Showing 66001 words to 69000 words out of 274096 words
Chapter 23 - DAULA BIYU Complet Document .txt
ta rike hannun shi. Jan shi suka yi tare da tafiya dashi, bin bayan su tayi tana kuka. Har kofar gidan su mahlika, tunda ta isa kofar gidan ta ga kusan rabin yan garin suna gurfane, kallon yaran damisar yayi yana kallon mutumin.
"Ku hukunta shi!" Da gudu ta shigo gurin, tare da rungume yayanta, tana ihu.
"Wallahi ba shi bane ya saka aka dauko su,nice na dauko su. Don Allah ku bar min Yayana don Allah ba zai kuma ba."
"Alhamdulillahi, Sultan mara lafiyan ta farka!"
Kiran Fudail yayi tare da mishi magana a kunne, sannan ya koma cikin gidan.
Yana shiga cikin gidan, yaga yadda nake kokarin tashi zaune. Tsayawa yayi a bakin kofar, tare da kura mata ido, gaba daya ji yaƙe kamar bashi ba, wani irin yanayi yake ji akanta, wanda ba zai iya daukar shi a karamin abu ba, shafa kan shi yayi sannan ya tako kamar mara gaskiya ya iso gaban ta,.ya ja kujera ya zauna yana kallon fuskarta.
Hannun shi ya kai saman kumatunta yana shafawa tare da kallon cikin idanunta.
Dukar da kai na, nayi ina wasa da hannuna ina kallon farcen hannuna, wanda suka samu nasu azabar, d'ago kai na yayi tare da cewa.
"Meye nufinki?"
Janye kai na nayi,.tare da kallon jikina yadda ya kama magani sosai, sake tambaya na yayi ban d'ago kai na kalle shi ba, asalima dauke kai nayi daga gare shi.
A na uku ne ya fusata tare da mik'ewa yayi wurgi da kujeran tare da daka min tsawa. D'ago kai nayi a hankali ina kallon shi..
"Kin rena ni?"
"Toh ka rabu dani mana, dole sai ka zauna da ni ne, ka tafi kayi rayuwar ka, ka bar ni na koma gurin ahalina na gaji da zama a kasan ka. Ka barni na tafi nayi rayuwa ta da wanda nake so. Yana gab da isowa inda nake.
Don Allah ka kyale ni, ka barni na."
Buge min baƙi yayi tare da shake min wuya, ilahirin jikin shi rawa yake, idanun shi sun firfito.
"Kika kuma kira min sunan wani namiji, sai na cire mishi gaban shi na ajiye mishi yayi rayuwa babu gaban shi."
" Na gaya maka ina da wanda nake so na kuma na gaya maka, Noman yana nan zuwa gare ni, sai dai ka kashe mu baki daya, mara imani da tausayi, ka rabu dani mana, dole ne sai na zauna a karkashin mulkin zalincin ka, mugu Azzalumi kawai. Kaje kai da Mahaifiyar ka sai Allah ya bi min hakkina. Ina fama da maraicina kuka rabani da farin ciki na, domin biyar bukatar kanku, baku san kome ba sai zalinci ko Allah madaukakin ya hana kan shi zalinci shi yasa baya zalinci dan shi adalin sarki ne.
Ku kuma dake dabobbi ne bak..."
Kifa min mari yayi tare da kara min, d'ago Ni tayi tare da hada ni da bango, ya shiga marin bakina, kamar zai watsar min da hakora na.
"A iya kai na kake nuna jarumtar ka me yasa baka fita kasan meye a ke yi a cikin garin ba, kana kiran kanka da suna sarki kana kashe mutanen ka. Hakkin mu ba zai Barka ba."
Cak ya tsaya yana kallon fuskana, a sanyayye wannan wacce irin rayuwa ce, watsar dani yayi a gurin tare da ficewa ya barni, Alimah tana jin su. Kasa hakuri tayi tare da shigowa dakin tana kallon yadda nake goge bakina, zama tayi tare da cewa.
"Me yasa kike mishi haka? Ko baki san babban mutum bane?"
Kallon ta nayi haka kawai naji a raina bata min ba, bakamar mijinta da yake da kirki ba, ita kuma fuskarta na kalla na Fahimci tana da fuska biyu, dauke kai nayi ban bata amsa ba, dan nima idan naji a raina ko Sultan da aka haifa a mulki sai haka, surutu tai ta min har ta gaji ta fita,
Na bita da harara. Haka na zauna ina nazarin rabona da ibada na, dan haka bayan fitar ta mijinta ya shigo da Fudail.
"Ina son yin sallah"
"Me yasa kike b'ata mishi rai ne?"
"Wa kenan?"
"Sultan Mehran mana!"
Ya faɗa a sanyayye. Yana kallon yadda nake kokarin yin alola.
"Toh sai me dan na b'ata mishi rai? Ba namiji bane shi, ai anyi shi dan na gaya mishi mara dadi da me dad'i, dan haka kai ma ka kara gaba kafin na kalli cikin idanun ka na fesa maka rashin kunya."
Na fada tare da dauke kai na, zuciya yayi shima ya fita.
"Y'ata ki daina yin haka, Sultan Aamaan yana matukar girmama Al'amarin ki, karki saka shi ya fara jin tsanar wasu matan."
"Baba! Na gaji da zama a kasan mutumin da babu Allah a cikin tsarin shi, Baba na gaji da ganin Mehran baya ibada, me yasa ba zai gane girman Ibada ba, yau da ace Ahlillu kitab ne zan mishi Uzuri, amma musulmi ya haife shi fa, daular da yake mulki a gurin Kawun Annabi ne ya kafata.
Shi waye da zai barranta kan shi da rahamar Allah, dan haka Ai Cigaba da jin bakakken magana har sai ranar da ya fara sallah. Zan daina mishi wulakancin"
"A'a babu dole a cikin addini karki tilasta shi bayan bai da niyya, ki bari dai idan shi ya bukaci hakan, kusan haramun ne tistalaw ayi addinin Musulunci dole. Karki yi haka, tunda yana jin maganar ki, kiyi kokarin ganin ya fahimci addinin kanta, Insha Allah zai yi yadda kike so."
Nasiha yayi min a cikin hikima da dabara, sannan ya nuna min illar abinda nakewa Sultan Mehran, tunda a kasar shi nake bai dace na yi ta mishi hawan kawara.
Ni kuma ina mishi haka ne da haushin Mahaifiyarshi.
.... Daukar yaran damisar nan suka yi tare da kai mata dajin suna bin hanyar da tabi, can suka ganta a yashe, Allah sarki duk da harbin jikinta bai hanata yunkurin mikewa ba, ajiye mata yaran yayi tare da kallonta, cikin dabara da hikima, ya zaga bayanta ya cire mata, kwarin da ya harba mata, sannan suka bar gurin tare da hawa bishiya, suna kallon ta, yaran shiga jikinta suka yi tare da fara shan nono, girgiza jikinta tayi tana lashe kan yaran, har suka gama sha, suka mike tare da barin gurin.
Abinda ya faru ya sanya shi kara tausayin Ikram, tabbas itama rabata aka yi da nata rayuwar, shi yasa ta zama wata irin baudaddiyar mutum mara dadin zama. A hankali suka sauko tare da barin dajin, tunda yazo garin jiya bai samu yayi wanka ba, dan haka suna isa gidan Yasaka Fudail ya hada mishi ruwan yayi wanka, sannan ya cire kayan marasa nauyi dai dai da shigar kowa ya saka, tare da ajiye na mulkin yana me jin shi sakayau.
Yana son zuwa duba jikinta dukda abin da tayi mishi, amma zuciyar shi tana hana shi, dan haka ya share batun ta ya cigaba da abinda yake yi, har dare. Kunna wutar itacce aka yi suka zauna a waje kasancewar an fara tunkarar lokacin sanyi kuma suma suna fama da dusar ƙanƙara.
Hira Fudail yake tare da Baban Mahlika, sosai ban da shi da yayi zurfi cikin damuwa, domin kuwa hiran da suke tayi mugun tab'a shi wanda kusan dukkan su akan addini ne, sai yake jin babu dadi. Dan haka ya mike tare da musu sallama, ya nufi gidan shi.
"Sultan baka duba Ikram ba?"
Girgiza musu kai yayi sannan ya wuce abin shi.
"Suna son junan su, amma rashin fahimtar juna yasa suke azabtar da ruhin su!" Inji Baban Mahlika,
"Babu kome a tsakanin su, kawai dai basa jituwa ne amma bana tunanin akwai soyayya a tsakanin su"
Dariya yayi irinta manyan sannan yace mishi.
"Akwai kauna a tsakanin su, me tsafta kuwa, dan haka karka yi mamaki suna kaunar junan su, kawai taran miskilai ne ba lallai kowannen su ya fahimci haka ba,sabida yadda suke mu'amalatar junan su, kamar zasu cinye kan su."
Haka dai yayi shiru, bai ce kome ba, dan yana dab da fasa ihun mara amfani, taya yayi sake har suka fara kaunar junan su? Taya Ikram da Mehran zasu ci amanar shi. Dan haka ya mike tare da mishi sai da safe, daga yanayin hiran da suka yi ya fahimci yadda yake boye shaukin shi akan wani abu na daban.
----
A hankali lafiya ta fara samuwa dan mun kwashe kwana goma sha tara, ina jinya har na fara fita waje, ana hira dani, dan ma ana sanyi sosai, amma kuma haka bai hana ka fahimci bana shiri da Mehran ba, Fudail ne abokin hirana da Baba, shima sabida ina ƙoƙarin daukar takobi ina koyan fada ne, tunda jikina ya sami lafiya.
Koyan yakin da nake a gurin Baba yasani fahimtar shima tsohon kashi ne, dan haka idan muka fara kamar ba zamu dai na ba, gashi wani lokaci har kuskuran shi nake da takobi.
Yau na kamar kullum muna cikin haka na yanke shi a damtsan shi.yarda takobin nayi tare da zuwa kusa da shi, ina cewa..
"Don Allah kayi hakuri! Bada gayya bane."
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Page 33
"Waye ya koya miki wannan zafin naman haka a fada."
Juyawa nayi tare da kallon Mehran da yake zuwa, ya d'aga ni daga jikin ba yace min.
"Baki da hankali!"
Daga haka ya cire kayan shi ya daure hannun baban yana ce mishi yayi hakuri bani da hankali, amma zai koya min hankali.
Daukar takobin yayi tare da nuna min na baban na ki dauka. Tsawa yayi min na dauke kai batare da yin banza dashi.
Haka yayi ta cira karshe dai Baba ne yayi ta min dariya yana zuga shi wai.
" Ai Sultan taji tsoro ba zata kula ka ba, dan haka ka kyaleta."
Cikin jin haushi na dauki takobin, na tunkaro Mehran, yana kallona, ina zuwa ya saka min kafa na fadi kai na ya lume cikin dusar kankara,cikin jin haushi na mike muka cigaba da azabben faɗa.
Fudail yana kallon mu, abin haushi yake bashi, dan haka bai damu ba, sai da yaji na kwala ihu tare da kiran sunan Allah. Ya juya da sauri yana kallon yadda jini yake zuba daga gefen cikina. Sam ko a jikin Mehran, asalima gurin baba ya nufa ya riko hannun shi zasu wuce.
"Fudail dauko min ita, yau tayi karo da Maza!"
Wani abu yaji ya tsaya mishi a ranshi, juyawa yayi a hankali ya kalle ni. Cikin idanun shi kuwa sakon gargadi nake gani, kar na sake Fudail ya dauke ni, idan ba haka ba! Take idanun shi suka shiga budewa da rufewa alamar zunzurutun masifa da yake tanadar min.
Koda Fudail ya zo ya dauke ni, kasa amincewa nayi dan wallahi Ni kadai nasan abinda nake gani a cikin kwayar idanun Mehran, da kaina na safe cikin, muna shiga gidan, dai dai ya fito zai duba ko an dauke ni ya hango ni ina jan numfashina, sabida jiran da yake dauka na, kamar ba gurina zai zo ba, ganin zan zube yayi maza ya tare ni. Lokaci guda numfashina yana wani irin fita tare da bugun zuciyata.
Dauka na yayi zuwa dakin yana tsaye Baba ya samin magani, sannan ya fito. Wani b'ata rai yayi yaki kula Fudail dan kishin Fudail yake, duk da bai san lokacin da ya fara jin ƙishin sama da haka.
--- bayan kwana biyu, muna hira a waje da dare. Baba da Fudail har dashi kan shi Mehran, hira muke. Can Baba yake cewa..
"Akwai lokacin da Sarki Abdus Samad mahaifin Sultan Mehran ya aike ni Askandariya, kusan shekaru ashirin baya, naga Yar sarauniya Amrah Joindatullah kamar ku da ita har ya b'aci, a lokacin ana batun auren ta da Sultan Zahil na kasan Yeman. Tun daga nan ban kuma ganin mace me irin halittar kwayar idanun irinta ba sai ke, dukda ance min Amirah Sariyah itama tana da irin idanun ta, amma ban tab'a ganinta ba."
Kura mishi ido nayi, ban ce kome ba.
"Amma Ikram daga wani yanki kike?"
"Sudan!"
"Toh taya aka yi kika tsinci kanki a Samaind?" D'ago kai nayi idanu na jajjur ba kalli Mehran, wanda shima Ni yake kallo.
"Sai da safe ku"
Nace musu,
Boyayyen ajiyar zuciya, mutane biyu suke sauke, lokaci guda. Fudail da Mehran, murmushi baba yayi, sannan yana kallon yadda kowannen su yake kokarin ganin ya kafa kan shi, lallai akwai aiki babba.
Washi gari.
Na taso da wuri, dan haka nida Fudail muka nufi daji saro itacce, lokacin da ya fito yayi ta raba idanu yana jiran yaga ta inda zata fito, yana son tambaya amma baya son abinda zai sanya kimar shi ya ragu akan idanun mutanen, dan haka yayi shiru har aka gabatar mishi da abin karyawa, daidai lokacin muka dawo muna dariya da hira, kan shi a sunkuye bai d'ago ba balle ya kalle mu, cin abincin yake a zuciye kamar wanda ake tura mishi.
"Sultan Mehran!" Dakatar da cin abincin yayi.
"Ina son zan fita wajen gari muga halin da jama'ar mu take ciki."
"Zan bika muje!"
Tari ne ya sarkafe shi sosai fa, kamar zai shiɗe, haka suka yi ta bashi ruwa, ina zuwa na fara shafa bayan shi, cikin jin zafina ya juya tare da ture ni na fadi. Kallon shi muka yi, tashi nayi a hankali ina kallon shi.
"Kazo muje Fudail"
Ran shi ne ya kuma b'aci bai ce kome ba, ya juya tare da cigaba da cin abincin shi, ko a jikina Ni kuma na fice tare da nufar waje, koda Fudail ya fito muka yi tafiyar mu.
Tashi yayi ya koma dakin shi, ya zauna yana jinjina qarfin rashin mutuncin da suka Mishi. Amma yana ji yana gani bai iya dakatar da ita ba, kasa hakuri yayi shima ya shirya ya fita ta baya, Baba yana kallon shi ya ratsa daji.
Haka yayi ta bin su ta daji, da hirarrakin su, tare da tsayawa suyi yan magana, tare da fahimtar kaunar da Fudail yake mata, suna cikin tafiya suka haɗu da kura, dan haka Fudail yace mata.
"Kinga wannan lutayen basu fitowa su daya, dole akwai yan uwan su a can gefe shiga tacan naji da wannan."
Kad'a linzamin dokin tayi tare da shiga cikin dajin da Mehran yake ciki, yana kallonta.. aikuwa sauran kurayrn suka farmata, shi kuma yana fama da wasu, tun daga nesa ake harbin su da kibiya, har suka shiga tsakiyar dajin, jin saukar abu dimmmm daga sama yasa ta juyawa, tana kallon shi ya zare gatarin shi ya juya da karfi ya shiga saran su, har dai da ya kashe su tass. Sannan ya juya yana kallon ta,
Kallon juna suke, dan tana mamaki yadda ya iya kashe dabbobi babu rangwame, fisgota yayi daga saman dokin, ya had'ata da bango, yau kan sai ya cire mayafin da take manne da fuskar ta, ya gaji da ganin kwayar idanun ta masu ban tsoron nan. Kai hannun shi yayi tayi maza ta rike, dan haka ya kalli yadda take zare.
"Don Allah karka tab'a min kimata."
Fuskar shi ya kai saman nata, tare da kai hannun shi bayan wuyarta ya tab'a a hankali take ta zube mishi a jikin shi, ajiyar zuciya ya sauke. Tare da rungume ta. Tsam yana ji kamar su dawwama a hakan. Kallon gefen fuskarta wanda yake baki kiririn. Gefe guda kuma me kyau, dukda da baya jin dadin zama da ita amma haka ba yana nufin baya jinta bane.
Matsalar shi da ita bata iya fahimtar lamarin shi bane, shi kuma ba Sakarai bane da zai ta bude baki yana ihu, dan aji halin da yake ciki, kuma idan duniya da gaskiya ita tafi dacewa ta fahimci waye shi,
"Ikrammmmmm!" Fudail ya kwala mata kira, juyawa yayi ya hango shi daga nesa, ajiye ta yayi a hankali, sannan ya ya dauki gatarin shi da gudun Bala'i ya bar gurin, jin motsin ana gudu yasa shi nufar gurin, koda ya isa ya samu babu kowa sai gawarwakin kurayen, gata can a gefe tana sume, da sauri ya isa gurinta, tare da sab'ata a kafada. Dokin ta ya kama ya daura ta akai, sannan ya hau nashi ya kad'a dawakan suka koma Madinatul Mah.
..... Yana kallon shi ya dawo, tare da shiga ya sauya kayan shi. Sannan ya fito tare da zama kusa da Baban Mahlika, duk da zaman kurame ne, amma bai hana shi gaya mishi gaskiya ba.
" Me yasa kake boye abinda zuciyarka take so? Sultan"
Cike da al'ajabi ya kalle shi sannan ya dauke kan shi yana lissafin lokacin da ya dace.
"Sultan kana son Baiwar ka?"
"Bana sonta, ban tab'a kaunarta ba, har abada ba zan kaunace ta ba. Kawai tana karkashin kulawata ce. Kabar wannan abin a tsakanin mu."
Yana kai aya, Fudail yana isowa da azabebben gudu, tare da ita.
"Malam Fudail lafiya kuwa?"
"Wallahi kuraye ne suka kai mana farmaki, toh ban san me ya faru ba, amma garin ta tsira da lafiyarta ne ban san me ya faru ba, ina ganin fadowa tayi daga saman....."
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, ba dai ta sami rauni ba?" Inji Baban Mahlika,
"Wallahi ban sani ba, domin sai gata nan a sume!"
Kamar bai san kome ba, ya cigaba da feke bakin takobin shi, kallon shi Baban Mahlika yayi yasan shi ya kai mata dauki, amma da za ayi.magana yace bai damu ba. Dan kar a Cigaba da harbo jirgin shi.