Showing 123001 words to 126000 words out of 274096 words
Chapter 42 - DAULA BIYU Complet Document .txt
fara niman mafita, domin haka nake kullum sai na tsokano mutane fada.
~~~
Oman.
Kallon shi Nawwas yayi tare da cewa.
"Sultan Abrad!"
"Kayi min shiru! Taya aka yi kabar Aamaan ya sami damar tunkarar Sakeenatu binti Abu Waqqas? Taya za ayi haka? Har maganar niman aure ya shiga tsakanin su?"
"Sultan ka daina tunanin cewa, Aamaan Mehran ba gama garin mutane bane,. kuma yana zaune kamar bai.san meke faruwa ba yana sane da shi. Kuma a halin da ake ciki na wanda aka dakatar dashi a mulkin kasar dole idan Ka sami matsala, dole su nimo shi na taimakawa.
Kuma banyi mamaki ba dan Bahrain sun bada goyon bayan ya auri Sakeenatu binti Abu Waqqas ba, don Allah Sultan mu rabu da shi mana, duk wannan rikicin sabida Ikram ce, kuma ta mutu me kake bukata da Mehran? Idan ka nace tabbas Mehran ba zai Barka ba, zai kure maka gudu."
Kallon Nawwas yayi cikin jin haushi, tare da cewa.
"Sai na sare kan dan iska, sai na ruguza mulkin shi, wallahi ba zan barshi ba sai na kashe shi kamar yadda ya kashe min Ikram dina."
Cike da mamaki Nawwas yake kallon Abrad dan ji yaƙe kamar yayi ta dukar banza, ko zai sami sauki, dauke kai yayi sannan yace mishi.
"Zan iya fita?"
"Hmm!" Yace,. Nawwas na fita ya bishi da wani irin kallo, me dauke da ma'anoni daban daban, kwara yayi sannan ya dauke kanshi irin zamu hadu nan. Shi yanzun ma zargin shi yake gani yake kamar shima yana son Ikram, dan duk lokacin da ya sauko zance Ikram da Mehran, take zai ga sauyi akan fuskar shi.
Anya ba zargin shi bane zai zama gaskiya, taya aka yi Ikram ta mutu bayan yana da labarin shine yabi bayan su Ikram, kuma shi ya kama Noman! Ajiyar zuciya ya sauke tare da dauke kan shi tabbas akwai wani boyayyen al'amari da ya kasa fahimtar shi kai tsaye. Koma meye Insha Allah sai gaskiya tayi halinta.
----
"Nawwas!" Azizatul Nissah ta kira sunan shi.
"Hmm!" Yace mata.
"Wai don Allah meke faruwa ne?"
"Yayanki zaki tambaya" ya bata amsa a takaice,
"Kamar ya shi? Kai na tambaya ba shi ba." Wani irin iska yaja kafin ya fesar sannan yace mata.
"Kin san me? Yayanki yana da son kai, burin shi ya mallaki kome ya hana kowa farin cikin rayuwar shi, toh kanshi yake bata ta kowa. Wallahi koda zan rasa rayuwata da kimata, Ikram ta haramta mishi, dan haka ya cigaba da haukar shi ai mulki ba hauka bane. Da zai saka mutane a gaba yana juya su kamar yaran shi."
Ya faɗa cikin jin haushin Abrad, yana ajiye mishi kyauta akan Ikram dan haka ya kuskura ya tinzira shi sai yayi mutuwar danasanin. Domin zai kashe shi da hannun shi. Ya wuce ya barta tsaye cike da mamaki.
Shiru tayi tana mamakin meye yarinyar nan tafi sauran mata da har maza suke karo akanta, wacce irin shaidaniyar yarinya ce haka? Wacce irin mutum ce ita haka da ta saka mutane a gaba da bala'i, matukar zata rayu ta dawo su hadu sai ta kashe yar akuya.
Tunda ta lura ita karuwancin ta, ba iya kananun maza takewa ba, hatta manyan maza bin su take, Shaidaniya kawai. Ta tsani Ikram. Kuma sai takashe ta idan ya ganta banziya karuwa kawai. Ta faɗa tana fidda numfashin takaici.
Koda ta shiga gurin Abrad, abinda ya faɗa mata shi ya kuma kona mata rai.
"Ikram!" Juyawa tayi tana niman Ikram din sai da ya dage goshinsa sanan yace mata.
"Azizatul Nissah zance kiyi hakuri, na kiraki da Ikram!" Kura mishi ido tayi ranta yayi mugun b'aci, bakinta na rawa tace mishi.
"Yaya nice Ikram? Wacce irin asiri tayi muku da har ka manta suna na? Na shiga uku na lalace yau naga masifa da idona, lallai sai na kashe kiran."
Ta faɗa tana kuka, kasa magana yayi tare da daka mata tsawa, tafita da sauri tana kuka. Wato abinda Nawwas ya faɗa gaskiya ne, bai san kowa ba sai abinda ranshi yake so. Itakan ta shiga uku bata da uwa bata da uba. Shi da yake d'an uwan ta, kuma mace ta mishi asiri ta mallake shi. Kuka ne ya kwace mata, tunda ya fita take kokawa, domin abin kuka ne ya same su. Akan mace kowa yana jin haushin d'an uwan shi, meye amfanin haka?
Me yasa Ikram ta zame musu bakar kaddara? Me yasa ta musu shigar sauri ta rabasu kan su. Kuka take tare da niman damar ina ma Allah zai kawo mata Ikram sai ta mata kisar gilla, lumshe idanun ta tayi tare da zubda kwalla. Me zafi kamar ranta zai fita dan bakin ciki.
~~~
SAMAIND.
Cikin tausayi irinta uwa da d'a, take kallon shi. Irin kallon Allah ya dawo min da kai cikin shiryar nan take mishi. Shi kuma dake ya lura da haka, sai wani dauke kai yake.
Kamar zata zubda kwalla tace mishi.
"Mehran!" Kallonta yayi tare da dauke kanshi yana kallon wajen da dakarun Samaind, kallon su yake yana murmushi wato yaga suna badda horo, shi yadda suke bada horon ne yake bashi dariya, bawai dan wancan maganar ba, kawai sai gani yayi, Sultanah Fazilatul nisa ta rufe labulen falon, tare da b'ata rai.
"Kai wani irin mutum ne haka? Meye a jikin Maza da zaka zauna kana dariya! Maza ne fa ba mata ba." Ta faɗa cikin tsawa.
Murmushi yayi sannan ya lashe bakin shi kad'an sannan ya juya ya kalle ta, shigowar su Narjis da Shairah sai yan mata, suna zuwa suka fara rawa.
Murmushi yayi yana kallon yadda yan matan suke juya k'ugun su, takowa yayi tare da kallon wata yarinya a cikin su, yana nuna mata yadda zata juya k'ugun ta..sake baki Sultanah tayi tana kallon shi wato dai duk ta inda zata bullo mishi ya wuce tunaninta, shi kuma ba kome bane yaja hankalin shi sai tuna Ikram ranar da aka turota fada.
Rawar take ne ya saka shi jin haushinta, murmushi yayi sannan ya kalli Yarinayr yace mata.
"Karki kuma zuwa nan"
"Toh Sultan Mehran!" Ta faɗa cikin sanyin murya, wato wani irin jin dadi, sannan tafito murmushi yayi sannan yace mata.
"Anne da maza aka kawo su min rawan nan zai fi dadi akan mata nan, mazan sunfi iya rawa"
🤣😹😂
_Wayyo Allah wai da gaske maza sun fi mata iya rawa🤣🤔😹_
*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu.
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
18
A hankali ta mike tare da barin fadan, zata fita niman yarta, tana murmushi babu wanda ya isa dakatar da ita juyin mulkin da zata yi. Dan haka ta ficce daga fadar ta wuce gidanta tare da tattara kayan ta baki daya. Aka nufi gidan ta da ke wajen gari.
Duk Sultanah ta saka a bibiyeta domin tasan tunda tayi shiru akwai wani abinda take aikatawa a kasa, dan haka aka yi ta bibiyarta har zuwa lokacin da ta gama shirya dakarunta masu yawa da zasu ruguza Amrah. Sai dai tun kafin su iso cikin garin, an musu zobe.
Sultanah Amrah ce ta isa gabanta, tana murmushin takaici, sannan tace mata.
"Nayi zaton dan na baki damar ki fahimci kuskuren ki zaki saduda ne? Na zata idan na baki dama ki Fahimci kuskuren da kika aikata ne, tirr Yarki baki san halin da take ciki ba, amma kina yunkurin sai kin fitar da mulkina meye nayi miki da zafi ne? Meye na tsare miki nida yarana ne? Kin salwantar min da Joindah ban hukunta ki ba, kin yi min sanadin da na auren da Zulaikha bai miki dadi ba, me kike son nayi miki? Zulaikha ma da bata da buri mulkin sai da kika rabani da ita.
Kisa sani yarinyar nan na tsane ta, bayan na rabata da wanda take so na bawa Abrad ita, shine zaki dawo ki kashe da sauran numfashina? Meye na tsare miki haka? Indai haka goyon d'an maciji yake Allah yayi min tsari da haka. Kije na kuma baki damarki na karshe Allah ya baki sa'a. Dakarun! Ku bar Nairah karku kashe ta, ku barta idan zata iya rusani karku dakatar da ita. Halayyarki shi zai kashe ki.
Daga haka ta juya ta nufi keken dokin ta,. tana kuka a cikin ranta tana kewar Yarta wacce makirci ya saka ta ki kula yarinyar. Yau tana tir da Allah wadaran iyaye masu irin halinta, akan me ba zasu saurari yaran su ba, sai su dauke kai kamar basu gan su cikin wani hali ba.
Bayan suna sane kamar yadda tayi ita ta lalata duniyar yaranta ta kyautattawa bare, a hankali ta shiga fadar ta tana kuka, kallon wancan shaidanin kujeran tayi, daga lokacin da aka baka damar zama akan shi, shi kenan an gama da duniyar ka,kana ji zaka rufe idanunka, kana gani zaka toshe kunnen ka.
Domin al'ummar ka dole ka ɗauke kanka, yau kujeran bai mata amfanin kome ba, tabawa wasu farin ciki, ita kuma ta rasa nata, ta saka wasu dariya ita kuma yau tana kuka da idanun ta, meye Nairah bata sani ba nata?
Meye Nairah bata gani ba, nata amma ta zabi lalata mata kome cikin ruwan sanyi, zama tayi tare da fashewa da kuka tana danasanin mara amfani, tana ji ina da kasa zata bude tabbas cusa kanta zata yi domin.kunyar abinda ta aikatawa Yaranta. Zama tayi a gaban kujeran tana kallon shi bata iya fahimtar kome ba sai lokacin da Joindatullah take ce mata.
_Ummyn ya kina ganin gari babu hadiri zaki yi wanka da kashi! Ummyn maliya sun rufe masoyanki! Ummyn karki yanke min hukuncin da zaki dawamma kina kuka! Don Allah ki tashi akan mulkin nan haka iyalinki muna bukatar ki_
Wani irin kuka ta sake lokacin da take ganin irin kallon da Joindah takewa Nairah, me yasa bata dauki matakin bindidigi ba sai da lokaci ya kure mata.
Haka suka yi da Zulaikha tace mata.
_Kowacce mace burinta miji na gari! Bayan tayi dace da iyaye na gari! Sai dai matsalar da aka samu da hannu ki gurin dauke Kanki aka nima min Abrad mutumin da kowa ya sani bai da kamun kai a cikin daular shi! Nan yazo a gaban jama'a ya nuna zai rungume ni baki dakatar da haka ba sai yau naji bakin labarin kin aura min shi Ummyn yadda kika yi sanadin da Joindah ta bar masarautan nan haka nima zan bari! Kina zaune da makashiyarki, amma baki sani ba zance ki kin sani kin gaza fahimtar zuciyarki! Ke kuma bakar munafuka na dawo kanki! Sai dai ki sani duk sharrin ki Insha Allah Ubangiji zai kawo karshen ki, Azzaluma macuciya, zaki biya abinda kika aikata da kudi mafi tsada._
Kifa mata mari tayi, tare da ture ta. Tana faɗin.
"Zulaikha Waziriyar kike gayawa magana?"
"Ummyn na gaya mata! Akan me zaku raba ni da wanda nake so? Akan me zaku bani Abrad da bai da kamun kai! Ko abin alfahari ne a ce ka auri mutumin da bai san darajar kan shi ba balle na macen da zai aura!"
D'aga hannu tayi zata kuma marinta cikin sauri Nairah ta rike hannun ta, tana faɗin.
"Karki dake ta, ai ba kome bane yake damun ta, sai dan zata auri Zab'in mu, kuma wancan ai ba kowa bane!" Cikin fushi Zulaikha ta dauki wata sunduki ya kwalawa Waziriya. Sai da goshinta ya fashe.
Kasa magana Sultanah Amrah tayi tana kallon Zulaikha, cikin bakin ciki tace mata.
"Daga rana irinta yau! Ni Amrah binti Khirash na haramta miki shigowa masarautan nan har abada."
"Ba dai akan ta kika kore ni a cikin gidan mu ba Ummyn? Toh ba makawa wata rana zaki yi kuka da cewa ina da zamu dawo gare ki mana! Zaki yi ta kuka ina kallon ko ina a matsayin me yasa kome ya wuce, kin samu nasara Nairah, mun amince zamu miki duk yadda kike so. Amma Allah baya barci sabida shi ya haramtawa kan shi zalunci dan haka zai isarwa kowa"
Wani irin ihu da kuka Sultanah Amrah take yi, wani irin tashin hankali take ji a rayuwarta dama da baya can, me yasa ta kashe yaranta da hannunta? Me yasa ta rusa yaranta da hannunta? Me yasa bata fahimci abinda suke gani ba? Yau tana kuka ne amadadin su ko amadadin cin Amanar ta da akayi .
Tuna wata rana da Joindah tace mata.
"Ummyn kin cika yarda da mutane, ya Waziriya Nairah zata kawo miki magana ki amsa bayan baki da tabbacin ya faru, kiyi bincike da kai. Ga wannan takardan ba abubuwan da suke faruwa ne a marautan nan kiyi kokari ki duba yana cikin akwatin ajiyar masarautan nan a cikin akwatin takula, amma Ummyn kina bincike kuma karki yarda da kowa, zan duba batun tafiyar yakin nan ne"
Sannan ta fita daga dakin Sultanah Amrah, hawaye ne ya zubo mata, tana zaune tare da kallon yadda yan matan yaranta suke farin ciki idan suka hadu su uku! Dariyan su hayaniyar su tare da guje guje, yau duk ya dawo mata kanta, kafin kace me fadar ya cika makil da Emirater councilor, zama suka yi tare da kallon yadda sarauniyar su take kuka kamar yarinya ƙarama.
"Meye laifina? Me yasa duk Alkhairin da na mata sai da ta zabi cin amana sama da kome? Shin laifine dan na kaunace ta? Iyayen mu daya? Domin dukkan mu Zuri'a daya ce! Me yasa ta tozartani? Me yasa ta wulakantani ? Me yasa ta rabani da iya abinda na mallaka a duniya? Da yau Nairah binti Namdar ta gaya min mulki take so! Na rantse da Allah maɗaukakin sarki da na ajiye mulkin na zauna a matsayin waziriyarta, me yasa ta cutar da Ni? Bani da matsala amma haka ta saka muka rasa Basadaukiyar da take tunkarar yaki kome girman dakarun yaki kuwa? Yaushe zan kuma haihuwa bayan ba mijin ne da Ni ba? Yaushe zan kuma samun yaran bayan tsufa ta cimma Ni? Meye nayi mata a rayuwar nan? Don Allah idan akwai wanda nayi mishi laifi ya rama? Idan akwai wanda na zalunta ya rama yau ranar ku ce ta rama zaluncin da nayi muku."
Ta faɗa cikin kuka me ƙarfi.
"Sultanah Amratu! Babu zalincin da kaki yi sama da zaluntar Yaranki biyu rak a duniya? Bayan nan dukkan mu nan kin bamu farin ciki, kin cika mana gida da adalci! Kin bamu damar muyi nasara akan kome naki! Sabida rashin Kusar yaki yasa kika zama kamar yar amshin sarakunan wasu daulolin, domin kare dukiyar alummarki da rayukan su, kika zama mace me rauni! Wanda a da can baya ba haka kike ba sabida kina da Zakanya a tare da ke? Kina da Zakanyar da take hana idanunta barci sabida al'ummar ki!
Kowa zai kwanta yayi barci Sarkin yaki tana zaga gari da kewayen shi domin al'ummar ki! Munyi kuka munyi tir da munafukin da ya raba Uwa da Y'ayanta, mun yi bakin cikin yadda aka yi Uwa ta gaza fahimtar yarta har take tambayar ta zata mata juyin mulki ne?". Kasa yayi da kan shi ya fashe da kuka! Sannan ya zauna yana rusa kuka, dan yasan Joindah mutum ce a cikin mutane, jaruma ce a cikin jarumai! Zakwakura ce a cikin zakwakurai! Itace ake mata da lakabin hadarin kaka lalata amfanin masalaci.
"Mir Aminuddin! Ba iya wannan ba! Jarumar da ta tunkari yaki tun tana da karamin shekaru take yaki! Tun bayan mutuwar Amidudawlah mahaifinta ta shiga filin yaki da shekara goma sha biyar! Bata tab'a faduwa a yaki ba! Bata tab'a dawowa bata yi nasara ba! Yau aka makala mata sharri yarinyar da ko yaki muka je ita take bawa mata kariya! Da bakinta take cewa.
"Ku iyayen mu mata ba zamu kama ku a cikin bayi da fursunonin mu ba, nima mace ce irin ku! Dan haka ba zan kai ku a bautar da ku ba, idan baku yarda ba bari na gwada muku! Kai mazaje ku sunkuyar da kanku Amirah Joindatullah zata sauya kaya."
Duk muka juya mata baya, sabida bamu tab'a ganin ta cikin kayan mata ba, koda ta fito muka ganta sai muka dimauce, sabida iya halittar kwayar idanunta abar so ne balle kuma kyau da halittar jikinta, Tun daga ranar ban kuma ganin ta cikin kayan mata ba, sabida yaki ne a gaban ta, nasara ne a gaban yaki! Sarakuna da sarakunan yakin su. Sun sha niman aurenta a filin yaki! Amma murmushi take tace.
"Ba soyayya bane mizani na? Nasarar mahaifiya ta, shine nasara ta! Shan bana da ra'ayin aure. Ina tare da mahaifiya ta, dan ta haife ni ne domin na kare lafiyarta. Don Allah ka fahimci abinda na gaya maka."
Haka kika juyawa yarinyar da takewa maza kallon yan uwnta ne, haka kika sa ta ajiye takobin Sarkin Yakin Amidudawlah mahaifinta ta ajiye ta juya sakamakon cewa da kika yi ko gawarki baki kaunar ta zo kai! Taje duniya sai ta koya mata darasin rayuwa! Eh da gaske duniya ta koya mata darasin rayuwar. Tunda a wulakance aka sami Sarkin yakin Mu maza shida sun keta alfarmarta. Meye yafi haka muni!"
Ya faɗa tare da fashewa da kuka, sannan ya d'ago kai tana murmushi.
"Bata mutu ba, sai da ta haifi Guguwar yaki! Sai da ta haifi wacce zata iya karawa da duniya domin kimarta a yanzun haka ta bazama duniya niman fansanta Tun daga lokacin da muka rabu da Joindah nake bibiyarta nakan yi