Showing 15001 words to 18000 words out of 274096 words
Chapter 6 - DAULA BIYU Complet Document .txt
Ana kai shi matar nan ta saka aka kwashewa dabbobin da muke kiwo, ban san yadda zance ba, amma bayan zaman makokin Baffa mun koma kamar zamu mutu,
Noman ne yake kawo mana abinci, yau na tashi da wani irin tashin hankali, haka kawai naji rai na bai kwanta da bakin da muka yi tun daren jiya ba, sun sauka a dakin Mamma.
Ina wanke kayan da suka b'ata, tare da wanke na wankewa, Airan kuma ta fita da dabbobin Mamma, ni kuma ta dakile ni a gida dan tasan bana kaunar Airan ta fita da dabbobin.
Sallamar Noman naji a kofar gidab mu, na leka.
"Ina Matar Baffan ku?"
Kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Tana cikin gida!"
"Kice ina magana da ita"
Da sauri na juya, dauke kai yayi idanun shi na cike da kwalla.
Noman fari ne ba can ba, yana da kira irinta sadaukai, sannan yana da matukar kwarjini da haiba. Sau dayawa a cikin garin mu, muna kiran shi sa Maza gudu.
Shi yasa Yan mata suke kishin akan nice kawai nayi sa'ar samun shi.
.... Fitowa Mamma tayi suka yi magana, ba tare da wani dogon tashin hankali ba, tace min.
"Ki bishi ki kado min Dabobbina, ita kuma karamar ƙaruwar ku dawo da ita."
Duk da ban fahimci abinda take nufi ba, amma sai da naji kamar zuciyata zata bar gangan jikina. Ban iya motsin kirki ba, haka na bi bayanshi har bakin rafi inda ake kokarin nimo Airan a cikin ruwa, ga dai alamar inda aka yi mata ta'asar, ya b'aci da jini.
Jikina na rawa lokacin da na sami takalmin ta, da sandarta sai zaninta wanda ya b'aci da jini kamar anyi yankan rago, wani irin kuka nake me mugun sanyi, amma babu ko digon kwalla a idanuna, dakyar aka samo ta cikin ruwan, dayawa sun dauka ta mutu ne, sai da suka. Ji bugun zuciyar ta a jikin hannunta suka ce.
"Tana raye!"
Duk sai na rikice na rasa abinda zan yi, daukar zanin. Indela tayi tare da daura mata, aka nufi gidan me magani,
Tunda muka kaita, matar nan take gaya min magana akan ita ba zata tab'a d'aga kai ta duba ta ba, sai mun bata silalar kudi me yawa.
"Ki dubata zan biya."
Inji Noman.
"Ko Anwarulkharim ba zai sani nayi abinda banyi niyya ba, dan haka ku ajiye min kudi na dubata."
Haka yafita ina gurin ya nimo kudin ya kawo, tace.
"Ba zan dubata ba, kudin yayi min kad'an"
Sake fita yayi, can sai gashi ya kuma dawowa, dakyar dai ta duba mu. Muna tsaye Mahaifin shi yazo.
Kallon mu yayi sannan yace min.
"Ina rokonki da Allah, ki rabu da shi, bai tab'a min sata ba sai akanki, ku ba mutanen kirki bane kuma bana son na rabaku da karfin tsiya, amma bari na miki misali, a hankali da kanwarki take ciki zaki iya kome saboda ita ko Bazaki iya ba!"
A hankali na zuba mishi ido, sanan nace mishi.
"Zanyi idan ta kama wasar rayuwa ko mutuwa."
"Alhamdulillahi, toh don Allah idan kina son na barku ku cigaba da zama a wannan yankin, ki fita a rayuwar shi. Idan ba haka ba, zan sanya a muku koran kare."
Daga haka yaja hannun shi zai tafi dashi. Kai na a kasa Noman ya rike hannuna,
“ina tare da ita Abba ba zan iya binka ba"
Kallona Abban shi yayi, sannan yace min.
"Kiyi mishi magana mu tafi!"
"Ka bishi mana,"
Ina fadar haka na juya mishi baya, ban kuma kallon shi ba, har suka bar gurin mu.
Isowar Mamma da wadannan mutanen ya sani kallonta.
"Ya jikinta?"
" Ana kan duba ta"
Murmushi tayi sannan tace min.
"Toh babu damuwa,;"
Sannan suka bar gurin, tunda aka gama kula da Airan, nake bin gida gida niman sadakar abinda zan ci, babu wanda ya bani. Dakyar na hadu da wani abokin Noman ya bani gurasa, na nufi gidan me magani, ina shiga na samu Airan tayi fitsari ko nace wanda yake fita a jikinta kowani lokaci.
Haka na bata na wanke kayan, sannan na zauna naci guntun.
Kwanan ta biyu a gidan matar ta kore mu, dan masu zaman jinya sun gudu wai masifa ce zata shafe su.
Masu zuwa ganinta kuma suka daina, haka na dauke yarinyar na sakata a bayana, duk inda muka bi sai anyi mana, ihu da atule. Allah kadai ya kai mu gida.
Shekarun Airan goma sha uku ne, wannan waki'ar ta same ta, haka nayi ta kula da ita, ga jikinta kamar lalacewa yake, haka zanyi ta wanke ta da ruwan zafi, har sai ta daina kuka. Sannan na saka mata tsuma na rufe mata gurin sabida fitsarin da yake zuba mata.
Muna kwance da daddare, Mamma ta shigo dakin.
"Ikram! Dama nazo ne na baki shawara ko zaki dauka akan ciwon Airan!"
Zubur na mike, ina zare ido.
"A cikin bakin da nayi ne tace min ko zaki shiga birni ne domin aikatau? Kinga idan kika tara kudin sai mu kaita asibitin a can."
"Na amince, indai zata sami lafiya zanje."
Murmushi nayi sannan ta nufi dakin ta, ta gaya musu, a daren ranar muka nufi babban birnin Sudan.
** Baya bata kaɗan.
Bayan tafiyar su, Mamma ta fito da kudin da aka bata, ta shiga dakin Airan take kwance, daukar ta tayi tare da nufar gidan me magani, dan dama itace tayi sanadin faruwar kome, tun daga fyaden da kin basu kulawa ta sayar da Ikram ita kuma Airan zata meda ta karuwa tana samun kudin shiga , dake Airan din bata tafiya dole ta goyeta.
Tana isa kofar gidan Airan tayi mata nauyi, kamar an daura mata shirgi.
Koda ya shiga da ita gidan, matar ta dubata ta, girgiza mata kai tayi alamar yarinyar ta mutu, tashin hankali ta shiga tare da niman taimakawa aka mata wanka akan gobe da safe za a kaita makwancinta na gaskiya....
(Me karatu wannan shine mafarin tafiyar mu🏇🏽)
***
*Andulus*
Yau kwanan su tara kafin suka iso babban birnin kasar, kallon juna suka yi sannan suka nufi gurin wasu yan daudu, gaisawa suka yi sannan suka tambayi.
"Kais! Muke nima?"
"Ai shugaban mu, toh sannunku yan samari, kuzo mara ba da manyan sadaukar kaga wani labcecciyar kirji me hana mata sukuni."
.suna magana tare da nuna su da yatsa, har cikin wata gidan alfarma suka shiga, sannan aka musu iso.
Suna shiga suka zauna, a kujeran da ya nuna musu. Zama suka yi tare da cewa.
"Muna buƙatar?"
"Aidah ki kawo musu bayin nan duk da na yammacin Afrika basu iso ba."
"Toh shiga ba, an gama!"
Yadda yayi maganar kamar wani mace,
Fita yayi, bayan kamar minti goma sai gashi dauke da wasu yan mata, tsirara suka nufi cikin dakin. Juyawa suke tare da nuna musu su.
"Ya sunyi?"
"A'a sunyi shekaru dayawa, bamu son me yawan shekaru!"
"Toh zaku yi mana hakuri nan da kwana goma kayan mu zasu iso. Kafin nan kuyi shagali!"
"Bashi bane a gaban mu, abinda muke bukata idan zamu sami kayan takasance babu wanda ya kutsira."
"Duk abinda nake ina yi da lissafi! Duk da bani da lissafi, amma ina fahimtar kidaya. Ku jira nace"
Da haka suka amince da shawaran shi.
**((Page 9)))
Muna isa da asuba, babu batun sallah, bakin tekun aka kai ni, inda aka yi ta zuba mutane a cikin wani abu ana rufewa. Fita mutumin Mamma yayi da matar da muka tawo da ita, suka tafi wani guri can sai gasu sun fito suna dariya.
"Toh Ikram Allah ya ƙaddara saduwar mu, matar Babanku ta sayar mana dake, ita kuma kanwarki zata cigaba da mata karuwanci,"
Ashe kuka rahama, ce dan bana iya cewa kome, sai ajiyar zuciya. Haka suka jani zasu wurgani cikin abun, na shiga ihu tare da cewa.
"Ba zaku tab'a sayar dani ba, idan na fito sai na kashe ku. Mugayen banza mugayen wofi."
Ina ji ina gani aka watsani cikin abun aka rufe mu.
Daga nan muka suka karasa sauran aikin tare da d'aga jirgin ruwan.
Wato ban san me zan gaya muku ba, tafiya ce wacce bamu san inda muke tafiya ba, bamu ganin juna, Bama fahimtar saye a kusa damu,.sai dai da zaran mutum ya.mutu da yinwa da ƙishirwa zasu bude mu, a cire shi a jefa cikin Teku.
Ban san iya adadin mu ba, amma a yadda nake jin hiran masu kuzarin cikin mu, muna dayawa, basu bamu abinci sai munyi kwana biyu, sannan a watsa mana gurasa, da dambe ake daukar shi.
Sannan kuma yawan mu bamu da karfin haka, tafiyar kwana goma, a cikin shi sau biyar muka ci abincin.
Mafiya yawan mutanen cikin mu, sun mutu an zubda su cikin ruwa, kafin muka isa, cikin talatimin dare, haka ayi ta zuwa ana fidda mu.
Har aka gama sauran kuma aka kai su tsakiyar ruwa aka zubda su.
Idan ka ganni nayi da kan da kan, na kode babu abinci. Muna shiga gidan kais aka turo mana katon tire da abinci, haka muka shiga warwaso, duk warwasonka za a kara maka, sai dariya ake mana.
A hankali muka nutsu tare da cin abincin, me dad'i. Ina ci ina kuka tare da tunowa da Airan, har muka koshi.
---- bayan mun haka aka kai mu wani katon daki daga nan muka yi wanka, sannan aka bamu wani dan kamfe, muka rufe gaban mu, kafin aka nuna mana hanyar fita.
"Ba zan fita da wulakancin ba, tsirara?"
Buge min baƙi su yi, tare da jana da karfin tsiya,. suka nufi babban falon Kais, aka watsar dani, da sauri na kare kirjina, tare da dunkulewa guri guda.
Sauran yan matan haka, suke tsaye.
Tasowa yayi tare da kama gashin kaina, ihu na saka tare da kai mishi duka,
"Ya kuka ganta!"
"Eh toh har yanzun gaskiya da sauran domin bamu ga fuskarta ba, ba zamu iya sayan!"
"Wallahi sai na kashe ku, Idan kuka saye ni!" Na fada ina zare musu ido.
"Tayi!"
"Me yasa kace haka?"
"Ban sani ba, amma tana da kyauta na musamman, ka duba kwayar idanunta!"
Haka ya ture ni sannnan yace.
"Dinari, dubu sau dubu."
"Mun kara maka da bugun tsabar dinari. Yau zamu koma"
"Wallahi ba zaku dauke ni ba."
Muka fara kokuwa dasu, wata yar riga aka saka min tare da daukata aka fice dani, ihu nake ina gaya musu sai, sai na kashe su,
Akan idanuna akayi ciniki na,.tun daga Sudan ake saka min furashi. Tafiyar asuba muka yi, dake zasu sauka a Askandariya.
Dole kafin mu isa can dare zai yi.
***
Sultan Abrad.
"Yau saura kwana tara su dawo, bana son kome ya kuma jagulewa ba a cimma matsaya guda ba."
"Insha Allah zasu dawo nan da bada jimawa ba!"
A bukatar shi, idan aka kawo baiwar a cikin kwana biyu, zai sallame ta.a yadda yace Kenan.
***
*Masarautar askandariya*
Ihu take tare da kai musu duka, tana tirjiya, su kuma samudawan matan suka dauke ta da karfin tsiya, suka makata da kasa, wani irin ihun take sauran matan suka fashe da dariya, suna ihu.
"Kai kuyi mana shiru. Gidan sarautar mu ba a hayaniya da ihu."
Inji wata mace wacce take da matsakaicin shekaru, yanayin fatar jikinta me duhu ne.
"Ku sake ni mugaye Azzalumin mai nice ajalin Sultan Abrad sai na shayar dashi gubar mutuwa. Sai na lalata kome nashi."
Buge mata bakinta aka yi, ta fashe da wani irin shakurarren kuka, lokacin da ta ji suna duba yan matancinta, sannan suka sake ta, tare da wurga mata towel ɗin ta, ta rarruma, ta daura tare da mik'ewa akan diga dudduginta.
Wani sabon kukan ne ya kuma kwace mata.
"Ki daina wannan haukar? Domin gobe zamu wuce dake Oman."
Had'iye yawun tayi, cikin kuka tace.
"Me yasa zaku kai Ni Oman bayan kunce Sultan Abrad ne ya saye Ni? Wai ma waye su?"
Wucce ta suka yi, basu bata amsa ba, daga bayanta aka ce mata.
"Ke yar Afrika bakar fata, wani izza kike ji dashi?"
Cikin zafin rai ta juya tana kallon su, gyara tsayuwar ta yayi, sannan tace.
"Ismi Bilqis ALMUSTAPHA! Wata ta kuma kirana da bakar fata sai na yanke harshen shi."
"Toh munji baiwa bilqis!" Cikin zubda kwalla, ta kalle su. Cikin kuka ta dauki duk wani abu ne hannunta ta shiga buga musu, suna gudu.
"Wayyo Allah na, meye nayi muka da zafi kuka rabani da ahalina?"
"Ke ki mana shiru! Ku kuma yan mata mu fita,"
Haka suka fito suka bar bilqis a cikin ban dakin tana kuka da ihu, yar kimanin shekaru goma sha bakwai.
Wadannan samudawan matan suka fidda ita da karfin tsiya, suka kai ta wani dakin da ake ajiye ta, tare da wurga mata kayanta.
Zama tayi tare da sake kuka me mugun cin rai, tana kallon yan matan da suke dakin..matsowa kusa da ita wata yar budurwa tayi, tare da daura kanta bisa kafad'arta.
"Yar uwa!"
Kuka ne ya kuma kwace musu, tare da rike junar su.
"Kiyi hakuri!"
"Sun saye ni kamar dabba, sun raba Ni da kowa nawa, sun mayar da rayuwata mata amfani!"
"Meye nayi musu? Meye na katse musu? Allah ya saka min."
.na Cigaba da kukana haka matashiyar yarinya ta Cigaba da rarrashina, tana bata hakuri.
"Gobe zasu wuce damu Oman!"
Wani irin kwalla ne ya shiga zuba min, ina kallon yarinyar.
"Wallahi ba zan tafi Oman ba, ko zasu kashe ni sai na gudu"
Na faɗa cikin tabbatarwa kaina zan aikata abinda na faɗa, shiru dakin yayi, babu wanda yayi magana.
~~~
A fadar Sultanah Amrah na kasar Askandariya. Dan dukawa suka yi, sannan suka ce mata.
"Muna godiya Sultanah Amrah da bamu masauki gobe Insha Allah zamu wuce Oman, mun gode ainun."
Ƙasaitacciyar murmushi tayi sannan tace.
"Tsakanin mu da Sultan Abrad akwai yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya, sannan babu amfanin hana ku masauki. Dan haka dukkan abinda kike bukata langesa zasu muku!"
"Mun gode ranki shi dad'e, mun sami kome ma!"
Ya kuma fada a karo na biyu, jinjina kai tayi sannan ta d'aga musu hannu.
Babu musu suka fita, daga cikin fadar.
"Nawwas, akwai matsala fa?"
Kallon shi wanda aka kira da nawwas yayi sannan ya cigaba da tafiya.
"Yarinyar nan!"
"Me ya faru?"
"Ta tabbatar da zata gudu gobe"
"Allah ya nuna mana goben.,"
Ya faɗa tare da murmushin mugunta.
Haka suka karasa dakin su, bayan yan matan gidan sarauta sun zo debe musu kewa, da yan kad'e kad'e da raye-raye.
"Kana tsoron kar ta gudu ne?"
Gyara zama Zur yayi sannan yace.
"Ban ga rashin tsoro a idanunta bane,"
Murmushi Nawwas yayi sannan ya cigaba da wasa da hannun shi yana faɗin.
"Zuciyarta a kone yake"
"Kamar ya?" Inji Zur,
"Daga yadda take iya sarrafa harshenta da fushinta!"
"Kasan ban lura da haka ba, domin nasan dai."
"Akwai ciwo a ranta wanda yasata kasa boye b'acin ranta, idan ta cigaba da sarrafa fushinta har aka kai ta Samaind, sunanta gawa. Sai dai yanayin kaddara idan ta sauya."
Ya faɗa haka yana kallon, wata da take rawa.
**
Gezira.
Kurawa mahaifin shi ido yayi cikin wani irin kaduwa. Bakin shi ya gaza furta kome, sakamakon kukan da mahaifin shi yake,
"Noman na cuci kaina, gashi saboda son zuciya na cutar da Yaran da babu ruwan su. Gashi ba aje ko ina ba, anyi....
#Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1032581704?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=6I7W6FRqTxinGtl9jgfvth%2BS5iQWEYUprgoAPgiWur5smXqzWL5Ee8uUktHwu3iZ2WdtcLySltEgKfb2Jk1Kb0GbW3xpNIkEcvn7jurBV9R91%2BsJQqQzRV5V0rw3oBhA
🐾ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜🐾
_The Historical_
~BOOK ONE~
Mai_Dambu
Bismillah Rahamani Raheem.
Page 10....
Wasu irin kwalla ne suke kokarin sauka daga cikin idanun shi amma ya dakatar dasu.
"Abba me yasa kayi min haka? Ka cutar dani ka cutar da Yaran da Babu ruwan su? A sanadin haka Har Airan ta rasa rayuwarta. Yau gashi nan abun ya faɗa kan mu"
Ya fada a sanyayye, gwanin ban tausayi.
Share kwalla yayi sannan yace mishi,
"Wallahi ban tab'a ganin Muguwar mata irin matar Malam Almustapha ba, ka yafe min ka yafe min abinda nayi muku."
Mik'ewa Noman yayi, tare da barin gurin mahaifin shi, gidan su Ikram ya nufa, tare da shiga kai tsaye. Ya sami gidan kamar ba ayi mutuwa ba. Domin ya cika makil da yan iska, sai karta ake ana ta sharholiya.
Kwallo ya shiga yi da kayan gidan, tare daka musu tsawa.
"Ku fita kafin na ci mutuncin ku"
Ganin yadda ya koma kamar wani zaki ya sa kowa ya shiga barin gidan, a tsora ce.
Takowa yayi idanun shi jajjur gaban Mamma,
"Ina take?"
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Bana tunanin tana raye ma, domin ko ta mutu an wurgata cikin ruwa ko kuma tana can cikin Sudan tana aikatau."
Da sauri ya juya tare da barin cikin gidan..
**
Askandariya.
Tunda aka kawo mana wani kunun alkama da madarar rakumi, sai wani dan fai-fan abu kamar burodi, dashi muka karya, a hankali na mike tare da