Showing 126001 words to 129000 words out of 274096 words
Chapter 43 - DAULA BIYU Complet Document .txt
wata uku kafin na isa gare ta, ina kai mata duk wani bayani akan ki! Sannan Allah gwanin hikima sai gashi ya had'ata da Amir Almustapha Mu'allim, duk da nasan labarin karshe sakamakon soyayya ce nayi fatar na gaya miki amma ta hanani!
Sun bar mulkin su, sun bar dangin su! Sun bar nasabar su, sun tafi wata duniya domin rufe kofar da za a tab'a kimar ku! Joindah ta kasa gaya miki juyin mulki ake son ayi miki na tsawon shekaru aru aru, sabida ance idan tayi yunkurin fada toh kanta zai koma! Shi yasa aka hada mata sharrin tana boyayyen alaka da wani makiyin mu, wato yahudawan garin Sir.
Ke kuma baki bincika ba, dan dama kin san cewa suna niman hanyar da zasu kifar da mulkin kinne shi yasa kika yi tunanin itace zata basu damar haka? Ina Amirah Joindatullah ba haka take ba, ba haka ta koya ba! Kece kika koya mata fadar gaskiya koda zaka ransa ranka ne, kuma.kika gaya mata ita gaskiya bata boya ko an boyeta zata bayyana.
Kin nuna mata ita gaskiya hanya ce ta mahadakr da ubangijin ka, toh shi tazo gaya miki wancan ranar! Shi tazo fada miki wannan lokacin da kika sa aka kashe Jermaya! Tare da shirya yaki! Karshe aka yi nasara kin zata sabida dakarunki Allah ya baki nasara! A'a, Allah ya baki nasara ne sabida ita......
How fa🤔🤣 Chakwakiyya zalla ko.......
200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641 Mai_Dambu..
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
20
"Subhanallahi!" Ta daura hannunta a bakinta, idanunta sun firfito waje, sake kallon shi tayi cikin wani irin tsoro. "Don Allah mata basu burge ka?" Ta tambaye shi cikin kaduwa tare da mugun tsoro,
Cuna bakin shi yayi kamar wani yaro karami,, sannan ya wani kwaɓe fuskar shi, ya wani jijjiga kanshi. Zaro idanu tayi kamar zasu fado kasa.
Tare da saka hannunta dukka biyu akan fuskarta, tana jijjiga kanta.
"Don Allah! Karka min haka"
"Kiyi hakuri Anne, nafi" toshe mishi baki tayi tare da tambayar shi.
"Tun yaushe kafara?"
"Hmm!"
Ya faɗa mata, ba tare da ya kuma kallonta ba, fita yayi tare da nufar inda dakarun suke horon.
da yayi sannan ya zuba musu ido, ganin yadda suke horon, shiru yayi yana tuna Ikram, murmushi yayi lokacin da suke bawa kansu wahala. Tawowa Mahlika tayi da tiren shayi.
Tana zuwa ta ajiye mishi sannan ta koma gefe, tana satar kallon shi, yadda yake jingine da wani matashi, murmushi tayi tana me jin yau zata sami kusanshi da shi Insha Allah, kallonta yayi alamar ta zuba mishi shayin. Cikin sauri ta fara kokarin zuba mishi.
"Sultan MEHRAN! Ga Amirah Jasrah nan shigowa!" Aka fada daga bakin kofar shiga gurin da suke. Bayi mata da maza suna bin bayanta, jikin Mahlika ne ya dauki rawa, har ta rasa yadda zata yi da butar shayin. Murmushi yayi daidai shigowar Jasrah, a hankali ya daura hannun shi, a saman na Mahlika, da sauri ta d'ago kanta tana kallon fuskarshi. Cikin Wata irin bazata, dauke idanun shi yayi akanta tare da juye mata shayin a hannunta, cikin sauri ta yarfe hannunta.
"Idan kina gaba karki kuma razana, gaba zan kona miki hannun sama da haka!" Gyada kai tayi da sauri, kallon takaici Amirah Jasrah tayi sannan ta harde hannunta a kirjinta, sai da ta bari Mahlika ta mike kafin ta kalli gabanta ta saka mata kamar kamar yadda Ikram ta tab'a mata .
Yana halkance dasu, amma ba zaka Fahimci haka, domin hankalin shi yana kan masu rehazal, faduwar kayan shayin sa ita kanta yasaka duk suka dawo da hankalin su kansu. Take mata hannun Jasrah tayi sannan ta durkusa.
"Wannan shine haduwar mu ta farko! Kar na kuma ganinki kusa da Inuwar Mehran! Balle kiyi kokarin shayar dashi shayi, idan ba haka ba ni nonar Mahaifiyarki zan shayar dake." Ta fadi haka tana karamin murmushi.
A hankali ta cire kafarta daga kan hannun Mahlika, sannan ta sake wata yalwataccen murmushi, tana kallon Mehran.
"Ko zan iya zama kusa da Sultan?" Lumshe idanun shi yayi tare da jingina hannun shi akan matashin sannan ya daura kan shi akan hannun shi, yana wata da d'aya hannun shi.
Ganin yaki mata magana yasata, kasadar zama a kusa da kafarshi. Aikuwa sai ganinta suka yi can tana dungure, domin shureta yayi da kafarshi. Da sauri dakarunta suka d'aga ta. Suna kallon Sultan.
Muryan Fudail ne ya katse musu, shurin da suka yi.ta hanyar cewa.
"Zaku iya tafiya da aita, laifi biyu tayi bayan ta ture baiwar shi, sannan kuma ta take mata hannun ta, kana kuma ta nemi zama kusa dashi, bayan bai bata Umarnin haka ba. Shi yasa ta sami damar tashi a raye."
A fusace ta juya tana kallon Mehran.
"Ni ka tozarta sabida wata kaskantacciyar baiwa? Sai na shayar da kai mamaki kuwa mu zuba mu gani" ta faɗa a masifance. Sannan ta bar gurin tana ji ina ma da zata sami dama sai ta hallaka Mahlika. A fusace ta bar gidan.
Tashi yayi tare da kallon Fudail, yace.
"Ka turo min ita!" Ya shige abin shi. Koda ya shiga dakin shi zama yayi akan wani kujeran hutawa, kan shi a kasa. Yana fadi a ranshi.
_Nasan da kece! Babu wacce ta isa ta takaki ta kwana lafiya! Ina kewarki idan kin mutu kuma Allah ya gafarta miki! Idan kina raye kuma Ubangiji ya dawo min dake cikin koshin lafiya!_ ya faɗa yana me kumshe idanun shi.
Karar bude kofar tare da sallama ya saka shi kumshe idanun shi bayan ya kishingida.
"Sultan!" Ta faɗa a sanyayye, wanda hakan ya nuna mishi cewa tayi kuka,
"Haka zaki cigaba da kuka?" Ya tambaye ta idanun shi kumshe, a hankali ta zube a gaban shi, tana me rike hannunta me ciwon.
"Ba dake nake ba ne?" Ya daka mata tsawa, zuɓewa tayi cikin kuka da tsoron shi. Dukda muryan shi bata bayyana b'acin rai, murmushi yayi sannan ya ce mata.
"Tashi ki bar nan" da sauri ta mike, har ta fita bai san lokacin da ya sake tsaki ba, a duniya ba zai kuma ganin mace me zunzurutun juriya da hakuri irin Ikram ba, dan haka ya juyar da kanshi yana me jin karin b'acin rai.
Wanda ya kashe kiran bai mishi adalci ba kwata kwata, yaso kanshi da yawa, taya yarinyar da babu ruwanta zata fuskanci wannan kisar gillan, gaskiya ba a mishi adalci ba, kuma ba zai tab'a yafe jinin Ikram ba.
"Sultan!" Fudail ya kira shi.
"Hmm!" Yace mishi.
Shigowa yayi tare da mishi magana a kunnen shi, sannan ya kura mishi ido, sabida shima Mehran shi yake kallo.
Mikewa yayi sannan yace mishi.
"Yau ka bugi cikinta mana!"
"Sultan!"
"Uhm!" Yace mishi, tare da juya dara darar idanun shi akan Fudail.
"Toh zan gwada haka" ya faɗa tare da barin d'akin.
"Amma Sultan! Ya batun dayan binciken?"
Yadda ya tsuke bakin shi ya saka Fudail shiru, yana mamakin irin wannan kishin Mehran.
"Afwa!" Ya faɗa a sanyayye, gyara zaman rigar shi yayi sannan ya juya ya fita abinshi, yana ji kamar ya rufe Fudail da duka, akan me zai tsananta binciken shin Noman ya kwanta da Ikram ko bai kwanta da ita ba, shi sakarai ne za zai yi wannan kuskuren. Da zai aikata wanda ba zai tab'a yafewa kanshi ba.
Kuma shima Fudail din bayayi mishi tunin da wata manufa bane, kawai sabida matsalar fada ne..
....
Kallon Jasrah Amir Hood yayi sannan ya sake murmushi.
"Akan me zaki tab'a wata baiwa a gaban shi? Ina ruwanki da tab'a wata mace akan idanun shi?" Karki kuma kar na kuma kama ki da laifin haka" ya fada tare da kallonta. Had'iye yawunta tayi sannan ta ce mishi.
"Naji Amir!" Ta faɗa a sanyayye, tana share kwalla da yake kokarin zubo mata.
~~~
SAHARA.
Dukar kafarta suka yi ta zube a gaban shi.
"Takaddirirancin ki yayi yawa, kullum da sabon labarinki nake kwana nake tashi, wacece ke?"
Banza nayi dashi ina kallon gefen da Izmah take zaune.
"Wacece ke?" Ya kuma daka min tsawa, dauke kai nayi, ya kuma hasala tare da mik'ewa tsaye.
"Wacece ke?" Juyawa nayi ina niman da wacce yake magana.
"Ina magana kin maidani sakarai?"
"Dama dani kake?" Na tambaye shi ina juya kaina gefe, murmushi yayi sannan yace min.
"Wacece ke?" Ya kuma tambaya na, murmushi nayi sannan nace mishi.
"Ba zan gaya maka kome a kaina ba, sai ka biyani."
"Niman kudi kika fito yi ne?" Ya tambaye ni,
"Farauta na fito, kuma duk wanda ya dakatar dani, kashe shi zanyi koma waye!" Na fada ina dariya.
"Me kike bukata?"
"Zaka iya dauka ta a matsayin yar kisar haya, zan kashe maka tun daga kan karamin makiyi har babban makiyi."
"Meye hujjar ki?" Ya tambaye ni, yana kallona.
"Ka bani umarni na nuna maka irin baiwata"
"Na baki! Ki kashe min Irffan bin Aslman!"
"Me kake bukata na kawo maka shaida?" Murmushi yayi yana me dauke kanshi ganin irin ba dan iya ba.
"Ki kawo min gawarshi!"
Juyawa nayi tare da mikawa Izmah hannun, muka fita.
"Wannan mahaukaciyar ina ce?"
"Wallahi kashe mutum bai da wahala a hannunta, har gwara kiyashi yana da nisan kwana da daraja."
Had'iye yawu, yayi tare da zubawa Sarautar Allah ido,
....
"Ikram meke damunki? Me yasa ba zaki zubawa Zuciyarki ruwan sanyi ba, bana son wannan yanayin, tsoro nake ji bana jin dadin yadda kike kashe mutane? Wacce irin kaddara ce haka?
Ya kin fito daga cikin manyan gidajen duniya kike irin wannan abun? Ikram iyayenki bazasu ji dadin abinda kike aikatawa ba, ba laifi bane fansa, amma kashe wani dan biyan buƙatar rai kuskure ne"
Tsayawa nayi na kalle ta, sannan na durkusa muna kallon juna, nace mata.
"Ba zaki gane ciwon da nake ji ba, sabida basu kashe miki muradinki ba, idan ina tare sai na cire kan Mehran, nayi ado dashi a mashigar Masarautan SAMAIND!"
Murmushi tayi sannan tace min.
"Kina kuskre! Kuma baki son gaskiya, zan so na rayu dan na ga yadda zaki Fahimci abinda kike aikata."
Banza nayi da ita, dan na gaji da maganarta, haka kawai za zata saka min tausayin kowa a raina ba, dan haka ya share batun ta.
Koda muka isa gidan Irffan, ban tab'a su ba, kai tsaye cikin gidan shi na nufa, kamar yadda na sami labarin ya dauke Nimrah, haka na same shi ya wulakantatta tare da ajiye ta a wulakance, jan iska nayi a hankali. Sannan nace mishi.
"Kuskure daya kayi bayan shi maza irin ka masu yunkurin aikatawa ba zasu kuma ba, me yasa ka tab'a yarinyar da bata san kome ba?
Meye laifinta? Meye taci maka? Me yasa mata basu da daraja a gurin ka? Lallai zaka biya kudin aikin da kayi domin a tsarina bana hakuri. Izmah Kinga dalilin da yasani kai gawan shi can" itama kuka take sosai, sannan na kalle ta tare da cewa.
"Rufe min gidan!"
Daukar wani mayafi nayi tare da lullube ta, sannan na zaro wasu kananun wuka, na wurga misho har sai da suka shige kirjin shi.
"Ban maka kisar da zaka mutu ba, zan kai ka ne can ka mutu a gaban Aabis!" Na fada mishi. Kakari yake sannan na juya abu na, tare da ɗaukar jakar da na ajiye tare da cire wata buhun algarara ma cusa shi, sai da na gama sannan na fito, tare da kiran mutanen shi suka saka min shi akan keken dokin shi. Tunda muka fito, yaran shine zasu min gardama, na rufe idanu nayi ta girbe yan banza, sannan na dauki wacce na biyo bayanta, muka nufi keken sannan muka bar gidan, tunda na kalle ta sau daya ban kuma kallonta ba, har muka isa fadan Aabis, na wurga mishi.
Kallona suka yi sannan suka bude buhun, aka ciro shi. Ana fidda shi yana mutuwa, murmushi Aabis yayi sannan yace min.
"Daga yau mun zama abokan ciniki!"
"Ina fatan babu cin amana?"
"Me yasa kike tsoron cin amana!"
"Sabida san iya azabar da duk wanda yayi min haka ne?"
"Ni kuma tsarinki ne yayi min!"
Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Bana hada harkalla da kai na, da ƙwaƙwalwata nake aiki."
"Wai! Toh zan so mu cancare!"
"Mmh!" Nayi murmushi me sauti, sannan na juya zan fita, yace min.
"Ke makashiya shin zaki fita anan cikin sauki ne? Ko ance miki zan kyale ki ne?"
"Aabis bin Ansar, dan gudun hijira daga SAMAIND! Koda yake banga laifin ka ba, zaka iya haka dukda Ni nafi kaunar kashe mutane sama da kashe dabobbin, Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran na biyu, ko ba zaka tafi domin daukar fansan mahaifinka bane? Idan ka shirya zamu iya kafa sabuwar harkalla, domin farautar da zanyi na gaba SAMAIND zan dirka a saman wuyar Zakin su. Nayi wasan kura da shi."
Murmushi yayi sannan yace.
"Ku kama su. Ayita azabtar dasu har sai sun fadi wanda ya turo su."
"Zan dawo an jima tayaka hira!" Na gaya mishi haka domin tabbas zan fita daga inda aka ajiye mu.
Tunda suka tafi da mu, suke azabtar damu, wallahi na sha wahalar da tunda nake a duniya ban sha ba, sun taramin gajiya iya gajiya amma ban yi musu magana na, har sai da suka gaji da kan su, duka kyale ni, kwanciya nayi ina sauke ajiyar zuciya, domin na gaji da wahala. Zuwa na SAMAIND ba shine matsala ba, yadda zan shiga masarautar shine matsalar, dan haka na koma gefen Nimrah ina shafa kanta, tare da cewa.
"Kiyi hakuri! Laifin Mahaifiyarki ce ya shafe ki, gashi baki ji ba baki gani ba kin sami tawayan Sa'a, kiyi hakuri zan maida ke amma ba yanzun ba, dan nima sai na fita daga gidan nan tukun."
"Me zanyi nayi a can? Bayan na san mahaifiyata bata aikata daidai ba, laifi laifi ne. Hukuncin da na samu ba wani me yawa bane, gashi nan kin kare rayuwata da lafiyarki ba, ki dauke ni a Matsayin baiwarki ....
*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
21
Wani irin tausayi ta bani, domin a girme ta girme ni, amma lokaci guda ta bada rayuwarta domin laifin mahaifiyarta, dauke kai nayi ina share kwalla da ta zubo min. Girgiza kai nayi ina kallon ta, sannan na dauke kai na, ina me kallon Izmah nace mata.
"Ba zan iya wannan b'arnan ba, ba zan amshi bukatar ki ba.
Ni ba kowa ba ce face, me niman fansa, idan na kammala kuma zan dawo gurin ahalina idan kuma na rasa rayuwata ku zaku iya tafiya inda yayi muku, amma ba zan iya daukar ku a matsayin bayi ba."! Na fadi haka ina me juya musu baya.
"Ikram ina tare dake, kuma bana jin zan iya rabuwa dake, dan haka zan biki duk inda zaki shiga a duniya nan"
Inji Izmah, matsowa kusa da mu, Nimrah tayi tare da daura kanta a kafadana tana faɗin.
"Gashi baki da shekaru masu yawa, amma Allah yayi miki baiwar jarumta, anya kuwa ba kashi daya bane a jikinki? Irinta Sarkin yakin Askandariya?" Murmushi nayi sannan na dauke kai na, sabida aman da nake ji, matsawa nayi, tare da kwara amai sosai.sannan na koma ina me kwanciya a kasa sabida cikina da ya kulle.
"Sannun Ikram!" Suka zagaye ni, tare da goge min zofar da ya karyo min, "Ikram! Ko zaki iya zama ne na."
"Karki damu wancan d'an iskan zai yi magana!"
A hankali barci ya kuma dauka na, bayan na farka na same su a takure, ruwa na nima nayi alola dukda bata wadacce ni ba amma kuma nayi yadda ya sawwaka, sannan na gabatar da sallah da suke kai na. Anan aka turo mana abincin da ake kawo mana kullum, nan muka tab'a sannan suka kalle ni,zasu yi magana na saka musu hannu a baki dole suka yi shiru. Bayan dakarun sun wuce nace musu.
"Ku daina yawan magana!"
Gyada min kai sukayi .
A hankali kwanaki suka yi ta tafi, ina son na fita amma kuma bana son nayi garaje, dan haka nayi kokarin koyawa kaina hakuri domin biyan bukata na, shine kadai mutumin da nasan bai da yar tsama da SAMAIND bawai dan bai da ra'ayi bane, asalima akwai fansa a ranshi dan haka nake son nayi amfani da fushinsa.
Da kuma wasu abubuwan da dole sai nayi hakuri zan same su. Ba zai yiwu na same su da karfi ba, dan haka nayi kokarin dauke kai na daga abubuwan da suke min.
Duk da yanzun kusan watan mu takwas kenan, a gidan yarin. Kuma bai tuna damu ba. Tun su Izmah basu saba ba, har suka saba.
Da na hada jimilar rabuwa na da SAMAIND shekara daya har da watanin, murmushi nayi ina Kuma hango tazarar da take tsakanin mu da SAMAIND, tabbas nisan tayi yawa, kwanakin na kuma tafiya.
~~~
SAMAIND.
Duk kwace kwacen shi, wannan karon kan an sami nasarar gabatar da zab'en dan kusan shekara daya kenan da barin Ikram garin kuma a yau za a gabatar da kome, amma idan ka ganshi zaka rantse fuskar shi bai tab'a murmushi ba. Sanye yake da kayan irin na sarakunan larabawa, fuskarshi me yalwacce da kwarjini