Header Ads
Showing 150001 words to 153000 words out of 274096 words

Chapter 51 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1375

Ads at the middle of Article

mishi. "Darakshan! Bani da abinda zance maka, amma wata rana zaka biya ladan aikin ka" sannan ya kuma duban mutanen fadar yace musu. "Wani dalili kuke niman Sultan Mehran?"
"Shi Sultan Mehran bai da bakin Magana ne inji Sultanah Hoyam?" Ta kalli Mehran, wanda kanshi yake sunkuye yana matsa hannun shi, kamar baya fadar. Kuma har ila yau sun kasa fadar abinda yasa suka nime shi, kasancewar ya zabga musu gargadi tun lokacin yakin da yankunan jazziratul Arab suka nemi shiga musu, ya dakatar.
Dayawan su dattijai ne, da suka manyanta amma kasuguman munafukai ne. Dan haka da gayya yaki magana kuma dole sune zasu fadi dalilin da yasa suka kira shi, amma kuma babu wanda yake da zarrar bude baki yayi magana.


Abin dariya sai wannan ya zunguri wannan, shi kuma ya zunguri na kusa dashi haka sukai tayi, karshe Amir Hood ne yayi shahadar kuda ya mike tare da cewa.
"Jiya Jasrah ta gaya min cewa taga Sultan Aamaan Mehran da wata mace wacce taci mutuncin shi a cikin masarautan nan, sannan ta keta Alfarmar masarautan nan akan idanun kowa bayan ta kasance daya daga cikin fadar nan, shin Sultan Aamaan Mehran ya yarda da ita ne har ya iya yafe mata, ko ba saurayi ta bi ba? Sannan kuma ba girman SULTAN Mehran bane yana yawo cikin gari da kaskantacciyar baiwa a cikin jama'arsa, kar Sultan Mehran ya manta yana cikin dokar hana fita ne me yasa zai karya doka ko ya manta akwai Amirorin da suke jiran ya bada kayan bikin fitilar al'ada a kai musu, amma anga kaya masu daraja a jikin Ikram da kawayenta shin wata irin matsayi take dashi haka? Sannan abisa al'ada ba a yarda wani sarki ya auri macen da tayi mu'amalanci wani namijin ba, kuma ta bayyana ƙarara Ikram namiji tabi, sannan kuma dokar masarautan nan ne, babu batun auren bazawara ko karuwa mafi munin lalacewa ace Sultan Aamaan Mehran ya kwana a gidan ƙaruwai, wannan Zubewar mutuncin masarautan nan ne, mafi munin abu ace Sarki Guda ya kwana a gidan Ƙaruwai? Don Allah ku duba wannan lamarin"

Lumshe idanun shi yayi yana jin kalmar karuwa da ya danganta Ikram dashi, jin yadda kalmar take dukar shi kamar ana saka bulalar k'aya karfe. Idanun shi yayi jajjur. Mikewa yayi tare da sauka akan kujeran shi dake fadar,.Yasaka kai zai fita daga fadan."kai waye da zamu yi magana ka mana shiru?" Suka daka mishi tsawa, wannan shine girman kuskuren da suka aikata mishi, dan haka ai ance shiru ma magana ne, dan haka ya fice daga fadan. Tunda yake babu wanda ya tab'a gaya mishi abinda ya saka shi bakin ciki sama da kowa ba, dan haka koda ya koma gida, Daki ya wuce ba tare da kalli inda Sultanah take, tunda ya shiga dakin bai kuma fitowa ba, domin kuwa baya son magana, fahimtar haka da Sultanah tayi yasa ta hana kowa yayi wani abun da zai saka ayi hayaniya ko wani magana me karfi.


A bakin Fudail suka ji labarin abinda ya faru, tashi tayi tare da shiryawa tayi zata fadar Fudail ya ce mata. "Sultanah a halin da yake ciki baya son karin damu, matukar zaki nufi fadar toh ba makawa kin lalata kome, dan haka ki zuba ido kiga abinda ya shirya. Yakin masarautan nan Sultan Aamaan Mehran ba zai iya shi daya ba, sannan kuma ke idan kika shiga mishi zasu iya aikata wani abu kuma su makala miki, ni tsorona daya karsu kaiwa Ikram hari domin kuwa zasu aikata haka kuskuren da zasu damu da kansu." Ya fadi haka a raunane, domin yasan haka ce zata faru. Idan ba wani ikon Allah bane ya hana faruwan haka.
Numfashi ta sauke tare da kallon shi tace mishi.
"Ina Ikram din take?"
"Tana wajen garin SAMAIND!" "Toh ka kai mata dauki mana, ko a tura mata dakarun da zasu kula da lafiyarta ".


"Karku fara haka!" Ya fadi hakan lokacin da ya fito daga dakin, yana me shirin barin gidan.
"Akan me?"
"Ba mace kawai bace ita!" Yana gaya musu haka ya ficce daga gidan baki daya, can wajen gidan ya nufa, dan baya son abinda zai tinzira zuciyar shi. Cikin yanayin bakin ciki yake kallon dajin, da yadda kome yake zaune cikin tsarin Ubangiji da ikon shi, yau yayi danasanin kasancewar shi daya daga cikin gidan sarautar ƙasar shi.


Damuwa tayi mishi yawa, bai san ta lokacin da ya b'ata a gurin ba, kuma ba zaka tab'a tsammanin yana gurin ba, dan ya saje da gurin baki daya, ya rasa inda zai cusa kanshi. Dan haka da ya gaji da zama ya mike zai dawo gida ne ya hadu da Fudail yana niman shi, kallon juna suka yi sannan yace mishi.
"Sun kaiwa Ikram hari"
Rab'a gefen shi yayi tare da barin guri a hanzarce ya isa gidan, kayan shi ya sauya sannan ya dauki gatarin shi ya nufi wajen gari.


Gani yake dokin da yake kai bata gudu, duk da kuwa saurin da yake yi bai hana shi ganin nisan gidan da Ikram take ba, jike kamar ya cire zuciyar shi ya gulla tsabar tashin hankalin, koda ya isa ya sami dakarun da suke kula da lafiyar ta, duk an kashe su, yana shiga ya same ta zaune akan saman gawarwakin mutanen da ta kashe, jini na d'iga daga gefen cikinta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako a hankali,yana murmushi ganin yadda take rike da takobin salon shi ta dauka, wato tayi kujera da mutanen.


Ganin su Izmah da Nimra a gefe bakin su a fashe ne ya sashi kallon su da son karin bayani.
"Muna zaune suka shigo, wai ance su kashe Ikram, shine tace inji waye? Sai suka ce mata Sultan Aamaan Mehran, ya umarce su, suka kasheta.mu kuma muka ce karya ne ba zaka tab'a sakawa a kashe ta ba, shine suka rufe mu da duka, daga nan ne ta ce su kyale mu ita ta yarda a kashe ta. Shine kawai suka juya kanta da dukka.


Har da janya, bayanta ma jini na zuba. Ganin sun kama mu zasu shigar da mu d'akin ne domin kudirin su, shine ta fara kashe su, wallahi bana son naga tana kashe mutane haka, dabi'ar tai mata yawa, mace ce kuma hakkin jini ba zai tab'a barinta ta huta na." Izmah ta karshe maganar cikin kuka da tashin hankali.
"Ikram bani takobin" ya mika mata hannu, bata d'ago kai ba, balle ya saka rai zata amsa mishi, a hankali ya taka har gaban ta, ya saka hannu ya tab'a kafad'arta, biyo shi tayi tare da zubewa a jikin shi. A kidime ya d'ago kanshi, tare da kai hannun shi bayanta, yaji wuka a suke a bayan ta, a hankali ya zare wukar.
Kallon Fudail yayi sannan yace mishi. "Maza ka koma ka dauko keken dokin" da gudu ya fita, tare da kallon su Izmah da suke kuka. Kamar me, gani yake kamar Fudail baya dawowa, kamar yayi kuka haka yake ganin ta, dan ma ya tab'a wuyarta yaji tana raye, amma zubar jinin yana d'aga mishi hankali. Dan haka ya kalli Izmah da itace zata iya bashi amsa Nimrah kan tsoro ya cinye ta baki daya. "Basu kira sunan wani ba?" Shiru tayi tana nazarin abinda suka fada tare da kallon shi, girgiza kai tai tare da cewa. "A'a" shiru yayi tare da sake wata tsaki sabida ganin har yanzun Fudail bai iso ba ji yaƙe kamar ya kurma ihu, dan haka ya dauke ta cak zai fita da ita sai ga Fudail nan.
"Afwa Sultan Mehran, dakyar suka barni na fito!" Ya kalli Izmah sannan yace musu.
"Ku fito!" Ya juya tare da bin bayan Mehran, yana fita aka bude kofar keken ya sakata a kujeran sannan ya juya tare da riko hannun Izmah ta shiga sannan ya kalli Fudail da yake rike da Hannun Nimrah da take kuka.
"Ina da abin yi!" Ya gaya musu a gaggaucce, da sauri sauri itama ta shiga cikin keken, hawa dokin shi yayi, Fudail ya hau gaban dokin.


Basu B'ata lokaci ba suka nufi masarautar, inda dakarun suka nemi hana Keken shi kasancewar Sultan Mehran yana baya, ganin shi ya dawo gaba duk suka zube akan gwiwar su. Tare da niman afwa. Nufar gidan Mehran yayi da ita, shi kuma Mehran ya nufi gidan likitan masarautar yana shiga yayi karo da Amir Hood.


"Zo muje ka duba min mara lafiya!" Ya faɗa a sanyayye, ko kallon Amir Hood bai yi ba,shima likitan haka, bai kalli inda Amir Hood yake ba, zasu fita yace.
"Aamaan ba dai akan karuwar na bace kake damuwa?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Bani da lokacin ka!" Suka fita a fusace, Amir shima ya fita daga gidan yana jin lallai dole ya kashe Ikram, wannan itace bakar kaddarar da aka ce zata shigo masarautan. Kuma ya fahimci haka ne tun daga ranar da Sultan Aamaan ya saka aka hukunta Zuhair, sannan bayan an konata Aamaan ya dauke ta suka yi balagoron har Madinatul Mah, wannan yasa shi kara fahimtar haka akanta. Amma baya fatan abubuwan da ya aikata su biyayya har yarinyar ta sani.


~~~
Tunda likitan ya isa gidan yake famar bata kulawa har ya dinke ciwon jikinta, Mehran yana tsaye akanta tare da sintiri, idan kana gidan sai ka fahimci yadda Mehran ya dawo, bayan wani lokaci likitan ya fito yana faɗin.
"Insha ALLAH zata samu sauki, sannan a kula da bayanta da kuma cikin ta."
"Zata ji sauki nan da sati biyu?" Mehran ya tambaya a dame,
"Eh Toh ya danganta da yanayin jikinta ne" rike bakin shi yayi sannan ya kalle shi, yace.
"Babu wani matsala bayan Ciwon jikinta?'
"Babu gaskiya"
"Mun gode!" Inji Sultanah,
Yana fita ta shiga dakin tare da kallon ikram, zucuyarta a raunane yake akan Yarinyar, amma tsoron goben D'anta take, tana gudun abinda zai je ya dawo mishi. Ikram itace ta dace da Mehran, amma idan ta duba yadda rayuwar su take, zai yi wuya kome bai faru ba, tana jin ciwon yadda kome ya cab'e mishi .

Shigowar shi da yayi ne ya sata dauke kanta daga Ikram.
"Naji kama tambayar zata sami lafiya nan da sati biyu. Meye kike nufi?"
"So nake ta shiga cikin zab'en matan da za ayi."
"Akan me?" Zuba mata ido yayi sannan ya sake murmushi.
"Sabida ta zauna a matsayin shugaban Kwarkwarorin na!"
"Yarinyar da take da sa'ar ce zata zauna a kwarkwarah? Hmm!.....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


32


Ta tambaye shi tare da kallon shi,bakin shi ya gaza furta kome, sai zare ido yake.
"Mehran ba zan hanaka abinda kake so ba, amma ya girman hatsarin shi a rayuwarka, iya yanzun ma an fara samun matsala ina kuma ta shiga harkokin cikin masarautan? Ka duba abinda nake nufi akan Ikram kayi hakuri ka rabu da ita, bata da Sa'a a rayuwarka. Idan so ne a duniyar nan babu wanda ya kai ni sonka da kuma kaunarka da Ikram, amma dole ce Kanwar naki zata sani na iya dauke kai na daga Ikram, don Allah ka rabu da ita"


Girgiza mata kai yayi, sannan ya juya tare da barin d'akin, numfashi ta sauke sannan ta kalli yadda ikram take barci cikin wahala, kafin ta juya ta fita. A gaskiya bata kin Ikram amma halin da zata jefa rayuwar shi ce take jin tsoron Allah akan haka, kuma tasan zai yi wuya ya rabu da ita, shi yasa take jin kamar ta kori ikram idan taji sauki ko kuma ta saka a a lalata mata jarabawar da zasu yi.


Amma kuma idan ta tuna yadda yarinyar ta b'ata lokaci tana zaune da Mehran sai taji jikinta yayi mugu mugun sanyi, taji bata da wani hanyar da zata iya cutar da ikram, sai dai kuma ba zata iya daukar kasadar barin shi ya zauna da ikram ba, Allah ya gani ba zata yarda da wannan tunanin ba, gwara duk abinda zai faru ya faru, amma tabbas zata raba su Insha Allah. Dan haka ita zata zauna da ikram har ta warke ta kuma maida ita garin su ta gaji yanzun son D'anta take bata jin zata bar shi ga kowa.


***
Kura musu ido yayi tare da cewa.
"Akan me zaku ce min Sultanah ta hana a cire al'adar duba al'urar mace? Gaskiya ba zai yiwu ba a cire shi ko kuma."


"Indai akan ikram ce kake wannan zakewar ba dai kai ka ba, domin haka da zaka aikata shi zai sanya kowa ya zargi wani abu daga gare ta, dan haka ka ɗauke kanka akan Ikram ko kuma na sanya a fidda ita daga Masarautan nan baki daya." Inji Sultanah, shafa kanshi yayi tare da kallon kasa, tabbas yana tinzira ta, domin bata tab'a juyawa muradin shi baya ba, sai wannan karon.


"Shi kenan, amma ba zan lamunci kasawa ba, dan wallahi idan aka min kuskure za a ga mugun tashin hankali.".ya fadi haka a zuciye, sannan ya bar gurin su....


..~~~ a cikin wannan yanayin aka fara shirya abubuwan da za ayi, duk da kuwa an fara tarb'an baki daga yankunan kasar. Musamman y'ay'an gwamnonin shi, Sakeenatu binti Abu Waqqas da Azizatul Nissah, sune kawai suka rage basu iso ba. Gefe guda kuwa zamu iya cewa Alhamdulillahi domin jikin Ikram ya d'an samu sauki, sai dai bata iya jure tsayuwa ko kuma wani abun da zai sanya ta zauna na wani lokaci. Sannan wani karin tashin hankali yadda take wasu abubuwan kamar tab'abb'iya, domin zata iya daukar wasu lokuta bata yi magana ba, idan kuma ka bata abinci zata na kallon shi kamar taga dodo, dan haka wannan yanayin ya sanya shi shiga tashin hankalin da ya kasa fahimtar kome. Itace dai yake sakawa a gaba da tunanin halin da zata kasance.


Ganin haka yasa Sultanah ta kuma niman Uwaisul Qarni, sunyi magana sosai har ya gaya mata cewa.
"Ku godewa Allah da iya haka ne ya same ta, domin ban da Allah ya taimaka na bata addu'o'in kwanaki ba da wallahi sai abin yafi haka, dan haka ku kai mata wannan, sannan karki zata abinda kike bukata zaki samu, karki kuma yunkurin rabasu, hakan kuskuren ne babba, karki nunawa Ubangiji wayonki, shi da ya had'a su shi yasan yadda zai yi da kowannen su. Dan haka kar na kuma jin kin ce zaki raba su, domin wani tunanin dake ranki."


Da wannan yayi mata sallama, tare da barin gurinta, haka ta kai wannan ruwan addu'o'in dakin Ikram ta bata, sai da ta shanye sannan ta fita. "Anne meke damun tane?" Ya tambaye ta ranshi a jagule, ajiyar zuciya ta sauke sannan tace mishi. "Jini yake bibiyarta, amma Insha Allah idan tayi barci ta farka zata ji sauki wasu abubuwan." Kasa jure bayanin da Sultanah tayi mishi, dan haka ya juya ya bar gidan. Bai tsaya ba sai shashin da Su Izmah suke ya shiga ya same su a tsaye Mahlika tana cin kaniyar su.
"Waye ya baki damar hukunta wasu?"
"Afuwa Sultan ba zan kuma ba!" Dauke kanshi yayi sannan yace musu.
"Muje" haka suka bishi, cikin jin dadi ya kawo musu dauki. Bayan sun bar gidan ya kai su lambun da yake cikin gidan, suka nufa. Tun da suka zauna yayi shiru kafin ya tambaye su.
"Izmah meye faru da Ikram domin na Fahimci kun jima tare," gyada mishi kai tayi sannan ta fara bashi labarin abinda ya faru, lumshe idanun shi yayi sannan yace musu.
"Lallai biri yayi kama da mutum, sai yanzun na fahimci dalilin da yasa take saurin fushi, dalilai na rayuwa sun sauya ta, Ikram din da na sani ba ita bace wannan,wancan Yarinyar bace da nasani, halin wannan ya banbanta na wancan."


A hankali yake gaya musu abinda ya faru, da yadda aka kashe Noman ba tare da sanin shi ba. Amma yasan koda yayi mata bayani ba kula shi zata yi ba, dan ranta yana kan fansa, dan haka ya kyale ta tayi yadda take so.


~~~
Sintiri take hannun shi goye a bayan shi, tun sati biyu ya sami labarin Ikram tana cikin Samaind bai yarda ba, sai da ya tura amintattun bayin shi mutane biyu, suka je har can suka binciko mishi ita, dan haka ba zai iya kyale ta ba, dan wallahi sai ya kuma dawowa da ita rayuwar shi. Shigowar Nawwas ne ya katse mishi shirun shi.
"Sultan Abrad!"
"Hmm!" Ya faɗa kamar zai zunduma ihu, kafin yace mishi..
"Ikram tana raye!". Cike da mamaki ya d'ago kanshi tare da kallon shi sannan yace mishi.."waye ya gaya maka?"
"Na tura har mutane biyu sun duba min ita, amma tana cikin masarautar bata da lafiya, ka tabbatar sunyi aure da Noman?"


Ya tambayi Nawwas yana me kallon shi. "Eh na tabbatar sunyi aure aka kashe shi." Murmushi Abrad yayi sannan yace mishi.
"Kace min a daren amarcin su ko?"ya tambaya tare da kallon Nawwas, had'iye yawun yayi sannan yace mishi."eh Sultan Abrad" wani irin murmushin mugunta yayi tare da kallon Nawwas sannan yace mishi. "Dole Mehran ya bar min ita, domin an ce min zai gabatar da ita a zab'en da zai yi, ya ka gani idan na fasa cewa ta tab'a aure?"


"Amma wannan kuskure ne babba, karka yi amfani da abinda kake ji akanta ka cutar da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads