Showing 81001 words to 84000 words out of 274096 words
Chapter 28 - DAULA BIYU Complet Document .txt
Ba zan miki dole ba, sai dai ki sani kece kika kunna fitilar Mehran! Kuma kece kika kashe fitilar Mehran, nasan koda na hanaki ba zaki hanu ba, amma bana cire rai da rahamar Ubangiji, zaki dawo gare mu."
Har ta isa bakin kofar ta, tace min.
"Ki tuna uwar da aka rabata da D'anta, aka kuma saubanta rayuwar shi domin Muradin rai! Ki tuna irin kukan da uwa take a duk lokacin da aka ce mata D'anta Ya faɗa matsala, ki tuna uwar da take faffutikar rayuwar D'anta ya inganta.
Nasan nayi laifi mafi girma a rayuwa ta, iya haka idan Ubangiji ya barshi a matsayin hukuncina yayi min gata, Ban tab'a kisan kai ba duk kuwa son mulkina, amma ina ji ina gani aka daura min Sharri yau kimanin shekaru talatin da takwas ina nan! Nagode Ikram!"
A hankali na duba a azurfan da ya bani, tare da kallon shi a raina ina cewa.
*Ina son ganinka!*
Sanyin da ya kuma dawowa cikin falon ya sani zuɓewa a gurin ina sauke numfashin wahala.
"Jikata!" Da sauri na mike tare da kallon shi. Murmushi nayi sannan na bude baki zanyi magana yace min.
"Nasan ba zaki tab'a fadan Alkhairi ba, abinda ya kawo ko nan min zo ne ki gaya min wato hada miki baki muka yi ko?"
Yayi murmushi sannan yace.
"Ko daya! Sai dai idan kika bar daular nan a cikin kwanakin nan,. Zaki yi ta fadawa hatsari har sai kin dawo gare shi. Zaki fuskanci meye asalin rayuwa! Zaki yi kokarin ganin kin dawo amma ina daular tayi miki nisa kafin ki cin mishi.
Ina miki murnan sabuwar rayuwar da kika zab'e fatan Alkhairi, a duk lokacin da kika Fahimci tazarar da take tsakanin ku zaki iya nima na, kai ki ambaton Allah kika yi sau uku sannan kika yi tawwasali da fiyayyen halittar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, zaki ganni amma kafin nan. Kamar yadda rubutu baya dama a saman Teku haka zaki ji kome ya tafi.
Kina zarra da kika gada a gurin Almustapha! Kina da Izza da kika gada a gurin Joindatullah! Jinin Amratu yana yawo a cikin jininki, ki shiga duniya niman nasabarki, nan zaki gane falalar da Allah yayi miki ya ajiye ki a cikn wannan daular."
Daga hana ya juyar da hannun shi, tsintar kai na ayi a falon, tab'e baki nayi a raina nace.
*Daka hanani magana sai me?ba zan zauna ba*
Gyara kwanciya nayi a gurin ina cewa.
"Yau nasan bani da arzikin kwanan daki" dan haka na yi kwanciya ta.
~~~
Tunda ya shigo gidan ya zauna tare da tari, jini ne ya shiga fita ta hancin shi da bakin shi, kafin ya sami damar dafe kahon zuciyar shi da take mishi zafi kamar an kunna wuta. Shigowar da Sultanah Hoyam tayi tare da ganin shi a cikin wannan yanayin, da sauri ta kira Darakshan ya kira mata likitan fadar.
Ba a bata lokaci ba, aka tawo dashi. A hankali ya shiga duba lafiyar shi,. Ya jima sosai akan shi kafin ya koma kasa tare da saka hannun shi a cikin jinin da yake kasa, murzawa yayi sannan a hankali ya juya tare da kallon Sultanah Hoyam, yace mata.
"Ranki shi dad'e! Ai matsalar da ake samu zuciyar shi ce take ciwo! Akwai abinda yake b'oyewa a ran shi wanda ya haifar mishi da ciwon zuciya. Ku tabbatar ya gaya muku, idan ba haka ba tabbas zaku iya rasa Sultan Mehran har abada, domin ciwon tayi mishi mugun kamu."
A hankali ya gama musu bayani sannan ya dauki yar jakar shi bayan ya basu maganin da zasu bashi, bayan tafiyar shi itama Sultanah Hoyam ta koma b'angaren ta, aka bar Fudail da Rakshan, suka zauna dashi bai farka na, sai tsakiyar dare. Ruwa suka bashi ya sha sannan ya koma zai kwanta ya kalli Fudail.
"Ina take?"
"Baka da lafiya Mehran, ka kwanta ka huta."
Lumshe idanun shi yayi sannan ya kwanta tare da Cigaba da barcin shi.
......
"Me yasa ba zaki zauna dani ba."
Bai tab'a zaton zata iya daukar wani abu ta illata shi ba, sai yanzun da ya gani da idanun shi.
"Me yasa Qurratulain? Mutuwa ta itace fansar ki?" Ya faɗa dai-dai hawaye na zuba daga idanun shi. Jini yana zuba daga kahon zuciyar shi.
Gashin kanta ya rufe fuskarta, kayan jikinta ya jike da jini jagab.
"Kin san iya adadin lokacin da nayi ina dankon ki? Me yasa Qurratulain bata bincike Ni ba?"
Shigowar wasu mutane da jajjayen kaya, hannun su rike da takuba, suka mata zasu yi cikin sani irin zafin nama, ya juyar da ita tare da cillata saman kujeran mulkin shi, sannan suka soka mishi takuban su, dukkan su bakwai har sai da takuban ya fito ta kowani kusurwa, zare wukar da ta soka mishi a kirjin shi yayi tare da tasa wani irin ihu.
Sannan ya watsar da takuban da suka soka mishi, ya juya da wukar yayi ta kashe su, yana gamawa ya isa gaban ta, tare da zuɓewa a gaban. Ya daura kan shi akan cinyarta.
Garin yayi wani irin Ja, tare da zubar jini ta ko ina, kamar ruwa, hayaki yana tashi a wajen garin, kukan al'umma da na dabobbi ya yawaita, kamar zasu fasawa mutane dodon kunne.
"Ki sosa min kai na." Hawaye ke zuba daga idanun shi, yana jika cinyar ta, itama kuma hawaye ke zuba mata, tare da fashewa da dariya. Ta ture kanshi, tare da fasa ihun da sai da tagar da suke cikin fadar na glass suka yi ta fashewa, tare da zuɓewa akan gwiwar ta.
..... A firgice ya farka tare da dafe goshinsa,. Yana mamakin wannan mafarkin me matukar girma da muni. Sanyin asuba ne yake ratsa jikinsa.
Ya lumshe idanun shi, tare da jin kiran Sallah daga can nesa, murmushi yayi sannan yana hango yadda take sallah.
---
A firgice ta farka tare da sauka a gadon ta fito falon da Ikram take zaune itama zufa take,cike da tashin hankali,kallon juna suka yi sannan Sultanah Fazilatul nisa tace mata.
"Kema mafarkin kika yi?"
A tsoro ce tayi tambayar,
Cikin fitar numfashina na kalle ta, sannan nace mata.
"A'a!"
"Eh shi kika yi! Idanun ki basu boye karya, sabida baki iya ba, kin iya boye damuwa ban da karya, mafarkin rushewar daular kika yi ko?"
Ta faɗa cikin kuka tare da kallona.
"Eh!" Na bata amsa a takaice, ina shakkar abinda zai biyo baya.
Juyawa tayi tare da rufe kofar, alola tayi sannan ta gabatar da sallah nafilla, tare da kiran Uwaisul Qarni.
"Sultanah! Ku barta ta tafi! Karki kuma dakatar da ita, Insha Allah, Allah zai sauya kaddarar shi, amma babu makawa kaddarar su a haɗe take, ƙaddarar shi ya shiga nata, haka kuma na nata ya shiga nashi.
Zata dawo amma ban san lokacin ba, ban san me zata dawo yi ba, Allah ya sani. Shi zai kawo mana karshen rikicin masarautan nan. Rabo me tsannanin zai dawo da kome a kuma Cigaba da abinda aka dakatar. Shi kuma kiyi hakuri Insha Allah zaki sha mamakin yadda kome zai sauya. Zai baki damar samun D'anki a hankali kuma a hannunki. Karki manta Addu'o'in da kika yi ta mishi a baya shine zaki Cigaba da mishi har zuwa lokacin da rayuwar shi zata yi kyau mafarkin ku da kuka yi Allah ya fahimtar dani wani abu kan shi. Ki barta ta tafi, idan kuka sake ta zauna ba mamaki hakan ya faru ,na barki Lafiya."
Gyada kai tayi tare da sauke ajiyar zuciya, abu biyu lokaci guda, farin ciki da bakin ciki, bata kuma zazzafa tunani ba ta cigaba da ibadarta kamar yadda ta saba.
~~~
Bayan wasu kwanaki abubuwa sun faru, a cikin shi har da mai dani shashin sa, zai sakani a gaba yana kallona, ina juyawa zai dauke kan shi fuskar shi a nanike, tab'e baki nake na cigaba da abinda nake, tunda dan bakin mulki dawo dani Office din cikin gidan yayi tare muke zuwa kuma muke kome, yayi ta wani cin magani kenan.
Yau saura kwana uku a fara hidimar zab'ar matan da zasu zauna kafin su saba ayi maganar auren shi....
----
*Wayyo Allah na! Labarin nan bai zama dole ya kare 40 ba maybe mu kara koda page 2 ne akan Free Pages din*
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 GTBNK Ramlat Abdulrahman Manga ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Page 40
*Last free Page"
Wato tun da na dawo nake lura dashi bai da lafiya, sai dai yaki bani damar fahimtar haka, zan ga wani lokaci yana amai, ina zuwa zai dauke kan shi tare da k'in juyawa ya kalle ni.
Yau ma da ake ta kawo mishi kayan da zai saka na zab'en tsaye yake tare da wani farin tsuma, juyawa yayi tare da kallon inda nake tsaye, nima na juya bayana tare da jin ba dad'i.
"Sultan wannan zai yi kyau! Sosai sannan zai dace da rana irin ta jibi ko Ikram?" Darakshan ya tambaye ni.
Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Zaifi dacewa da wancan itace kalar maza, sannan wannan kuma shigar mutanen Sham ce." D'aga kayan aka yi tare da nuna mishi.
"Bana bukata!" Ya faɗa fuskar shi a haɗe, dole zai min haka, amma kuma bai dame ni ba, haka na wuni suku suku, da magariba ina zaune na saka abinci a gaba, ina kallon shi ya shigo abin shi bai kalle ni ba, sai dai naji yana tari. Koda na isa tare da bashi ruwa buge hannuna yayi sannan yace min.
"Bana bukata!"
"Wai meye nayi maka ne?"
"Baki san me kika yi ba? Toh tashi daga nan"
"Amma Aamaan me nayi da zafi ne rayuwa kowa na da nashi ra'ayin da kuma abinda ya zab'e me yasa kake son tilasta min na zab'i abinda ba zai amfane Ni ba?"
Idan dutse zai magana Mehran zai yi magana, shan giya yake hankali kwance, har ya fara buguwa kallona yayi tare da nuna ni da yatsar shi. Mik'ewa yayi tare da nufo ni. Mikewa nayi zan gudu ya saka min kafa, na fadi zai juye min ruwan na buge hannun shi tare da mik'ewa.
Wani irin fada ne ya shiga tsakanin mu, duk da Ni kare kai na nake shi kuma so yake sai ya kai ni bango, take min kafa yayi na maza na sake shi. Ya hada ni da bango. Tare da d'ago kai na.
Kokari yake mu hada idanu amma naki kan shi ya kai wuyana tare da kai baki shi yana sumbatar wuyar.. rike rigar shi nayi tare da ji kamar zan zube ƙasa,
Matse ni yayi tare da d'ago haɓɓa na, kai fuskar shi yayi nayi saurin rufe idanuna, jin saukar numfashin sa akan fuskana ya sani bude ido na, a hankali. Sai cikin nashi Idanun. Kasa janyewa nayi ina kallon shi da kyau, tare da karanta sakon shi a sanyayye.
A hankali zaka Fahimci inda ya dosa, tare da duk wani abinda yake tattare cikin idanun shi.
"Mehran! Me kake SO?"
"SO! Ban tab'a son abu na daban ba, dan haka ba zan tab'a yarda naso abinda ba zai kai ni labari ba, kina da damar tafiya duk inda yayi miki. Sai dai alqawari na tabbatacce ne, domin zan kashe shi!"
"Akan me? Nice na dace da mutuwa ba shi ba, karka tab'a min shi. Domin ba zan tab'a yafe maka ba idan jinin shi ya zuba a banza!" Na fada mishi tare da kwace kai na, daga gare shi. Ina jin kwalla na zubo min.
.....
Washi gari.
Ana gobe zasu yi zaben shima kuma yana na shi shirin, a baya an sa taron sai dare ne, amma ya maida abun yamma, dan haka an Kawata fadar da ko ina gwanin ban sha'awa, tare da gyara ko ina, murmushi nayi ina jin wani irin yanayi yana shiga na, daga nesa yake hangota, yau tafi mishi koda yaushe kyau da kamala, kallon yadda take murmushi iska yana kad'a rigar jikinta tare da baza gashinta dake baya a zube cikin nutsuwa.
Lumshe idanun shi yayi tare da tuno sunan da ya kirata da shi a mafarkin shi, dafa kirjin shi yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace.
"Qurratulain!!!" Ya kira sunan a hankali, kamar wanda yayi kiran da karfi sai da ta d'ago kanta tana kallon inda yake, tsuke fuskar shi yayi alamar baya kaunar tana kallon shi ma,
Table baki nayi sannan na dauke kai na, tare da kallon kasa indai wannan mutumin bai daina min tijara ba, zai ga tsiya iya ganin idanun shi. Murguda baki nayi tare da dauke kai na, daga kan shi.
.....
"Ku saka idanu akanta, ku nutsu ku duba ta inda zai shigo, idan kuka ganshi, ku kashe shi!" Yana gama fadar haka ya juya abin shi. Bin bayan shi da ido Fudail yayi shi kadai yasan meye yake ranshi.
Ya kuma kara sanin cewa dole ya dauki mataki kan duk wanda zai kawo mishi cikas. Tun tasowar shi yake bauta mishi ba tare Ya tab'a bijire mishi ba, sai dai wannan karon sunyi tarayya akan Abu daya suke so! Kuma ba zai iya hakura da ita ba sabida shi ba, sai dai a rasa kowa wannan shine kudirin shi akan Mehran, ba zai tab'a bari a cutar da shi ba.
Amma kuma ba zai taba barin shi da Ikram ba, itama ta sami abinda take so shine adalci. Ya kwana da sanin akwai masu son kashe Mehran amma basu sami damar idda nufin su ba, saboda kwarjininsa da kaifin shi. Ya sani ko a cikin taron su na masu kula da lafiyar shi, akwai mutanen da yake zargi, yazo jikin Mehran ne saboda Sultanah Fazilatul nisa,. Daukar fansa mahaifin shi Rizwan, Darakshan kuma ɗan Amir Fujai,
Yasan cewa dukkan su Abu daya suka zo yi, amma baya fatan su sami galaba akan Mehran, duk da yasan ba lallai bane su fahimci cewa Mehran bai san kome akan Mutuwar Iyayen su ba, akwai wasu suna nan zuwa kuma yasan fansa zasu zo dauka. Matukar basu so a gobe ba zasu cigaba da tanadin fansa har zuwa lokacin da hakan ya zo musu.
Duk da yasan mahaifin shi babban mashawarcin Sultan Abdus Samad ne, bai tab'a kawowa har zasu zubda jininshi sabida rashin imani ba, sannan yadda ya kasa fahimtar kome, ance Fazilatul nisa ce ta kashe Sultan Abdus Samad,. Toh meye mahaifin shi yayi aka kashe shi?
Babu makawa yasan abinda aka shirya ne, kasancewar shi ma shawarci a cikin gidan. Kuma babban Aminin Sultan Abdus Samad. Akwai abinda ya kasa fahimta sam,.sai yanzun ne yake ganin beken shi na zama har na tsawon shekaru kusan ashirin babu wani abinda ya karu dashi.
Ajiyar zuciya ya dauke tare da sunkuyar da kanshi, yana kallon ƙasa.
--- A shashin Sultanah Hoyam, kuwa rutsa Darakshan tayi tare da gyara zamanta tana kallon shi cikin nutsuwa sannan tace mishi.
" Har yaushe zaka Cigaba da had'iye fansar ka?"
Ta d'aga kafa daya ta daura akan daya cikin wani irin yanayi take kallon shi, sunkuyar da kanshi yayi sannan yace mata.
"Sultanah, ke Mahaifiyarshi ce kuma ban san me yasa kike son lallai sai munyi mummunar alaƙa ba, zai fi kyau ki sare kai na, da cin amanar da kike son nayi."
Tasowa tayi tare da nufar shi tana shafa fuskar shi, tare da zagaye hannun ta, akan fuskar shi har ta sami damar tab'a mishi agogon karfen shi, zillo yayi mata sannan ta sake murmushi.
"Zaka iya daukar fansan mahaifinka?"
"Zan iya!" Ya faɗa jikin shi yana rawa sakamakon rike shi da tayi, kamar zai fasa ihu, sannan tayi kokarin dai da suka fada gadon, tare da kallon shi. Sannan yace mata.
"Sultanah Hoyam, ki rufa min asiri."
"Zan kara maka matsayi! Sannan kai ma zan fitar da kai na nuna musu kai jinin sune d'a ga Fujai. Idan kuma kaki yarda tabbas sakamakon ba zai mana kyau ba!"
Jikin shi yana rawa, tare da rintsa idanun shi, haka tayi ta aiki da tsarin shi tare da bawa ranta da zuciyarta abinda take kwadayin samun shi, tunda yake ko bayi bai tab'a jin yayi wani abu dasu ba, amma yau ga Sultanah Hoyam tana amshi mishi samartakan shi, tare da sarrafa shi yadda ranta yake so. Gaji sosai, dan akan ta ya fara sanin mace, amma bai tab'a sanin zata iya sarrafa shi har haka ba, idan ya duba yadda ta manyanta.
Kwanciya tayi a jikin shi tana fidda numfashin wahala, ta kalle shi sannan tace mishi.
"Kana da dadin mu'amala, ban yarda ka ajiye ko baiwa ba, dan yin haka zai iya haifar mana da tarzoma, Ni daya ce a ranka kuma zaka Cigaba da ajiye ni "
Ta fadi haka tana me mik'ewa daga jikin shi, ta nufi ban dakinta tana me