman gadonta, gaba ɗaya ta kife sumar kanta duk ta tarwatse saman mattress ɗin, Juyawa Giant ɗin Yayi ya koma inda sauran ƴan uwan nashi suke, buɗe ƙopar su kayi suka fuce tare da datseta,

Kusan atare su Azeeza suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa suka nufi angel, wadda tunda giant ya wurgar da ita saman gado bata ƙara motsi ba,

Jikinta gaba ɗaya ya mutu, tamkar wadda aka zarewa laka, Ta furgita sosai lokacin Daya jefar da ita, har wasu baƙaƙem turari masu wutsiya ta dinga gani acikin idanuwanta,

Hayewa saman gadonta, Batool hanna da azeeza sukayi, Sai kokari suke yi wurin ɗago da ita,

Su javed mubeen da Su Deeja duk suna a kewaye da gadon,
"Angel,angel.pls wake up! dan Allah ki tashi angel, Muna atare dake Kinji?
Suna magana suna jijiga jikinta, Haris yace"laifinta ne, tun farko saida muka gargaɗeta amma saboda taurin kai irin nata taƙijin maganarmu, yanzu wa gari ya waya " yayi maganar Cikin halin ko'in kula,
Eve tace"bari naje na fada ma tsohuwa, azo a duba lafiyar jikinta" da hanzari ta juya ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa, Kafin ta kwankwasa ƙopar ɗakin sai ga tsohuwa ta buɗe ta fito hannunta ruƙe da sanda,

"Meke faru wa ne yara"? Her voice was shaking tace"an...gel...ce
.....bata motsi...'
"Keep calm and tell me what's wrong, with her? is she not feeling well?

Jinjina kai Eve tayi"Giant ne ya wurgar da ita, Tun ɗazu muke akanta, bata farka ba, ko motsi ba ta yi"

Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kan tsohuwa suna jira suji amsar da zata basu,

Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tare da cewa"Yarinyar ce taci ka kafiya, sam bata jin magana, shiyasa bana so kuna yin koyi da ita, domin kuwa zata 6ata maku tarbiya ne, tun tana yarinya ba ƙaramar hatsabibiya bace......." gaba ɗaya tsohuwa ta takwashe tarihin rayuwar angel ta sanar dasu, hatta bugun da tasa ƴan ƙato da gora su kayi ma Mahaifinta, kuma a ƙarshe tace masu itace silar da mahaifinta ya rasa ranshi,' da alama tsohuwa tana ƙoƙarin dasa masu kiyayyar angel acikin zuciyoyinsu ne, gaba ɗaya sun saki baki galala suna kallonta,

Batool ce tayi kokarin cewa"Amma angel ta faɗa mun cewa daddynta wasu ne suka kashe shi, kuma shine ya jefa ta Cikin ruwa, " bazawarin murmushi tsohuwa tasaki tare da girgiza kai tace"Ƙarya take yi maku, muguwar makirace, Ta faɗa maku hakanne don ku tausaya mata ba"

Aruɗe azeeza tace"amma angel bazata ta6a yi mana ƙarya ba, saboda tana son mu dagaske, Kuma idan bazan manta ba, lokacin da aka kawo ta kurkukun nan, kefa da kanki kika ce zaki faɗa mata waɗanda suka kashe mahaifinta, meyasa yanzu kuma zaki ce mana itace tayi silar mutuwar shi!"? Cike da tuhuma azeeza ta jefa mata tambayar, sam tsohuwa batayi tsammani wani daga Cikinsu zai iya yi mata gaddama ba, tabbas an fara samun matsala,

"Kinyi shiru baki bamu amsa ba tsohuwa? Kodai azeeza tayi gaskiya ne?
Lamarin yayi matuƙar ɗaurewa tsohuwa kai,
Javed yace"Nima idan zan Iya tunawa keda kanki tsohuwa kika ce Iyayenta sun rasu, hakan na nufin ita kanta angel ɗin batasan cewa iyayen nata sun rasu ba, sai a bakin ki taji hakan, But why kike kokarin ɗaura mata laifin kashe Daddynta? anya kuwa tsohuwa?ya kai ƙarshen maganar da alamun kokwanto,
Haris dai ya rasa bakin magana ba, hatta sauran duk sun natsu suna jiran amsar da tsohuwa zata basu,

Rai amatuƙar 6ace, tsohuwa ta buga sandar hannunta kasa, Nan take kowannan su ya toshe kunnuwanshi, sakamakon sautin buga sandar daya doki dodon kunnuwansu,

Da kakkausar murya tace"Zan sake maimaita maku, Kudaina yarda da maganarta, Ni kaɗai ce na isa da ku, Babu wani mahaluƙin daya isa ya sarrafa tunaninku, Ina fata an fahimce ni" Da sauri suka amsa mata da toh,
Cigaba da magana tayi"Angel ba sonku take yi ba, sam bata ƙaunarku, tana so ta shiga tsakanina daku ne, Ni kuma bazan bari hakan ta faru ba, saboda bana so ta gur6ata ku kamar yadda take gur6atacciya" A ladabce suke amsa mata da toh, deeja tace"Amma idan muka ce zamu ƙi bin Umarninta, Zata karanta mana charman dudu ne Cikinmu ya kumbura, shiyasa muke jin shakkarta",

Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta saki aranta tace"Yarinya sai ɗan banzan wayau uwa dila agari" a fili kuma tace masu"Charman dudu ba wani mummunan abu ne, Angel tayi maku wayau ne don ta tsoratar daku, Saboda ta lura bakusan ainihin ma'anar kalmar ba" cike da mamaki suke kallon Juna, Jin abunda tace, Batool tace"zamu iya sanin ma'anar Kalmar"?
Jinjina kai tsohuwa tayi, Cikun hikma ta fayyace masu komai game da asalin kalmar charman dudu, har waƙar ta raira masu, ' ransu ya 6aci sosai, irin yadda angel ta azabtar dasu da kalmar ashe ma waƙa ce ba abun cutarwa ba, sunji haushi sunji takaici, musaman haris da Deeja,

"Daga yanzu, Ku daina yarda da duk wani abu da zata faɗa maku, saboda wayau ne da ita, so take ta burkita maku lissafi" acewar tsohuwa,

Parveen tace"Amma tsohuwa menene ma'anar Sunan Allah dakuma Bil'adama? Angel tace mana Allah shine Ya halicce mu dagaske ne"?

Har saida tsohuwa ta zabura jin tambayar da parveen tayi mata, Lokaci ɗaya kuma ta murtuƙa fuskarta tare da cewa"Shima duk ƙarya take Yi maku, babu wani Allah, idan harta ƙara matsa maku akan Ku yarda cewa akwai Allah, Ku sanar da ita cewa Ta kira maku shi ku ganshi da idonku, Kafin Ku yarda dashi anan zaku tabbatar da cewa ita ɗin babbar maƙaryaciya ce," takai ƙarshen maganar fuskarta ɗauke da wani irin munafukin shu'umin murmushi, irin na tantiran ƴan duniyar nan waɗanda suka ga jiya suka ga yau,

Aka ce rashin sani yafi dare duhu, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar tsohuwa,

Ganin taci galaba akansu yasa ta Juya tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, Tare da jan ƙopa ta datse,

Abunda ya faru tun lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, gaba ɗaya Tunaninsu ya canza, daga gardamar da suke yi mata zuwa bin umarninta, yanzu gaba ɗaya sun ɗauki maganarta, aransu duk sunji sun tsani angel saboda ta kashe mahaifinta, tsoronta ma suke Ji yanzu kada suma ta kashe su, ga haushin ƙaryar da tayi masu na Kalmar Charman dudu da take yi masu barazana da ita, jira suke tafarka suci ubanta, Bayan wannan kuma tayi masu ƙaryar cewa akwai wanda ya halicce su, lallai angel tana a tsaka mai wuya fidda ta sai ALLAH,

Ta yi matuƙar karya masu zuciya, Jikin su duk yayi lakwas tamkar an zare masu laka, tafiya suke yi kamar mashayan giya, Idon kowa na akan gadon angel dake kwance magashiyan rai hannun Allah, Ji suke kamar su rufe ta da bugu har saita gaza tashi,


Komawa su kayi saman gadajensu Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar 6acin rai, Kowa ya shiga faɗin Laifin da angel ta aikata mashi da kuma irin fansar da zasu ɗauka akanta idan ta farfaɗo, don sunci alwashin sai sun raunata Sassan Jikinta,


Tsawon awanni angel ta ɗauka, Ba ita ta ta shi farkawa ba, Sai Wuraren marece, Da wani irin yunƙurin amai ta farka, da gudun gaske ta duro daga saman gadonta, idanuwansu akanta babu wanda yayi yunkurin zuwa ya taimaka mata,

Toilet ta shige a galabaice Ta zuƙunna gaban tap tana kwarara amai, bakomai ke fitowa daga Cikin bakinta ba, face xallar ruwa, Cikinta sai tuƙuƙun azaba yake yi mata, har wani jiri take Gani, Cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan Batool don tazo ta taimaka mata,

Batool tana jin muryar angel cikin mawuyacin hali amma zuciyarta ta hanata zuwa inda take, Kowa haushinta yake ji, An canza masu tunaninsu, hatta azeeza da tafin kowa jin tausayi ayau itama ta juya ma angel baya,

Koda taji batool bata amsa mata ba, sai ta shiga kiran sunayensu ɗaya bayan ɗaya, suna jinta amma su kayi kunnan uwar shegu da ita,

Numfashinta sama sama yake fita da hucin zafi, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai, hakanan ta dinga jin kamar wani abu zai faru da ita, dakyar ta samu aman ya dakata da zubowa, ta kunna tap ruwa ya shiga kwararowa, Ta tarba tafin hannayenta, ruwa ya taru acikinsu, ta kuskure bakinta tare da wanke fuskarta,

Sam takasa ta6uka komai, saboda tashin zuciyar da take ji, Ga jiri da take gani acikin idanuwanta, temperature ɗin Jikinta yayi zafi sosai da alama zazza6i ne ke shirin yi mata mugun kamu, tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa cos she's feeling dizzy idan ta yi attempting miƙewa tsaye,

Bata fasa neman ɗauki daga wurinsu ba, Taci gaba da ambaton sunayensu"Batool! Azeeza! hibba" muryarta a disashe take maganar daƙyar ma take ƙoƙarin ɗaga muryarta, Jin basu amsa mata ba, yasa ta soma kiran sunayen mazan dake acikinsu

"Javed! Mubeen! Naufal!' nan ma taji shiru basu amsa mata ba, lumshe runannun idanuwanta tayi tare da cizon lower lip ɗinta,

Daga Can Cikin ɗakin kuwa, Hankalin batool yaƙi kwanciyar, tana so taje ta taimaka mata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai, Idan ma tayi motsi kamar zata sauko daga saman gadonta, sai haris ya dakatar da ita tare da cewa"duk wanda ya kuskura yaje da niyar taimakata, babu ruwan mu da shi," tunzurasu yake yi duk don saboda kada suje su taimaki angel

In taƙaice maku zance, A gajarcanshi Har dare yayi babu wanda ya motsa daga Cikin su, Sun bar angel acikin toilet ita kaɗai, tun tana kiran sunayensu har tagaji tadaina, baiwar Allah ta shiga mawuyacin hali, anan cikin cikin toilet ɗin ta kwanta saman floor ɗin, abu uku suka haɗe mata a lokaci ɗaya, Ciwon kai, raɗaɗi da Cikinta ke yi mata da kuma matsiyaciyar yunwar data addabe ta, yinin ranar ko ruwa bata kora ma maƙoshinta ba, ya bushe ƙamas har wani ƙaiƙayin azaba yake yi mata,

Kafin su kwanta bacci, sai da suka cinye abincin angel da batool ta ajiye masu ita da haris, Koda su ka kammala cin abincin, Zaman jiran dawowar Danish Suka tsaya yi, har saida tsohuwa ta fito daga Cikin ɗakinta ta same su a zazzaune saman gadajensu, ganin damuwa akan fuskokinsu yasa tace"Akan danish ne"? Har suna haɗa baki wurin amsa mata da eh, Shiru ta ɗanyi tana kallonsu kafin tace"ku ƙara haƙuri, danish bazai samu damar dawowa yau ba, jikin nashi yayi tsauri sakamon Illar da ƴar uwarku angel tayi mashi, akwai wani dafi a hannunta wanda ku baku sani ba, idan har ta yakushi mutun kota gartsa mashi cizo, ya ɗauki tsawon lokaci ba'a bashi emmergency treatment ba, Dafin yana Illata sassan jikin shi ne, kuskuren da mu kayi shi ne, da bamu yi gaggawar miƙa dashi zuwa treatment room ba, lokacim da Angel tayi mashi wannan jahilin bugun, Shiyasa har Dafin yayi mashi illa ajikinshi........." dakatawa ta yi da yin maganar fuskarta duk a harmutse duk don su yarda da abunda take faɗa masu, Cikin jin ƙunar rai haris yace " idan har ɗan uwanmu ya rasa ranshi saboda ita, bazamu ƙyale ta ba, ita ma sai mun kashe ta" yana rufe baki deeja tace"Ae dama ba son shi take yi ba, muguwa kawai, tun da tazo gidan kurkukun nan, ta ɗaura mashi karan tsana ni bansan me danish ya tsare mata ba, " takai kai karshen maganar tana huci,

Haris Yace" Yadda tayi ma danish Jahilin bugu, muma sai mun rama mashi, In yaso suyi jinyar atare"

Yasmin tace"ƙwarai kuwa, Muje mu same ta har inda take, mu nakaɗa mata bugu har sai ta kasa tashi,"

Tsohuwa ta fakaici idonsu ta saki wani irin kafin murmushi, hanya mafi sauƙi da zata koya ma angel hankali, saboda rashin kunyar da take yi mata,

Cikin sanyin murya batool tace"Bai kamata mu ce zamu bugeta ba, wannan ba dai dai bane, saboda ita ɗin yarinya ce duk mun girmeta, bugu bashi zaisa ta gane kuskurenta ba, idan muka daina shiga sabgarta ma ya wadatar, daga yanzu babu ruwanmu da ita, har sai danish yaji sauƙi ya dawo cikinmu tukunna zamu waiwayeta,"

Azeeza tace"na goyi bayan shawarar da batool ta bada," suma sauran su ka ce duk sun goyi bayanta, banda haris da deeja,

"Tsohuwa yanzu Sai yaushe kenan zamu sake ganin ɗan uwanmi? Idanuwanmu sun yi maraicin rashin ganin shi" javed ne yayi maganar muryarshi a sanyaye,

Tsohuwa tace" A yadda mu ka tattauna da giant, Ya sanar dani cewa"Danish zai ɗauki Tsawon kwana Biyar Kafin ya dawo cikin ku,"

Ransu ya ƙara 6aci jin cewa sai ya ɗauki tsawon kwana biyar kafin ya samu sauƙi, Kamar su ɗaura hannayensu saman kawunansu su fasa ihu, haka suke ji saboda tsabar takaici, tsanar da su kayi ma angel ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarsu,

"Kowa ya je ya kwanta, Mu kwana lafiya Yara na" takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana dogara sanda Ta nufi ɗakinta, ta shige tare da jan ƙopa ta datse,

Kallonsu batool tayi"Mu yi haƙuri muje mu kwanta," gyaɗa kai su kayi kowa Ya wuce zuwa saman gadon shi Ya kwanta,

Gaba ɗaya duk tattaunawar da su batool su kayi tare da tsohuwa akan kunnan angel, baiwar Allah da rarrafe ta fito daga Cikin toilet, ɗin abakin ƙopar shiga ɗakinsu, Ta zauna tare da jingina bayanta, saboda takasa ƙarasa tafiya cikin ɗakin, Kaf taji irin ƙalin sharrin da tsohuwa tayi mata, sai yanzu ta gane dalilin dayasa suka juya mata ba, Lokacin ta take ta kiransu acikin toilet don su kawo mata agaji, ashe sun jita suka ƙi zuwa, saboda tuggun da tsohuwa ta ƙulla mata,

Jikinta duk yayi sanyi, zuciyarta ta karaya, Don sun ɗauki gaba da ita wannan ba damuwarta bace, ta yi masu uziri saboda jahilcin dake ɗawainiya dasu, ita tausayinsu ma take ji, yadda ake ta juya masu tunaninsu, wanda da ace suna da wayau babu wanda ya isa yayi masu haka,

Abu uku ne yafi tsaya mata arai, na farko shine Batool, bata ta6a tsammanin batool zata Juya mata baya ba, Tunanowa tayi da maganarsu ta jiya da kanta take faɗa mata cewa"Koda ace kowa zai juya mata, Ita tana atare da ita, kuma a koda yaushe zata kasance a hannun damanta, amma sai gashi yau ba irin kiran sunan batool da batayi ba aka tazo ta taimake ta amma taƙi zuwa, Abu na Biyu kuwa meyasa tsohuwa take Yi masu ƘARYA? da girmanta tsofe tsofe da ita? ƙaryafa alamace dake nuna cewa mutun baida gaskiya, lallai wannan matar ba ƙaramar makira bace, abu na ƙarshe daya tsaya mata aranta shi ne DANISH! A wani hali yake ciki? Meke faruwa da shi? meyasa baza'a dawo da shi cikinsu ba? Jiyafa tsohuwa da kanta tace masu yau zai dawo, amma kuma yau sai gashi ta canza magana, meyasa❓❓❓

Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta,

A hankali ta kifa kanta saman gwiwowinta, yalwatacciyar sumar kanta ta yi mata rumfa tamkar hijabi, shessheƙar kuka taci gaba da yi ita kanɗai a cikin toilet area, tarasa ina

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads