Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 287659 words

Chapter 7 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1765

Ads at the middle of Article

naki sai dai kash ni ban yi sa'ar mata ba,"
Juyawa ta ɗanyi jiki a sanyaye ta soma tafiya tana tunkarar ƙopar ɗakin sai da takusa fita tukunna ta ɗan dakata da yin tafiyar, A tsanake ta soma magana,
"Zan ta ya ka addu'a Allah ya baka mace ta gari wadda ta fini" tana kai ƙarshen maganarta, da sauri ta fuce daga ɗakin,

Murmushi taj ya ɗan saki, tare dakai hannu ya shafa sumar kanshi, juyawa ya yi tare da koma wa gaban mirror, lokaci guda kasala ta baibaye shi, ƙamshin turaren aneelerh ne, Ya cika mashi hancin shi, ita koda yaushe Cikin ƙamshi take, Zama ya yi a saman chair din gaban mirror, Ya kura ido yana kallon fuskar shi ta cikin mirror,


A 6angaren aneelerh kuwa, Da sauri ta fuce daga Cikin gidan, Tana shiga falon gidanta, A saman sofa ta zauna tana faman mayar da nunfashi kamar wadda tasha gudu, tarasa dalilin dayasa a ƴan kwanakin nan take jin faduwar gaba aduk lokacin da ta ci karo da taj,

A tsanake Ya kammala Shirya kanshi Cikin farar t shirt,tare da jeans ya feshe jikinsa da turare mai kamshi,

Yasan aneelerh bazata bar angel da yunwa ba, Shiyasa ma baiyi tunanin shiga kitchen ba,

Wayarshi ce ta soma ringing, da sauri yakai hannu ya dauke ta daga saman drawer,

Kallon screen ɗin wayar yayi sunan Aminina ne ya bayyana akai, murmu shi ya ɗan saki tare da yin picking call ɗin ya manna wayar a kunnanshi"Assalamu alaikum, ɗan uwana rabin raina"
On the other hand Uzair yace"Ka koma gida lafiya"?
"Lafiya lou, Yanzu na fito daga wanka ma"
"Ka ci abinci"?
Dariya taj yayi sosai, jin irin tambayoyin da yake yi mashi sai kace wani ƙaramin yaro,
"Meyasa ka ke mun dariya? yau nafara tambayarka hakan"?
Tamkar yana agaban shi Ya girgiza kanshi"Nop, just naji abun wani irine, kana tunamun rayuwar mu agidan Uncle"
Muryar shi ya jiyo da sautin murmushi "Unforgettable momeries, Allah Yabar ƙauna aminina, Zan shiga stadio Sai mun haɗe anjima"

Taj yace"Okey, take care of ur self for me pls"
Uzair yace"U too" fuskarshi ɗauke da murmushi ya yi rejecting call ɗin,

Yana ajiya wayar saman drawer, Yajiyo muryar baba maigadi daga Can cikin falo, Yana kwala sallama,

A hanzarce Ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, Yayin da yake amsa mashi sallamar"Wa'alaikum Salam"

Cikin falon Ya nufa, A bakin entry ɗin ya same shi a tsaye, ƙarasawa Ya yi yana kallon shi,
"Barka yalla6ai"ya amsa mashi da "yawwa barka"
"Dama baƙo ne ka yi"
Da ɗan mamaki akan fuskar taj yace"baƙo kuma"? yayi tambayar ne don shi a iya sanin shi, ba su yi da kowa zai zo gidansa ba,

"yalla6ai, Wannan malamin ne daya ta6a zuwa yi ma angel ruƙiya?' cike da son fahimtar da shi baba maigadi ya yi maganar,
"Kana nufin maisalati"?
Da sauri baba mai gadi yace"kwarai kuwa shi ne"
"Okey, Ka ce ma shi ya shigo"
"To yalla6ai," Yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar falon,

Tajo na atsaye Yana jiran ƙarasowar malamin Ya ji sallamar shi, Fuskar nan dauke da murmushi, Jikin shi na sanye da jallabiya wadda tsayinta bai kai idon ƙafar shi ba, Hannunshi na ruke da cazbaha Kanshi yasha uban rawani, Wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,

Sakar ma shi fuska taj ya yi tare da miƙa mashi hannu cikin girmamawa suka soma gaisawa
"Allah ya gafarta malam, barka da rana Ya iyali ya jama'a ya ƙoƙari, Allah yataimaka, Allah Ya kara ɗaukaka"
"Ameen ameen tajo, Fatan na sameka lafiya ya aiki, ya kuma ɗiyar mu"

Taj yace"Alhamdulillah, Duk muna lafiya Mu shiga daga Ciki," ya ruƙo hannunshi, suka nufi sofa ɗin falon, maisalati ya zauna asaman 2 seater, Sae faman sakin murmushi yake yi, Dama shi haka yake kullum fuskar nan a washe, Da wuya kaga bakin shi a ƙulle.

"Bari na kawo maka ruwa" da sauri Malam maisalati ya dakatar dashi"samu wuri ka zauna tajo, Magana ce mai mahimmanci ce ta kawo ni,"

Tunda Taj yaji hakan, Sai ya zauna saman 1 seater ya tattara kwandon hankalin shi a kan maisalati yana sauraron shi'

"Game da ƴarka injila" da sauri taj yace"Angel sunan ya ke"
"Oh toh, eh ita ɗin dai" shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara yi ma shi jawabi.
Taj kuwa ya tsare shi da ido, Jikin shi har tsuma yake yi, don a ƙagare ya ke ya ji me angel ɗin ta yi,

Gyaran murya malam maisalati Ya yi kafin ya soma magana a tsanake,
"ranar da aka kirani Inyi mata ruƙiya, nayi wani laifi laifin kuwa shine bansanar dakai wani abu da nake hasashe akan yarinyar ka ba, bama hasashe bane inanda tabbaci kan shi,"
Tunda taj yaji hakan,nGabannshi ya faɗi rass aruɗe yace"malam wani abu kenan"?
Numfashi ya ɗanja kafin yaci gaba da kora mashi jawabi tiryan tiryan
"Akwai abunda na gani a tattare da yar wurin ka, A lokacin da nake yi mata ruƙiya, Sai dai tsoro da firgici ya hana in faɗa maka, gaskia yana da matuƙar daure kai saboda ba ƙaramar sarqaqiya bace a cikin lamarin kuma ni kaina na kasa tantance sihiri ne a jikinta ko kuwa saboda gaskiya abunda nagani a jikinta babbar al'amari,
Tuni jikin taj ya soma kakarwa, muryar shi na kerma yace"Malam dan Allah ka yi mun bayani, hankalina a tashe Yake wlh"

Cigaba da magana malamin ya yi"Kaitsaye bazan Iya ce maka ga abunda nagani atattare da ita ba, Amma ina da tabbacin akwai wani abu dake faruwa da ita a jikinta .......",

Muryarshi na ɗan rawa yace"am..amma malam ni inaga kamar lafiyarta ƙalau, yanzu haka da nake maka magana mun samu sasanci a tsakanina da ita, Tana sona ina sonta ba kamar lokacin baya ba"

Murmushi maisalati ya yi dama yasan zaiyi wuya taj ya fahimce shi, jinjina kai yayi tare da cewa"Shin ka ta6a tunanin ka zauna da ita ka tambaye ta game da abubuwan da take yi maka a baya gamon kanta ne ko kuwa? kuma bata ƴan gane gane haka"?

Shiru taj ya ɗanyi, Shi kaɗai yasan halin da zuciyar shi ta ke aciki, duk da yana kokwanto akan kalaman malamin amma kuma yana tsoron Zancen shi ya zama gaskiya," girgiza kai yayi alamar aah, gyara zama ya yi to gaskia abinda ya kamata kayi kenan dan musan Mike faru da ita ta hakane xamu samo bakin zaren"
"Shikenan malam in sha Allah zan tambayeta,"

Maisalati yace"Yawwa ko kaifa, Sannan kuma shawarar da nake so na baka, Ka tabbatar kana Yi mata addu'o'i akai akai, idan bata iya ba ka koya mata, hada azhkar na safe dana marece, ka kuma koya mata addu'ar shiga toilet, idan zata kwanta da dare ka yi mata addu'oi'in neman tsari, kuma a koda yaushe ta kasance kanta akwai ɗankwali, ka lullu6e mata gashin kanta, Hatta kaya idan zaka sanya mata ka yi mata addu'o'a, Daso samu ne ma duk in zaka kwanta bacci ka kunna maku karatun al'qur'ani mai girma ku kwana da shi," sosai malam maisalati ya ba shi shawarwari a ƙarshe yace"Idan Allah yasa ƙarshen wahalar ta kenan sai kaga Allah ya yaye mata, Amma dai ina ƙara gargaɗinka kada kayi sakaci wurin Yi mata addu'a akoda yaushe, na manta ma ban tambayeka ba, Tana zuwa islamiyya"?

Dakyar ya iya buɗe baki yace"Eh amma ta jima ba ta je ba,

Girgiza kai maisalati yayi"Banso haka ba tajo, kanaso ka yi mana buƙulin samun Hafizar al'qur'ani, wadda zata yiwa addini hidima nan gaba, kamar yadda nake fata, Allah ya baka yarinya mai wayo tubarkalla, ga hali kamar na manyan mutane, bai kamata kayi wasa da wannan damar ba, Gaskiya ina mai baka shawara ka hanzarta mayar da ita makaranta, idan da hali harma tahfeez ka sanyata,"

Ajiyar zuciya taj ya dan sauke"in sha Allah zanyi hakan, Nagode sosai malam, Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka, Allah ne kaɗai zai iya biyanka, Allah dai yasa ka maku da alkhairi," sosai taj ya yi ma shi godiya, Koda ya miƙe zai tafi saibda taj ya ƙara tambayar shi ya kawo mashi ruwan sha,
Yace a'a, Shi dai burin shi ya yi ƙokari wurin ceto rayuwar ƴar shi, Shi ma kuma zai taimaka mata da addu'o'i shida ɗalibansa,daga haka su ka yi sallama dashi Yabar gidan,

Tofa, Bayan tafiyar malam maisalati, kasa zama taj ya yi saboda ruɗanin da zuciyar shi ta shiga, Zarya ya shiga yi a falon, Zuciyarnshi a cunku she take, wani irin faduwar gaba yake ji, tabbas yanyi kuskure sosai akan angle wurin rashin maida hankali ya yi bincike sosai lokacin da take cikin wannan halin"

A hanzarce Ya juya ya nufi bedroom ɗinnshi, tunkafin Ya ƙarasa shiga Ya hango angel zaune saman gadon Ta jingina bayanta jikin headboard(kan gadon)

Ƙura mata ido ya yi yana kallonta, ganin ta lumshe i danuwanta, tamkar mai tunanin wani abu,

Shiga cikin ɗakin yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna yana fuskantar ta,

"My daugher" da buɗar bakin ta sai cewa tayi"Daddy, Malam mai dogon gemu yazo ya cika ka da surutu kamar radiyo mai jini ko" idanuwan ta a rufe ta yi maganar,

Da mamaki akan fuskarshi yace"Taya akai kikasan yazo ke da kinke acikin ɗaki"?

Bude idanuwanta ta yi a hankali,

"Tun dazu nafarka daddy, har leƙa ku nayi,"

"Kinji me muka tattauna dashi" girgiza kai tayi"ae ka hanani yi maka la6e, shiyasa ban tsaya ba, nadawo na zauna"

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, Kafin ya kuma cewa wani abu ta riga shi cewa"aunty aneelerh ce ta kawoni gida"? ɗaga mata kai ya yi alamar eh,
"ta kawomin uniform ɗina da kuma bag dina"?ta kuma jefa mashi tambaya,
"A'a,zanje na kar6o maki su anjima"

Jinjina mashi kai kawai tayi,

Shiru sukayi na dan wani lokaci,kafin ya ruƙo hannunta cikin na shi,
"My daughter"!
Ware ma shi manyan idanuwanta tayi"na'am daddy"

Murmushi ya ɗanbsaki, ya rasa ta ina zai taro zancen, kamar maijin tsoron ta,

Can dai ya daure Ya soma yi mata magana antsanake"Nasan kina sona sosai,bkuma kina kyautatamun, koba haka ba?

Da sauri tace"Hakane daddy"

Jinjina kai yayi"um..Yanzu kina sona,nba kamar lokacin baya ba da kika ɗauramun karan tsana tamkar ni ba daddyn ki ba ne, Pls inaso na tambaye ki, a wannan lokacin ke ki ke ƙuntata mun da kan ki ko kuwa akwai wani ɗan mutun mutumi dake sanya ki kina yi mun"?

Cikin rashin fahimta tace"daddy i don't understand me ka ke nufi"?

"Ina nufin, A time ɗin da kike 6ata mun rai, Wake sanya ki kina yi mun,i know there must be a reason, babu yadda za'ae ki tsani mahaifinki lokaci ɗaya,"

Wurga eye balls ɗinta sama ta yi tana kallon ceilling, ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana kallon ceilling ɗin yasa shima ya ɗaga kai yana kallon shi, wai ko zaiga abunda take gani,

Ganin bata da niyar daina kallon ceilling ɗin yasa shi dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Pls explain to me kin ji babyna"

Mayar da idanuwanta kan shi ta yi taɗan turo baki irin na shagwa6a66u,

"Nidai bansani ba, Amma bani nake yi ba, kamar ana ce mun inyi kaza ni kuma sai inyi" takai ƙarshen maganar tana ƙyafƙyafta mashi ido,

"Magana a ke yi maki acikin kan ki ko kuwa"? ya kuma tambayarta,

"Daddy nifa bana ganewa"

"Angel kina mafarki"? ya kuma tambayarta, bubbuga hannuwanta ta yi saman Mattress ɗin"Wlh daddy ni ka yi disturbing ɗina, kana rikita ni"

Lallashinta ya shiga yi"Am sorry, wannan ce tambaya ta karshe, idan ki ka bani amsa, Zan ba ki wayata, kiyi game," yasanta mayyar wayace, aikuwa da sauri ta soma kora ma shi jawabi
"Daddy, ko yanzu dana kwanta,na yi mafarki kuma kullum ina yin mafarki,"

"Faɗamun meke faruwa acikin mafarkin"?a ƙagare ya yi maganar,

Angel tace"Ina ganina a cikin wani ƙurmin daji mai duhun gaske mai ban tsoro, kuma idan nayi mafarkin ina ganina Acikin wasu mutane masu sanye da baƙaken kaya, Bana iya ganin fuskar su, hannunsu zako zako da akaifa, Ni kuma Ina sanye Cikin jajayen kaya, riga da wando,kuma bani kadai bace hada wasu ƴan yara, Kuma suma red uniform ne a jikinsu,Daddy akwai tsorofa mafarkin Kuma babu alkairi a cikinsa"

Tunda ta soma magana zuciyar taj tashiga harbawa da ƙarfi da karfi, tamkar zata faso daga kirjinshi,

"Amma kinsan kina irin wannan bad dream ɗin shi ne baki ta6a sanar mun ba"?

"Banaso na tayar maka da hankaline, Aunty aneelerh tace in dinga faranta maka rai, kada na 6ata maka rai, Zaka Iya mutuwa ni kuma banso na rasa ka, sometimes ma in nayi yinqurin fada maka sai wani abu ya daukemin hankali na manta" fashewa tayi da matsanancin kuka,

Da sauri Ya janyota jikinshi sosai ya rungumeta, baisan lokacin da hawaye suka soma sauka akan fuskar shi ba, yana jin kukanta har cikin zuciyarsa

"In sha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na ceci rayuwarki, Bi'iznillahi duk wani mai nufinki da sharri zai koma masa ne, Tabbas akwai wani maison shiga tsakanina dake, akwai wanda yake Yi mun maƙarƙashiya, Bansan wanene ba!!Amma Allah ya sani, Kuma zai bayyanar mun dashi ne, duk mun daren daɗewa"!

Yayi maganar ne don yasan Yana da maƙiya a wurin aikin shi, masu yi mashi hassada saboda ɗaukakar daya samu, kuma har akan idon shi suna nuna mashi ƙiyayya, shiyasa ya yi zargin kodai wanine keson ya 6ullo mashi ta bayan fage, shine a kayi amfani da ita wurin cutar dashi,

Sun jima a wannan yanayin manne da juna shi da ita, sai da aka fara kire kirayen sallar la'asar, tukunna Ya ɗago da ita daga Jikin shi, Ganin ta fara bacci Ya dan jijjigata, firgit ta farka"time din sallah yayi daga yanzu bana so kina wasa da sallah, kinji ko'?

Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ya kuma cewa"Addu'ar shiga toilet kin iya"?ɗaga mashi kai tayi"Eh"yace to karantamun, nan ta shiga karanto mashi, ya kuma tambayarta addu'ar kafin a kwanta bacci da kuma in an ta shi daga bacci duk ta karanto mashi Yace"masha Allah, haka nake son ji My daughter, Sannan kuma zan koya maki azhkar da zaki dinga yi na safe dana marece, pls ki bani haɗin kai, ki dage kin ji indai bakyaso a rabani dake"da sauri tace" zanyi daddy,"yace that's good, yanzu tashi ki shiga toilet kiyi alwala ina jiranki"

Amsa mashi tayi"toh" da sauri ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, harta kusa shiga ya dakatar da ita"wait" ta tsaya tare da waiwayowa tana kallon shi, saukowa daga saman gadon ya yi ya nufi can cikin ɗakin wurin closet ɗinsu, buɗewa yayi tare da kai hannu ya ɗauko hijabi da mayafi, asaman gadon ya ajiye mata hijabin shi kuma mayafin ya taka zuwa inda take ya ɗaura mata shi a kanta, sosai ya lullu6e mata gashinta"yawwa daga yanzu haka nake so gashin kanki ya kasance a lullu6e, sannan kuma idan kin kammala sallah, ki dinga karanta surorin da nake koya maki" amsa mashi tayi"toh"kafin ta bude toilet ɗin ta shige ciki,"

Tsayawa ya yi har saida ta fito tukunna ya sanya mata hijabin,kafin ya wuce cikin toilet, lokacin daya fito salla ya same ta tana yi, baisan lokacin daya saki murmushi ba,yaji daɗi har acikin ran shi,


Da sauri ya fuce zuwa masallaci, a bakin gate suka ci karo da Uzair yana ƙoƙorin shigowa ciki, dama biyo ma shi yayi don su tafi masallaci atare,

Bayan tafiyarshi, Angel ta kammala sallah ta zauna tana karanta surorin daya koya mata irin su falaki da nasi, su ta yi ta biyawa, duk don saboda yace tadinga yi indai bataso a rabasu, Tana cikin yin ƙira'ar, Wayar shi daya manta saman gadon su ta soma ringing,

Zumbur ta miƙe takai hannu ta ɗauke ta, Sunan Uncle ne Ya bayyana, Kafin ta ɗaga kiran ya katse, ganin wayar babu finger print din daya ke sanya mata, dama tun lokacin da suka shirya da ita ya cire security din wayar shi, Zama saman gadon ta yi ta dinga buga game na spider man,

Sai da ta yi mai i sarta tukunna ta shiga contact dinshi, Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira, wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya, Har ya katse kiran, ta kuma haɗa wasu numbobin ba'a ɗaga ba, kusan number waya biyar ta kira ma shi wasu ba'a ɗaga ba, Sai na ƙarshene a ka ɗaga kiran,

Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana, shiru taji ba'ace mata uffan ba, kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karaɗe kunnuwanta"who is on the line"?

Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace"Angel ce,"

Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta"kinsan dawa kike magana"?

Girgiza kai ta yi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace"a'a,"

"Ur age"? ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinya ce ƙarama,

"7yrs" voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?

"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"

"Can i call u video"?

Da sauri tace eh,

Nan take ya mayar da kiran Video call, ɗago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan ta yi picking, Bata ga komai ba a screen ɗin sai duhu sosai, Amma shi wanda take wayar dashi da alama yana kallonta,

"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale ido,

Shiru ta ji baya magana, saukowa ta yi daga saman gadon, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, Tana Cikin zagaye palour Tajiyo Sallamar daddyn ta,

A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers ɗin data kira, tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci,


Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna,

"Ban fada maka bane kawai, Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana da aljanu, zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta same su tunda a nan Benazir ta haifeta, kuma kaga shi toilet madaddalar su ce,"acewar uzair,
Jinjina kai Taj ya yi"Yanzu menene mafita"?
Uzair yace"Mu tayata da addu'a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za'a dace ne,"

Taj yace"Allah Ya yarda, duk na damu wlh,"

Uzair yace"ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads