Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 274096 words

Chapter 32 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1393

Ads at the middle of Article

ai ba matsala ta bace kawai na share batun na shiga na gaba na, har kusan asuba na tashi nayi ibada na yadda ya dace, sannan na kwanta, ina nazarin yadda rayuwata take garawa,. Barci ya dauke ni.
~~~
*SAMAIND*


_Budaddiyar wasika!_
``` Ba zan muku sallama ba. Sai dai izuwa yanzun kun yi kuskuren sauke Sultan Mehran! Kuma zaku biya bashin da kuka ci!```


Kallon juna suka yi sannan kuma suka kalle Sultanah.
"Ranki shi dad'e! Wannan sakon daga ina yake?"


Cikin wani irin mulki da yake bin jikinta ta kalle su, sannan tace musu.
"Taya zan sani? Bayan kune kuka fini sanin suwaye makiyan masarautan nan!" Ta faɗi haka cikin rashin kulawa da abinda ya faru.
Shiru suka yi, sannan ta bude baki zata yi magana aka ji ihun karkeji, tare da fashewan dutsen da yake cikin tekun SAMAIND. Da gudu aka yi ta nufar cikin gidaje, ana b'oya..


Kallon juna suka yi sannan suka ce.
"Toh meye haka yake nufi?"
"Jini! Za a zubda jinin mutane, al'umma zasu zubda kwalla! Kafin nan ya faru mu fara dakatar dashi. Domin wannan babu karya a cikin shi zamu iya rasa mutanen mu a filin yaki"


Inji Mir Umdatuddawla,
Shiru suka yi sannan suka ce,ku nimo mana kwararru akan wannan harkan."
Dakarun bakwai suka fita can sai gasu nan da wani tsoho, kallon shi suka yi, sannan suka ce mishi "meke faruwa?"


Watsa wani abu yayi tare da kallon shi,ya cigaba da abinda yake har ya kusan karewa, sannan yace musu.
"Kunyi kuskuren babba, ba zaku daina tashin hankali ba sai ranar da ya dawo mazaunin shi.


A duk lokacin da aka tara taron namun daji, ana niman zaki yayi jawabi ko yayi jagora ne, babu yadda za a saka biri ya jorancin namun daji, idan shi mashin yaki ne, itace kansakalin yakin shi, idanun shi zaki ne ita zakanya ce, kuyi fatan ya dawo matsuguninshi, koda ya dawo bai zama dole su cigaba da kasancewa ruwa biyu ba, amma tabbas zasu iya zama abu daya. Idan ya kasance, zuciyar su."


"Kai boka! Ba tatsuniya muka tambaye ka baka halin da kasar mu take ciki muke son sani?" Mir Rahil ya daka mishi tsawa.
"Kwantar da hankalinka! Kasar ka nan amma babu kwanciyar hankali ne,babu wanda ya isa dakatar da shi sai Allah. Kuyi addu'o'in kar zubda jinin yayi yawa."


"Dalla kama na shiru ka cika mana kunne, sannan ka gaya mana ya zamu yi da wannan al'amarin, daga nan sai muga abinyi."


Koran kare suka mishi tare da alƙawarin zasu kashe shi idan ya kuma zuwa. Dan haka suka shiga niman manyan malamai da bokaye, aka fara binciken su ana gaya musu abinda zasu aikata, ana haka har Allah ya kawo shi.


Gaishe shi yayi sannan yace musu.
"Dakarun SAMAIND da al'ummar da suke fita zasu mutu! Ina me baku hakuri, abin bai tab'a faruwa ba zai iya faruwa a wannan lokacin, kuma a wannan karnin kuka zai yawaita, tashin hankali da fargaba zai zame muku taburman ku.


Ku dakatar da kuskure baya, Karku dake ƙasar ta shiga halin halu'i.

Cikin sanyin jiki suke kallon bokan, Kafin Darakshan yace Mishi.
"Jeka Bama bukatar ka, domin SAMAIND jarumai take nima, ba ragwaye ba, ka kwaso tsufarka zaka juye mana haukar a nan"


Haka suka yi ta koran manyan malamai da bokayen da suke gayyatowa, karshe suka nufi gurin dan kankanin Mutum mutumin da Sultanah Hoyam ta ajiye a cikin gidan, shi ya gaya musu cewa.
"Yakin ba wata shiryayya bace, amma kuma zaku yi asara dakarun ku, akwai dalilin da yasa aka shirya yakin, domin wasu manufarwa wasun ku, dan haka ku gano munafukin bai da muhimmanci kamar ku gano yadda zaku dakatar da yakin dan ko basu ci garin baki daya ba, tabbas zasu raunana sojojin ku.


Kuma zasu durkusar da ku, zasu muku kisar mummunke, kuyi kokarin dakatar da yaƙin"


Dan haka yana gama koro musu jawabi, aka fara shirin yaki, a hanyar Amir Hood na komawa gida ne aka saka mishi bugu aka kaiwa Sultanah Fazilatul nisa.
Kamar yadda yake watsar da kayan wankin haka suke watsar da shi, sannan suka cire mishi mayafin, arba yayi da Yar shi.


Tsoron ganinta ya saka shi ja da baya, yana zare idanu waje.
"Nifa Mahaifinki ne! Kuma duk abinda nake saboda ke nake yi"


"Sabida kanka kake yi dai ko? Ina kuka kai min gudan jini na?" A firgice yake kallonta sannan yace mata.
"Fazilatul nisa, ai mun manta wannan maganar, sannan kika fito a halin yanzu kika ce MEHRAN D'anki ne kuwwar hauka zasu miki"
Dukar tabirin gabanta tayi tare da cewa.
"Babu wani shegen da zai min kuwwar hauka, idan baku bani d'ana ba, wallahi billahi azim zaku ga balbalin bala'in da zai tunkaro SAMAIND baki daya, ku bani D'ana domin shine Kusar Yaki na"


Yadda tayi maganar har gidan na amo yasa Amir Hood ya kaskantar da kan shi, yana bata hakuri.
"Zamu maida miki shi, amma maganar gaskiya, gurin da yake akwai hatsari, domin guri ne me dauke da macizai da mugayen kananun kwari masu cutarwa, don Allah"


"Ce maka akayi zuciyata ta cika da bukukuwan duniya ce? Ko ce maka akayi ina da burin na zauna daga gefe guda ina kallon shi yana cikin damuwa? Bani da zab'i kuma bani da buri shi kawai nake bukata, idan ba zauna dashi duk wata sadaukarwa zata biyo baya, ba kun kai shi darul AlHarami bane? Sai aka ce maka zan iya barin shi ya zauna baya ga maraicin da ya taso cikin kaɗaici bai isheku ba, har sai nanu duniya ce sama dashi?"
#Mai_Dambu....


```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


05
Yadda ta daka mishi tsawa da madaukakiyar murya sai da Yasaka shi razana, tare da ja da baya, sannan ta nuna mishi hanyar waje.
"Tabbas zan je gare shi, sai dai idan kun so dakatar da hakan Ni kuma zan baku mamaki, kamar yadda ka rabani da Iyayena!"


Ta faɗa tare da juya mishi ba, tana zubda kwalla, yanzun ta fahimci dalilin da yasa Uwaisul Qarni yace mata.
"Ki godewa Allah, da Hood bai cutar da fahimtar ki ba, dan ya kashe mutane dayawa, dan haka kece ya kasa kashewa ya kawo ki nan ki zauna, a matsayin matar sarki, kuma kinyi nasarar zama matar sarkin sai dai Abdus Samad babu soyayya a cikin tsarin shi, ban sani ba ko zaki iya samun soyayyar shi.


Kiyi hakuri nayiwa Mahaifinki alqawarin rike bayan shi, dan haka ina tare dake babu wanda ya isa ya cutar dake face abinda Allah ya zana miki a cikin littafinki?"


"Waye ya gaya miki cewa ke ba yar cikina bane? Ni na haife ki, kuma."
"Mir Khulaifa Alhashim. Bakuraishe daga yankin makka, mahaifiyata Hajna daga d'ayifa, gidan Amirai. Sun baka dukkan goyan bayan su, har kama waye kai. Amma daga baya ka tura har Makka aka kashe su, sannan ka saka aka sato ni, duk da Mahaifiya ta, ta fito daga cikin babban gida ne, haka bai maka ba, sai da ka amshe dukkan arzikin mahaifina, ka fara kuka tun kafin kukan yazo maka, dan wallahi sai na tsaya akan kafana na saka ka gudun ceton ranka!"


Wani irin tsoro ne ya bayyana mishi, shekaru sama da hamsin yau a dawo da maganar, tabbas dole ya kashe ta. Domin kuwa tana sako wannan batun sunan shi, hallakakke, domin hallaka shi zasu yi har lahira.


Ajiyar zuciya yayi tare da ficewa daga gidan, amma sai ya dauki matakin da har abada ba zata dashi ba.
Dakinta ta shiga tare da yin alwala, tayi sallah sannan ta kira Uwaisul Qarni, ta gaya mishi.


"Yanzun zaki bar gidan na, Insha Allah domin zasu turo a kona gidan, yin haka kuwa daidai yake da manta tarihinki, amma idan kina kusa da Mehran babu kwaron da ya isa cutar miki"


Gyada kai tayi tare da sakawa a kashe kayanta kaf, sannan aka hada da na su Shairah da Narjis, suka bar gidan. Basu zame ko ina ba sai hanyar gidan Mehran, har suka isa kofar gidan, yana sama can yana kallon su, saukowa yayi tare da fita bakin kofar shiga gidan, yana isa yaji masu tsaron kofar suna cewa.
"Ba zaku shigo ba, ku koma sai gobe da."
"Barsu man!"
Da sauri ya juya tare da gaishe da Mehran, sannan ya bude musu kofar shiga, bayansu shiga ne yayi gaba abinshi, tsayawa suka yi, suna kallon gidan a hankali.


A kasar zuciyarta kuwa cewa take.
*Ikram Allah ya albarkaci rayuwar ki a duk inda kike yau kin dawo min da abinda na rasa yau nice Mehran yabawa izinin zama kusa da shi! Kai Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran ga mahaifiyarka nan*


Kamar wanda yaji abinda ta faɗa ya juyo a hankali, ya zuba musu ido, sannan ya tako a hankali har gabanta yace mata.
"Kuzo ku shiga cikin gidan, akwai sanyi sosai a wajen nan!"


A hankali tayi gaba yana Binta a baya, har suka shiga gidan, ya nuna mata wani kofa, sannan ya kalli Darda yace.
"Ka koma bakin kofar shiga gidan, kayi musu bayani!"
"Toh Sultan Mehran!"
Ya hade hannun shi alamar yaji, sannan ya juya tare da barin gidan. Sake kallon Shairah yayi shima ya nuna mishi hanyar fita babu musu, ya juya abinshi, sai Kayan hannun Fazilatul nisa ya amsa tare da wuccewa.suna bin bayan shi. Har dakin dake kusa da na Mahlika.


Ya nunawa Narjis inda zata zauna a dakin Mahlika, ita kuma Sultanah ya bude mata dakin, ganin yadda yayi kura yasa shi kallonta, sannan ya juya ya rufe kofar, tare da nufar sama, tana bin shi a baya, har zuwa dakin shi da yake kwana.


Ya saka kayanta a dakin sannan ya bar dakin tare da nufar daya dakin hutawar shi.


Tunda ya shiga da ita hawayen da take dannewa ya digo mata, kallon shi tayi yadda yake tafiya a hankali, kamar mahaifin shi. Tana tuna daren da ta gama hailarta.


Suna lissafin kwanakin daukar ciki da Narjis.
"Sultanah Fazilatul, idan har Allah ya amsa mana, kika shiga cikin turakar Sultan a cikin wannan kwanakin da kika gama aladarki Insha Allah ciki zaki samu, dan haka da izinin Ubangiji kin kusan daukar dakin na kanki "


"Toh Allah yasa, dan bana son wancan Yarinyar ta rigani daukar cikin yarima anan gidan."
Dariya suka yi sannan Narjis tace mata.
"Ai masarautan nan tab'awa mace ko namiji damar mulki, dan haka ko Mace ce muna bukatar ta,!"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace mata.
"Haka ne, idan ma macen na samu alhamdulillahi zan iya rike abuna har ta zama shugaban wannan daular."


Dariya suka saka tare da kawwata kome yadda mafarkin su zai tabbata.
Bayan sun mata iso da sultan, ta shiga har turakar shi, a wannan kwanakin da ya hanata fita, sai da tayi sati sabida tun tana al'adar take gyara jikinta, har sai da tayi shar da ita, sannan ta gama toh wani irin dad'i tayi mishi, dan haka ya manta da wata Hoyam sai da suka barje amarcin su, sannan ta fito tare da bawa sauran Kwarkwarorin shi damar su karasa abinda ta bar musu.


Sam ta manta da batun cikinta da take da burin samu, tunda ya shiga yayi ta ciyar da ita soyayyar shi, sai taji iya haka ma ya ishe ta, haka ma ya wadatar da ita ba sai ta nime wani abu daga gare shi ba, ya nuna mata har duniya ta tashi yana jinta yana kuma kaunar ta.


Dan haka a duk lokacin da zata kasance dashi kamar zata zautar dashi take, a hankali kome yake tafiya har ta sami wata biyu, anan ne bata ga hailarta ba, shine ta saka a ka kira me magani a sirtacceen aka duba ta, ganin ciki ne ta tashi da kwarin gwiwar ta, ta gayawa mahaifinta, anan kuma aka sami Matsala.


Domin yayi murnan cikin amma kuma bayan nan tana barin gurin. Kome ya sauya ƙaddara mara dadi suka sauya a rayuwarta.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon kofar, alwala tayi sannan tayi sallah raka'a biyu, sannan ya kwanta a gurin. Can dare ya leko nan ya ganta kwance a kasa, a hankali ya shigo tare da jan bargo ya lullube ta, yana me jin sonta a ranshi, da tausayinta. Yana fita ya nufi wata kujera ya zauna tare da kallon kofar tagar dakin, yadda farin wata ya haska ko ina.


_Ni ban zo nan dan karasa rayuwata ba! Dalilin ƙaddara ta kawo ni rayuwarka don Allah Sultan kayi min izini na bar gurin nan! Shi wancan shine mafarina_


*Ikram! Ni ba zan hanaki tafiya da shi ba, sai dai na miki alkawarin duk wanda ya kuskura yace zai rab'eki wallahi Sudan shi gawa!*


Dafe goshinsa yayi cikin tashin hankali.
"Toh waye ya tsaya a karkashin maganata nayi? Tabbas akwai wanda ya san nayi wannan furucin! Shi ya karasa aikin da na fara."


Lumshe idanun shi yayi tare da tuno abubuwa masu yawa kanta, yarinya ta zuba mishi guba a zuciyar shi, da tasan yadda ta illata mishi zuciyar shi da har abada ba zata nesata kanta dashi ba,, da tasan yarda ya kashe rayuwar shi da bata bi wani namijin na,.yayi imani da Allah ciwon da ta bar shi da itace ajalin shi.


Ikram zanen ƙaddarar shi ce, ita bai san yadda zai nunawa duniya halin da ta jefa shi ba, amma baya jin ko yaki ne zata iya cinye shi kamar yadda ta mishi. Babu yakin da yake Illata lafiyar d'an adam sama da irin yakin da Ikram tabar zuciyar shi da ruhin shi suke faffatawa, ta kashe mishi rayuwa tun daga lokacin da ta shigo gare shi. Ta mishi illa bata sani ba.


Wannan yarinyar dub duniya babu mayakin da yayi nasarar huda Sulken yaƙin shi ba sai Ikram, ta huda mishi kirji da halayyarta ta tafi tabar shi da Ita, ta fasa mishi zuciyar shi da dabi'arta ta tafi ta barshi.


Lumshe idanun shi yayi yana me jin ina ma da zata dawo gare shi, ina da zata Fahimci abinda yake faruwa a zuciyar shi da har duniya ta tashi, ba zata kuma nisanta kanta da shi ba, tazarar da ke tsakanin su ya zarce tazara da take yawo cikin shekaru a duniya.


A cikin abinda bai wuce sati Daya ba, amma jin shi yake sakakke mutum. Ga baki daya duk wata izzar shi da mulkin shi ta tafi masa dashi, bai tab'a kawowa da bazatarta yake rawa ba sai da ta tafi da shi ta barshi a gurin.


Mulkin shi bai mishi ciwo ba, kamar yadda Ikram tayi tafiyar ta, kuma har yau mahaifiyar shi bata zo gare shi ba, me yasa duniya ta cika da tsananin son kai?


Me yasa mutanen da kake ganin suna kuka domin ka basu kukan sai dai su saka ka kuka? Wato shi yayi mata matashiya da cewa.
_Karki sake abokin adawar ki ya fahimci shine silar kukanki!_


Yau kuma ta zame mishi silar kukanki shi, yau gashi yana ihu babu me jin sautin bugun zuciyar shi, yasha saka kanta domin taji halin da tasaka zuciyar shi amma, yarinyar nan ta juya baya tayi tafiyar ta.


A daidai lokacin da ya dace ta tallafa mishi tayi tafuyarta, waye zai san halin da yake ciki? Waye zai gane firgicin da zuciyar shi take ciki?
Shi nan an kashe su A banza, indai har haka da tayi mishi illa wata zata kuma shiga tarihin rayuwar shi toh har abada yayi katangar karfe ga zuciyar shi.


Ba zai kuma yarda wata ya mishi kamun kazar kuku ba, kamar yadda Ikram tayi mishi. Ba zai kuma yarda a sake ratsa tsakanin zuciyarshi a mishi illa ba, tayi na farko kuma babu wanda ya isa yayi na karshe Ikram ke daya na bawai amanar kai na da zuciya ta. Ya fadi haka a kasar zuciyar shi.


Sanyin asuba ne ya dawo dashi dogon lokacin da ya ɗauka yana karanta wasikar jaki, ya mike tare da fita yayi, a can yaje suka yi sallah asuba, sannan Malam Abul Bashar ya shiga musu karatun su, musamman shi da Allah ya mishi baiwar daukar abu, gashi a cikin sati guda kacal amma yana daukar hadda.


A hankali yake sauke ajiyar zuciya, lokacin da ya shiga cikin gidan yaji ya dauki kamshin turaren da na girki, Ikram ce ta fado mishi. A hankali yake takawa cikin gidan, yana hango yadda bayi mata suke ta shige da fice, tare da gaishe shi. Tsayawa yayi sannan ya kalle su a cikin katon kitchen ɗin da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads