Showing 18001 words to 21000 words out of 274096 words
Chapter 7 - DAULA BIYU Complet Document .txt
gyara zaman rigana, dan sabulewa yake.
Sannan na daure gashin kai na, da kyau na mai dashi tsakiya, sannan na koma na zauna.
"Baki gaya min sunanki ba?"
"Inam!" Yarinyar ta amsa min.
"Me yasa zaki gudu?" Dauke kai nayi sannan ta cigaba da gyara rigana bayan na yaga kasar shi.
Daukar igiyar nayi sannan na daure k'uguna dashi yadda rigar zata zauna min, guntun igiyar na daure wuya ta fashi.
Can kuwa sai ga dakarun Oman. Haka suka tasa keyar mu, muna fita waje inda zai fitar damu daga garin. Nace musu.
"Ko ku barni na yi tafiya ta ko kuma na kashe kai na,"
Caaaa suka min da takuban su. Aikuwa na, kuma sheke wuyata. Sake jan igiyar nayi, kuma duk muna cikin gidan sarautar Askandariya, ganin da gaske kashe kaina zanyi suka shiga ƙoƙarin hanani, Ni kuwa damar guduwa nake nima toh sun zagaye Ni.
..... "Toh mun gode, Nawwas idan har ka isa Oman ka sanarwa Sarkin ku, nagode sosai abisa yarda da yayi dani." Inji Sultanah Amrah.
"Godiya muke!"
Daga haka suka fita bayan sun yi sallama da ita, yana fitowa farfajiyar masarautan ya hango yadda ake da Ikram, a hankali ta taka tare da ratsa dakarun shi.
A hankali ya saka hannun shi a saman wuyarta, zuɓewa tayi a jikin shi ta baya, zuciyar shi ce ta shiga wani irin bugawa, da sauri ya ture ta, tare da barin gurin su baki daya.
A lokaci guda haki da wani irin yanayi na fitan numfashi ya taru mishi, sosai yake jin bugun zuciyar shi.
A hankali ya juya tare da kallon yadda aka dauke ta, za a fita da ita. Duk da ya ganta babu kaya a jikinta, bai ji wannan yanayin ba, sai yanzun da ta haɗu da jikin shi. Lallai zuciya baka da ikon sarrafa sai yadda ta sarrafa ka.
**
*SAMAIND*
"Narmin! Ban san me yasa nake jin babu dadi ba!" Inji Sultanah Hoyam.
Gyara tsayuwa dattijiwar tayi sannan tace mata.
"Ina ga yana nasaba da."
Buga mata kofa aka yi, ta kalli Narmin, fita tayi ta sami Khabir,
Shigowa suka yi, tare da gaida Sultanah Hoyam.
"Kina da baki Sultanah."
Kafe shi tayi da ido,
"Gwamnonin yanki nan baki daya ne suka tawo" ya faɗa mata.
A hankali ta mike tare da saka alkyaba ta fito.
Tunda ta shiga fadar suka mike baki dayan su, har da Amir Hood. Suka gaishe ta.
"Sannunku!"
Zama tayi ta daura daya akan daya,. tana kallon su.
"Sultanah mun zo da wani batu ne, da fatan zaki fahimce mu,
Gyara zaman ta, tayi sannan ta zuba musu ido. Daya daga cikin gwamnonin wanda ya kasance shugaban su baki daya yace mata.
"Sultanah ne sunana Mir Kamshad, ina rike da yankin arewacin kasar nan, Sultanah mun zo da batu me girma ne."
Ya zuba mata ido,.yana kallon yadda take sauraron shi.
"Kasancewar kin jagoranci dogon lokaci akan karagar mulki, shine muke rokonki, da kibawa D'anki dama sultan Aamaan Bin Abdus Samad Bin Aamaan Almaktum, damar jagorantar mu! Sanan munyi mubaya'a baki dayan mu akan jagorancin mu."
Kallon su tayi baki dayan su, cikin wani irin juriya da jarumta, murmushi tayi sannan tace musu.
"Sai me?"
Mik'ewa wani gwamnan yayi tare da cewa.
"Suna Mir Umdatuddawla, ina jagorancin yammacin kasar nan, Sultanah a labarin da muke samu, sultan Aamaan ya san Y'a mace, bayan kuma Daular nan an san cewa duk basaraken lardin nan dole sai ya bayyana cewa yayi tarayya da Y'a mace.!"
Fasali yaja tare da kallon ta, ya cigaba da cewa.
"Abisa ka'idar daular nan, dole ko baiwa aka kawowa sarki yayi tarayya da ita dai ya shaidawa duniya haka domin muna sakan ran zamu sami magajin shi."
Yana kai aya ya zauna, tare da zubawa gwamnan kusa dashi ido.
Mik'ewa yayi sannan yace.
"Suna na Mir Ihsanul Hak! Sunana na, Ni ne gwamnan kudancin kasar nan, Sultanah abisa al'ada kafin ki kasance shugabar mu sai kin kasance a matakin tanttancewa.
Amma saboda kaunar da Abdus Samad yake miki, kika sami damar zama Sultanah, dan muna koron a shigar mana da jarabawar zama Magajiyar sarauta a cikin wannan daular kamar yadda aka yi shekarun baya, sannan shima Aamaan din muna bukatar ya fito ayi mishi jarabawar zama sarki na gaba."
Yana gama fadar haka ya zauna,
"Suna na Mir Fawwaz, ina rike da wasu abubuwan na shige da ficcen na kasar nan, dani aka tafi Baghdad, akan sulhu. Sultanah Hoyam tabbas kin rike daular Abbasid fiye da yadda suka rike Daular Umayyad, amma maganar gaskiya shine sun janye ne sabida Yawan dakarun mu, miliyan uku da rabi.
Yayinda suke da dakarun miliyan daya da rabi.. a takaice zamu iya shafe daular baki daya, amma sabida yadda suka kawo sharuddan su, sai da suka yi magana akan mulkin da kike yi bayan kin hana d'anki damar mulki, sannan suka ce su yar su ba zata zama baiwa ba, matukar zata zama baiwa toh zancen zai iya zama na kasa da kasa."
Zama yayi sannan Amir Hood ya mike,
"Ya shugabana, batun su haka yake, sannan abisa al'ada muna bada daman ayi jarabawar zama sarki da matar sarki, idan har aka sami damar haka toh muna, iya fuskatar tozarci a gurin wasu sarakuna.
Ba laifi bane bawa mace mulki, amma mafi muhimmanci shine ta sauka ta barwa namiji damar haka."
Zama yayi sannan wazir din ta ya mike me suna Burhan ya mike.
"Zamu duba wannan batun, sannan Sultanah zata tabbatar da tayi yadda kuke so."
A hankali aka shiga kus-kus, tare da jin eh ta amshi kuskurenta kuwa ko.
"A yafe Ni! Da zuwa a makare. Sunana Mir Rahil, ni ne me shige da fice na masarautan nan ta harkan haraji, Sultanah Hoyam ana fitar da dukiyar al'umma ba tare da sun gani a kasa ba, sannan an tsawallawa talakawa haraji, Sultanah muna gudun abinda ya faru lokacin Margayiya Sultanah Safrah ya kuma faruwa a wannan lokacin,. Idan da hali a duba maganar nan"
Dake mace ce lokaci guda suka hade mata kai, tare da nuna mata lallai sai ta sauka ta bawa D'anta. Har suka gama magana babu abinda tace. Karshe sai da safe tayi musu, tare da barin fadar.
Tunda ta shiga cikin turakarta, take kwance, ta kasa cewa kome, kallon Abubuwan da ya faru take, a hankali ta fita ta kofar shashinta ta baya, tare da nufar inda wani sirtacceen d'akin ta shiga bayan ta zauna.
"Zaki dawo dama?"
"Tuba nake!"
"Ai kinyi kuskuren! Ki tafi abinki, kamar yadda suka yunkura haka zaki hakura sannan kuma akwai wasu gaba, d'anki nan dai dole kiyi hakuri da shi. Kamar yadda kika."
Mik'ewa tayi da sauri ta bar cikin ɗakin, wani irin bala'i take ji, kamar zuciyarta zata buga, komawa dakin tayi, sannan yace mata.
"Ni na amince zaki ce!"
Ajiyar zuciya tayi sannan tace.
"Sai me kuma!"
"Kije kawai!"
Wani irin dariya ta sake tare da cewa.
"Ni Sultanah Hoyam."
***
A hankali na bude idanuna, na kalle ni a daure.
"Kan Uba! Ku dabobbi, shegu mugaye Azzalumai marasa imani, ku sake ni ku gani idan ban kashe ku ba, yan iska mugaye."
Ihu nake ina zagin su, tunda muna yankin mu larabci muke yi, kuma suna fahimtar abinda nake fada.
Takowa yayi gaba na, ya saka d'an mukulin ya bude ni, zubur nayi tare da kai mishi duka ya tare hannuna, tare da hada ni da jikin jirgin na bugu.
Riko gashin kaina yayi, "ki iya harshenki, idan ba haka ba wallahi zan baki mamaki, karki kuma d'aga min murya."
Cikin fusata na kalli idanun shi.
Dauke kan shi yayi da sauri.
"Bar kallona da shegen idanunki nan masu kama da na aljanu."
Sake fusata ni yayi na cigaba da kallon shi. Sauran bayin suna kallon mu, sake daka min tsawa yayi ban dauke kai na akan shi ba.
A hankali ya saka hannun shi ya keta min rigana har ƙasa, rungume shi nayi, tare da cusa kaina cikin kirjin shi.
Wani irin mutuwa jikin shi yayi tare da kasa aiwatar da kome.
Cire rigar samar jikin shi yayi tare da rufa min, kan shi ya kai dai dai kunne na, yace.
"Ki daina taurin kai."
Sannan ya yankince ni daga jikin shi ya ficce. Faduwa nayi tare da bin bayan shi da ido, ina huci, gyara zaman rigar nayi a jikina.
Abincin da suka kawo min, bai min ba nayi kwallo dashi.
"Ni bazan ci wannan abincin ba!" Na fada da karfi.
Dauka Inam tayi ta haɗa da bata aikuwa na shiga musu diban albarka.
Haka ya kuma shigowa da wata riga ya wurga min, sannan ya durkusa a gabana.
"Kin san me? Zan kunya taki a gaban jama'a! Idan baki son haka ki ci abinda aka baki."
Tofa mishi yawu nayi, tare da cewa.
"Idan ka fasa ka rena Uwarka da Ubanka, meye ya rage min kun sayo ni domin ku maidani baiwa ko? Toh nice ajalin Sarkin ku."
Goge fuskar shi yayi, tare da mik'ewa yasa aka kawo min, abincin shi. Ihu nayi tare da kiran daya daga cikin dakarun shi nace mishi.
"Kai kare! Zoka ga babban jaki ya kawo min abincin shi."
Basu kula ni ba, haka na ci abincin na turawa sauran matan, aikuwa suka cinye abincin.
Tsiya kala kala, nayi musu Iskanci kuwa da nake yiwa Nawwas da Zur Allah kadai ya sani, amma a duk lokacin da na tuna da kanwata Airan, idan ba fara kuka. Duk sai sun ji babu dad'i, dan suka rasa me zasu iya min nayi shiru.
Dan haka idan suka ga ba shiga damuwa, ina kuka sai su shiga min kid'a. Wanda suke ganin kamar haka zai sanya ni, saukowa da wuri.
Idan na gama kukan kuma, na shiga tsula musu Iskanci duk sai sun kasa yin kome. A hankali tafiyar kwanaki ƙalilan, ya jamu kwanaki sama da goma sha biyar, kafin muka isa. Dalilin b'ata lokacin ma Nawwas ne yake hana su tafiya da sauri.
Da safe muka masarautan, a hankali muke tafiya, jama'ar garin suna kallon mu, sai nuna mu suke.
Lokacin da muka shiga cikin farfajiyar, mun samu ana ta hidimar mulki kawai, haka muka zama yan kauye muna kallon yadda aka zuba dukiya me tarin yawa aka gina daular.
A hankali nake juyawa, ina kallon ko ina.
"Nawwas! Nifa idanun yarinyar nan tsoro yake bani!" Murmushi Nawwas yayi sannan yace masa.
"Babu abun tsoro fa,sai dai yau zata iya bazawa Sultan Abrad halin ta, zan so naga yadd..."
Kallon juna suka yi sannan Nawwas yace.
"Kasan me?"
"Amirah Sariyah matar Sultanah da tarasu, wallahi kamar su daya."
Sai lokacin Nawwas yayi murmushi, sannan....
🙄🤭
Sultanah Hoyam?
Nawwas?
Ikram?
Shuwagabannin yankunan kasar SAMAIND?
Sultan Abrad?
Amir Hood?
Fazilatul nisa?
Sultan me jiran gado....
*Alqur'an akwai matsala 🤔🤣 Chakwakiyya zalla 👌🏼*
#Paidbook
#Mai_Dambu
*Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ko katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641*
Happy weekend 💞💝
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1033128340?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=0hWPUPP4EB2me9%2Bvw5nt7Z%2FDqwYO3s4%2BGS7vBQWXokANARTOhHKVLw8%2Bp%2BHOFoec1Edf8fruBacauoAQ5%2FkXjvfowuFI57CvmlYdViv1eM0F4E%2Fap5Mu3ehqgtdE1I%2BO
🐾ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜🐾
_The Historical_
~BOOK ONE~
Mai_Dambu
Bismillah Rahamani Raheem.
Page 11...
Sake baki Zur yayi tare da kallon Nawwas, girgiza kai yayi tare da karawa gaba, tare da juyawa yana kallon hanyar da aka tura bayin.
.. tunda muka nufi hanyar, jikina yayi sanyi, dan na fahimci akwai sassauci game da wannan masarautan, muna shiga aka nuna mana cikin inda zamu zauna.
"Ya ku yan mata, zaku iya wucewa ban daki kuyi wanka tare da sauya kayan ku!" Inji wata babbar mace.
Tsaki nayi tare da dauke kaina, na nufi hanyar da aka nuna min,.tunda muka shiga kowa ya cire kayan shi amma naki cire nawa, ina tsaye kamar gumki.
"Ke ba zaki cire naki bane!" Juyawa nayi ina kallonta kafin nace mata.
"Ni ba dabba bace, balle ki ce na tsaya na cire kayan jikina." D'ago kai tayi tana kallona, cike da mamaki. Cikin rawan jiki ta bar ban ɗakin, siririn tsaki naja tare da komawa gefe na hade daya akan daya.
Can sai ga ta sun shigo da wasu matan, haka suka yi ta kallona, kafin suka kama ni da karfin tsiya, suka min wanka dan tsakani da Allah nake son basu ciwon kai.
Bayan sun gama tare da buge min bakina, duba mu suka shiga yi,suna ware wasu yan matan.
"Ban da munafunci meye yasa kuke ware mu?" Kallona suka yi sannan d'ayan su tace min.
"Duk wanda kika ga an ware ta, toh zaki samu ta tab'a daukar namiji ne, duk."
Sake baki nayi ina kallon ta,kafin nace mata.
"Idan ta dauki namijin ina zata kai shi?"
Cike da al'ajabi suke kallona, kafin suka share ni.
"Kuna nufin ba zaku gaya min gaskiya bane?"
Banza suka ba ajiya na, Inam ce ta riko hannuna.
"Suna nufin wadancan sun tab'a kwana da maza ne!"
Da sauri na rufe mata bakinta, jikina har yana karkarawa. Su kansu sai da suka fahimci a tsorace nake, kafin wani lokaci na fashe da kuka. Airan ce ta fado min, kuka nake har da shasheka. Dakyar suka duba gaban mu,tare da sallamar mu.
Kasancewar mu yan yankin nahiyar Afirka, mune muka fi yawa a wurin, sai muka sami saukin abubuwan, babu kyara ko hantara, dan yadda na Fahimta, kamar suna son zama da d'an Afirka. Ba yabon kai ba, duk inda dan afirka yake zaka same shi yana zaune ne dan niman na kanshi, zai yi wuya kace bai san aikin shi ba.
Kaya aka mika mana, tare da nuna mana yadda zamu saka, sannan suka ce muje wani daki mu gyara gashin kan mu, tunda muka shiga dakin muka shirya.
Abinci muka ci a nutse, sannan suka ce mana.
"Idan kun gama zamu kai ku shashin Sultan Abrad,
"Toh!"muka ce musu.
Muna gama cikin abinci kuwa, suka tawo, tare da bamu mayafai muka rufe fuskar mu,.sannan muka nufi babban dakin hutawar shi. Babban burina bai wuce na gaya mishi bakar magana ba, yadda zai ji haushin yadda yasa aka sayo ni,.muna shiga kuwa yana zaune.
Tunda muka shiga bai d'ago kai ba, har matar ta nufi inda yake tayi mishi magana, ko a jikin shi. Bai mata magana ba ya cigaba da abinda yake yi. Mun gaji da tsayuwa, kawai na sake musu tsaki. Me shegen karfi.
A fusace ya d'ago kai, ba iya shi ba dukkan su wai nima na suke,.
"Wacce mara mutunci ce tayi tsakin?"
"Nice!"
Cikin zafin nama, tazo ta finciko ni, sai da na zube akan gwiwata, zuba min ido tayi, kafin ta fita zai gata tare da dauko wasu fadawa, suka zo da bulalar su.
Nan suka shiga zane ni, bakina bai mutu ba, kuma ban fasa abinda nake yi ba, domin bakar magana nake gaya musu, tun maganar baya shigan shi, har ya d'ago kai tare da kafe ni da ido, nima shi nake kallon da idanuna jajjur.
"Sai na kashe ka! Wallahi."
Na fada da idanuna jajjur.
"Ya isa haka?" Ya dakatar dasu.
Mik'ewa yayi tare da isa inda yake sakale da takuba, biyu ya ciro tare da wurgo min, sai tawo a hankali yace min.
"Tashi gani ki kashe ni"
Cikin zafin rai, na mike da gudu sai da ya bari na dauki takobin nazo da gudu, ya goce tare da saka min kafa na fadi.
Murmushi yayi sannan yace.
"Idan kika yanke koda rigar jikina zan bada jirgi a mai dake garin ku, da dukiya me yawa. Idan kuma Ni nai nasara akanki, zaki zauna a cikin masarautan nan har zuwa lokacin da yayi min ki bar masarautan."
Cikin kwarin gwiwa, na kuma mik'ewa, kai naga mugu na karshe da yasan cewa ba iya kashe shi zanyi da sauki ba, shine ya shiga bani wahala, tare da mai dani abin wasar shi. Idan na kawo mishi sara haka zai goce ya make keyata, ko kuma yaja Jelar gashina.
A takaice dai haka ya mai dani kamar wata mage da b'era, musamman idan ta sami Bera mara wayo, haka yake ta min rashin mutunci. Karshe janyo ni yayi gaban shi, tare da saka hannun shi a gefen cikina, daya hannun kuma ya rike tare da takobin, cikin jin haushi na fara kiciniyar kwace kaina, yana ta juya takobin da hannuna, karshe ganin na takura mishi da juye tare da make shi da take mishi kafa ya ture ni gefe, yayi tafiyar shi.
Yana murmushin mugunta.
"Bakin mugu Azzalumi, sai kinyi kukan da nayi."
Da sauri matar da ta kawo mu, tazo tana faɗin.
"A kul da wannan maganar da kike mishi."
D'ago kai nayi ina kallonta, sai lokacin ta lura da hannu na da yayi jajjur, sabida hada hannun shi da nawa, d'ago ni tayi muka bar shashin.
... Tsaye yake gaban wani tangamemmen hoton da aka zana da wasu irin kallon launi, mace ce tsaye, sanye da tufafi masu nuna alamar itama yar babban gida ce.
"Sariyah! Na yarda da ana mutuwa, shi yasa na amince da hakan, amma yau ganin me kama dake ya kuma dagula al'amurra na, sama da kome."
Gyara tsayuwar shi yayi yana kuma hango kaman ta da Baiwar da tace zata kashe shi.