Showing 30001 words to 33000 words out of 274096 words
Chapter 11 - DAULA BIYU Complet Document .txt
ne a gidan kuma Maraya ne bai da kowa, shi yasa Noman ya amince su tafi tare ko babu kome zai su ji dadin tafiyar tunda sun san juna.
Guzuri suka diba me yawa, da ruwa wanda zai taimaka musu sabida tafiyar da zasu yi a yankin sahara idan sun tsallaka teku.
Da haka suka yi sallama da kowa na garin tare da niman albarkan iyayen shi.
(Saduwar Alkhairi)
**
Oman
Washi gari. Sanyin asuba ce ta tashe ni daga barcin da nake, a hankali na zuba mishi ido, babba ne babu laifi. Amma kuma Ni duk haushinsa nake ji, a hankali na janye jikina daga gare shi tare da nufar ban daki nayi wanka, sabida jiya ma haka ya gama jagwalgwala ni, sannan ya samu barci.
...ina fitowa yana tashi shima. Dauke kai nayi tare da saka kayana nayi kokarin gabatar da sallar asuba. Ina idarwa yana tadda na shi sallah. Ina zaune a gurin nayi shiru, ina kewar Airan ne, kewarta nake sosai a raina. Dan haka ina kallon ya idar da sallah ya matso kusa dani, sannan yace min.
"Don Allah Karki cire abin fuskar ki, ki barshi haka kinji"
Janye idanun na nayi akan shi tare da kallon kofar dakin shi.
Shima zubawa kofar yayi ido, sannan ya mike ya rike hannuna.
"Don Allah Karki yi abinda zai kusanta ki da wasu mazan, kinji bana son na.."
"Rasani kawai kasa a ranka zaka rasani ne, domin kuwa ina ji a jikina Jarumina yana nan tafe."
Damke hannuna yayi sannan yace min.
"Na rantse da Allah, duk wanda ya Kuskura ya bibiyeki zan kashe shi."
Kuyi hakuri......
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1034332478?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=ZG1SK2xVFREr7hRhBhywpRJFGcG%2FU04IT0c4iD2112GhzLOAlOkhgZul%2BFXxbRvW%2B5B65PK0%2FIBcXT7tIPL5xgrIrj4qJCiAhPQYYo%2F9B%2FvjAek8Z02xB3mvkJTKj6qe
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Page 16...
Wani irin kallon nake binshi da shi daga sama har kasa, kafin nace mishi.
"Yana da kyau ka manta dani, ka kuma manta da abinda ya haɗa mu, domin kayi iya na kudinka sauran kuma ka ajiye zan amshe shi da hannuna."
"Me yasa baki da tsoro da hangen nesa?" Kallon shi nayi a kai kaice, kafin na tabe baki na, sannan nayi gaba abuna,
"Ba zaki tsaya muyi sallama ba?"
"Iya wanda kayi da jikina bai isheka bane?"
"Ya ishe ni kan, amma ba haka nake bukata ba"
"Toh sai ka cinye ni, ko kuma ka boye ni sabida rashin adalci."
Na fada ina bashi amsa a takaice.
"Kina min kama da wata shashin rayuwata!" Ya fada dai dai na rike hannun kofar,
"Wannan kuma matsalar ka ce, ba iya shashi ba ko rayuwar kace bai tikani da kasa ba, balle naji zafin jiki na."
Ina bude kofar, muka yi idanu biyu da Nawwas, kura min ido yayi sannan ya dauke kanshi.
"Barka dai mara dariya!"
Na fada ina kallon shi. Tab'e baki nayi tare da matsawa zan wuce.
"Meye sirrinki?"
Cike da al'ajabi na kalle shi, murmushi nayi sannan na bar gurin ina tafiya cikin nutsuwa,nasan ba a haife ni cikin gidan Sarauta ba, amma kasancewata cikin gidan sarauta yana sani jin kamar an haife ni ne domin mulkin baki daya.
Duk inda na wuce bina ake da mutuntawa,har na isa kofar da zata sadani kofar bayi.
"Ke bakar fata? Ba a gaya miki cewa dake za a tafi daular Abbasid ba?"
Kallonta nayi domin bani da amsar bata, yaushe aka shirya wannan tafiyar ba a sanar min ba, daki na shiga na sami su Inan suna ta shirya mana kayan mu.
Dauke kai nai sakamakon yadda bayin suka zuba min ido, sabida kamshin turaren Abrad, matsowa Inam tayi sannan tace min.
"Yar uwa jiki kin kwana a turakar Sultan ko?"
Murmushi nayi mata sanan nace mata.
"Eh!"
"Don Allah ya jiyar dake dadin da."
Kallonta nayi tare da kallon sauran bayi matan,
"Sirrin mu ne, bana fatan na zama mara sirri."
Daga haka Narga ta kawo min abin karyawa tana faɗin.
"Ana son gobe da asuba mu isa SAMAIND Insha Allah, dan haka ki shirya cikin sauri"
"Bai zai yiwu ba, idan gaggawa kuke toh kuyi tafiyar ku, ni ba a tilasani cin abinci ban shirya ba, kuma ba a sani cin abinci da zafi, kuma idan ya Huce dole a nimo min wani."
Na fada cikin daurewar fuska, ina bude abincin. Sak kamshin abincin da naji a shashin Sultan Abrad da alamu abincin shi ne.
--- Bin bayan ta yayi da ido, zuciyar shi kamar ta diro kasa, wani irin kishinta yake ji yana cika zuciyar shi, dan haka koda Sultan yayi mishi izinin shiga cikin dakin, ranshi a sose ya shiga, asalima wani irin kallo yake bin gadon da suka tashi daga barci, kasa kasa yake kallon dakin kafin ya maida idanun shi kan Sultan Abrad da abinda zai fada.
"An gama shirya kome, ku a ke jira Ikram din ma."
"Eh toh gaskiya dole a jira ta, dan naga bata gama shiryawa da wuri ba. Tunda bata fita da wuri ba!"
Murmushin takaici Nawwas yayi tare da kallon shi, shima ya fice.
...
Kutuful aka yi da tiren abincin gaba na, ban tab'a jin wulakantani da aka yi ba sai yau, kallon Azizatul Nissah nayi cikin al'ajabi, kai hannun ta tayi tare da kai min mari na rike da sauri, mik'ewa nayi domin ba zan yarda da duka ba.
Cillar da hannunta nayi tare da kallonta,
"Ba zan lamunci duka ba, sayata Abrad yayi ba yana nufin mallakata yayi ba, kika mare ni zaki ga abinda zai dame ki."
Cikin fushi da b'acin rai ta kai min dukar da gaske, aikuwa nayi maza na make mata gefen cikinta sai da ta zube a kasa, ihun da tayi ne Dakarun da suke kula da lafiyar ta suka shigo. Zasu fita dani sai ga Abrad da Nawwas, sun shigo. Ganin Dakarun zasu tab'a ni ya dakatar dasu.
Cikin kuka take gaya mishi abinda nayi mata, ba tare da ya tambaye ni ba, kallon kasar dakin yayi yace mata.
"Waye yace ki zubda mata abincin ta? Sannan meye ya kawo ki shashin bayi? Bana son haka kar na kuma ganin ki a nan, sannan kiyi maza kishirya kayanki, domin dake zamu nadin sarautar Sultan Aamaan Abdus Samad Aamaan na biyu."
Juyawa tayi tana kallona, na dauke kai na, tare da mik'ewa zan fita ya d'an buge hannuna. Juyawa nayi na kalle shi.
"Ki shirya."
"Zan tafi babu abinci ne a cikina."
"Toh zasu baki!" Nawwas ya bani amsa a takaice,
Tab'e baki nayi sannan nace mishi.
"Na koshi ma"
Daga haka na bar gurin baki ɗaya.
*
Askandariya
Kallon waziriyarta tayi cikin sanyin jiki, tace mata.
"Zaki wakilci masarautan nan zuwa birnin Samaind, ba zan sami zuwa bikin sarautar Aamaan na biyu ba."
"Toh ranki shi dad'e, Ubangiji ya cika miki burinki na sarari da na boye, ya warkar dake ciwon da yake damunki na tsawon shekaru, Sultanah Amrah. Allah ya kara miki hakuri da dangana."
Murmushi tayi sannan tace mata.
"Amin Ya Allah, babu kome ya wuce zanen ƙaddarar mu ce a zane a gurin."
Kwalla Waziriya ta goge cikin tausayin Sultanah yadda ta amshi kaddarar su hannu bibbiyu, bata tab'a kawowa wata rana zata saka ayi mata duba ko tsafi. Har yau tana saka ranta zata kuma niman damar.
"Toh Yalqoot karki damu, Insha Allah Ubangiji yana ki yana gani zai kawo karshen kome."
Cikin karfin hali tace.
"Insha Allah." Ta faɗa tare da matse kwalla.
.... Bayan barinta fadar Sultanah Amrah, a hankali ta isa gidanta ta shirya kayanta, sannan ta fito ta bar yankin baki daya. Dan su zasu iya isa bata yi magana ba.
**
Garin SAMAIND ya cika makil da al'umma, maza da mata. Kowani kusurwa na yankin ya cika da al'ummar Annabi.
Tun safe akewa garin tsinke dan haka suka zuba dakaru dubu dari bakwai a cikin garin..sannan daga wajen gari akwai dubu talatin da bakwai.
Kasancewar an rigada ansan da zuwan baki Karku ga yadda aka tsara garin ya koma mafi girma da kyau, gashi yan kasuwan su suna baje kolin su.
Wani irin cigaba aka samu na Kasuwanci a cikin birnin. Daga can katangar masarautar, wasu mutane ne tsaye, suna ta hidiman su.
..... Tun jiya ake raba kyauta tun daga masarautar har zuwa wajen masarautan, kyautar tufafi da abinci ake badawa,
*
Madinatul Mah.
Wata karamar birni ce me dauke da mutane bazasu wuce dubu talatin ba,. kasancewar su musulmai kuma manoma.
Sannan shugaban yankin me suna Hilali Bin Mahfuzur. Mutumin kirki ne, kuma yana dauke da adalci a cikin yankin shi.
Kasungumin mayaki ne, wanda ya jima yana aiki da dakarun Samaind, kafin haka kore shi sabida ya nuna halin gaskiya da gaskiya.
Wata matashiyar budurwa wacce ba zata wuce sa'ar Ikram ba, yake bawa horon yaki, cikin zafin nama da kwarewa yake kai mata sara.
Amma yarinyar tana karewa.
Fitowa tayi dauke da kwando, tana kallon su. Har yau bata cire burinta da tsammanin zama wata a cikin daular Abbasid ba, kallon yarta gudan jininta take, cikin tsananin kaunar ta tace.
"Mahlika!"
Da sauri yar ta juya tana kallon uwar, sannan ta kare sarar da mahaifinta ya kai mata.
"Anne, kirana kike?"
Murmushi tayi tare da kallon Hilali.
"Mijina karka kai mata sarar, kyale sarauniyar GOBE!"
Sake takobin yayi tare da cewa.
"So nake tayi iyakan kokarinta, ta wanke miki zuciya a birnin Samaind."
Wani murmushi tayi sannan ta zauna, tana kallon shi.
"Idan kuma ta fadi ba?"
"Zata yi nasara!"
"Na fadi sabida cin amana, kana ganin yanzun ma zan kuma samun nasara?"
"Idan kika yi aikin alkhairi zaki yi nasara, dole ki sami Hoyam!" Ya fada mata kai tsaye yana kallon ta,
Girgiza kai tayi tana faɗin.
"Hoyam! Ba zata yarda dani ba, zata iya kashe ni ma."
"Kai Anne wanda yace zai kashe ki ai sai inda karfina ya kare." Ta faɗa tana kallon iyayenta.
"Mahlika, karki damu da yarda Allah sai mun amfana dake."
Wannan kenan.
**
Tafiya ce da suka gajarce mana ta jirgin ruwa, akwai wata baiwar Azizatul Nissah, me suna maimana. Kallona tayi sannan tace min.
"Sultan Abrad yana kiranki."
"Kice ba zan zo ba"
Na fada kai tsaye,
Dafani Inam tai tana kallon yadda na hade fuska.
"Don Allah tashi kije"
"Dake nasanta da mugun tsoro mik'ewa nayi tare da bin bayan Maimana,
Dake jirgin ruwan babba ne, ba na wasa ba. Ina Binta har wani babban falo. Yana tsaye da takobi guda biyu a hannun shi.
Muna shiga ya wurga min daya.
Kallon shi nayi ina kuma kallon takobin.
"Zama a cikin Samaind sai da d'igon jarumta da kuma kirsa da kisisina, uwa uba makirci, kasuwancin da tafi karɓuwa kenan, dan haka dauka na fara koya miki yadda ake kare kai."
A hankali na kalle shi sannan nace mishi.
"Waye ya gaya maka ni abinda zai kai ni cikin masarautan kenan? Ko ce maka aka yi ni munafuka ce? Bana son damuwa."
"Ki dauki takobin." Ya fada min haka cikin lalluma, ganin yadda ya kwantar da kai, ya sani dauka. Ina kallon shi,
Jan takobin yayi tare da kirana, murmushi nayi sannan na juya takobin kafin nayi kanshi da sauri.
Tare da bin shi zan sare shi.
Buge takobin yayi tare da buge kafana da kafar shi. Faduwa nayi sosai.
Durkusa yayi gaba na, tare da dafe goshin sa.
"Kin san yadda na tsani faduwar ki nan! Sabida nasan gobe zaki amfana da wannan yanayi, tashi zaki sami wanda zai baki horon yaki Insha Allah. Akwai mutumina a cikin masarautan, ba zan gaya miki sunan shi ba, dan ba hankali ne dake ba."
Haka ya cigaba da bani, horo har dare ya raba, muna abu daya sallah da abinci muke ci, mu cigaba da faffatawa, na gaji tilis faduwa nayi ina haki.
"Toh tashi muje ki kwanta," gwalo idanu nayi tare da kallon shi fuskana a murtuke nace mishi.
"Haila yazo min yanzun!"
"Baki da kunya ce?"
"Ai babu kunya a tsakanin ku, idan na barka abinda zaka min ko kunyar rayuwata ba zaka ji ba"
Na mike ina barin falon, bin ta yake da wani irin kallo, tare da jin kamar da ruhinshi take tafiya,
**
Karfe uku na asuba muka isa bakin gaɓar tekun SAMAIND, mun sami kome da kuma kowa, a hankali muka shiga sauka har inda suka tanada mana Dawakai da leken dawakan, sai sauran bayin irin su Inam da zasu shafo da kafa.
Ni na shiga keken Abrad ne, tunda na shiga cikin keken zance na shiga uku, domin kamar tsohon mayye haka ya takura min, har Addu'a nake, Allah ya rabani da kazugumin mara mutunci nan.
Karfe hudu saura muka isa gidan bakin da aka sauke mu, muna shiga kowa ya kama gaban shi, fitowa nayi sakamakon mantuwan da nayi, zan wuce naji an fisgo ni, tare da kai kanshi wuyana.
"Baki san Yakana da kawaici nake miki bane? Ko baki ga zanen da take cikin kwayar idanuna bane? Baki Fahimci dalilin dauke kai ba bane? Kina azabtar dani, kuma wallahi zan iya lamunci na ga wani ya rab'e ki ba, idan kuwa haka ta faru. Wallahi sai na raba mutum da numfashin sa."
"Toh sake ni, tun baka kashe kowa akai na ba, zaka kashe ni. Wai ku meye matsalar ku da rayuwata ce? Shi wancan ya gama abinda zata yi kai ma ka dasa daga inda ka tsaya, ba zan fasa gaya muku ba ina da wanda nake so! Ina da abokin Rayuwata." Daga haka na juya zan bar gurin, muka hadu da Azizatul Nissah.
Kallon juna muka yi zunzurutun kishi na addabar ta, bata san lokacin da tace min.
"Karya mara daraja!"
"Babu damuwa, sirrina ne maza suyi yaki a kaina, martaba ta ce duniya ta bagwaza akai na, Alfahari na ne, zaratan maza su tsaya a bayana. Daukaka ce na zama kalabi tsakanin rawuna!"
Na fada ina kallon ta, d'aga hannu tayi za....
#Mai_Dambu
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Page 17...
Marina zatayi Nawwas ya rike mata hannu.
"Kana jin tana gaya min magana akan idanun ka?"
Ta faɗa a fusace,
"Meye a cikin shi? Gaskiya ta gaya miki, ita din kalabi ce a tsakanin rawuna, karki d'aga mata hankali, ki barta a zauna lafiya."
"Akan wata banzan yar karamar kasa? Wacce take fatar..."
"Wai meye haka?"
Inji Abrad wanda ya fito, kafin Azizatul Nissah tai magana, Nawwas ya mishi magana tare da nuna mishi babu kome, riko hannuna Abrad yayi ya wuce dani.
Wurga ni yayi saman shimfid'ar shi.
"Meye kike bukata? Ba zaki nutsu ba ke kenan fada kamar wata kar.."
"Abrad nice karya?"
"Ba haka nake nufi ba!"
"Lallai kuwa."
Mik'ewa nayi da sauri zan fita ya riko hannuna, kwacewa nayi tare da fita daga dakin, zunzurutun raina ya b'aci sosai, ko kallon gabana bana yi.
Ban tsaya ba, na nusa dajin dake cikin birnin, sai da nayi tafiya me nisa, sannan na fara jin maganar mutane kasa kasa.
"Dole gobe na idda nufina, Sabida na rantse babu nada shi da zasu yi. Kuma nasan dole zai fito ran gadi cikin satin nan matukar ban kashe Mehran ba shege."
Ji nayi an rufe min baƙi daga bayana, tare da juyar dani, kallon juna muka yi, cikin wani irin murya da zan iya rantse da Ubangiji da ya Halicce ni, ba mutum bane, ya saka min hannu a bakina, tare da kai kanshi kunnena, yana sauke wata irin numfashi, rike rigar shi nayi sakamakon jin da nayi kafaffuna basu iya daukata.
"Karki yi ihu!"
Wani irin abu naji ya daki zuciyata, lokaci guda naji ina kokuwa da numfashina, a hankali yake janye fuskar shi daga kunnena na, zuwa wuyar shi. Sai ga d'an kunne na ya rike rigar shi, wani irin numfashi naja tare da damke shi, a hankali ya d'ago hannun shi, kamar wanda ake koya mishi aikata kome ya kai kunne na, ya zare dan kunnen, sannan ya ya kalli fuskana da take rufe, da sauri wanda yake hade da sanyin dabi'a, ya janye a jikina, sannan ya rankwafa yana ƙoƙarin d'ago kai na, ina kauce wa, shafa bakina yayi da yatsar shi, yana kallon gurin mutanen, a hankali yakai hannun shi kan takobin shi, a tare muka kalli juna, hasken farin wata hade da reshen biya yayi mana iya ka da kallon kwayar idanun juna.
Hancin shi ya goga akan nawa, wani irin abu muka ji kamar an watsa mana ruwa, ala tilas ya janye hancin shi, lokaci guda ya tab'a wuyana. Daga nan ba san kome ba, kuma ba zance na san yanayin fuskar shi da kome nashi ba, abu daya na sani shine muryan shi wacce take bugawa kwalkwalawa ta, da zuciya ta wani irin yanayi.
A hankali na bude idanuna, akan Abrad, wanda ya damu sosai. Kallon su nayi naga nima kallona suke, tashi nayi zaune tare da cewa.
"Nayi gamo ko?" Na tambaye su.
"Bamu sani ba, amma mun ganki a kwance gefen ki kadan an kashe wasu mayakan kisa!"
Zubur nayi ina kallon su.
"Wallahi aljani ne, ban tab'a jin ko ganin irin shi ba, don Allah ku nimo min malam ruki'a su duba ni!"