Header Ads
Showing 54001 words to 57000 words out of 287659 words

Chapter 19 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1783

Ads at the middle of Article

dake wakana,
"Zanje na kwanta, Amma kafin nan i naso ki faɗa mun sunan ki, duk da naji ɗazu kamar tsohuwa ta ambace shi, sai dai ban ruƙe ba," muryar batool ce ta katse mata zancen zucin nata,
Ajiyar zuciya angel ta sauke kafin tace"Sunana ANGEL ke fa?" batool ta bata amsa da cewa"Ni sunana BATOOL inaso ki ɗauke ni tamkar ƴar uwarki, kuma ina so ki saki jikin ki acikin mu, ta hakanne zaki samu duk abunda ki ke so,"
"Kin wahaltu sosai yau, ki samu ki yi bacci, takai ƙarshen maganar tare da jan bargo ta lullu6e fuskar angel da shi,
"Sleep well my lovely sister" ƙasa ƙasa da murya angel ta furta mata"thank u, Sister" murmu shi batool tasaki ba ƙaramin daɗi taji ba, da angel ta kira sunanta da sister, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta kwanta, kamar daga sama ta jiyo muryar hannah"kin gama kula da jinjirar ta ki? Tsoki batool taja" mind ur own business" tana faɗin hakan bata ƙara tanka mata ba,
Kowa ya runtsa a daren ranar banda mutun ɗaya! Dama taya zata iya bacci? ya yin da zuciyarta ke a cunkushe a ƙuntace da rashin mahaifinta, duk da har yanzu bata gasgata kalaman dattijuwar nan ba, ita dai tana ji aranta daddyn ta he's still alive! kuma taci alwashin duk runtsi duk wuya sai ta nemi hanyar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, ni dai nace Allah ya ba mai rabo sa'a,
Ataƙaice cikin ƴan kwanakin nan ba irin haukan da angel ba ta yi masu ba akan su fitar da ita daga cikin kurkukun amma duk a banza, babu mai saurarenta acikinsu batool ce kaɗai ke lallashinta, duk ta bushe ta rame dama ba ƙiba gare ta ba, yadda kasan ɗiyar roba haka ta koma cikin sati ɗaya kawai, duk ta fita hayyaci kuma taƙi sakin jiki da su, musamman mazan haushin su take ji, saboda wannan Danish ɗin da basa jituwa da shi, ta tsane shi kamar mutuwarta shima haka ya tsaneta ko kallon arziƙi bai haɗa ta da shi, ko fira suke yi ta sanya masu baki to ya gama magana, ita kallan ɗan iska ta ke yi ma shi saboda doguwar sumar dake akan shi ita a ganinta ta ya yana namiji xai tara suma? tsayin sumar shi har ya kusa taddo nata, gaba ɗaya dai haushin mazan take ji saboda an haɗa su rayuwa a wuri ɗaya sam bata so ko kallonta su na yi ae ita a wurinta iskanci ne hakan, abunda bata sani kwata kwata basu da feelings a tare da su, suna ɗaukar kansu tamkar jinsi ɗaya da matan, ita ce kawai ta sanyawa ranta hakan, bakomai ya ƙara ɗaure mata kai ba fa ce rashin barin su yin ibada, batool ta sanar da ita cewa basu da addini, duk wanda ke rayuwa acikin kurkukun ƙaddara baida addini, rayuwa kawai suke yi tamkar arnaku ko sunan Allah basu ambato acikin maganar su, ba sallah ba sallati, bama su san yadda akeyin ta ba, dokar prison ɗin ce ba'a ibada acikinsa, wani irin kurman kurkuku ne, baka sanin lokaci dare ne kaɗai idan ya yi suke ankara saboda hasken ɗakinsu da ake ɗaukewa sai kuma idan safiya ta yi sun ta shi daga bacci, ita kanta angel ɗin ta ta6a gigin yin sallah, duk da basu da hijabi, ranar da tayi alwala ta yafa bargon lullu6arta da sunan za ta yi sallah, zagaye ta su ka yi suna kallonta da mamaki don basu san menene take yi ba, da zarar ta ɗaura niyya zata kabbara, sai ta dinga jin kukan mahaifinta, idanuwanta su dinga nuna mata fuskar tajuddeen wuta na ƙone jikin shi, gaba ɗaya take rikicewa ta gigice ta dinga kuka ire iren irin wannan gane gane da take yi yasa ta daina yunƙurin yin sallar, abun yana affecting ɗin ta

Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah ido, ta daina haukan guduwa daga cikinsa tun da ta ga babu hanya, amma fa bawai hakan yana nufin ta haƙura ba, tana nan akan bakanta! ta lura cewa idan har zata cigaba da borin haukan da take yi masu tofa bazata ta6a samun nasara ba, wannan dalilin ne yasa ta nema ma kanta maslaha, tayin rayuwa cikin salama don ta samu damar yin bincike ta gano ainihin sarƙaƙiyar dake acikin Kurkukun ƙaddara, don tun daga kan ma'anar Sunan kurkukun fassara ce me zaman kanta, Kuma kullum tana cikin yin azhkar na safe dana mare ce, wanda daddynta ya koya mata, har tsakar dare bata runtsawa xama take yi tsakiyar gadonta, ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i akan Allah ya kawo mata mafita acikin rayuwarta,

*Boss Bature✍️💋*


*After some weeks*


Zaune take a tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, idanuwanta suna arufe fuskar nan ta yi jawur idanuwan sun kumbura, ga busassun hawaye duk akan fuskarta,
Kasancewar safiya ce ba su jima da farkawa daga bacci ba,
Sautin dariya taji ƙasa ƙasa taji muryoyinsu suna yin gulmarta "Wari take yi, tun da tazo bata yi wanka ba daga gani dai ƙazama ce," can ta ji muryar wani ya kuma cewa"idan muka ƙyale ta mu zamu cutu, jiya fa daƙyar nayi bacci saboda warin jikinta gaba ɗaya ya cika ɗakin nan," tuntsure wa su ka yi da dariyar shaƙiyanci,
"Ku ta shi muje muyi mata magana, ta je ta yi wanka, in ba haka ba mu zamu yi mata da kan mu," haris ne ya bada wannan shawarar,
Angel dai ta natsu tana sauraronsu, dama mugun haushin su take ji, tana jiyo sautin tafiyar su a bakin gadonta suka tsaya kusan su shida,
Gyaran murya ɗaya daga cikin su yai mata"ke tashi ki je ki yi wanka" a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗan kalle su, wanda ya yi magana shi ne Haris, a halitta baƙi ne yana da jiki,
"Ba zamu zuba maki ido kina cutar damu ba, jiya nan daƙyar mu ka yi bacci saboda warin jikin ki, don haka ki tashi kije ki yi wanka ko mu yi maki da kanmu" cike da ƙwarin gwiwa javed ya yi maganar, dogo ne launin fatarsa chocolate,
Jin ta yi banxa ta ƙyale su yasa Mubeen jinjina kai ya kalli naufal dake a gefen shi yace "je ka cika mana bokiti da ruwa," ya yi maganar yana naɗe hannun rigar shi,
Danish da ke a kishingiɗe saman gadon shi bai tanka masu ba, yasan suna yi duk don su ƙuntata mata ne saboda tsanarshi da ta yi,
ƴan matan dake a tare da su Deeja da yasmeen, sun ruqe qugu suna sakin murmushin mugunta,
Da alama dai hada ƙuruciya ke damun su, don dukan su gaba ɗayan su baza su wuce shekara shabiyar ba, mazan cikinsu ne ke akwai ƴan shekara sha bakwai, kamar danish dasu haris,
"Bakya ji ana maki magana"? muryarta na kerma tace" duk wanda ya yi gigin ta6a ni, zanyi mashi illah, babu ruwanku da rayuwata," tamkar xata fashe da kuka ta yi maganar,
"Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, zamu gani mu dake wazai ma wani illah," haris ne ya yi maganar, tare da naɗe hannun rigarshi yace dasu Naufal su ɗauko mashi ita, akaita toilet su yi mata wankan tsarki,
Jin haka yasa ta durowa daga saman gadon, Duk da jikinta ba ƙwari daure wa kawai take yi, hannu haris yakai zai ruƙo kwalar rigarta, aikuwa ta daddage ta ɗaga kafarta tare da kai mashi naushi tsakiyar cikin shi, azabar zafi yasa ya yi saurin dafe cikin shi, rai a6ace javed ya kai mata bugu aikuwa ta damƙi ƙafar shi ta hagu ta dinga janta har saida ta yarfar dashi ƙasa, faɗa ne ya kaure a tsakaninsu, bugu tadinga kai masu da naushi, dama ta ƙware wurin iya cixo da yaku shi, duk sai da ta raunata su, sai faman nishi suke yi, da taga ta gama da mazan ta koma kan matan,

Haɗe kawunan su tayi, ta ruƙo gashin kansu, tadinga ja tamkar xata tsunka su, kuka hada majina suka dinga yi,

koken koken da suke yi ne ya farkar da su Batool da sauran ƴan uwan nasu dake bacci, ganin yadda Angel take Mazgarsu yasa suka sauko daga saman gadon suka nufeta suna ƙoƙarin rabata da su, daƙyar suka samu nasarar janye Angel gefe ɗaya, sai huci take yi kamar kuranya, Su deeja da yasmin suna zuƙunne ƙasa, dafe da kawunansu sai kuka suke yi,

Duk wannan abun dake faruwa tsohuwa tana a tsaye baƙin ƙopar ɗakinta, hannunta ruƙe da sanda, ta yi tsaye tana kallon sabuwar ƴar wasan damben da suka samu,

Danish kuwa dake kishingiɗe saman gadon shi, hankalin shi kwance dama yasan za'a rina, shiyasa bai shiga cikinsu ba, koda suke xancan zasu je suyi mata magana akan wanka, don ya lura ƙarfi ne da ita, gashi duk cikinsu itace ƙarama amma tafi su ƙarfi,

Gyaran murya tsohuwa ta yi, da sauri angel ta ɗago tana haki, suka haɗa ido da ita,

"Aikin ki ya yi kyau, tsanar da ki ka yi masu har takai ga bugunsu so ki ke ki kashe su?"
Rai amatuƙar 6ace tace" bugun su yanzu na fara idan har ba su daina shiga gona ta ba, kuma wlh idan har baku fitar dani daga cikin kurkukun nan ba, zan addabi rayuwar kowa ne, nace banaso ku ƙyale ni inyi rayuwata na tsani gidan nan, Natsani kowa dake acikinsa, kince nan gidan marayu ne kuma za'a gatanta mu but why kuka killace mu sai ka ce dabbobi? haka ne gatancin Abinci sau ɗaya a rana? Kun hana mun yin ibada, uwa uba kun haɗa mu rayuwa da maza a ɗaki ɗaya? Me hakan yake nufi iye"? Idanuwanta azazzare ta yi maganar, tamkar ta sanya hannu ta shaƙo wuyan tsohuwar hake take ji,

Maimakon tsohuwar ta bata amsoshin tambayoyinta sai ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya,
Runtse ido angel ta yi cikin jin zafin dariyar tsohuwar, cije lips ɗinta ta ɗanyi kafin ta buɗe eyes ɗin nata,

"Wlh ban yadda dake ba, saboda gaba ɗaya babu gaskiya acikin kurkukun nan, idan kun 6oye mana manufarku ta killace mu anan baku isa ku 6oyewa Allah ba, yana ganinku kuma asannu Allah zai warware mana komai, ni nasani zuwana gidan kurkukun nan jarabawa ce ta ubangiji........."daƙyar takai ƙarshen maganar saboda hawayen da suka cika mata idanuwanta,

"Dabbar dake yawo a daji, tafi mu gata tafi mu ƴan ci, idan su basu damu ba, zai iyayiyuwa don sun taso rayuwarsu acikin kurkukun ne, kuma sunsan basu da kowa, amma nifa ina da dangina masu sona, hakanan anje an sato ni an kawo ni cikin wannan munafukin ƙaddararran kurkukun mara kan gado,"
"Angel" muryar batool ce ta ambaci sunanta, a harzuƙe angel ta juya baya tana kallon batool tace,
"Nasan bai wuci ki ce xaki bani hakuri ba, akan inja bakina inyi shiru, Batool bazan Iya ba, narasa gane meyasa bakwa fahimtata ne, iya cutuwa an cutar da rayuwata, tun ina jinjirata mahaifiyata ta gudu tabarni a wulaƙance cikin kwamin wanka, nata so cikin so da ƙauna na mahaifina, An raba ni da shi, An kashe mun shi duk da har yanzu ban gasgata hakan ba, sannan na faɗa hannun fulanin daji, na rayu acikin daji tare dasu a matsayin tsintacciya, wai ni Angel ƴar gidan daddynta, na shiga mawuyacin hali na rashin mahaifina atare dani, na saba dashi mun shaƙu sosai, komai shi yake yi mun wanka, ya gyara mun gashin kaina mu kwana rungume da juna, dama haka rayuwa take? Lokaci ɗaya narasa gatancin nan, na dawo ina kwana a saman tabar ma cikin bukka, bani da abinci daya wuce gasassar masara da fura, yanzu kuma gashi na tsinci kaina acikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, ya a ke so inyi da raina? Wlh da rayuwa acikin kurkukun nan kwara na ƙare rayuwata a hannun fulani daji, koba komai zan sha iskar duniya, in yawata inda nakeso, inyi rayuwar ƴan ci, Amma nan fa? Ta karfi ta tsiya aka kawo ni cikin shi banma san ta ina aka shigo dani cikin gidan kurkukun nan ba, don kuwa sai da aka fara gusar mini da hankalina tukunna, in banda munafurci taya xa'ace gidan marayu ne? Meyasa da za'a kawo ni cikinsa ba'a barni cikin hayyaci na ba? Meyasa za'a hana mu shige da fice, An tauye mana haƙkin mu na rayuwa an hana mu sakat wai da sunan za'a gatanta mu......................'

(SHIN ME KU KE TUNANI AGAME DA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? MU HAƊU A NEXT PAGE IN ALLAH YAKAI MU DA RAI DA LAFIYA, HAR YANZU FREE PAGES NE WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA YI MUN MAGANA 08103884440, WASAN FA YANZU AKA SOMA BUGA SHI, DOMIN KUWA BAMU NUTSA CIKIN LABARIN BA, YANZU AKA FARA)*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*


Daga alƙalamin Boss Bature✍️

Cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, hawaye ta ko'ina akan fuskarta, tabbas jikin kowannan su ya yi sanyi, banda mutun biyu, danish dake kwance saman gadon shi sai Haris dake zaune ƙasa ya dafe cikin shi,
Saukowa batool ta yi tare nufar inda angel take tsaye agaban tsohuwa, ta dafa shoulder ɗinta"I feel ur pain angel, abun da ciwo labarin ki akwai ta6a zuciya, dole kiji ɗaci aran ki, kuma dole ki ƙuntata acikin kurkukun nan, abunda yasa kika ga mu ba mu damu ba saboda bamu da wanda zai yi kukan rashin mu! Mu matattu ne a idon jama'a kamar yadda tsohuwa ta faɗa mana, a gidan nan aka raine mu agidan nan muka taso, tunda mu ke bamu ta6a yin tozali da hasken daya fito daga wajen kurkukun nan ba, ina yawan tambayar kaina koya wajen kurkukun nan zai kasance? Ya mutanan dake rayuwa a wajen sa su ke? Bani da amsar tambayata amma ina fata wata rana nima wata rana in fita daga cikin sa, sai dai nasan abune mai wuya......" cikin sanyin murya takai ƙarshen maganarta,
"Zan iya zuƙunnawa saman gwiwowina in roƙe ki akan ku fitar dani daga cikin kurkukun nan, inaso na rayu cikin ƴan uwana" angel ce ta yi maganar muryarta a rauna ce,

Jinjina kai tsohuwa ta yi a yayin da take binsu da kallo da waɗannan kwarkwararrun idanuwan nata, tsawon mintuna kafin tace"koda ace kin zuƙunna saman gwiwowin ki don ki roƙe ni akan in fitar dake daga cikin prison ɗin nan, hakan bazaiyi aiki ba idan ku ka yi haƙuri a sannu zaku fahimci manufar wannan kurkukun na tara ku acikinsa, Amma a yanzu shawarar da zan baku shi ne, ku so junan ku tun da baku da kowa ku xama naku ku kaɗai, ku kasance masu faranta ma juna" daga haka bata ƙare cewa komai ba, ta dogara sandarta tare da juyawa tana ɗangyala ƙafa ta nufi cikin ɗakinta, tana shiga taja ƙopa ta datse,

Zubewa angel ta yi saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsancin kuka mai cin rai tamkar ranta zai fita,

Rankwafawa batool ta yi tare da ruƙo hannayen angel cikin nata, ta miƙar da ita tsaye, ta rungumeta ajikinta tana lallashin ta, sun ɗauki tsawon mintuna, kafin ta raba jikinsu,

Kallon sauran ƴan uwan nasu ta yi, kowa yana a tsaye banda Danish dake kwance

Ɗaya bayan ɗaya ta shiga kiran sunayen su"Hannah, Hibba, deeja parveen, Eve, yasmin, rubina, Aziza" kowa ya kasa kunne yana sauraron abunda zata ce masu, juyawa tayi kan mazan dake acikinsu ta ambaci sunayen su one by one"Danish, javed Haris, mubeen, naufal" sai faman huci haris yake yi saboda haushin bugun da angel ta yi masu,
Calmly ta soma magana cikin sanyin murya"kamar yadda tsohuwa tace mu so junan mu, Let's consider ourselves as blood relatives, inaso mu yi ma juna alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, Sa'annan bana jin daɗin yadda ku ke ware angel acikin mu, i thought we are all the same, bamu da banbanci jinsi ɗaya ne mu da ita duk abu ɗaya ne, idan ba mu so juna ba, wa zamu so? Nasan kuna jin haushin angel ne saboda abubuwan da take yi wanda bakomai ya jawo hakan ba face ƙuntata rayuwarta da a ka yi, taya mutumin da ya saba rayuwar shi a sake rana ɗaya a tsamo shi daga cikin danginshi a kawo cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA! taya bazai ƙuntata ba"? dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana bin fuskokin su da kallo,
"Batool ni dai inason Angel, kuma bazan ta6a faɗa da ita ba, zan ɗauke ta tamkar yadda na ɗauki kowannan ku," bakowa bace ta yi maganar fa ce AZIZA, yarinya ce me ƙarami jiki fara ce sosai duk cikin su babu me gajartar ta,
ɗaƙyar angel ta iya buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗaura su akan fuskar aziza da ta yi maganar, ba ƙaramin son yarinyar ta ji ba, saboda ita kullum a cikin fara take baka ta6a ganin fuskarta a ɗaure,
"batool, nima xan ɗauke ta tamkar yar uwata," kallon wadda ta kuma yi magana angel ta yi, hibba ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,
Lumshe ido angel ta ɗanyi tare da buɗe su tana ci gaba da kallon su,
"Nima na goyi bayan Batool, angel tamkar ƴar uwa take acikin mu" acewar Parveen
Murmushi batool ta ɗan saki, har cikin zuciyarta ba ƙaramin daɗi taji ba,
Miƙa hannunta na dama tayi saman iska tare da kallonsu tace"ina so muyi wa juna alƙwarin kasancewa atare, zamu so juna kuma zamu

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads