Header Ads
Showing 135001 words to 138000 words out of 274096 words

Chapter 46 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1396

Ads at the middle of Article

yana kallonta, kafin ya isa furta.
"Bana sonta, ban tab'a jin sonta a raina ba! Asalima tunda aka ce ta rasu na ajiye kome akanta, na shirya amsar kowacce irin mace matukar zaki yi na'am da ita."


"Me yasa kake ganin Ikram ta mutu?" Kasa yayi da kanshi tare da lashe bushashen lebben shi, sannan ya shafa kan shi tare da mik'ewa a hankali, ya nufi bakin kofar d'akin, kamar ba zai magana na, kasa kasa yayi maganar domin idan kana kusa dashi zaka fi jin abinda yace, amma a hakan bai hana Sultanah Fazilatul nisa fahimtar kome da abinda ya faɗa ba. Kalmar dai ta kullum ce da tana raye da tazo.


Murmushi tayi sannan tace.
"Idan kuma tazo da?" Tab'e baki yayi sannan ya girgiza mata kai, kafin ya fita, dan bai cika son yawan magana akan Ikram ba, yana takura mishi sukuni. A hankali ya nufi dakin shi, ya zauna tare da kai hannun shi dukka biyu haɓɓar shi, yana me nazarin abinda ya faɗa.


_Kana son Ikram?_
_A'a bana sonta! Ban tab'a jin kaunarta a raina ba_
Wannan shine kalaman da suka yi ta yawo a kanshi har kusan awa guda,.kafin ya tattara su guri guda, ya manta da su. Dan yayi alƙawarin ba zai kuma d'aga hankalin shi akan Ikram ba. Ya kuma rufe babinta har abada, kai ko itace autar mata ya hakura da damun kanshi akanta.


_Dole ka koyi rarrashi!_
Toh waye zai lallab'a? Wacece take buƙatar rarrashin sa? Ai yana ganin iya Anne ce ta dace ya rarrasheta, "hmm." Ya faɗa da dan karfi, kafin ya cigaba da Nazarin abinda yake ganin zai ficce shi, yana ganin gwara ya amshi tayin matan da ake turo mishi zai fi mishi sauki da ace kullum ana samun matsala da shi ba dasu ba, duk da ba laifi sun d'an iya abincin. Shi matsalar shi wacce zata yi abinda da zai gamsar dashi yake nima ba wacce zai kare ruwan jikinta babu biyan bukata ba. Lumshe idanun shi yayi, bai buɗe ba,


Karan bude kofar aka yi amma bai ji alamar za a shigo ba, dan haka bai bude idanun shi ba, amma yace.
"Don Allah, na gaji!" Dan haka Fudail ya juya abin shi, bai ce kome ba.


---
"A gaskiya Sultanah Hoyam ya kamata kiyiwa wancan shegen yaron me mugun taurin kai, magana shekara na uku kenan, kullum bin shi ake da mata yana wulakantawa waye shi? Meye yake ji da shi."


"Mulkin da kike ji dashi mana, shi yake ji dashi a jikin shi. Ku kyale shi wannan lokacin ba zai tsallake ba, dole ya zab'i daya daga cikin matan kuma ya haɗa da Kwarkwarorin."
Ajiyar zuciya Amir Hood ya sauke sannan yace mata.
"Ga wani hikima me zai hana muce idan ya zab'i matar da yake so zai dawo kan kujeran shi" ya faɗa yana me kallonta.


Shiru tayi cike da rudani, sannan tace musu.
"Duk yadda kuka gani, idan haka shine Alkhairi ba shikenan ba, ya dawo kan mulkin shi ai ya shekara uku ai." Ta faɗa a sanyayye.
Murmushi Amir Hood yayi yana shafa gemun shi, cikin nutsuwa domin ya harbo jirginta bata son rabuwa da mulkin, kuma zata rabu dashi ko taso ko taki, shi yasa ya shigo da batun, dan ta san dole wata rana zata ajiye mulkin shi yasa ya sako maganar kuma yaga yadda jikinta yayi sanyi, alamar zata iya sauka cikin lumana.


~~~
Tunda gari ya waye muka karya, sannan muka shiga sabon tafiya, gashi tafiyar ba ta, ruwa bace, dan haka yau babu wani hira, domin tun jiya da ta ga Uwaisul Qarni, take jin babu dad'i. Har suka kusan shiga garin SAMAIND wanda yasata bude tagar keken dokin. Sannan tayi musu alama da su tsaya anan wajen gari su kama masauki dake basu da yawa, su hudu ne. Dan haka koda suka isa asalin garin basu shiga masarautan ba suka tsaya a wajen masarautan suka kama masauki. Bayan sun ci abinci. Suka shirya tare da nufar cikin masarautar, domin binciken.


Duk fuskar su a bude yake su uku, banda Ikram da ta rufe nata fuskar da bakin mayafi, koda ta shiga. Tun da suka shiga suke niman yadda zasu sami labarin Mehran, suka gama yawon su babu wani labari, suka fito.


Washi gari ma haka suka gama yawon su babu labarin inda yake asalima kamar shakkar tambaya suke, a ranar da suka cika kwana uku da zuwa ne suka, fita kasuwa a hanyar dawowar su. Suka ji wasu matasa suna hira.


"Eh Abul Bashar ke koya mishi karatu, yace an fidda shi daga cikin masarautan, shekaru uku da suka wuce, yana can darul AlHarami, yana zaune da dakarun shi. Sai bayi maza da mata."
"Sultan MEHRAN din? Yaushe suka dakatar dashi?" Shiru mutumin yayi sannan yace.
"Toh Allah kadai ya sani amma baya cikin gidan sarautar gaskiya domin d'an uwana yake koyar dashi."
Wuce su muka yi sannan muka koma masaukin mu, kallona suka yi sannan nace musu.
"Kusan inda aka kai shi kuwa? Hmm sunso kashe shi ne fa, domin gurin cike yake da kananun dabbobin masu cutar da d'an Adam"


"Toh yanzun kinga ko baki kashe shi ba, dabobbi zasu kashe shi."


"Insha Allah gobe garin SAMAIND zata amshi sakon mutuwar ka Mehran gani nan akanka." Na fada a hankali,


---
Shayi yake sha kamar wanda aka kirashi zai amsa, haka yaji lokaci guda ya kware, tare da jin wani irin bugun zuciya, dafe kirjin shi yayi yana me jin kamar zuciyar shi zata buga, wani irin harbawa take da girgiza, kamar zata diro.


Numfashin shi ma, bibiyu take fita kamar wanda yayi mugun gudu, yanayin shi yana wani irin sauyawa, lumshe idanun shi yayi lokacin guda Fudail da Sultanah suke mishi sannun, ajiye kofin ruwan da yasha yayi tare da kallon su. Idanun shi yayi ja, bakin shi har rawa yaƙe.


"Kirjina kamar zai fashe zuciyata ta fado!" Ya faɗa a gajiye, rike shi Sultanah tai tana me jin kamar ta fashe da kuka.
"Mehran, meke damun ka?" Ta tambaye shi a dame, murmushin karfin hali yayi sannan ya kalle ta, cikin girgiza kai alamun babu. Kasan ranshi sunan Ikram ce, take hawa da sauka kawai. Kwantar da kanshi yayi akan cinyar ta, yana jin kamar ya cire zuciyar ya huta da wannan tashin hankalin. Ya rasa ya zai yi da Ikram a zuciyar shi, ya rasa yadda zai daina jin ta tana motsa mishi zuciyar shi.


Yaushe zai huta da kewarta? Yaushe zai daina najin tashin hankali akan ta? Yaushe zai daina zaman jiranta? Me yasa tayi tafiyar bazata da ruhin shi, Ikram ta gama dashi, yasan ko bai furta yana kaunarta ba, zuciyar shi ta gama furta mata, zuciyar shi ta gama amsar ta, toh me zai ce bayan shi kanshi bai da iko ku izinin sarrafa kanshi.


Yarinya karama ta hana zuciyar shi hutawa, me yayi mata da zafi haka ya addabe shi? Me yayi mata ta hana shi sakat, Ya Allah ka bayyana min ita na tambaye ta meye nayi mata haka take son ganin karshe na.


---
Ina kallon kowa ya kwanta, dan haka na dauki kayan da nake yawo dashi bakake, na saka sannan na nufi bayan masarautan, na shafa maganin maciji da kwari, na haura katangar, ina shiga na sake zarga igiyar da ya kawo ni cikin gidan, na kuma zargawa na sauka
Ban tsaya na nufi can gidan da yake da mugun gudu, ina isa naga dakarun da suke tsaron kofar shiga, dan haka na, koma da baya, sannan na haura bishiyar da take jere har katangar gidan,, ina shiga gidan nan dirka ba, dai na koma bin katangar, sannan na nufi asalin saman gidan na haura, kafin na samu kofar da yake bude a sama, shiga nayi sannan na, na fara ƙoƙarin zare makamina.


Ina shiga na same shi zaune, yana karatu, jikina ne yayi sanyin musamman jin muryan shi da take karonti suratul hajji, a hankali na isa bayan shi tare da ɗaukar wukar zan caka mishi a wuyar shi yayi maza ya rike hannuna lokaci guda, zuciyar shi ya shiga wani irin bugawa. Tare da murɗa hannun sai da ya juyar dani, anan na shiga kai mishi duka, tare da hargitsa ko ina da fada, Allah ya bani Sa'a na yanke shi a wuyar shi, sannan na samu na gudu, domin yana kai min mugun duka ne kamar zai kashe ni, ina guduwa yabi bayana, tare da haurawa ta saman gidan, babu ni babu labarina, tuni na isa inda nafi wayo, hannuna ne dai na targad'e, koda na isa gidan mu, kwanciya nayi tare da cire kayan dakyar saboda ciwon hannuna.


"Mehran lafiya?" Sultanah ta tambaye shi, ganin jini na zuba a wuyar shi.
"Wallahi hari aka kawo min, yanzun nan!" Kafin kace kwabo dakarun gidan sun bazama niman wanda ya shigo kisar, har gari ya waye babu alamar wanda yayi yunkurin kashe Sultan Mehran.


--- washi gari da kaina naja hannuna, babu wanda yayi min magana a cikin su, dan sun san bazan yarda na dauki shawarar su ba, haka na wuni a ranar babu walwala, da dare ma basu bi ta kaina ba.


... Shiru yayi yana shafa wuyar shi, tare da kallon Fudail, wanda suke tattaunawa akan lallai dole a dauki mata a cikin gidan,domin basu.
"Babu matakin da za a ɗauka, zasu kuma dawowa. Zanyi kokarin kama koma waye!" Ya fadi haka tare da rike inda zuciyar shi take bugawa, idan bai yi karya ba, zai iya cewa. Zuciyar shi tayi na'am da me kawo mishi hari, amma me yasa? Yaji ya damu da son sanin waye ne ya kawo mishi hari?


Me yasa yake jin bugun zuciyar shi sama da kullum.
"Bani ruwa!"
A birkice suna mika mishi ruwan, ya sha sannan ya kama tari, me hade da ruwan jini jini.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Fudail nimo mana likitan masarautar."


Fita yayi tare da nufar masarautan can, ya dauko likitan, wanda yana zuwa ya saka hannun shi kan goshinsa, sannan ya kuma dafe kirjin Mehran din, kafin ya riko hannun shi, yana me kallon fuskarshi.


"Fudail! Sultan MEHRAN yana fama da ciwon zuciya ne, wanda yake samuwa ta hanyar shiga damuwa da firgici,sai yawon tunanin abubuwan da suka faru, sakamakon rasa wani abinda yake so ko ya tashin hankali. Uwa uba, Soyayya tana iya haifar da ciwon zuciya ma. Sultan MEHRAN zaka sami sauki idan ka cire abinda kake b'oyewa a ranka, ko kuma ka rage yawan damuwa da tunani.


Idan kuma zaka iya fadan matsalar ka babu damuwa." Lumshe idanun shi yayi sannan ya dauke kanshi ai babban abun kunya ce ya bude bakin shi ya gaya musu, yana tsananin kaunar Ikram, wai gwara ya bar zuciyar shi ta buga, akan ya furta wannan kalmar da zata zame mishi abin dariya daga kan shi har dangin shi, dan haka ya dauke kan shi bai ce musu kalla ba, tunda bawai maganar ce yake jin yinta ba,


Sannan yadda ya fahimci bayanin likitan nan, yana daga cikin mutanen da so yayi musu mugun kamu, lallai so bata yi nisa adalci ba, yarinyar da ya gama cewa baya kaunarta, yau aji yayi amai ya lashe....
*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


25
Ina zai kai tilin abin kunyar da ya faɗa? Ya zai fahimtar dasu ba laifin shi bane na zuciyar shi ce da bata da adalci? Ina gwara ya had'iye kome koda haka na nufin ciwon da ke zuciyar shi itace ajalin shi.


Da kunya ya bude bakin shi yace soyayya ce ta maka shi da kasa, da wani ido zai kalli jama'ar fadan shi, da wani bakin zai gaya musu ba yin shi bane zuciyar shi ce da bata san Yakana ba, kai tir da wannan kalama me sunan *SO*, bata mishi adalci ba.


"Allah ya baka lafiya, ga magani nan za a baka naka sha, don Allah ka rage damuwa da tunani." Ya fada mishi, juyawa yayi tare da hada kayan shi, ya fita daga gidan. Jungu jungu suka yi tare da kallon shi. Lumshe idanun shi yayi yaki magana, dan gani yake kamar zasu kasance tsaf abinda yake damun shi. Shi yasa ya juya musu baya, dan baya son su karato abinda yake damun shi.


~~~
Da gaske Mehran ya targada min hannun, asalima irin targad'en nan na kan wuyar hannun ne, dan haka naji bakin cikin ainun.
"Ikram me ya sami hannunki?"
Murmushi nayi sannan na maida hannun na rufe.
"Faduwa nayi?" Na fada a gakile,
"Amma sai wannan bai kama da faduwa ba, sai dai ko an murɗe hannun aka yi, don Allah waye ya miki haka?"
Tashi nayi zan koma cikin dakin. Suka sha gaba na.
"Ikram! Kin fita daren jiya gidan Sultan Aamaan!"
"Babu inda naje!"
"Matsala baki iya karya bane dubi yadda fuskar ki yake nuna alamun karya kika yi? Idanun ki juyawa fa suke? Kalli yadda kike kyafta su, wallahi baki iya karya ba, kin yafi jiya ganin Sultan Aamaan ko?"


Suka sani a gaba da tsokana, tare da cewa.
"A haduwar farko aka targad'en hannun haduwar gaba, ba zata muku kyau ba wallahi!" Suka fada suna dariya, tsaki nayi tare da barin su a gurin ina jin haushinsu.


Zama suka yi ina jin su, suna gulma ta, share su nayi ina kula da hannuna, domin bana son damuwa da zata kuma kara min ciwo na.


Da dare ma, sun ta zuba ido ko na fita, suka ga ban nuna alaman zan fita ba suka hakura, dole suka kyale ni.
~~~
"Sannun Sultan Mehran! Ashe baka ji dadi, d'azun Darakshan yake sanarwar a fada." Murmushi yayi sannan ya kalle su. Fuskar shi a sake kamar babu abinda yake damun shi, nan kuwa kasar zuciyar shi, Ikram ce take yawo har da ingiza shi akan a duba garin ko anyi baƙi daga wani gurin.


Ya bude baki yayi magana yana ganin kamar wani katon aiki ne, shi yasa yake bin su sa ido, shigowar Sultanah ya sashi mik'ewa zaune.
"Anne!"
Wani irin dad'i taji a ranta,. Musamman yadda yake kiranta da Uwa, zama tayi a bakin gadon.


"Mehran! Ga maganinka, sannan don Allah meke damunki? Aamaan ka gaya min don Allah meye matsalar ka?" Murmushi yayi sannan ya juya yana kallon Mahlika da take dauke da tiren maganin, a yanzun yana bukatar mace a kusa dashi, dan haka ya dauke kanshi dan baya jin kome akan ta, duk da yana bukatar mace, baya jin Mahlika takai matsayin Ikram.


"Miko min na bashi yasha." Ta mika mata, hannun. Cikin girmamawa ta bawa Sultanah.
"Anne barta ta bani!" Ya fadi hakan cikin wani irin yanayi, da ta fahimci yana bukatar nutsuwa, dan haka na shafa kanshi tare da cewa.
"Ko Mehran zai barni na kintsa mishi ita?" Kasa d'ago kanshi yayi domin yana matukar jin kunyar ta, ganin bai mata magana ba, yasa ta ajiye maganin sannan suka fita.


Bayan wasu mintinan, sai gata ta dawo d'akin. Murmushi yayi sannan yace mata.
"Zo nan!"
Durkusawa tayi a gaban shi, murmushi yayi sannan yace nuna mata tiren maganin, bayan ta bashi ya sha, sannan ya ce mata.
"Zaki min wani aiki ne!"
Nutsuwa yayi tare da kallonta, saka hannun shi yayi a haɓɓar ta, tare da d'ago ta.
"Zaki shiga cikin gari"
Kura mata ido yayi sannan ya kuma kai kanshi fuskarta, a hankali yake yawon da hannun shi cikin jikinta, tare da kai kunnen ta, tare da faɗin.
"Kina da kyau!" Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, domin kuwa ta shiga cikin wani irin yanayi, tare da rike shi. Wato Mehran wani irin mutum ne da ya san kan tafiyar da mace, domin cikin siyasa da hikima yake birkita mata lissafi,kafin ya bata aikin da zata mishi bayan ya kai goshinsa kan gefen fusakarta. Yana goga hancin shi har zuwa wuyarta, rike rigar shi tayi tare da sauke wata irin ajiyar zuciya.


"Sultan!" Ta kira sunan shi, tare da shigewa jikin shi.
"Kinji abinda nace miki"
"Eh Sultan naji kuma Insha Allah zan yi yadda kake so."


Shafa fuskarta yayi tare da cewa.
"Maza yarinyar kirki, jeki maza."


Jikinta na rawa ta mik'e, kamar zata fadi, fisgo ta yayi tare da cewa.
"Zo nan!"
Kafaffunta ne taji kamar ba zata iya daukarta ba, shimfid'a ta yayi tare da gyara mata kwanciya, a jikinshi. Wani irin yanayi yake ji, tabbas idan yayi haka kamar yaci amanar zuciyar shi ce, dan haka ya mata masauki a jikin shi, tare da shafa bayanta, har ta fara sauke ajiyar zuciya, kafin ya d'ago kanta. Ganin yadda idanunta tana juyawa, shafa fuskarta yayi tare, da shafa bakinta tare da kallon yadda take kuma tsima, da mugun sha'awar shi.


"Ikrammmmmm!" Ya ja sunan kasar makoshinsa, kafin ya d'agota yace mata.
"Maza ki tafi inda na Turai"
A hankali ta sauka daga gadon, tabbas tana bukatar shi, amma anya jin koda wasa ba zai bata wannan damar ba.


Domin wallahi mace daya zai iya bata kanshi da ruhin shi, gangan jikin shi ta da ruhin shi mallakin Ikram ce, dan haka yake jin ba zai iya sake ya bawa wata mace ba. Ita daya ce nata ne kuma baya jin zai bata kuma.


Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads