Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 274096 words

Chapter 12 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1351

Ads at the middle of Article

Zaro idanu suka yi, lokaci guda na birkice musu, kalmar *Karki yi ihu* yake yawo a kunne na, aikuwa ban san lokacin da na shiga zunduma musu ihu ba, ana tare tare dani, lallai sai sun yarda na gamu da aljani.
Dakyar suka danne ni, aka yi ta min Addu'a, kafin na sami barci, me cike da mafarkai masu mugun ban tsoro.


Tafiya nake a sahara, ruwana da guzurina ya kare. Har dare ya cimmani, a hankali nake tafiya hango wata alkarya nayi tana ci da wuta. Ga Abrad da Noman suna ƙoƙarin riko ni.


Gefe guda kuma gawarwakin mutane nake tsallakawa, har na iso alkaryan.


"Ikram!" Naji muryan Ammyna. Juyawa nayi tare da kallon su. Zuciyata suke da murna na fara isa gare su. Mika kofi tayi na amsa, amadadin ruwa jini na gani a cikin shi.
"Ammyna!"
"Rayuwar Duniya cike take da faffutikar ganin samu da rashi, wannan ruwan shan shi ba zai miki sauki ba, amma kuma zaman shi a cikin ki zai fi kome baki wahala. Idan da hali ki kashe wancan wutar da ta taso cikin wancan alkaryan."


Juyawa nayi tare da kallon alkaryan, zan basu amsa suna b'ace min, hango wani mutum nayi a tsaye hannun shi goye a bayan shi, yana gaban wata kujeran mulki, wanda take zubda jinin da yake gangarawa ta wani gurin yana isa alkaryan wutana na kara kama cikin alkaryan.


Da sauri na ajiye kofin na shiga ƙoƙarin tona rami, ina jin kukan mutane da dabbobi kamar suna kiran.
"Ikrammmmmm!"
Wani irin rudewa nayi, sakamakon jin kiran da nake, gashi ina ƙoƙarin toshe hanyar tafiyar jinin nan.


Sai rike hannuna aka yi tare da d'agani cak, ina ganin mutumin nan ya juya abin shi, daukata aka yi da kofin ruwan jinin nan aka kawo ni bakin alkaryan aka ajiye ni.
"Ikram!" Juyawa nayi ina kallon su.
"Kizo mu koma nahiyar mu!"
"Ikram ina kaunarki, kizo mu koma daulata."
"Ikram!"
"Ikram! "Ikram! "Ikram!"
Haka suka yita kiran suna na, suna biyo ni duk na birkice sakamakon yadda suke zubda jini, sake kofin hannuna nayi tare da fasa ihun da ta saka. Na farka a tazame jikina yana rawa, haka Abrad ya rungume ni, wani irin kuka nake tare da cewa.
"Na haɗa ka da Allah ka mai dani gida, wallahi ba zan iya zama a nan ba mutuwa zanyi."
Kifa kaina yayi a kirjin shi, tare da shafa bayana.
"Kiyi hakuri, zaki min aikin shekara daya ce, da izinin Ubangiji zan dawo daukarki kinji , ki taimakawa Kanwata don Allah."
A hankali yake shafa bayana, tare da lallashina, har na sami nutsuwa, sannan na kalle shi.
"Ina jin yunwa kuma banyi sallah ba "


Da kanshi ya kai ni ban daki tare da cewa.
"Dama kina sallah kika hana ni sukuni dake a cikin jirgin ruwa ranar?"
Share shi nayi, sannan nayi uzurina na fito, ina idarwa naci abinci tare da sallah sannan na koma na kwanta, sabida bazan iya fita koda nan da kofar gidan ba. Ina ji ina gani suka fita suka barni. Har da bayi.


**
Masu shirya sarakunan masarautan na musamman aka kawo, domin shirya garnakaki. Ana shirya shi ana kuma kara fitar mishi da haibar shi.


Wani irin kyau da kwarjini ya kuma sosai, musamman da suka saka mishi wani kambun azurfa, a saman rawanin shi. Wanda ya kuma fidda shi na musamman.


A hankali suka sunkuya tare da daure mishi zaren takalmin shi, sannan suka nufi hanyar fita bayan sun gama. Zama yayi tare da kallon Rakshan da yake murmushi.


Shigowar Fudail yayi cikin hanzari, tare da karasawa kusa da Sultan ya gaishe shi sannan yace mishi.
"Sultan Mehran! An kawo hari dajin da yake wajen masarautan amma an dakile faruwar haka, bayan an musu kisar gilla, Sultan abin mamaki mutanen nan ba a san daga inda suke zuwa ba, sannan akwai masaniyar za a kai hari gurin maka wankar sarauta."


Watsa hannun shi yayi tare da mik'ewa, ya nufi kofar fita, yana tare idanun shi yana yawo cikin al'ummar castly din shi. Sai zuɓewa duke tare da kwasar gaisuwa, shashin mahaifiyar shi ya nufa, har ya isa cikin gidan tana tsaye ana shirya ta, yana shiga duk masu aikin suka fito,


Mika mishi hannu tayi wanda yake cike da gwala-gwalai, ya sumbata.
"Allah ya tayaka riko Mehran!"


Murmushi yayi sannan ya juya zai zauna ta rike hannun shi, suka fito daga cikin ɗakin, a hankali take takawa yana gefen ta,
Khabir da Fudail da Darakshan,suna bin bayan su. Dakarun kimanin dubu biyu suka bin bayan su, koda suka isa farfajiyar masarautan, kimanin dakaru sama da dubu dari shida suka kewaye su.


A hankali ya isa inda keken dokin da zata kai shi filin da za a bashi mulkin yake, yana shiga Darakshan da Fudail, suka hau dokin su, Fudail a gefen dama, Rakshan a gefen hagu. Ga jerin gwanon dakaru, masu iya sarrafa takobi, suna baya, masu aiki da kibbau suna gaba, masu iya sarrafa Gatari suka tsakiya, sannan masu sarrafa nashi suna tsaka tsakiya, nasu amfani da majajjawa suna karshe.


Sannan suna tafiya tare da kiran "Mehran"


Tafiyar da bazata wuce minti goma kacal ba, sai gashi ta kwashe minti talatin da wani abu, kafin suka isa gurin, sannan a saman katangar gurin akwai da karu sama da dari hudu suna jiran kota kwana.


Wannan shirin duk na kare lafiyar Sultan Mehran ne.
.sarakunar larabawa da wasu sakarunnan wasu alkaryoyin duk sun halarta, zaune suke ana gabatar da kome, bayan Rakshan ya sami babban limamin kasar ya kora mishi jawabin waye Mehran, shiru yayi sannan ya cigaba da gabatar da abinda yake gaban su.


**
Kwalin kwal kamar mayya suna barni a gidan, dan haka ina tashi na nufi ban daki nayi wanka, sannan na fito na shirya cikin wata riga da wando kayan maza ne, sai yar mayafin da na rufe fuskana, kallon shigar nayi cikin tunanin kar na fita na janyowa kai na fitina, sai na sauya tare da barin fuskana a yadda aka samun wannan bakin abun na fito. Na sami dakarun suna gadina, dole nayi musu bayani, sannan na nufi inda na je jiya.


A hankali nake tafiya ina raba idanuna, har na isa gurin da naga yasha ambaliyar jinin, sai karnin jini yake tashi, kasa jurewa nayi na fara amai, tare da wani irin jiri.


Faduwa nayi a gurin, ina jin gurin na juya min, a hankali idanuna suka rufe, ban kuma farkawa ba, sai bayan wasu lokuta kafin na farka a cikin wata yar bukka.


"Sannun!"
Tashi nayi zaune tsoho ne tukuf, me yalwacce da farin gashi.
"Ayya baba,.yaushe nazo nan"


Murmushi yayi sannan yace min.
"Idan na canka dai-dai, sarauniya bilqisul Ikram nake magana da ita ko?"


Tankwashe kafaffuna nayi, tare da kallon shi.
"Ko kai ma aljani nine?"


Murmushi yayi sannan yace min.
"Ko daya! Ni bawan Allah ne kamar ke, saba'in ke kina rayuwa ce a kasan wasu ni kuma ina rayuwa ce a karkashin mulkin Ubangiji na."


"Eh toh ba zan ce ba, kuma ba zan iya zartawa ba, amma ba makawa wata dalilin ya sanya nake nan a zaune ko?" Cikin murmushi yace.
"Ita dabi'a koya ake, al'ada mutane ke samar da ita, halayyarka kuwa halitta ce a jikin ka, manuniya kadai ke isar da sakon zuciyar mutum"


"Ban fahimci Hikimar ka ba?"
"Zamowa ko zartawa daga ahalin babban gida yake samuwa, sai dai ina kuka da kukan da zaki yi! Ina tausayin tausayawa da zaki yi, dole haka zata faru domin zanen ƙaddara bata karya kuma bata shiga gamin gambiza."


Kallon shi nake cikin mamaki wallahi duk na kasa Fahimtar abinda yake nufi.
"Alkarya tana ci da wuta! Zakwakurai suna huci da sunanki! Duniyar ta cika da gawarwaki, ƙishirwa a cikin zafin sahara! Duk baki Fahimci hikimar Ubangiji ba. Toh shikenan. Ga wannan sarewar ko koyi bisa shi wata rana zaki nemi idan halin haka ya samu."


"Baba! Baka gaya min sunan ka ba!"
Juyawa yayi ya kalle ni, sannan yace min.
"Uwaisul Qarni!"


Kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Sunan mutumin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace Sayyiduna Umar idan yana nan lokacin da uwaisul Qarni zai bayyana toh yayi kokarin rokon shi akan ya roka mishi Allah ya gafarta mishi. Lallai Baba sunan ka me daraja ne, dukda ban san kome akan ka ba, sai dai zanyi fatan Alkhairi a rayuwar ka. Nagode."


Daga haka na mike zan tafi, yace min.
"Bilqisul Ikram! Baki dauki sarewar ba, karki manta jiya ba gamo bane, aiki zakiyi da zuciyarki da karfin ki, ki ajiye batun Soyayya, kiyi aikin da duniya zata yi alfahari dake. Kuma karki zauna jiran sai an koya miki kare kanki, kiyi hakuri da inda zaki zauna da koyarwa. Dabi'arki bata karamin kofa bace, muna da masu ilimin duniya suna ganinki zasu iya fahimtar da magautar Daular nan a rufe tarihinki.....


*Kun dai ji! Abinda yace! Gashi tayi gamo! Ga Chakwakiyya sai kara habaka yaƙe! Ga mafarkin da tayi! Ga wasu zantuntuka da Tsoho Uwaisul Qarni yayi! Karku manta duk yadda ka tafi a labarin zaka dawo domin karnin baya aka koma! Like kwarkwarah 💝💞😹🤣🤭*
*ABIKRAM*
*NOKRAM*
*NAWKRAM*
*MALAM GAMO baka da team*
Littafin na kuɗi ne!.
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1034823697?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MsMwT9n73chbpIbB7ZAzir6cYIsdC0zoLvn6XiQp94WiQ2YNqavnWKJP6fWtpJwKQ1bQOgzPnEIGILQaW8foUCMbMUkPgQHUkffR474WwVSFVgpsHqKpB8v5o%2BYVwY2O
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

*Toh ni dai ban san me zance muku ba! Musamman Yan team din Abrad 😹! Noman Anwarulkharim da Nawwas basu da team ko? Toh wanca kurman fa! Gaisuwa ta ga Yan team din Kalabi tsakanin Rawuna Wato Bilqisul Ikram💝💞*


Murmushi nayi sannan na juya ga tsoho Uwaisul Qarni, kallon shi nayi sannan cikin nutsuwa na koma bakin inda na zauna, sannan na dauki sarewar.


"Na gode sosai baba!" Murmushi yayi sannan yace min.
"Karki damu da yau, goben ki zaki duba, shine kafin ya iso miki zaki fahimci girman ƙaddara da soyayya, asa'ilin zaki Fahimci soyayya ba kome bane matukar zaka sadaukar da rayuwarka domin mutanen da suke jin ƙishirwa domin ka. Ba mamaki Mahaifiyarki tasaka miki Bilqisul Ikram ce dan kanta ba mamaki kuma ta saka miki ne kawai dan soyayyar sunan ko kuma ɗan kasancewar gobenki tayi kyau."


Murmushi nayi ina kallon shi domin zantuntukarka shi bai wani dame ni ba, amma kuma ina kan auna shi. Kafin nace mishi.
"Baba zan tafi!"
"Toh Sultanah Bilqisul Ikram!"
Kallon shi nayi tare da cewa.
"Baba Sultanah kuma? Ina Ni ina wannan matsayin sai jinin sarauta"
Na fada ina murmushi, kallon tausayi tare da jinjina yayi min, sannan ya ce min.
"Allah ya ƙaddara saduwar mu."
Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Amin Ya Allah!"
"Karki manta ki rike ibada da Addu'a domin itace makamin mumini, kuma bata tab'a shaida mutumin kirki sai da Ibadar shi. Addu'o'in kuma su tamkar Sulken yaƙi ce, duk yadda makiya suka kawo miki hari matukar Allah ya amsa miki addu'ar, babu abinda ya isa ya miki. Sai dai su kare da makircin su.


Karki sake tsanani ya sa ki manta Allah, ki tuna dashi ki rike shi a ranki yana sane dake, gwabzawar ba karama bace, kasadar babba ce, zanen ƙaddara kenan, a haife ka a cikin mutane ka mutu a cikin dokar daji, karki sake wani ya sauya miki alkibla yin hakan zai iya targada miki nakasunki. Ikram ki tsaya akan kanki karki tsaya akan ra'ayin kowa."


Daga haka ya nuna min hanya, yana biye dani, amma kuma bakin shi bai fasa kiran Allah ba, har ya fidda ni bakin hanyar da zata kai ni masaukin mu. Yana min addu'ar dacewa.


** Wato a cikin birnin Samaind kuwa, an rantsar da kurma injin yan majalisan shi. Lokacin da aka bashi damar yayi magana, a hankali ya tako gaban amsa kuwar, yana kallon miliyoyin al'ummar da suka kasance jama'ar shi. Kallon su yake tare da jin kuncin rashin abokin hira da raba damuwar juna. mahaifiyar shi bata bashi damar zama da kowa ba, su kansu mutanen da suke kewaye da shi kawai an basu damar kula dashi ne.


Bawai su shaku dashi ba, rasa abun da zai ce yayi yana kallon su, suna kallon shi. Toh me zai ce musu? Bai san abinda zai iya fada ba, kawai tsintar kanshi yayi da sake musu murmushin jin dadi. Daga haka ya sauka daga inda zai yi maganar.


Dariya Abrad yayi tare da cewa Nawwas.
"Kaga lusaranci, maganar ma ya kasa sai dai mabiyan shi suyi, a haka zan dauki kanwata me daraja na bashi ita. Wani abun zai mun isa liyafar dare."


Shi kuwa Nawwas wani irin haushin Abrad yake ji, musamman da yasan yadda yake kaunar Ikram, wani irin kallo yayiwa Abrad.
"Ba lusaranci bane, mulki ne yayi mishi yawa, Sultan Aamaan bai da lusaranci, ko kafin muzo shekaran jiya an kai mishi hari, shi.daya yaji da tawagar mutanen da suke yakar dakaru dari da yan kai..a kira shi lusari? Allah ya nuna mana lokacin da zai nuna bajintar shi."


Daga fadin haka ya mike domin an bawa Sultan Mehran mulkin tare da saka mishi wata alkyaba, daga nan aka mika mishi takobin da suka gada tun daga kan tub daga Abbasid.

Ga baki daya ya gaji an hana shi sukuni, dakyar yake d'aga kafarshi, har aka gama taron lafiya. Sannan suka fito.


Haka kawai ya juya tare kallon Fudail da Darakshan. Cikin sauri suka saka shi tsakiyar su. Tafiya bata yi nisa ba. Kawai sai ji suka yi an sake ruwan kibbau.


Take garkuwan yaki suka kare su, nan aka shiga guje guje, domin ceton rayuwar al'umma. Sake sakewa suka yi aka samu aka tura Sultanah Hoyam cikin keken doki, wasu dakaru kimananin dari biyar suka kewaye ta, tare da barin gurin da ita,


A hankali ya zare takobin yana janta a kasa, bai cire kome na shi ba.


Takobin kawai yake ja a kasa, tare da d'aga hannun shi yana kallon dakarun shi.
"Ku ajiye makaman ku, ku barni na kare kujerar mulkina"


Yadda yayi maganar cikin wani ɗan karen murya me mugun dadin sauraro, yasa duk suka dare. Zunzurutun mugunta da mugun hali yake ji yau a ranshi sama da koda yau she.


Kallon Rakshan yayi dan maganar da yayi yanzun ya sashi jin gajiya tsakanin wuyar shi da kai shi. Kallon dakarun yayi.
"Dakarun Samaind su koma can, maharan kuma, Sultan yace idan kuka yi nasarar kwarzanin shi yayi alƙawarin zai zube a gaban jama'a ku sare kanshi."


" Kai lusari, munyi alkawarin koda zaka shafe wasun mu, sai mun share tarihinka da izinin Ubangiji, dan haka a gwabzawa kawo."


Da sun san waye yake tsaye a gaban su, ba zasu yi kokarin cimma shi da karfi da yaji ba, amma ina basu da hankali, sun makance da son lallai sai an shafe shi.


Wato yadda suka tawo da mugun gudu, suna ihu. Bai saka ya d'ago kai ba, balle yayi musu shirin kota kwana ba, suna isowa dab dashi suka mishi wani irin zobe, yadda zasu dargargaji dan banza.(Masu karatu kuyi hakuri domin gaskiya wannan labarin yazo da sabon tsari, babu domin akwai abubuwan da dole sai na tafi dashi domin labarin ya tafi min yadda nake so. Dan haka ba wancan labarin da za'ayi soyayya bane a tashi labari ne me matukar bukatar fahimtar bai ɗaya)


Yadda suka mishi rumfar nan, haka bawan Allah nan yayi ta girbe halittun Allah cikin kwarewa da zafin nama,.kafin minti talatin da biyar, ya tara gawarwakin su ya jibge su. Sannan ya koma ya haura saman su..ya. Zauna tare da suka takobin shi a jikin su..yayi irin zaman sarakuna masu shegen izza da takama.


Take Al'ummar kasar shi suka fara ihu tare da murnan sun sami mai ceton su. Ya jima yana zaune a gurin tare da su Fudail. Yana jiran daga ina sauran zasu fito.
Ganin babu kowa yasa shi sauka akan su, ya wuce gaban dokin shi da ya dace ya fita ayi rangadi tunda anyi nadin sarautan, sai dai babu inda za shi domin yana bukatar nutsuwa da ruwan zafi. Bai cika son magana ba, amma daga lokacin da aka tabbatar zai zama sarki yake cikin duhun damuwa, kowani dan banza nima yake lallai sai ya kashe shi.


Koda suka nufi cikin gidan sarautar, hankalin Sultanah Hoyam bai kwanta ba, sai da ta ganshi, sannan tayiwa Allah godiya. Zata addabe shi da magana yayi wucewar shi abin shi dan baya son hayaniya.


---
Kallon Juna suke shida Nawwas, cike da al'ajabi. Kafin yace mishi.
"Na yarda da lokaci ne zai tabbatar da lusaranci da Jarumta, yau naga wani irin yanayin da ban tab'a gani ba, Nawwas kalli yadda yake musu kisar gilla, kamar bai tab'a jin tausayi ba a

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads