Header Ads
Showing 21001 words to 24000 words out of 274096 words

Chapter 8 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1345

Ads at the middle of Article

**
*SAMAIND*


Shigowar ta fadar kenan, ta kalli mazaunin duk wasu masu fada aji na masarautar yau basu nan, ta nemi guri ta zauna cike da mamaki. Ita gwamnonin nahiyar ta zasu juyawa baya, a hankali ta mike tare da kallon Khabir.
Sannan tace mishi.
"Ka duba min a ina suke"
"Ki gafarce ni, suna can gidan Amir Hood."
"Akan me?"
"Sabida jiya kinki magana"
Lumshe idanun ta tayi tare da gyad'a kanta.
"Ka kashe min su"
"Ranki shi dad'e, ba zai yiwu ba. Sabida idanun kowa na kanki, mafi alkhairi a gabatar da Sultan Aamaan."


"Umarni kake bani?". Tambaye shi a tsawace,
Sunkuyar da kanshi yayi tare da cewa.
"A'a ranki shi dad'e, shawara nake baki!"
"Idan baki fa?" Ta tambaye shi, ranta a harzuke.
"Ranki shi dad'e, ki Fahimci wani abu, guda."


Takowa yayi gabanta sosai, yayi mata maganar da yasata sake murmushi, sannan yace mata.
"Sunci amanarki, kuma ba zai tab'a barin ransu ba, dan haka ki duba magana ta."


Murmushi take tare da gyada kanta kamar kalangariya, sai wani irin dad'i take ji,


**
Sultanah Fazilatul nisa.


Rike take da bulala take, idan yarinyar tayi kuskuren kad'an sai ta watsa mata bulalan. Har sai ta ce.
"Auch!"
"Jasra!!!" Ta daka mata tsawa,


"Idan baki nutsu ba, zan baki mamaki. Ki Fahimci Abu daya muke son yaka, fansar jinin Mahaifinki." Inji Sultanah Fazilatul nisa.
"Amma Sultanah! Ita daya ba zata iya aikin ba."
"Ina sane da hakan!" Ta bawa Shairah amsar a takaice.


A hankali take nuna mata yadda zata yi tare da daura mata darasin rayuwar masarautan,
Jasrah Abdul Mannan, shekaru goma sha biyar kenan da aka kashe mahaifinta, abisa kama shi da aka yi da munafurci sosai abin ya tab'a mahaifin shi Amir Hood, domin yana ji yana gani ana salwantar da rayuwar yaran shi, amma saboda dauke kan da yayi yasa har yau baa taɓa jin tace sai an kwace mishi hakkin shi a gurin Sultanah ba.


Ita kanta tasan ya kai kololuwar hakuri, amma ba haka bane bukatar ta, dole idan zaka yi yaki kasan da wanda zaka yi.
--
Amir Hood.


Shiru yayi yana sauraren su, sannan ya mike dai dai lokacin da aka bude kofar da Sultanah Hoyam zata shigo.


Murmushi yayi sannan ya tashi a inda yake ya nuna mata inda zata zauna.


Zama tayi sannan ya koma bayan kujeran ta ya tsaya, murmushi tayi sannan tace musu.
"Kifar da mulki na rabo ne na zubda jinin mutane, dan haka ga damar da zan iya sakewa, Ni Sultanah Hoyam Ghanim, na sauka kujeran mulkin na bawa Yarona Zakina ya cigaba da mulkinsa fiye da lokacina."


Ta faɗa tare da kallon su, dukar tabirin tayi, aka bude kofar.
Sanye yake da wata riga da wando, bayan shi wata mayafi ne me hade da rigar. Kyakyawa ne dogo me yalwan doguwar gashi, wanda ya sauka har dokin wuyar shi.


Gashin giran shi a tsatsaye yake, gashin idanun shi kuwa idan ya lumshe idanun shi, sai ya sauka akan fuskar shi, tsabar tsayin su. Hancin shi ya daidaita akan fuskar shi. Sarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.


Mik'ewa dukkansu, suka yi domin kayan jikin shi kawai zaka kalla ka tabbatar cewa sarki ne sukutun da guda, Fudail da Darakshan sune suke take mishi baya.


Dukka manyan mutanen fadar sai da suka mik'e, a hankali ya karasa inda aka ware mishi kujeran shi, Fudail ya isa gurin kujeran ya tsaya tare da dubawa sannan yaja shi baya, Aamaan ya zauna. Kafin kowa ya zauna. Tunda ya zauna bai d'ago kan shi ya kalle kowa ba.


Haka zalika bai ce kome ba, Darakshan da Fudail, zuciyar su cike take da farin ciki zasu ji muryan shi, tsawon shekarun da suka yi a tare bai tab'a musu magana ba.


Tunda ya zauna yake wasa da zoben hannun shi, kamar yadda yake cikin karamin yatsar shi.


"Yanzun dai kin hakura, duk da haka zamu iya cewa za a rantsar da shi nan da kwanaki, sannan mu gwamnonin nahiyar baki daya zamu turo Yaran mu nan da shekara me zuwa, domin halartar bukukuwan murnar cika shekara daya a kujeran mulkin shi tare da zab'ar matan da zai rayu da su, me kuka gani akan hakan?"


Kura mishi ido suka yi, ganin yadda fuskar shi take nuna bai yi na'am da abinda suke bukata ba, yasa suka kuma cewa.
"Mun baka nan da wata uku, bayan baka saurautar." Dunkule hannu yayi tare da kallon me maganar.
Sunkuyar da kai Mir Umdatuddawla yayi.
"Afwa Sultan Mehra!"
Ya faɗa, kallon su yayi sannan ya mike, tare da barin su a gurin.


Suna kiran shi da Mehran kasancewar shine Aamaan na biyu da ya amshi masarautan, kuma Sarkin su na gaba.


Tunda ya fita Sultanah Hoyam ta mike tare da cewa.
"Na bawa namiji mulki kamar yadda kuke bukata saura me?"
"Saura ki zare hannunki a cikin mulkin shi, idan kika barshi yayi mulkin shi cikin nutsuwa zaki samu kwanciyar hankali, idan kuma kika shiga cikin wannan lamari.


Zamu yi wasan zubda jinin al'umma, wanda haka kuma zai iya kawo juyin juya halin a daular Abbasid."


Ya fada cikin Izza da mulki.
Murmushi tayi sannan tace.
"Mir Rahil ni kake gayawa magana kai tsaye?"
"Na gaya miki magana ne a matsayin namiji, wanda yake da karfin al'umma a kasa shi, Hoyam!"


Wani irin kallo take mishi tare da gyada kanta. Irin zamu hadu nan gaba.


*Ku danyi hakuri kai na yana ciwo wallahi*😢
*Alqur'an akwai matsala 🤔🤣 Chakwakiyya zalla 👌🏼*
#Paidbook
#Mai_Dambu


*Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ko katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641*


Happy weekend 💞💝
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1008832612?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=hV0o6BRzWV9PE%2FPSkh1CA2aeSMIhkctp%2FU0dOLVFW44lHA944Is10c8h8lv2s34K68eKo39RK%2FCg10dJp4XTqTiWBApgP0IPngp9nByELBwl9t%2FKYgEJ0qvROFec78bS
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
```HAPPY BIRTHDAY To You MUHAMMAD KARIM, Ubangiji ya karo shekaru masu Albarka```
🍦🍰🥧🎂🍭🍮
Page 12..
Murmushin da ba zaka iya fahimtar na me ba, ta sake tare da gyad'a kanta. Har ta nufi hanyar cikin gidan shi. A hankali take takawa kasancewar gidan ya dauki shiru, baka jin ko motsin rai.


Abinda ya faru tsakanin su da Aamaan yake kuma dawo mata a rai, lokacin da tazo Mishi da batun ya amshi mulkin shi.


Tun da ta fara magana yake wasa da wata kofin da kayi shi da karo me hade da danyen azurfa, matar inda karon yake.


Kaskantar da kanta tayi cikin sanyin murya da rarrashin, tare da kalamai masu laushi da taushi me hade da tsantsar siyasa da hikima tace mishi.
"Mehran! Yau gani gare ka, da kokon barana akan wannan zaman da kake ya isa haka!"


D'ago kai tayi tana kallon shi sannan ta sunkuyar tare da cewa..
"Mehran, duk duniya bani da gatan da ya wuce kai, Mehran Daular Abbasid sun dauke min Ubana sun dauke min Uwata! Mehran ga mahaifiyarka tana zubda kwalla tare da niman ka amshi mulkinka domin na fara fuskarta juyin juya halin dangin ka."


Matse kofin karon yayi sai da karfen azurfan ta suke shi jini na d'iga daga hannun shi. Ya kafeta da idanun shi masu kama da na mashaya, har wani hazo hazo suke, idanun ya bude su kuwa wani irin kyali suke tare da tara ruwa.


Ƙwayar idanun shi kuwa dauke take da wata irin ruwan zinari ko zaiba za a ce, tsakiyar idanun kuwa d'igon ruwan toka ce, me shegen kyau.


Matukar zai kura maka idanu, kaifin idanun shi sai Yasaka ka sunkuyar da kanka, a sanyayye tayi kasa da kanta.


Baya jin zai mata magana, dan haka ya dauke kanshi tare da wasa da jinin da yake d'iga a hannun shi.
"Mehran! Sunci mutuncina, sun wulakanta ni, yanzun kuma suna ƙoƙarin kwace mulkin ka da karfi, idan suka sami nasarar haka, tozartani zasu yi, Mehran"
D'ago zafaffan idanun shi yayi, ya zuba mata su. Fuskar shi babu alamar wasa ko sauki akan shi. Dauke kai yayi tare da mata alamar tayi tafiyarsa kawai. Mik'ewa tayi a hankali ta tako gaban shi. Tare da kama hannun shi ta sumbata.
"Allah yayi maka tsawon rai da albarka, ya bamu ikon rike mulkin kasar nan a tare."


Kai hannunta tayi kanshi, lumshe idanun shi yayi abinda ya rasa kenan, shekaru masu yawa. Yau gashi ya same shi, duk da bai son magana sai dai Allah yayi mishi wani irin dabi'a, shi mutum ne me mugun bukatar kulawa. Ko yayya ka nuna kulawar ka akan shi toh bai da damuwa zai iya zama da kai.


Shima zaman na kurame, dan har sun saba da halin shi. Na rashin magana da shiga sabgar kowa.


Sai dai yana da mugun dabi'ar da ya kasa rabuwa da shi,ba kome bane sai idan dare yayi yana shan barasa,idan ya sha haka zai kwana a duk inda ya hantsila, sai dai Darakshan da Fudail su kinkime shi zuwa makwancin shi.


A hankali ya zare hannun ta akan shi, tare da kallon kofar, babu musu ta juya ta fita. Sunkuyar da kai yayi sannan a ranshi yake cewa.
*Bayan shekaru da dama yau zan fara fita waje? Hmmm"*


Ya faɗa yana me juya al'amarin, a hankali ya tab'a wata karfe, take karar ya cika falon, ko minti biyu ba ayi ba, Fudail da Darakshan, suka shigo.


Kallon dakin shi yayi, da sauri Darakshan ya wuce, shi kuma Fudail ya nufi waje can sai gasu tare da wani tsoho, yana zuwa ya fara kunce kayan hannun shi, a hankali ya ciro kayan aikin shi. Cire kwalbar karon yayi tare da wanke ciwon sannan ya saka mishi magani, kafin ya mike tare da cewa.
"Sultan Allah ya baka lafiya!"
*Allah?*
Ya tambayi kanshi, a iya sanin shi bai tab'a jin wannan kalmar ba, sai a bakin tsohon likitan masarautan.


Watsar da abin yayi tare da kallon su Rakshan yayi, sannan ya mike, dakin shi ya nufa. A hankali ya shiga ban daki, wata katon kwarmin wanka ya gani cike da ruwan zafi, wanda aka zuba mishi turarruka, a hankali ya shiga tare da zama. Bayan ya cire kayan shi. Daura kan shi yayi inda ake tanada wani matashin kai me laushi.


A hankali yake bude jikin shi ruwan na ratsa shi, ya jima yana jin dumin ruwan, tare da jin amon kalamun Mahaifiyarshi,


---
"Sultanah! Dole Sultan Aamaan zai bukaci bayi mata, masu rawa, masu kula da saka mishi kaya, hada mishi ruwan wanka!" Inji Narmin,


Cike da jin zafi abinda ya faru, kallon shi tayi sannan ta daidaita nutsuwarta tace.
"Bayin da za a kawo daga Oman zasu zo dai-dai lokacin da ake bikin nadin sarautar shi, sai mu zab'a mishi wanda muka ga sun dace da zama a shashin sa."


"Kuma Kinga kome zai zo miki da sauki!" Kurawa Narmin idanu tayi.
"Ba dai dai bane, domin ai kowa yasan Abrad ya bada Kanwar shi, bayin da zata zo dasu zasu tashi a matsayin namu ne, rashin kunyar da yayi min,Kanwar shi zata fuskance shi.


Dan sai na tozartata, na wulaknta ta, abu daya nake so.kar a yarda Sultan yaji wannan kazamin labarin"


Gyada mata kai tayi sannan tace mata.
"An gama ya shugabana"
"Idan kin fita ki kira min Khabir"inji Sultanah,


Bayan fitar Narmin,sai ga Khabir ya shigo, kallon juna suka yi, sannan ya gaida ita.
"Ka san inda Alimah take?"
"A'a Sultanah, sai dai na saka a miki cigiyarta!"
Alamar ya tafi tayi mishi, aikuwa da sauri ya bar dakin mu.
"Akwai abinda Alimah ta sani? Wanda yaja Sultanah koranta. Tabbas sai inda karfina ya kare, domin sai na nimota a fadin duniyar nan!"


**
Oman.
Yau kwana hudu kenan, da zuwan mu. Ina zaune aka kirani, a hankali ya mike tare da saka takalma na, na fice.


Ina bin bayan wacce tazo kira na, wani katon fili ne, yana tsaye rike da takobi yana, kara bawa wasu horo. Tsaki nayi a hankali idanuna ya sauka akan wata yar karamar wuka.


Me kyau na cin tufa. Dauka nayi a hankali na bi ta bayan wasu ganye masu tsayi, ina isa inda yake..na wurga mishi wukar. Kamar wanda yake gani na,kaucewa yayi wukar ta sami daya daga cikin mutanen da suke daukar horon ya'ki.


A tsorace nayi baya, zan gudu. Ji nayi an damke ni. Fito dani aka yi tare da wurgani gaban shi. Sai lokacin na lura Ashe su uku ne, Zur da Nawwas, wukar ma yar banza Zur ta samu.


Takowa yayi gaba na, ya zauna. Diban kasa nayi tare da watsa mishi zan gudu, ya damki hannuna tare da, rike wuyata zuba min ido.


Jikina ne ya mutu, nayi kasa da kaina,.a hankali na fara ƙoƙarin kwace kai na, watsewa su Zur da Nawwas suka yi, kura min ido yayi cikin jin dadi.
"Har yanzun kin kasa kwatar kanki, da kin kashe ni zaki iya tafiya ko yanzun." Tashi nayi da sauri na ɗauki wukar,


Dariya yayi sannan yace min.
"Amma da alamu yarinta yana damunki. Maza zo nan"


Kasa motsi nayi ina kallon shi yadda yake dariya, a hankali na sulale kasa na zauna. Sai a lokacin na sami damar zubda kwalla.
"Tashi."
"Ba zan tashi ba!"
Mik'ewa yayi tare da ɗaukar wukar ya iso gaba na.


Zama yayi muna kallon juna, a kura min ido yayi cikin nutsuwa.
"Me yasa kike son komawa gida?"


Kallon renin hankali nake mishi sabida yadda tambayar shi ta zama ta renin hankali, mik'ewa nayi zan bar gurin.
"Har yanzun kina da'irar birnina, dawo ki zauna."


Zama nayi ina kallon kasa, tare da wasa da kasa, A duk lokacin da na lumshe idanuna, Airan ce a cikin shi.
"Wacece ke"
"Ka kirani ne dan kaji tarihina?"


"Ban Kiraki dan naji tarihinki ba, sai dai ina jin a jikina baki cancanci zama baiwa bace!"
"Idan kuma zanen ƙaddara ta ce fa?" Na tambaye shi,
"Babu shakka, ba zan yi sake reshe kama ganye ba, dan haka wacece ke?"


"Ni ba mutum bace, ko baka ga kwayar idanuna bane?" Gyada kai yayi sannan yace min.
"Haka ma yayi."


Idanuna na kan wukar shi, dan haka burina d'aya na yanka shi ko ta halin k'ak'a, mik'ewa yayi nima na mike tsaye, tare da wukar, ya bude baki zai min magana kawai, sai jin kaifin wukar yayi a gefen cikin shi.


Kura min ido yayi, cikin mamaki.
"Meye kika aikata?"
Sai lokacin na sake wukar, tare da kwala kara, jikina yana rawa, shigowar Nawwas, tare da wasu manyan fadawa guda biyu, ya sani fashewa da kuka, tasani suka yi a gaba, har kurkuku.


Shi kuma Nawwas ya rike shi suka nufi cikin gidan sarautar, tunda ya zaunar dashi bai, iya cewa kome ba, har Azizatul Nissah da Yar shi Ilham suka zo, sun same shi ana gyara ciwon.

"Bata da laifi, ni na sakata yin haka!"
"Yaya meke faruwa ne?"
Kafin yayi magana Nawwas ya rigashi, kura mishi ido tayi sannan ta bar d'akin, duk da yana kiranta bai sanya taji a ranta zata kula shi ba, can kurkuku ta nufa, tare da sawa a dauko mata Ikram.


Tunda aka fito da ita, take kallon ta, cike da mamaki. Yadda tayi mugun kama da Mamar Ilham, dauke batun tayi tare da sawa a dauko bulala, ana kawowa tasa a shiga dukarta.


Cikin mugun kiyayya nake kallonta, haka itama. Dukda dukar da ake min bai sani dauke kai na akanta ba, har sai da suka min dukar da ko kai na kasa d'agawa.


"Kuyi ta azabtar da ita har sai ciwon jikin Yayana ya warke." Haka ta faɗa tare da barin gurin, suka jani zuwa cikin kurkukun.


Inda aka shiga azabtar dani, duk taurin kai na, sai da nayi sanyi, bana iya kuka sai na zuci. Amma izuwa lokacin zuciyata tana gida. Dan haka duk abinda ake min gani nake domin lafiyar kanwata ake yin shi.


Sai da na kwashi kwana goma sha daya, sannan yazo da kanshi. Kallon juna muka yi, sannan na wuce zan bar inda yake. Dawo dani yayi tare da kallona.


"Me yasa baki da hankali?"ya tambaye ni,
Shiru nayi tare da juyawa zan bar gurin ya riko hannuna, ya ratsa cikin gidan dani, sannan ya fito dani ta babban kofa.


Kwace hannuna nayi, ina hararar shi.
"Me yasa kika tsani kowa? Me yasa ba zaki yi mu'amala da mutane ba? Ke kin fi son kullum."
"Kasan me? Idan baka da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads