Header Ads
Showing 105001 words to 108000 words out of 274096 words

Chapter 36 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1404

Ads at the middle of Article

Tare da jin wani irin abu akan yarinyar, har aka nuna mana kwari da bakan, Yayan Sultan Mu'allim, waɗanda da suka rasu, kallon kari da bakar nayi tare da shafawa, wato na Amir Almustapha. Cireta nayi tare da kaɗe ta.


"Ki ajiye za a baki wani."
"Don Allah ka barni nayi gwajin dashi." Kallon Sarkin kira yayi ya gaya mishi. Shi kuma ya gayawa Amir Sulaiman ya kalli Amir Rahil ya gaya mishi, cikin rawan jiki yace.
"A bata ko Baba na"
Kallon Abdullahi da Abdul Rahman yayi, harara suka zabga mishi, tare da su Ahmad.


Maida kallon shi yayi ga Sultan, cikin sanyin murya ya gaya mishi bukatar shi, murmushi yayi mishi sannan yayi alamu a barta ta dauka. Su Amir Yazeed da Yasir, da samir sunji haushi. Domin shi Yasir dan gurin Raziyana ce.


Kallon mutumin yayi sannan yace min.
"An amince kiyi amfani da shi, amma don Allah karki karya alkadarin kwari da bakan, domin ta zama na tarihi, me shi ba rago bane, sannan tarihi yake kafawa da ita ba rushe tarihinta ba."


Ya faɗa min a sanyayye, amsa nayi tare da kallon shi. Haka kawai nake jin wani bayani yana zuwa min.


_Wata rana wannan yanayin zai amfane ta Fudail! Zai amfane ta Rakshan, ku rufe mata idanunta ta harba kwarin jikin wancan bango!_


Kallon gurin nayi tare da jin kalaman kamar yanzun ake gaya min, ban san waye shi ba, amma tabbas zan so Allah ya kuma hadani dashi. A hankali na nake taryo maganar da wasu ma.
_Dole kiyi aiki da ƙwaƙwalwar ki sama da zuciyar ki, ki auna nisan inda kike da inda zaki harba kwarin ki, haka zai taimaka miki wurin_


"Magana ake dake!"


Juyawa nayi tare da kallon shi, sannan nace mishi.
"Kace me?"
"Sunyi harbin ko zaki yi!"
Kallon su nayi tare da ganin duk sun sami abun da ake bukata saura ni ce.


"Akwai kyale ka rufe min idanuna?" Na bukaci haka, juyawa yayi ya dauka domin akwai a jikin inda kwarin yaƙe, dariya suka saka ganin ana rufe min fuskana, Amir Sulaiman kan yasan zan ci, domin yana mamakin baiwar da Allah yayi min.
Ana gama rufe min idanuna, na saka kwarin a cikin bakar, sannan na ja a hankali, ji nayi kamar anzo dai dai bayana, an kai hannun kan cikina, sannan aka d'aga hannuna da naja kwarin.
_Zuciyarki ta buga kamar yadda zaki dake kwarin, karki fadi domin idan kika fadi asara na ne, so nake Nasara ya aure ki_


Jan karin nayi da karfi, sannan na sake shi cikin wani irin nutsuwa da fitar numfashina, naji karan isar shi gurin domin yayi kara "fitttt"


Kafin faruwan haka ina jin karan bushe bushe, amma ina sakewa naji shiru kamar an dauke ruwa.
"An gaida sarauniyar baka! Bude idanunki."


A hankali na warware abin ina kallon gurin, wato da ya caki abun sai da ya huda shi har wajen idanun.


"Ku dauko min ita!"
Inji Sultan, har inda yake na isa sakamakon sakani a gaba da dakarun suka yi. Ina zuwa na zube a gaban su.
"Yarinya meye sunanki?"


"Salwah!"
"Ina iyayenki?"
Murmushin gefen baki nayi sannan nace mishi.
"Ban san su ba"
"Kamar ya? Ki iya furucin ki, domin a gaban Sultan kike"
"Ni kaina ban san kai na ba, abu daya na sani an kashe min d'an uwana, kuma zanje daukar fansa, bayan nan hatta garin da na fito ban san shi ba. Iya sunana na rike"


"Baki iya tuna kowa ne?" Sultan ya tambaye ni,
"Mmm!" Na fada tare da sunkuyar da kaina,
"Waye ya koya miki harbi?"
Damke hannuna nayi sannan nace mishi.
"Wallahi ban san shi ba! Kuma na manta dashi baki daya!"


"Kinyi harbin da sak Almustapha ne yake iya harbin, dan haka zan saka ayi min binkice akanki."


"Nagode!"
Na fada. Sannan na mike, tare da komawa gurin. An nuna min yadda zamu yi wasa na biyu, duk sauran suna da masu horon su. Nice daya bani dashi. Takobin katako aka bamu, dan haka tunda ka hada ni da wani, na kayar dashi,.aka kuma hadani da wani na kayar dashi.


A take aka fara nuna rashin jin dadin yadda nake kokarin rushe tarihin samari ukun nan, ga baki daya duk abinda aka yi sai na nuna zarra, dan haka muna gama amfani da takobin aka ce zamu yi gwajin damtse.


Anan ne mutane da yawa, suka shiga murna dole na fadi, shi kuma al'amari irin wannan dabara ce ba karfi bane, dan haka Ni abokin karawa na, duka daya nayi mishi na biyu kuma sai da na kwantar da shi, sannan na koma gefen, abinda yafi basu mamaki zafin nama na.hakan muka gama sannan aka sallame mu.


Duk yadda yaso ya dame ni, hana shi magana nayi, har dare ina zaune sai ji ina son fita, dan haka na shirya na fito, haduwa nayi da samari ka uku nan.
"Gwana!" Kallon su nayi sannan na dauke kai na, sake tare ni suka yi, naga zasu bani ciwon kai,


Shine na sauki wani karamin itaccen da na a gefen hanya, na shiga hada musu zafin kai dashi, sai da suka gudu da kafar su..


~~~
SAMAIND


Zaune yake yana bitar darasin shi, Fudail ya shigo yau kimanin wata guda har da sati biyu Baya faru, zama yayi a gaban shi, cikin murmushi suka kalli juna sannan yace mishi.
"Sultan da fatan na same ku lafiya!"
Murmushi yayi sannan ya kalle shi, iya murmushin yayi ne saboda Fudail, zama yayi. Ya shiga mishi bayani ne. Mika mishi wani kaya yayi sannan yace mishi.
"Kamar yadda ya faru dai tayi auren, har nazo da abokin shi. Sai dai a daren da muka fito niman su, aka kashe shi. Bari na kira shi"


Ji yayi kamar ya cire zuciyar shi ya huta da wannan tashin hankalin, haka Fudail ya shigo da Sarwat. Yana ganin Sultan ya zube tare da fashewa da kuka.


"Wallahi iya bakin kokarina nayi amma ban ganta ba, banga dalilinta, lokacin da na dawo na sami Noman kwance cikin jini yace min.
Na dauke shi mu bar gurin, kuma nayi kamar yadda yace min, sannan yace min don Allah kar na sake ban nimo ta na kawo maka ita ba, Yasan ba kai ka tura a kashe shi ba, domin bayan faduwar mu, ruwa yaji daya daga cikin mutanen yana cewa.


Sun kashe dakarun Samaind, baki daya, saura Fudail ne kuma yasan suna hanyar zuwa, sai yake gaya min, don Allah na gaya maka kayi hakuri da ita, domin ba zata tab'a yarda ku zauna lafiya ba, karka biye mata domin ba lallai bane ta fahimce ka, don Allah kabita a Sannun, sannan yace min idan da hali na zauna a jikinta a matsayin me tsaron lafiyan ta."


"Bayan kai waye yasan tayi aure?" Fudail ya tambaye shi.
"Waɗancan dakarun sun san tayi aure.". Sarwat ya faɗa.
"Zaka iya boye maganar aurenta har abada a cikin masarautan nan?"


Jinjina kai yayi, sannan yace.
"Eh Fudail!"
"Tashi ka tafi!"
Cikin sanyin jiki ya bar gurin, kallon Mehran Fudail yayi sannan yace mishi.
"Sultan!"
Dakatar da Fudail yayi tare da cewa.
"Kowa yana da damar zab'ar abinda yake bukata, ita rayuwar ta take bukata ya sabunta, Ni kuma na ajiye ta a guri daya. Shin kana ganin haka zai mana kyau?


Shi masoyinta ne, Ni kuma uban gidanta ne, shin nayiwa kai na adalci? Dan haka ka bar kowa yayi rayuwar da ya dace dashi, ya kuma zabi abinda yake bukata, karka tilasta wa wani yayi abinda bai da niyya sabida kai."


Cikin damuwa da jin ba dad'i yace mishi.
"Sultan Mehran! Amma ai maganar gaskiya idan za ayi ta dole a cire son Rai, kana bukatar yarinyar a rayuwarka, kana Sonta."


Wani irin juya hannun shi yayi tare da rike wuyar Fudail, kakari ya fara idanun shi sunyi jajjur, murmushi yayi sannan yace.
"Sultan MEHRAN! Kana son Baiwar ka"
Ture shi yayi sannan yace mishi.
"Karka kuma ambaton soyayya a nan, idan ba haka ba, zan hallaka ka."


Cikin bakin ciki da takaicin halin Mehran yace mishi.
"Idan kaso karka barni a raye mana kai ka sani, amma kana son Ikram, soyayya me hade da kishi ma kuwa, kai kanka baka san wani irin so kake mata ba"


Lumshe idanun shi.yaui ba tare da ya kuma kallon Fudail ba, haka yayi ta magana tare da masifa yadda yake boye shaukin shi.


Bayan fitar Fudail, ya sake fuskantar shi kamar zai yi murmushi, sannan ya kuma daure fuskar, murmushin da bai shirya bane ya fado mishi, tare da tuna ranar da zasu bar Madinatul Mah, murmushi ya sake sannan abinda ya faru a ranar ya dawo mishi kamar yanzun abun ya faru. Babu abinda ya fi d'aga mishi hankali, kamar ranar da suka kwana tare, haka kuma Noman ya ratsa tsakanin ta.


Wani irin ajiyar zuciya yake saukewa kamar wanda ya sha kuka ya koshi, kuma zunzurutun kishi ne yake damun shi, dan haka ya lumshe idanun shi. Yana kuma hango cikin ƙwayar idanunta. Juya kan shi gurin kunshin da Fudail Ya kawo mishi yayi a hankali ya janyo tare da fara warware shi.


Turo kofar da aka yi ya sashi dakatarwa. Mahlika ce dauke da tire na azurfa, sai kofinan shi da yar butar ruwan zafi, tana zuwa ta ajiye a tabirin kusa da shi, ta fara zuba mishi.


Da wutsiyar ido ya kalle ta, tana aikin jikinta yana rawa.
"Kin zuba min guba ne?"
Sake kofin tayi daga hannun ya ya fadi kasa, murmushi yayi sannan yace mata.
"Zoki min tausa!"
Jikinta yana rawa, ta mike tare da nufar bayan shi, ta kai hannunta a hankali tana mishi tausar wuyar shi.


Ta jima a tsaye kafin ya sallame ta, sai da ta kwashe abinda ta zubda ta gyara wurin, sannan ya fita, Cigaba yayi tare da duba kayan, karamar fatar jimina da kayi rubutu a jikinta, nad'ewa yayi kafin idanun shi yakai kan Tambarin kasar marocco, sai wani tafar kura da aka yi rubutun shima da shi. Wanda yaga tambarin Askandariya, juyawa kayan yake tare da kallon su.


Ko shi yasa take da tsananin zafin rai, toh amma ai wannan shaidar ba zai tabbatar da cewa ta fito daga babban zuri'a bane, kawai dai sun saka ne domin, mata bayani. Baya tunani me idanun nan kamar tsaka ta fito daga wata babban gida ne....
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```


#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


11
Cikin takaici ya kuma kallon kayan, yana mamakin halin irin nata, sam bai tab'a ganin me taurin kai kamar jaki irin, gashi garin shegen rashin kunyar ta, ya janyo an kashe ta a banza.


_Kana tsammanin zata mutu cikin sauki ne?_
Wani shashi na zuciyar shi yayi mishi tambayar, dafe goshinsa yayi, a sanyayye yace "amma kuma ance ta mutu?"
_Toh kai ka yarda ne?_
Yayi, tare da dunkule hannun shi,
_Idan har ka yarda ta mutu! Tabbas Zuciyar itace zata fara gamsuwa me yasa kullum_
Mikewa yayi dan ya fahimci, matsalar Ikram da shi, zata iya sakawa a fara kiran shi tab'abbe.


Koda ya fito falo ya sami Sultanah Fazilatul da Fudail, sai Sarwat da yake basu labarin yadda aka kashe Noman, kallon su yayi tare da isa jikin tagar falon me dauke da furanin, yana gyarawa da wata wukar gyara fure.
"Abinda suka fada ya sanyani jin tabbas Sultan Mehran bai mata adalci" shiru yayi tare da jan fasali, kafin ya cigaba da cewa.
"Don sanye suke da kayan dakarun Samaind, kuma suka tabbatar mana da cewa, Sultan Mehran ya turo su."


"Ba shi bane!" Inji Sultanah Fazilatul nisa, ta faɗa a sanyayye tana kurb'an shayi, kallonta su kayi, sannan ta cigaba da cewa.
"Ba dakarun SAMAIND bane, sabida lokacin da kuka fita idan baka manta ba, kun hadu da wani mutum, a wani jirgin ruwa, kusan kunyi tafiyar tare ne!"


Shiru yayi yana nazarin abubuwan da ya faru, a hankali ya d'ago kanshi.
"Tabbas anyi haka!" Wani boyayyen ajiyar zuciya ya sauke daga can yana jin yadda Sultanah take wanke shi.
"Toh mutumin ya biku har inda aka daura auren nan, sai dai bayan ya bar gurin ya dawo, inda zai tafi yayi na shi uzurin,. Bayan ya koma inda Ikram take ya samu an tadda garin, dama na tura shi ya dauko min ita ne!


Ko da yabi ku dajin yace ya samu ana ta saran Noman, dan haka ya dawo, a hanyar dawowa ne ya hadu da dakarun Samaind da aka kashe su tare da watsa musu wuta suna ci, sannan haka ya tabbatar mishi cewa wad'ancan ba dakarun SAMAIND bane, domin a cikin masarautan ai mutanen da Ikram ta hana su kwanciyar hankali, ta saka Mehran a Jikinta, ba tare da ita kanta ta sani ba. Zuwan ku ya kara musu kwarin gwiwa, amma dama can an shirya kashe ta a ranar da za a bawa Mehran damar zab'en yan matan da zasu zauna dashi."


Cike da mamaki yake kallon ta, sannan ya cigaba da abinda yake idanun shi sun yi jajjur.
"Shigowar Ikram masarautan nan, a yarjejeniya sulhu ta shigo. Kuma da aka shigo da ita an tabbatar matukar ta haɗu da Mehran zai yi wuya tafiyar su bata zo daya ba, shi yasa aka barta a karamar baiwa har aka kawo ta shashina."


Mikewa tayi sannan ta nufi inda Mehran yaƙe, ta amshi wukar hannun shi tace mishi.
"Koma can ka zauna!"
Ba musu ya iso gurin su Fudail ya zauna, tare da sunkuyar da kanshi.
"Nice na turo ta gare ka? Ina bukatar ta a tare da kai! Duk macen da zata zauna da kai dole ta zama me ilimin addini! Me iya hukunta duk wanda ya aikata laifi! Me iya fada maka gaskiya kamar yadda babu wanda zai gaya maka! Sai abu uku da take tare da shi. Bata da tsoro! Bata da gulma ko munafunci, sannan mafi girman abinda ya ja hankalina akanta bata karya duk abinda zata yi akan gaskiyar ta take yin shi! Bata sakewa da kowa sai da kanta, kuma babu abinda ya dame ta da kai dan kasan ta ko baka santa ba. Wannan shine ya saka Ni na turata gare ka. Ina da yar da naso ta zo gare ka, amma ba zata yarda ka bata wahala kamar yadda ka bawa Ikram ba, ba zata iya jurewa ba, shi yasa naki tazo.


A yanzun haka na tabbatar Ikram tana raye,. Abu na gaba da take yi ba mamaki tana faffutikar sai tazo daukar fansa abinda aka mata, tasan halin ka, ka san nata, ka fara shiri kafin tazo gare ka."


"Amma kuma Sultanah na duba kasar ruwan baki daya ban same ta ba, nayi iya bincike na, bata cikin ruwan, sannan dakarun da suka aikata hakan sun dubata bata cikin ruwan." Inji Sarwat,


Wani irin murmushi tayi sannan ta dauke kanta, daga gare shi.
"Tana raye," ta faɗa bayan taja numfashin ta, kura mata ido suka yi, kafin suka jinjina al'amarin.
"Ikram ba gama garin mutane bane, tana da juriya da jarumta, zata dawo domin koda ta mutu dole za a kuma haihuwarta, dan haka ku saka a ranku zata dawo, kai ma baka tsira ba, domin duk ranar da ta shigo ta ganka sunanka makiyinta."


"Toh don Allah meye nawa? Ikram da dama can haushina take ji wai Ni munafuki ne, ina sane nake barin Noman kula yan mata, balle kuma yanzun ta gannin a gurin Babban makiyinta ina ga cewa zata yi Ni ne na saka baki aka kashe NOMAN." Ya fashe da kuka. Me Fudail zai yi ban da dariya, shi kansa Mehran sai da yayi murmushi. Ganin haka Fudail yayi ta saka shi yana fadan halayyar Ikram, sai ganin Sultan Mehran suka yi ya kishingida yana me sake murmushi.


Musamman yadda take tafiya kiwo, tare da yadda take cin kaniyar yan matan dasuka ce zasu so NOMAN, sai gashi sam bai tab'a jin kishin noman ba, asalima jin dadin yadda ake fadan halayyar su yake, inda ya fahimci cewa. Noman yana da saukin hali, kasancewar ita kuma tana da zafi kome kashin abu zata iya dakatar wa.


"Sai dai duk da wannan zafin na Ikram a cikin gidan su, kare yafisu daraja." Ya faɗa hawaye na zuba mishi.


"Tun bayan mutuwar Mahaifiyar su, sai suka kasance kamar marayu, duk da kowa yasan mahaifin su, shi yake horar da duk wani matashin dake garin Gezira fada, Mahaifiyarta kuma tana horar da Mata yadda ake amfani da kibiya, ban tab'a ganin uwa me son yaranta ba, duk da basu son nunawa yaran muhimmancin rayuwa, kamar a baka damar kayi walwala cikin Arzikin da wadata.


Sariya itace baiwar Mamar su, kuma tana matukar kula da yaran, dan haka da Mahaifiyar su zata rasu, ta bukaci mijinta ya dakatar da horan da yake bawa mutane, domin halin da ta tsinci kanta yana da nasaba da horon da suke bawa mutane ne, har wasu matasa daga wani yanki daga cikin garin suka farmake ta,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads