Showing 204001 words to 207000 words out of 274096 words
Chapter 69 - DAULA BIYU Complet Document .txt
daya ne kawai zai fidda Ni cikin duhun da nake ciki.
"Karki ga laifin shi. Sultan Abrad yayi mishi wasu maganarki wanda ban san me ya gaya mishi ba."
Bakina yana rawa na kura mishi ido, sannan na juya tare da barin shashin sa, na nufi inda nake da zama, a hanyar wucewa ta naji Kwarkwarah shi wato Sakeenatu binti Abu Waqqas tana faɗin.
"Idan mace ta isa bata bin namiji shi yake binta" halin da nake ciki bana jin zai barni nayi magana kawai na kad'a kai nayi gaba abuna, sabida ba zan iya daukar tashin hankali biyu ba, ga nashi ga na wad'anda ban san kansu ba.
....
Tunda na zauna nake kallon madubi, abisa ka'idar zan kai mishi abinda da kuma zama dashi dan hira, sai dai shigowar Sultanah ta zuba min ido.
"Me yasa Mehran ya bukaci Jasrah bake ba."
Murmushi nayi sannan nace mata.
"Eh naje d'azun nan kuma gaskiya ni bana son na amshi ragamar shi sai ranar da aka daura min igiyar shi a kaina, su kuma suna da damar shiga gare shi. Tunda matar da zai aura ce ni kamata yayi nabi tsarin addini da na Ubangijin."
Takowa tayi gabana, sannan ta zauna kamar yadda na zauna..kafin tace min.
"Addinin ki da Ibadar ki yasani mishi kwadayin ki, idan ba wani abu me karfi ba,.nayi imani da Allah ba zaki juya mishi baya ba, domin kuwa babu kwaɗayin duniya a ranki don Allah ga Mehran nan ki tsaya mishi Insha Allah zaki yi nasara."
Murmushi nayi domin kuwa ban san me zance mata ba, amma kuma ina tunanin zan mata yadda ta bukace ni.
*Ana dara ga dare yayi....*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
36
Kasa gane kan MEHRAN nayi kowa yana jin dadin mu'amala dashi ban dani, tun Fudail yana ƙoƙarin gano yadda zai magance matsalar mu ya kuma sassanta mu, abin yaci tura. A cikin kwana uku kacal Mehran ya nunawa kowa baya tare dani, domin kuwa Zanyi kokarin tinkarar shi domin magana yana gani na zai mike ya nemi hanyar barin gurin. Ko kuma yana gani na zai tsira fushi da b'ata rai.
Bana jin dadin haka ko babu kome bai dace sabida Abrad ya gaya mishi magana ya nemi juya min baya, ranar da ya nime jasrah. Dan sai da tayi kwana uku a cikin turakar shi, kafin hudun ta fito, nan ne tana fitowa aka bata matsayin (Lady royal) tafi kwarkwarah ta kuma fi karfin a kirata da kuyanga, matsayi ne wanda yafi na kwarkwarah. Shi yasa tana fitowa ta fara gudanar da aikinta yadda ya dace. Abinda ta fara shine ta turo da wasikar lallai sai dai ina fitowa cikin su ina cin abincin.
Sannan ta zab'a min bayi mata guda biyu, sannan ta turo min su.
Ajiye takardan nayi sannan na kalle su, a tsanake kafin nace musu.
"Nagode! Sannan ku gaya mata bana bukatar kowa, ina da yan uwana na jikina bana bukatar masu taimakona. Batun cin abinci kuwa kice mata shima na gode ni mace ce kamar zinariya baka cin abinci a gaban kowa sai wanda ya ajiye ni da kuma yan uwana."
Haka suka fita abinsu, ban san me ya faru ba, sai gata tare da Mahlika. Suna zuwa basu yi wata wata ba, tasa aka rufe Izmah da Nimra da duka.
_Dole zasu biyo ki! Musamman yadda suka fahimci kina da matsala da Mehran, kiyi kokarin dauke Kanki kansu_ inji Fudail.
Dauke kai nayi haka suka musu lillis, kafin suka juyo kai. Tare da takowa har gabana, sauran matan suna bayan ta.
"Na saka doka kuma dole kibi yadda nake son domin nice budurwan masarautan. Idan zaki ga Mehran dole sai kin biyo ta hannuna."
Ban kalli inda suke ba, dan haka suka juya suka fita. Da sauri na isa gurin su Izmah zanyi magana tace min.
"Karki damu, ai Sultanah ta gaya mana. Dole zaki fuskanci wannan yanayin, ta bamu hakurin mu tayaki jurewa, Babban matsalar ki kama Mehran a hannunki, idan kika kama shi har abada ba zaki kuma fuskarta matsala ba."
Hawaye ne ya zubo min tare cewa.
"Dole na nimo Abrad, naji meye ya gayawa Mehran haka?" Kallona suka yi sannan suka ce.
"Babu Matsala a fitar ki? Don Allah Karki kuma yin abinda zai jefa ki cikin matsala."
"Babu kome zanje ba zan jima ba. Kayanki zaki bani Nimrah." Had'iye yawun tayi sannan ta mike ta cire, sakawa nayi sannan na fita a saɗaɗɗe. Ina samun na bar harami na sauke ajiyar zuciya. Ban tsaya ba, sai masaukin su. Ina zuwa na sami Nawwas yana tare da wasu dakarun. Ka rasawa nayi gurin shi. Sannan nayi mishi magana.
"Ikram!" Ya ambaci sunana da mamaki.
"Ina Abrad?"
"Yana cikin gidan!" Nufar hanyar cikin gidan nayi, ban tsaya ba sai da na dangana da cikin dakin da yake. Tun a bakin kofar shiga, na dauki takobin shi. Ina shiga na same shi da mace shi banyi wata wata ba, na saka mishi tsinin takobin a kirjin shi.
"Meye ka gaya mishi?"
"Dama nasan zaki zo aiki, abinda na gaya mishi kike son sani?"
"Maganar banza nake son ji?"
"Wannan kuma duk ke ta shafa, dan haka ina tayaki murna domin tarko na d'ana miki kuma yanzun haka Mehran yana bayanki! Zai zo ya same ki a cikin gidan nan."
Cikin fushi na yanke shi da kaifin takobin, cike da mamaki yake kallona idanun shi waje.
"Ko zaki kashe ni ba zan fasa gaya mishi magana ba, kuma zaki gani da idanun ki idan ya karaso!" Cikin mugun b'acin rai na kuma dukar shi da kasar takobin, abinda ya bashi damar riko hannuna, daidai lokacin da Mehran ya bude kofar dakin kenan.. shi kuma ya fisgoni na fada kanshi. Ya kuma yi amfani da karfin ya juyar dani akan idanun Mehran.
Juyawa yayi tare da barin kofar d'akin, ina mik'ewa na kai mishi duka a gaban shi dai da ya suma..sannan na fita na damu yana tafi ko dokin shi yaki dauka haka Fudail shima ya kasa hawa kan dokin Nawwas yana bin shi tare da mishi magana. Amma bai kula shi ba. Da sauri na sha gaban shi.
"Aamaan ka saurarre Ni, wallahi yadda kake tsammani ba haka bane."
Dariya ya saka wanda tunda nake dashi ban tab'a ganin shi yana dariya ba, sai murmushi. Sosai yake dariya har da dafe bishiya.
"Aamaan don Allah ka saurarre ni, wallahi nayi kuskuren zuwa amma kayi alakari da abinda ya baro ya kawo ni gurin shi."
Kura min ido yayi sannan yace min.
"Kiyi yadda kike so! Gashi nan nan da sati daya zaki koma inda ake bukatar ki."
"Mehran me yasa kake son tilasta zuciyarka ganin laifin da ba nawa ba?"
"Akan me ba Zanga laifin ballagaza karuwa makashiya, sha-sha-sha me kwanciya da mijin Kanwar mahaifiyarta? Akan me zan yiwa kaina adalci bayan ta sani kawo datti cikin masarautan da babu dad'i a cikin shi. Ke kazama ce. Wallahi da iya auren Numan kika yi zan yarda na zauna dake akan kwanciya da wancan kazamin, zaki iya tafiya. Amma karki yarda ki bar min kome da yafito daga hannunki."
Ban tab'a ganin abinda ya sani kuka har na kasa hawaye ba, sai kalaman Mehran, yayi min zafi da ciwo. Ina kallon shi ya bar ni a gurin kuka nake sosai. Kamar raina zai bar jikina Mehran ya min mugun zato. Haka suka tafi Nawwas kadai ya zauna a kusadani yayi ta bani hakurin. Karshe haka na mike tare da barin gurin.
***
Tunda na shiga cikin gidan ban kuma sha'awan fita ko kofar gidan ba, sai da naji labarin ana bikin maidawa Mehran kujeran shi, ban ko leko ba Kwarkwarorin shi suka yi ta bidiri, a lokacin Fazilatul nisa ta Fahimci akwai tashin hankalin a tsakanin mu, ta same shi ayi magana yaki bata lokacin shi sai uzirin da yayi ta kawo mata, ni kuma na kasa cewa kome.
Ranar da akayi bikin da yamma Baƙi daga Merocco da Askandariya suka zo. Kukan da nake sabida farin ciki ya kasa misaltawa.
Tunda suka shiga falon shi. Yake juye- juye, yana niman ta inda zata fito. Cikin shigar alfarma nayi sallama a katon falon shi. Suna zaune.
Da sauri ya mike tare da nufar inda nake yana faɗin.
"Salsabilah na." Rungume ni yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Kuka ne ya kwace min tare da kai hannuna na rungume shi..ina kuka sosai.
"Kiyi hakuri, gani nan nazo gare ki babu wanda zai kuma saka ki kuka kinji.". Jinjina mishi kai nayi tare da rike rigar shi. Kokarin danne tashin hankalin da yake ciki yake amma tabbas da ace mutanen gurin zasu Fahimci halin da yake ciki da su da kansu zasu bukaci Amir Rahil ya sake Ikram dan ji yake kamar kirjin shi zai fashe da tashin hankali.
Zafin da yake ji ya hana shi sakat, dan haka ya dauki ruwa ya shanye tass, sannan ya dauke kanshi daga gare su. Janye jikin nayi tare da kallon yan uwa da dangin mu, zama nayi a kusa da sultanah Amrah,. Wacce kamar ta daya da Ummyn mu, zama nayi ina me jin kuka yazo min tunda na kifa kaina a kafad'arta nake kuka, domin nayi imani da Allah idan na tafi ba zan kuma dawowa SAMAIND ba.
"Ya isa haka?" Ta faɗa min a sanyayye, Wazir din Merocco ne ya fara bayani a hankali tare da girmama juna, sannan ya kuma faɗa mana makasudin zuwan su.
"Alhamdulillahi mun gode Sultan Mehran, gashi zamu dauke maka ita, sannan muna me baka hakuri abisa abinda zamu gaya maka. Mun yiwa Ikram Miji Amir Rahil. Wanda shine Sarkin mu na gaba, dan haka zaka yi hakuri da yadda muka zo a makare."
A razane na d'ago kai na, ina kallon Rahil da yake ta zabga min murmushi. Sannan na maida kai na, ga Mehran wanda ko a jikin shi babu abinda ya dame shi.
Cikin dakewa ya kalli inda nake amma kuma zuciyar shi sai girgiza take, sannan ya fesar da iskar bakin shi kafin tace musu.
"Babu damuwa! Allah ya bata zaman lafiya..Insha Allah nima zan so zuwa bikin"
Kura mishi ido nayi hawaye na zuba daga cikin idanuna. Ina kuma kallon shi. Dani zai yi Yakana??? A kaina zai saukar da YAKANA?? Wato sabida rashin adalci ya gwammace ya hakura da aurena saboda na tab'a mu'amalantar wani da namiji, rike hannun na, Sultanah Amratu tayi tare da cewa.
"A duk lokacin da muka ga hawaye a kan idanun jama'ar muna da yakinin suna cutuwa ne da mulkin mu. Amma idan aka wayi gari munga wahale akan sarauniyar mu, tabbas muna da yakinin abu biyu ya sata kuka. Farin ciki da bakin ciki,. imma soyayya mara iyaka,.indai akwai daya cikin biyun da nayi magana akai toh wajibi ne Ikram tayi hakuri tare da YAKANA!"
Yadda take maganar babu wanda zai fahimci magana take sabida yadda take yi a sanyayye, share kwalla nayi sannan.. na sake mata murmushi, kafin muka nufi cikin gidan. Muka shiga hada kayana,. Ita kuma Sultanah Amrah ta nufi Shashin Sultanah Fazilatul nisa, anan suka shiga hira, mazan kuma aka kai su masaukin su.
Banda Rahil da yace babu inda zai je, ina zaune ya turo naje. Tunda na isa gurin a bakin wani tafkin da agwagi suke wanka, muna zauna dashi.
"Tun bayan tafiyar ki nayi ta jinya."
"Toh Sannun;"
Rau-rau yayi da fuska, kamar zai fasa ihu.
"Na zata zaki tambaye ni akan me nayi jinyar?"
"Toh kayi hakuri, ?gaya min akan me kayi jinyar."
Dariya yayi sannan yace min.
"Akan sonki mana" kallon shi nayi domin banyi mamaki ba, amma kuma ni bana jin wannan yanayin a tare dashi, ji nayi kamar ana kallon mu na juya. A hankali, sake labulen tagar shi yayi. Nima a sanyayye nake kallon ruwan gabana. Ina me jin zafi da ciwon abinda ya faru.
---
Kallon yake tun da suka fito yake kallon su, bai tab'a ganin mutanen da suka dace da juna kamar Rahil da Ikram, a hankali ya sauke ajiyar zuciya bayan ta juyo tana kallon shi, sake labulen yayi.sannan ya kalli Fudail ya ya jima da shigowa.
"Me yasa kayi shiru ba tare da ka gaya musu yadda kake kaunar ta ba? Me yasa ka xabi'a YAKANA akan kaunar da kake mata? Wannan babu adalci.".
"Ya isa haka. Karka manta na ce maka na rabu da ita, na rabu da ita har karshen rayuwata, dan haka karka kuma kawo min batun wata Ikram." Ya dakawa Fudail tsawa, ka rabu da ita kake leken ta? Ka rabu da ita ka gaza rike hawayen Soyayya! Dubi Cikin idanunka zaka Fahimci itace muradinka don Allah karka kashe abinda ba zaka iya raya shi ba. Zaka iya kashe so amma raya shi nada matukar wahala, don Allah karka rabu da ita, ka koma ka gaya musu ita ce zab'inka zasu Fahimce ka."
Kamar ya daki Fudail yake ta huci, shi dai bai fasa ba kuma bai daina gaya mishi gaskiya ba, har dai da ya kore shi daga dakin sannan yace mishi.
"Kaje ka aure ta, na yafe maka ita."
Dariya Fudail yayi sannan yace mishi.
"Tun duniya na kwance naso aurenta Allah bai nufa ba dai yanzun da nasan tana cikin zuciyar Mehran. Kawai kayi wani abu a gyarota."
"Ba zanyi ba! Ba zan iya ba. Ba zan tab'a yarda na zubda kimata ba dan haka ka barta ta tafi. Ni dai na yafe Ikram har karshen rayuwata.
Ta zalunci rayuwa ta, ta lalata min rayuwa,tayi nasarar jefani ....
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
37
"Wani irin rayuwa ta lalata maka? Wannan ni banga wani laifin da kake danganta da shi ba, sabida ai a baiwa tazo masarautan nan, kai kana da tabbacin." Kasa fadar abinda yake son ya faɗa yayi tare da kallon Mehran dan yasan maganar ya yi mishi girma.
"Ba budurcin ta nakewa hidima ba, itace nakewa hidima. Idan har zan iya hakura da shugabanci na, domin laifinta an kansa bata da abinda zan iya samun a gare ta fansan abinda na rasa, kawai na hakura da ita ne." Ya faɗa a sanyayye. Sannan ya juya, yabar gurin baki daya.
~~~
"Sultanah ga koshi ga kwanan yunwa, domin kuwa nasan Ikram na barin SAMAIND Za'a daurawa Sultan Mehran Jasrah abinda ake gudu zai faru." Inji Narjis.
Cikin dakewa tare da ɓoye tashin hankalin ta, ta sake murmushi sannan tace mata.
"Allah yana tare da Mehran, shi yasa koda an ɓullo mishi ta wani gurin ,zai kauce ta wani gurin. Ita kuma Jasrah karki damu da ita." Ta faɗi haka tare da ɗauke kanta.
Wato kuka take son yi, amma bata son Narjis da Shairah su karaya,. Balle shima Uban garin yaji labarin. Kasa dannewa tayi ta mike zuwa ban daki ta zauna tare da fashewa da kuka. Kuka irin me tab'a zuciya da ruhi, kuka take tare da jin ina wannan ranar bata zo ba,.me yasa Ƙaddarar su take da zafi ne haka? Ga baki daya bata da inda zata kama tace gashi shine mafita a gare ta.
Tana ji tana gani zata kuma rasa Ikram, a hankali ta wanke fuskarta tare da fitowa d'akinta, ta same su. Suma kuka suke, cikin juriya ta zauna tana kallon su.
"Idan Allah ya baka lafiya sai kai ta jin dadi da farin ciki, idan kuma ya baka Arziki baka da kwanciyar hankali, idan ya baka mulki kai da farin ciki har abada.
Gashi ya bashi kome amma ya hana shi farin cikin rayuwar shi, soyayyar da yake riritawa itama ta subuce mishi. Mulkin da yake kai ya rasa, dukiyar da yake da ita bata amfane shi da kome ba, sai tarin tashin hankalin da damuwa. Ita da nake ganin itace kwarin gwiwar shi ashe ba haka bane.." ta karshe maganar cikin rawan murya alamar zata yi kuka. Duk wanda yake dakin sai da ya zubda kwalla. Dan haka suka zube gwiwar su a kasa suna kuka.
Murmushin tausayin MEHRAN tayi sannan ta juya tare da cewa.
"Ku kira min Ikram"
Da sauri Narjis ta fita.
...“Mace idan ta isa mace ta zauna a daularta ba sai ta biyo namiji ba, amma ayi mace mara daraja da kima, don Allah ku hada kaya ku koma can."
Kallon Yesmin nayi sannan na sake murmushi kafin nace mata.
"Zan bar muku Aamaan Abdus Samad Mehran na biyu, zan tafi na barshi kamar yadda nazo na same shi." Dariya ne ya kwace min sannan na cigaba da cewa.
"Idan na tafi kunyi ban kwana da farin ciki, kun daina ganin dariyar shi da murmushin sa. Kuma ai dama ba ma'abocin yi bane dan haka sai kinyi danasanin mara amfani."
Shigowar Narjis ya sani kallonta, kafin na juya zan tafi tace min.
"Amirah Ikram!" Juyawa nayi tare da amsa mata.
"Sultanah tana mahaifiyar Sultan Aamaan Mehran, tana son ganawa dake. Sirikae mafi soyuwa a zuciyar Sultanah Fazilatul nisa"
.kallon Jasrah nayi sannan na juya kai na, kafin nace musu.
"Mulki ya haife ni, amma yadda nake jin shi ko kuda aka haifa cikin masarauta ba zaku nuna min mulki ba. Uwar Mehran! Mahaifiyar Aamaan Mehran take don ganawa dani. Daga mahaifiyar shi sai ni kaf daular nan babu wanda ya isa