Header Ads
Showing 246001 words to 249000 words out of 274096 words

Chapter 83 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1356

Ads at the middle of Article

kamar zata fadi.
Hannun shi yasaka dukkan biyu ya zare zanin kirjinta, ya kai hannun shi kan halittar kirjinta zuwa ramin Cibiyar ta, wani irin yarrr taji bata san lokacinn da ta sake wani irin ajiyar zuciya ba, hannun shi yakai saman cinyoyin ta, yana murzawa zuwa kirjinta, a hankali jikinta ya fara rawa tare da jin kamar zata zauce. Rike hannun shi tayi tana girgiza mishi kanta, janyota yayi ta faɗa kirjin shi yana matsa mazauninta, jin jikakken gashin kanta ya sauka a fuskar shi bai san lokacin da ta juye mishi Ikram ba, kura mata ido yayi tare da juya ta, yayi tashi zaune yana kallonta. Yana son sauke nauyin da yake damun shi amma zuciyar shi tana hana shi, tare da hasashen ikram, zata zama nashi watan wata rana......
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayen Mu_


9....
Mik'ewa yayi daga gadon ya nufi ban daki, ruwa yayi ta kwarara kanshi har ya ji sauƙin yanayin da yake ciki, yana fitowa ya kalle ta sannan ya dauke kanshi tare da ca mata.
"Zaki iya tafiya!"
Tana fita ya juya ban daki ya kuma alola ya tada sallar nafilla, ya jima yana rokon ALLAH ya kawo mishi dauki a rayuwar shi, har zuwa wani lokaci.. kafin ya kwanta a gurin, yana tuno yadda ikram take zama a gurin, tare da jin wani mugun kewar ta yana taso mishi.


A hankali ya gyara kwanciyar shi ba tare da ya kuma koda yunkurin niman wata mace ba.


Safa da marwa Azizah take tana kallon kofar da zai sada dakin Mehran, ganin Mahlika tafito yasata saurin fitowa daga cikin d'akinta tana kallon yadda take tafiya ko ta kwanta da Sultan, ganin babu abinda ya sauya a tare da ita ya sata mata magana.
"Kina ganin kin isa ne da Mehran zai bukaci haka shimfid'a dake? Ai baki kai ba, haka ma babu macen da ta isa ta haɗa shimfid'a da mutumin da na ware shi domin kai na."


"Bani zakiwa iyayi ba, wanda ya kirani turakar shi ma, shine zakiwa kashedi" d'aga hannun tayi zata mare ta, aka rike hannunta.
"Bana son hauka, wuce abinki." Ya cewa Mahlika.
"Mehran me kake nufi?" Banza ya bawa ajiyarta, sake binshi tayi zata mishi iya shege ya daka mata tsawa, sai da ta shiga hankalinta, fita yayi daga gidan baki daya, ya sami saukin abinda yake ji.


Yadda iska ke ƙadaiwa sai yake jin kamar Ikram tana kusa dashi,. Da wutsiyar idanun shi ya kalli gefen da yake tsammanin haka yaga babu kowa, mai da kallon shi yayi inda yake hango kad'awa bishiyoyi. Duk da dare ya fara yi amma kewar Ikram a jinin shi take, shi yasa ya zabi zama a inda yake ganin nan ne zai ɗebe mishi kewa.


---
Tun da yamma ya shigo garin SAMAIND, amma kuma yadda zai shiga Cikin masarautan ya rasa, dan haka ya nemi masauki ya kwana a guri, abincin da aka kawo mishi ya tab'a sannan yayi Sallah bayan yayi wanka ya kwanta,


Washi gari
Da wuri ya isa fadar Sultan Mehran, ya nime iso dashi. Ana gaya mishi ga Amir Rahil yazo yace a kai shi falon ganawa ba baki, tunda ya shiga yake kallon yadda yanayin gurin yake, yana nazarin littafan da aka ajiye su na tarihi da na addini.


Da sallama ya shigo, a hankali ya juya tare da amsa mishi. Yana murmushi.
"Ya naga kamar Sultan Aamaan Mehran ya faɗa ko jinya kayi ne bayan tafiyar abincin ruhu ka?"


Murmushi mara sauti yayi sannan yace mishi.
"Me kake tunani? Ai namijin duniya ba a san shi da saka tunani a ranshi ba, domin kullum ana mishi kallon sadaukarwa ne. Meke tafe dakai dan samari?"


Ya zauna bayan ya daura kafa daya akan daya, murmushi yayi sannan ya zauna shima yana kallon shi.
"Na zata zan zo na samu anyi bikin ka ne da Yayan gwamnonin ka? Ashe ba haka bane. Koda yake babu wacce zata iya da halinka sai Ita, gashi kuma wacce kake so tana can zata zama matar da zan aura nan da kwanaki, toh kasan mata irin su Ikram ba kowa yake samun shi ba domin tsada ne dasu, shi.yasa naki barin damar na rasata na kafe zan aureta, koda yake ba zaka gane haka ba, domin baka bada damar haka ba, ga sakon gayyatar mu nan, ko zaka bikin mu."


Duk da ya gama jin haushin abinda yake mishi amma bai ji a ranshi ko zai iya mishi wani abu ba, asalima girmama shi yake sabida ko babu kome a cikin wata uku yaga wani na kusa da Ikram. Murmushi yayi sannan yace mishi.
" Ayya kazo a lokacin da bai dace ba domin Al'umma ta, tana faman da fari, ba zan iya tafiya na bar su cikin.wani yanayi ba, ina muku fatan Alkhairi."


"A'a kace dai ba zaka iya kallon wani namijin ya auri matar da kake matukar kauna ba? Koda yake ai ba sabon abu bane dan kaki zuwa auren mu, amma abin kunya ne a ce mutumin da Ya rike hannun Ikram na shekara daya ya kasa zuwa bikinta, ban ga laifinka ba, tunda Abrad zai je da sauki. Amma zan gaya mata gaskiya da take damuwa akan ka kai baka dace a damu da kai ba, sabida cikin gidan ka cike yake da Kwarkwarorin. Ita"
"Ya isa!" Ya daka mishi tsawa, kafin ya mike yana kallon Rahil.
"Kai kamar Ubane a gare ta domin ku biyu ne kuka ragewa Sultanah Balkisu Ikram. Ina girmama Ikram dan haka kai ma haka nake girmama ka, me yasa zaka kawo min shirme? Ba zan sami zuwa ba, Allah ya baku zaman lafiya, na gaya maka ina da Uzuri!"


"Uzurin ya kai na wacce take kukan akan ka ne? Ko ya wuce nata ne? Kasan yadda namiji yake ji idan ya fuskanci macen da yake so bata kaunar shi wani take so? Mehran meye kafi ni dashi da Ikram take kuka akanka?"


Kura mishi ido yayi a tsannake, yana tuno ranar da yayi mata tambayar meye Noman ya fishi take kuka akan shi yau gashi Rahil yana tambayar haka. Cike da Mamaki yake kallon Rahil.
"Dama yana kuka ne akai na?"
"Ga sakon daurin auren mu, idan kana son amsar shi ka halarci bikin mu, zaka sami amsar da kake nima." Yana gama fadar haka ya juya abin shi.


Tabbas idan ya cigaba da zama a Samaind kome zai faru, dan haka ya juya tare da barin garin baki daya, domin so da kishi sun mishi yawa, idan ya cigaba da tuna Ikram tayi mishi nisa zai iya yunkurin kashe Mehran, haka kuma zai saka a kashe shi.


Tausayin kan shi yake, sai dai ya barwa Allah zavin duk abinda ya bashi Alkhairi ne.


Tunda ya bar Mehran a falon baki ya shiga rudani domin baki daya ya rasa abinda zai yi ya zama gaskiya, gani yake kamar karya ne Ikram ba zata yi kuka saboda shi ba, ashe kuwa zama bai gan shi ba, ba zai iya wannan sadaukarwa na, ya hakura da Ikram kamar ya hakura ne da rayuwa shi hade da mulkin shi. Lumshe idanun shi yayi bayan ya gyara zaman shi a kujeran da yake, ya zubawa takardan gayyatar, bude lumshasshen idanun shi yayi tare da kankancewa, yana jin wani irin yanayi yana kuma kara tabbatar mishi da kasancewar shi da ita. Duk da yana kewar ta haka sai ya shi jin kamar ba gaskiya bane da Rahil yake gaya mishi tana kuka da kewar shi,


Kenan itama tana jin yadda yake ji akanta, kenan dukkan su suna yiwa juna kurman Kauna? Toh indai karayar da ya gani akan idanun Rahil, haka ne toh ba maka ba zai zare rai akanta ba, ba zai cire samunta ba. Ba zai cire yakinin zama da ita a inuwa d'aya ba. Kai wannan abun yayi mishi dadi bai tab'a jin labari me dad'i irin shi ba kamar na yau.


Lallai shi din dan gata ne, ashe akwai lokacin da Ikram zata yi kuka akan shi, murmushi ya sake sannan ya gyada kan shi yana me jin lallai shi din me rabone, dan haka duk me yiwa dole ya tafi ya ganta kodan yadda yaji labarin tana mishi kuka.


Murmushi ne me sanyi ya sake ba tare da ya shirya hakan ba, ya mike zuwa fada, kallon manyan mutanen yayi cikin tsantsan farin ciki yace musu.
"Kuyi duk yadda zaku yi, sannan Ni zan tafi kasar Yamma domin gudanar da bincike akan maganin da zamu yi amfani dashi na kashe farin, nan da kwana uku ne tafiyar kuma zai kai ni sati biyu Insha Allah. Sannan a rabawa mutane abinci da abin amfani kafin Allah ya dawo dani."


Ya faɗa tare da mik'ewa zai bar fadar,kallon juna suka yi kafin suka ce.
"Amma dai baka shirya tafiyar ba sai da ka sami labarin Auren Baiwarka da..."


A nutse ya juyo yana kallon Zuhair, wanda shi yayi magana, murmushi yayi mishi sannan yace mishi.
"Bikin zan je, akwai matsala ne?"
Ganin yadda ya juya cikin wani irin izza, yasa duk suka nutsu. Matsalar Mehran ba wai kawai iya magana bane a bakin shi kwarjinin shi hadda kayan jikin shi yana bayyanawa, mutum ne da yasan darajar abinda zai fada. Shi yasa yayi musu zarra, gashi nan dai yaro ne a cikin su,sai Zuhair amma a ruwan sanyi ya kusawa manyan da suka yi jika dashi tsoron shi.


Suna masifar shakkar abinda zai biyo baya, shi yasa idan yayi magana kamar yankan wuka jikin shi har rawa yaƙe.
"Akwai abinda ka ajiye min ne?"
Ya tambayi Zuhair bayan ya dawo fadar ya zauna, kallon manyan fadar yayi sannan ya cigaba da juya zoben hannun shi na azurfa.
"Tambayar ka nake?"
"Kayi hakuri Sultan Mehran! Yaro ne bai san kome ba."
"Nasan da haka" ya faɗa tare da jingina kan shi yana me kumshe idanun shi, kafin ya tsinkayo Muryan Zuhair yana faɗin.


"An gaya mishi gaskiya, shi waye da zamu ji tsoron shi, mulki hauka ce, ko aba a bashi yan mata bane? Sannan meye Jasrah tayi da za a kai ta gidan Azaba?" Murmushi yayi sannan ya kuma kallon Amir Hood da hankalin shi yayi mugun tashi, danne Zuhair yake amma fir yaki shiru zai da ya tsinka mishi mari yayi shiru. Mikewa Amir Hood yayi zuwa gaban Mehran.


"Kayi hakuri kasan Yarone kuma bai da hankali, duk abinda ya fito bakin shi yake faɗa." Bude idanun shi yayi akan Amir Hood, sannan yace mishi.
"Meye ya faru?"
Jikin kowa ne yayi masifar sanyi.
"Kayi hakuri Mehran"
Kurawa Hood idanu yayi sannan ya tab'e bakin shi, sannan ya kalli Fudail ya gyada mishi kai. Ya fita.


Tare suka fita. Kallon shi Fudail yayi sannan yace mishi.
"Sultan me yasa kaki amsar hakurin da yake ba? Sannan kuma baka hukunta shi bayan kuwa sunyi maka laifi." Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Kasan me yasa na tura Mahaifiyata daga jikina? Kasan me yasa naki magana akan Mutuwar Mahaifina? Shi yasa naki kula batun shi, Amir Hood yayi laifi bana son na hukunta shi idan na tab'a Zuhair har abada ba zan iya hukunta kowa ba, sabida zasu ce ina amfani da mulkina ina zalinci, Babban Damuwa na talakawa na, suci su koshi..bana son na bar garin suna cikin wani yanayi na wahala.


Sannan idan na hukunta shi ,.daga baya suka sami labarin naje daurin auren Ikram zasu rena ni, amma da nayi shiru zanyi magana ba, ai ya wuce.. koda sunji labarin ba zasu zarge ni ba, kaina Yana ciwo sai magana nake, kuma ban gama ba."


Haka suka koma dakin shi, yana yiwa Fudail bayanin abinda yake shiryawa, tare da tsarin da zasu bi a taimakawa Talakawan shi.


----
Kwance nake hawaye na zuba daga rufaffen idanuna, ina jin kome da ake yi amma bani da ikon na amsa musu, sai dai ina jin su da tattaunawan da suke a kaina.
Suna son na bude idanuna amma fir naki, sai ma kara rufe shi da nake yi..shafa hannuna Sultanah Amrah take yi tana gogen min zufar da nake.


"Ikram meye yake damun ki?"
Ta tambaye ni kumshe idanun na kuma yi, ajiyar zuciya na sauke,.a sanyayye sannan na bude idanuna akanta kafin nace mata.
"Mehran!"
"Shin ba zaki hakura dashi bane? Mutun kamar wanda yayi.miki asiri na fara gajiya."


"Amma dani ko? Domin ni bana gajiya da Mehran. Kuma ba dan tab'a gajiya dashi ba har karshen rayuwata, Mehran naso Mehran zan cigaba da so.


Koda kuwa haka zai zame min.rayuwa da mutuwa amma Mehran wani tubali ne a rayuwata,.da zaran na rasa shi na rasa kome na duk na Shine."


Buge min baƙi tayi iyaka razana na razana, kuka na fashe da shi ina kallon ta, nace.
"Me yasa kike son Rabani da rayuwata? Me yasa kuke son tirsassa min? Da iyayena na raye ba zasu tab'a min dole ba, kowa zai bani abinda nake so ne?


Ko tausayina matsayin mariniya baku yi amma kuna son nayi muku biyayya bayan nima ba bani abinda nake so kuka yi ba, sannan ku Fahimci ni da ku akwai bambancin ra'ayi da al'adu. Ku mulki ya ginaku, kun taso cikin al'adar shi.ni kuma na taso inda aka boye min asalina me yasa ba zaku kyale Ni ba, wallahi nayi imani matukar kuka bani damar zama da Mehran zan yi farin ciki har karshen rayuwata, amma idan kuka bani wanin shi zan amsa da nayi muku biyayya ne ba dan na fahimci irin gatan da kuke min ba. Ya dace ku duba ni ku duba maraicina, Mehran wani yanki ne na rayuwata. Ba zan iya samun wanda ya fishi ba, ya koya min son shi tun ban kai haka ba, shine namijin da na zauna dashi bai tab'a yunkurin keta min mutuncina ba.


Shine namijin da kome zanyi baya kallona da idanun shi sai ma ya dauke kanshi wani namiji ne kuma basarake za same ni bai kwanta dani ba, tunda baiwar shi ce Sai Mehran, sabida ba jikina ne a gaban shi ba, Ni ce abar son shi. Shi kenan shi kenan, shi kenan na hakura dashi domin nayi muku biyayya....
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayen Mu_


10
"Ba hanaki farin cikin ki muka yi ba muna hango miki abinda yake tattare da wancan daular ce, kiyi hakuri iya gatar da zamu miki kenan."


Girgiza mata kai nayi tare da kallon yadda take kokarin nuna min gaskiya,
"Ba zan Fahimta ba, ba zan tab'a Fahimta ba, zuciyata kawai nake fahimta bayan ita ba zan iya fahimtar kome ba, idan kuka bani damar zama da wanda nake so zan yi alfahari da haka da akan. Amma ba kome ba kome. Shi kenan."


Na fada tare da juya mata baya, tabbas wannan shine abinda ake cewa an b'ata goma daya bata gyaru. Yarinyar duk ta fita hayacinta, sai dai gaskiya barinta tayi aure a Samaind kamar kashe ta da rayuwarta suka yi.


Kukan da nake ne yake kuma tab'a mata zuciya, shafa bayana tayi sannan ta mike tare da barin d'akin, tana jin kamar tayi kuka.
Fadar Sultan Mu'allim ta nufa, inda tace Mishi.
"Sultan ina son ganawa da kai"
Jinjina kai yayi sannan yace mata.
"Ki shiga cikin gidan gani nan zuwa."


"Nagode!"
Ta juya tare da komawa gida, tana jiran shi, bayan wani lokaci ya shigo suka sake gaisawa. Sannan ta gaya mishi abinda ya kawo ta, shiru yayi sannan yace mata.
"Kiyi hakuri! Na rigada na yanke shawara, ta shiga hankalin ta karta sake nayi fushi da ita aure ne babu fashi."
"Allah ya huci zuciyar ka." Ta gaya mishi sannan ta tashi tabar falon sai yanzun take kuma hango kamar akwai son zuciya akan auren domin dai ba wai dan suna son Yarinyar bane sai dan kawai ta biya musu bukatar su.


Allah ya kawo mata dauki, ta faɗa a ranta. Domin kuwa bata hango yadda zata iya taimaka mata. Da wannan zancen zucin ta isa cikin gidan, tasa bayin da suka rakota fara shirya tafiyarta zuwa wani sati su dawo.


****
A hankali yake takawa har cikin haramtacciyar fada, zama yayi tare da kallon Sultanah Fazilatul nisa, kan shi a sunkuye. Sannan yace mata.
"Zan tafi bikin Ikram"
"Allah ya tsare hanya."
Mikewa yayi tare da barin gidan.


..... Haka suka shirya cikin.dakaruk karta kwana da Sarwat da kuma Fudail bayan ya barwa Zunnoon garin shi, a karo na biyu. Ana bikin saura kwana biyu. Suka nufi Merocco. Tafiyar da ta dauke su wuni daya da rabi.


Dan sun yi tafiyar ba tsayawa, sun shiga garin ana shagalgular bikin. Duk da dare ne sosai, amma ana akan shagali. Masauki aka kai shi yayi wanka tare da hutawa, sannan ya fito kamar yadda kowanni sarki yaƙe, ya nufi gurin shagalin.


...... Tunda aka shirya Ni sanye nake da zinari bayan kayan da aka sami, sai zinarar da aka min wanka dasu, hannu da wuyana. Kai na har da kafana, ko yayya nayi motsi sai kaje karar su. Kaina a sunkuye ina me kallon zobben Mehran karamar azurfa wacce ta kuma kara haska hannuna da yake dauke da zinarai. Riko hannuna Rahil yayi tare da cewa.
"D'ago kanki mana na nuna miki wani abu"
Kamar ba zan d'ago ba. Na dai d'ago ina kallon shi. Nuna min wani guri yayi da idanun shi. Mehran na hango a zaune fuskar shi tayi wani irin kyau, kasa dauke idanuna nayi. Sannan na

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads