Header Ads
Showing 216001 words to 219000 words out of 274096 words

Chapter 73 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1365

Ads at the middle of Article

a ruwa!"
"Sultan Abrad!"
A fusace ya juya ga Rab, had'iye yawun yayi sannan ya sunkuyar da kanshi,bai kuma cewa kome ba. Amma tabbas wannan shine abinda ba zai iya dauka ba, dan haka yana ganin an dauki gawar Nawwas, aka fito dashi shima yabi bayan su da gudu, kafin yayi wani yunkuri an wurga cikin teku bayan dakaru sun rike shi.


Ihu yake tare da kokarin kwacewa a hannun su, amma suka kara rike shi, yana ji yana gani gawan Nawwas ya nutse cikin ruwan, kuka yake tare da ihun. Buga mishi kasa takobi Abrad yayi. Bai kuma fahimtar inda kan shi yake ba.


***
Wurgi yayi da takobin hannun shi, tare da fasa kara yana huci.
"Tabbas Abrad yasan zan dawo na bi takan shi, wato shine ya gudu. Fudail Darda ina Nawwas din?"
"Sultan MEHRAN! Tun jiya muke binka akan Nawwas, amma baka tsaya munyi magana ba, shi yasa da ya gaji yayi tafiyar shi bai..."


Yadda ya kafe Fudail da ido ne, yasa shi sunkuyar da kai kasa, yana had'iye yawu.
"Sultan MEHRAN!"
"Ina jinka, meye yace?"
Ya tambaye shi, tare da kallon gefe. Fita suka yi daga cikin gidan..sai da suka yi tafiya me nisa, sannan yace mishi.
"Sultan MEHRAN! Nawwas bai gaya min kome ba!"
Cakume wuyar shi yayi tare da fidda huci.
"Ni zaka mara da takalmin kafarka? Ko zaka samu damar boye min abinda yake ranka? Gaya min meye laifina da kuke boye min abinda ya dace na sani."


"Kayi hakuri bai gaya min kome ba, amma yace na nime bawan shi Rab." Wani dirkeken naushi ya kasake a jikin bishiyar da Bayan Nawwas yake jingine. Sai da hannun shi ya farfashe. Sannan ya takarkare ya fasa ihu. Sai da dajin ya amsa.


Zafi biyu yake ciki, babu wanda zai gaya mishi gaskiya kenan? Ya rasa Ikram ya rasa wanda zai gaya mishi abinda ya faru kenan, dan haka ya tashi cikin tashin hankali ya juya zai tafi. Ya kuma juyawa ya kalli Fudail, sannan ya saka kai zai bar gurin. Ajiyar zuciya Fudail yayi sannan a ranshi ya ayyana cewa.
*_Ba zan tab'a yarda na gaya maka gaskiya ba! Sai har na gama gabatar da abinda yake gaba na, ba zan tab'a yarda na kyale wanda ya cutar da ikram koda da bakar magana ce balle da farar magana! Kayi hakuri Sultan Mehran_*


Ya faɗa a sanyayye, yana me jin tausayin Sultan Mehran. Domin a yanzun gaskiya yake nima idanu a rufe, kuma baya jin zai gaya mishi koda kuwa zai rasa rayuwar shi, Dole kuwa Azizatul Nissah taji a jikinta itama. Abin kunyar da suke amfani dashi ga rayuwar Ikram itama taji yadda tozarci yake. Amma kuma idan ya tuna rokon da Nawwas yayi mishi sai yaji tsoron kar haka kuma ya tab'a kimarta.


Dafe goshin da yayi tare da bin bayan Mehran, yana tafiya yana zancen Zuci. Har ya isa inda dokin shi yake, dan yanzun kan yasan Mehran yayi mishi nisa, koda ya cilla dokin shi ya hango su, dab da Masarautan. Amma kuma koda ya isa Fir dakarun suka hana shi shiga. Wannan shine karon farko da Mehran ya mishi hukunci me tsauri ta hanyar amfani da hana shi, shiga SAMAIND! Dan haka bai yi fushi ba, ya zauna a gurin gashi garin da alamun shigowar damina.


Duk sai yaji babu dad'i a ranshi, yau shine Mehran yayiwa wannan hukuncin, dan haka duk dai yake gani kamar tozartawa ne, ga wani muzancin da yake ji a ranshi. Kanshi a sunkuye har aka fara yayyafi. Bayan wani lokaci ruwa ya fara me mugun karfi da yawa. Yana tsaye a bakin kofar shiga masarautan..


----
Tunda ya shiga cikin gidan, ake mishi magana kome ya gani fatali yake dashi, har ya shiga cikin dakin shi. Huci yake ya rasa yadda zai yi da Fudail idan kowa zai ci amanar shi yana tunanin ai Fudail ba zai tab'a yarda a cutar dashi ba.


Kuma yayi imani da Allah akwai da yake boye shi, kuma ba zai tab'a yarda da munafunci ba, domin idan ba munafunci ba akan me zai boye mishi maganar da yake bukatar yaji, dan haka babu abinda zai hana shi bai hukunta shi ba, sai ya hukunshi sosai domin kuwa ba zai yarda da wannan wulakancin ba, tsaki yayi tare da kutufal da kayan shayin gaban shi, yana jin ana buga kofar shi amma fir yaki buɗe sabida yayi fushi anci amanar shi...
(See me see trouble😹😂😹🤣 ta ina aka ci amanar ka Yau ga D'an Uwan Jamal🤔)
+2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


02


Kaiwa yake yana komowa, tsabar yaji haushin abinda ya faru. Jin cidan hadari tare da rugugi ya sashi zare ido cikin takaici da bakin ciki.
"Duk irin zaman da muka yi da.". Bude kofar shi da aka yi yasa shi had'iye sauran maganar da da zai yi, ya zubawa kofar ido. Shigowa tayi tare da ajiye mishi ruwa. Sunkuyar da kai tayi cikin girmamawa tace mishi.
"Sultan MEHRAN gashi."


Kallon ta yayi tare da tuna abinda Abrad yayi mishi dan haka ya a nufi ruwan bai ce mata kome ba, ya dauka ya shanye tass. Ya ajiye kofin kafin ya zauna yana kallon ta.
"Me yasa yayi min haka?"
Kallon shi tayi a razane tare da ja da baya, tana girgiza mishi kai.
"Ni."
"Tambayar ki nake zaki dawo min da tambaya na" wani shegen tsoro ne ya lullube ta, tare da zaro idanu waje, jikinta yana rawa. Tabbas duk rayuwarta da tayi bata tab'a ganin wanda iya tsawar shi abar firgita ce kamar Mehran.


Shin dan ya kasance Shugaba ne? Koko dan ya kasance Zaki ne kisabo, wallahi ita har tsoron had'a idanu take dashi. Ganin taki fita ya sashi fahimtar akwai abinda take buƙata, bai tsaya da tunanin shi ba, yaji marar shi kamar an daure mishi. Wani azazzaben sha'awar kasancewa da mace ya taso mishi. Kura mata ido yayi ganin yadda take kallon shi. Komawa yayi saman kujeran ya zube yana sauke numfashin sa.


A hankali ta tako gaban shi, tare da tsayawa tana kallon yadda yake lumshe idanun shi, wato shi ba zai kira mace ta taimaka mishi ba, ya gwammace koda zai mutu ne gwara ya mutum, zare kayan jikinta tayi suka zube a kasa. Sannan ya taimaka mishi suka shiga d'akin.


A wannan lokacin shi kanshi idan ka tambaye shi wani hali yake ciki bai sani ba, amma tabbas yaji a ranshi yana kwance da mace. Sai dai har yau kamar can baya da yaki matan dan kanshi ya kyamaci haka a ranshi. Duk da kyamar bai hana shi buga mata isa ba. Ya kasance ta da iya karfin shi da lafiyarta, tun tana kallon haka a matsayin abin da bai kai ya kawo ba, har ita da kanta ta fara dukar shi tana kuka.


Shi kuma wai yayi haka bane dan lafiyar shi, haka ya faru ne dan abinda ta bashi ya sha, shi yasa ya rasa tunanin shi ya hake mata Sosai. Komawa gefe yayi tare da kwanciya rub da ciki. A hankali barci me nauyi ya dauke shi. Kallon shi tayi sannan ta mike a hankali. Bata tsaya wanka a dakin shi ba, ta saka kayanta tare da fita daga d'akin bayan ta ajiye mishi wani tambarin da zai iya wargaza mishi kome har karshen rayuwar shi.


~~~
Sai da ruwan nan ya kare tsaf akan Fudail ya shigo Masarautan, koda ya shiga shashin sa ya nufa yayi wanka da ruwan zafi sannan yana wankan tare da murmushin abinda Mehran yayi mishi bai wani damu can ba, sabida ko shi aka yiwa haka iya hukuncin da zai yanke kenan.
Dan haka babban abinda yake shirin akan Azizatul Nissah ce.


~~~
Munyi tafiya me nisa wanda muka bar yankin Farisa sannan muka nufi kuduncin jazziratul Arab, anan muka yada Zango. Tunda muka tsaya aka gama shirya mana tantin mu. Na shiga gurin Sultanah Amrah, na zauna duk da ba hira muke ba, amma kuma haka yana sani jin kamar ina tare da Ammyn na ne, dan haka bayan munyi sallah na kwanta a gurin, ita kuma ta cigaba da abinda take, lokaci zuwa lokaci tana kallon yadda nake barci.


Hawaye ne ya zubo mata, ta girgiza kai sannan ta cigaba da aikinta, tana tuna abubuwa dayawa akan yaranta da mulki yasa ta manta da su. Tabbas mulki matukar baka nemi Izni Allah akan shi ba, zai iya kai ka ya baro ta,


Kamar yadda ya kaita ya baro ta, sai dai ta wani gefen zata iya godewa Allah tunda akwai Ikram da Ilham, Yar gidan Abrad. Murmushi tayi bayan ta shafa kanta, tana me jin kewar Yaran ta.

... Zan iya cewa barcin da nayi me cike da gajiya da mafarkai marasa kyau da dad'i, karshe dai haka na farka da sunan Mehran. Da gudu Rahil ya shigo tantin. Da sauri ya iso gabana, fadawa jikin shi nayi ina haki. "Me ya faru?" "Mehran!" Na fada kamar zanyi kuka. Juyar da kan shi yayi. "Ba zaki daina kwadayin ganin shi ba?" "Karka raba ni da shi, zuciyata halittar shi ce." Matse bakina yayi idanun shi cike da kwalla. "Ni kuma sabida ke aka halicce ni, ina sonki Ikram. Nasan idan ba zama daya muka yi ba, ba zaki daina kwadayin shi ba" ya faɗa bayan ya cire hannunsa a bakina, kokarin hada bakin mu yake na kawar da kaina. "Meye kike nufi? Ba zaki." Ture shi nayi tare da mik'ewa, ya kuma tasowa yana kallona. Kamar zai yi kuka yace.
"Meye yafi Ni dashi? Meye na rasa da ba zaki amshi tayi na ba, wallahi yau sai na dasa miki kaunata a ranki." Fada sosai muka yi da Rahil domin ya kafe sai ya fahimtar dani yadda yake sona. Ni kuma na rantse ba zan yarda da wannan tunanin na shi ba haka muka gama dakyar na kwaci kai na.


Sam na kasa nutsuwa a raina, domin kuwa, haushina yake ji kamar ya kashe ni, bayan fitar shi Sultanah Amratu ta shigo, fadawa nayi jikinta ina kuka. Tare da cusa kai na a jikinta.
"Zuwa yanzun ya kamata ki cire Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran, a ranki domin kwanaki ƙalilan zaki kasance matar Rahil. Don ki daina tunawa da sultan Aamaan."


Kallonta nayi baki sake, kafin na sauke idanuna kasa, ina kuka.
"Ummyn!" Yatsar hannunta ta saka min akan bakina, tare da girgiza min kai.
"Kowa yasan cewa kece kwarin gwiwar shi, ki taimaka ki sauko ayi kome cikin ruwan sanyi."


Hawayen da nake tarewa suka daga cikin idanuna, na kasa magana baki daya sai kallonta nake.
"Tsarin masarautar mu, cike yake da kawaici da YAKANA karki yarda ahalin Mahaifinki su fahimci kin sayar da zuciyarki ga wanin su. Domin haka tilin abin kunya ce gare mu!"


"Toh dole ne sai na rayu cikin mulki? Me yasa ba zaku gan.." d'aga min hannun tayi tare da kallon, yadda bakina yake rawa. Kifa kai nayi a tafin hannuna, na fashe da kuka. Ina girgiza kai,


Tashi tayi tare da bar min tantin kuma ta hana kowa shigo min, domin tana ganin matukar suka shigo min zan iya tsarewa. Gurin yan uwan Baba na, ta nufa suka tattauna. Anan suka ajiye shawara ita zata wuce Asakandariya su kuma su wuce dani can Merocco. Idan ita mace ce mai rauni tausayina zai iya sakawa ta bani abinda nake so.


Su kuma ahalin mahaifina babu wannan yanayin a tare dasu, dan haka su tafi dani. Bayan ta dawo ne, take kallon yadda na kifa kai ka a saman gwiwar kafana.
"Zaku wuce Merocco."
Da sauri na d'ago kai na, zanyi magana ya juya min baya bata bani damar ma tambayarta ba, ta cigaba da abinda take, ni kai na nasan ba zan iya tababa da ita ba, amma kuma ya kamata su fahimci abinda nake so. Bayan mun huta aka kuma tadda tafiyar. Ina ji ina gani ta tafi da Nimrah.


Ni kuma muka tafi da Izmah, bayan mun sha kuka. Tunda muka dauki hanya, banzan can yake wani shige min. Ko kallon shi banyi ba, har muka wuni a hanyar, dab Magarib muka shiga garin, wanda tun kafin mu iso labari ya iso musu muna kan hanyar mu, sakamakon wani mahayi da aka turo shi.


Dan haka garin ya kasance kamar ana bikin sallah, wani irin biki ake me cike da shagali. Haka muka isa har fadan, inda aka muka yada zango a falon Sultan Mu'allim. Mika min hannun yyi. Da sauri na isa gare shi. Ina isa na zube gwiwata a kasa, kai na a bisa kafadar shi, na sake kuka me cin rai. Takaici yasa Rahil fita a gidan.


Kuka nake wanda idan ka tambaye ni ba zance maka ga abinda aka min ba, amma kuma a cikin raina, ina kuka ne domin na rasa Mehran. Yadda nake kukan ya sashi sake murmushin jin dadin. Sannan ya shafa kai na, yace.
"Kiyi hakuri! Haka muke tsara miki baki rayuwar. Da karen layi gwara Zakin gidanka koda kuwa zaka zane shi da bulala ne, kiyi dan mahaifanki da kanwarki. Ba akan ki da soyayyar ki ba. Mun rigada mun yanke kuma al'adunmu sun sha banban da kowane, mukan iya binne abinda muke so! Mukan iya boye abinda muke kauna, matukar hakan zai bamu damar fuskantar matsalar.


A tsarin mu, bai zama dole mace ta samu abinda take so ba, matukar zata bawa Mulkin mu. Gudunmawa dan haka na zab'i ra'ayin shi sabida ki bashi gudunmawa. Yanayin ku yayi daidai da mulkin, abinda ake bukata domin mulki kin hada, dan haka ki amshi Rahil a matsayin abokin rayuwar ki."


Hawaye ne ya shiga zuba min, na kasa magana tare da sunkuyar da kaina, domin yayi min kwarjini. Haka aka fitar dani har dakin Bilqisul Ikram, tankwarata. Shafa kaina tayi sannan ta kira amintattun bayin ta, suka shiga dani ban daki. Aka hada min wani irin ruwan wanka tare da turaruka masu dadi. Sai furen kamshi da wanka aka watsa a ruwan, sannan suka shiga cudani. Hawaye na zuba a idanuna. Shi kenan na rasa Mehran. Na rasa Jarumina, me yasa tun tuni ban amsa mishi ba. D'ago kai nayi sannan nace a raina.
_Toh amma ai bai ce yana sona Ba? Toh amma kuma ai duk abinda yake min duk na soyayya ce! Kishi da zafin rai akai na duk abinda masoyi ne kaɗai yake yin shi! Toh Ni me yasa na shiga zab'en? Kenan bawai na shiga dan shi bane sai dan ina son shi?_


Kwalla ne ya zubo min, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, haka suka taimaka min nayi wanka na fito bayan sun bani wani yadi na lullube jikina, tare da fitowa daga ban ɗakin, tunda na fito suka shiga shafa min wani abu kamar mai kamar sabulu, ina zaune ina kallon su. Kwallar da nake sharewa a kai a kai, yasa Bayin suka shiga rarrashina, kamar dama jiran su nake na fashe da kuka. Hannun daya daga cikin su ta saka min a bakina.
"Abin kunya ne babba ga Sultanah Balkisu Ikram aji cewa babbar Yar D'anta na farko tana kuka akan SO kinsan yadda muke boye kalmar a ran mu kuwa? Toh koda kuwa zaka rasa ranka akan sone yana da kau kayi hakuri da shi, idan baso kike mulkin kasar nan ta gagari Amir Rahil ba.


Don Allah ki hakura da Sultan Aamaan Mehran. Mun san yadda kike son shi, amma duk wanda zaki gani a cikin masarautan nan yana da tab'on soyayya, dan haka karki sake a Fahimci zuciyarki tana ga wani da namijin domin abin kunya ce ga Kakarki."


Haka suka kashe ni da magana tare da nuna min illar abinda nake aikatawa, nayi kuka da sunan Allah kuma nayi bakin cikin zamowa ta, daya daga cikin ahalin babban gida. Ina ji ina gani ranar aka mai dani kamar wata yar tsana, zunzurutun wanke nan shafe ne. Ana gyara min jikina. Har kusan tsakiyar dare a sannan nayi wankar karshe tare da sallah na kwanta,. Ranar barci na zance kacokan mafarkin Mehran nayi tayi. Ina kuka ina kome haka zan farka naga bayin nan suna rarrashina.


..... Washi gari ina farkawa kafin nayi sallah asuba, suka bani madara dafaffiya,, sai da na wanke baki na shanye tass, sannan na shiga wanka tare da Alola ina idarwa, aka kuma kawo min yankanken y'ay'an itacce, wanda aka zuba madara da zuma na shanye shi, ina ji suna faɗin.
"Kirjinta muke son ya cika kafin zuwa bikin su." Shiru nayi domin bani da bakin magana sai yadda suka yi dani...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


03
Wato ma'ana bani magani suke tare da abinci me gina jiki, duk abinda suke idanuna a rufe suke, bana budewa wani lokaci haka zasu yi ta magana ina jin su, bana tanka musu, idan suka gama min kuwa a gurin nake kwanciya. Ina kuka duk taurin zuciya ta da taurin kai na, sai da ya kai komi kashin b'acin rai kuka yake sani.


Rabona da Izmah kuwa sai dai na shafe kwanaki goma kafin aka barta ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads