Header Ads
Showing 141001 words to 144000 words out of 274096 words

Chapter 48 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1399

Ads at the middle of Article

yana ajiye kofin ina fesa mishi ruwan a fuska, saka hannun shi yayi tare da cire abinda nake rufe sauran fuskana.


Yana murmushin mugunta, tare da kallon fuskana, ajiyar zuciya yayi ta saukewa, bai kuma min magana ba, har sai da yaga na fara ƙoƙarin mik'ewa sannan, yace min.
"Toh yanzun meye laifina? Da ake kawo min wannan harin?"


Kasa magana nayi domin dai yada yake natsuwa jikina ya soma razana ni, a hankali yake balle rigar shi. Kallona yake har cikin idanuna, had'iye yawu nayi tare da cewa.
"Karka kuskura kace zaka tab'a ni, karka yarda kace zaka min abinda ban.."
Hannun shi naji akan cinyata, duka na kaiwa hannun ya janye tare da ture ni, yana murmushi yace.
"Ki koma ki shirya Mehran kainuwa ne dashen Allah, babu wanda ya dasani sai Allah, Ikram indai har zan baki damar ki huce haushinki ai kin san ba karamin dalili bane, dan haka bana son na kuma ganinki, a cikin Samaind. Idan kuma na kuma ganin ki, zan ajiye kome zan baki kyautar da bai riske ki ba "


"Kai waye da zaka ce min na bar Samaind? Ai nazo Samaind kenan sai na kashe ka zan bar kasar nan idan yaso kun kama ni karku min ta dad'i....."


*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


27


"Mhh!" Yayi murmushi me sauti sannan ya kuma ware idanun shi akai na, kafin yace min.
"Har yanzun ke baiwa tace, dan haka na baki damar barin SAMAIND"
"Ni kuma har yanzun niman ranka nake na baka damar kayi rayuwa kafin na dawo gare ka!"


Amadadin naga fushi ko fusata haɗe da b'acin rai, sai naga kamar babu abinda ya dame shi.


Hannun shi ya kai wuyana, tare da kallon yadda nake kokarin kwace kaina. Matse ni yayi da bango, yana kallon cikin idanuna kurawa juna ido muka yi, ya sake murmushin da zaka Fahimci farin ciki ne zalla a ranshi, a hankali ya cigaba da kallon cikin idanuna. Ban san lokacin da kasala tare da kaifin idanun shi suka saukar min ba, tsintar kai na nayi da lumshe idanuna, na kifa kai na a kirjin shi, ina me rintsa idanuna kamar zan fashe da kuka.


Hannun shi ya kai haɓɓa na, tare da d'ago kai na, had'a fuskar mu yayi yana sauke ajiyar zuciya.
"Bana son rashin da'a."
"Idan nayi maka zaka yanka ni ne?"
Janyewa yayi daga jikina, tare da cewa.
"Ina lafiya, bazan iya aikin masu hankali biyu ba," da gaske Mehran Magana ya gaya min, dan haka na juyar da kaina, tare da kokarin kwace kaina.


"Me yasa kike kokarin gudu?"yadda yayi maganar muryan shi can ƙasar makoshi sai da ya kara jefani cikin wani irin kasala, domin yayi maganar ne tare da fesar da iskar bakin shi, a wuyana.
Kokarin kwace kai na nake , amma na kasa domin kuwa matse ni yayi sosai, numfashina yana fita sama sama. Shafa fuska na yayi tare da kallon fuskana sa nake kokarin b'oyewa a kirjin shi.domin wasa gaske Mehran sai da ya kashe min jiki murus. Da sauri na d'ago kai nayi cikin wani irin rawan jiki.
"Hmmm! A da kina amfani da miski, me yasa baki amfani da shi yanzun?" Yayi maganar kama wanda yasha abin maye.
Hannun shi ya kai fuskana tare da tallabo fuskar. Hada bakin mu yayi tare da lumshe kaifaffun idanun shi. Kasa motsi nayi domin ji nake numfashina yana niman barin jikina, hankalina yayi mugun tashi. Idanuna sun gaza fidda kwalla, rike rigar shi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Tunda Uwata ta haife ni ban tab'a sanin akwai irin wannan abun ba.


Sannan banda Abrad ban tab'a ganin wanda yayi min irin wannan abun ba, cikin hikima da dabara, sai da ya min masauki a gadon shi sannan ya shiga sumbatar ko ina a jikina, tare da rawan jiki, kamar zan gudu daga gare shi, goga kanshi yake daga wuyana zuwa kirjina, ban san lokacin da na birkice mishi ba, kuka ne ya kwace min, tare da rike hannun shi.
"S...." Hada bakin mu yayi, babu duka babu zagi sai da naji kamar bakina da harshe na, rike hannun shi nayi. Ya bude idanun shi fess a kaina, tare da sumbatar wuyana.
"Karki kuma yunkurin zaki."
"Ka cuce ni! Allah sai ya saka min."
"Ai haba? Toh bari mu karasa bidirin a gadon."
Zaro idanu nayi tare da fashewa da kuka, ya kuma cigaba da jefani cikin tashin hankali, dakyar ya kyale ni, lokacin aka kiran sallah farko, har ban daki ya kai ni, wai zai min wanka bayan na san ba zan iya ganin kato a tube ba.


Sai da ma bari ya shiga kwarin wankar na juyo tare da ɗaukar kayana, tare da barin gidan baki daya. Murmushi yayi domin ko babu kome ya cusa mata tsoro ko ba dukkan ba, wanka yayi wanda rabon shi da yayi hakan tun kafin ya kwanta jinya, ga wani irin iska da yake shigan shi ta ko ina, kaya ya saka tare da gabatar da sallar nafilla, sannan ya fita zuwa masallacin, suka yi sallah. Anan ya koma gefe suka shiga karatun, dan gari ya waye. Duk wanda ya san Mehran sai ya gane yana cikin farin ciki da nutsuwa.


Har ya gama karatun, sannan ya nufi gida, koda ya shiga ya sami Sultana tana ta famar nuna yadda za a jera abincin, fuskar shi a sake ya gaishe ta, sannan ya juya ya nufi sama.
"Yau ba zaka karya bane?"


"Anne kina kirana ne" ya tambaye ta cikin fara'a, yayinda Narjis take kallon shi sosai, nuna mushi tabirin tayi da ido, da sauri ya dauko tare da zama, sai dai duk abinda yake idanun su yana kanshi domin ya kasa boye farin cikin shi. Da yadda yake ciki.


Duk wanda ya kalle shi dai ya fahimci, yana cikin farin ciki ainun, duk da ba hira yake ba, amma baya minti biyar bai tsaya ya kalli abincin sannan ya kuma sake murmushi, gabaki daya ranar sun kasa fahimtar kome akan shi babu fushin nan da dakewa, babu dogon miskilancin, sai ma wani irin yanayi na ban mamaki, wanda babu wanda ya sanshi da ita, magana akan aure tare da bawa Fudail labarin ai tazo, kuma sun kusan raba dare suna tare, da farko Fudail bai yarda ba, sai da ya hade rai sannan ya kuma dawowa ya nuna amincewar shi.


~~~
Da bakin ciki da kuka tare da nufar gidan, a hankali naji ina son ganin Uwaisul Qarni, har na isa gida, na sami Izma zaune. Zama nayi tare da dauke kai na, dan gani nake kamar zasu karanci Iskancin da wancan sikagon yayi dani, dan haka na shiga ban daki nayi wanka tare da rage kazamtar jikina,ina fitowa na gabatar da sallah nafilla da sallah asuba, sannan na kwanta wani barci me cike da gajiya suka dauke ni, sai dai ban yi nisa ba, na farka sakamakon ganin Uwaisul Qarni.


"Bilqisul Ikram! Ba zaki ajiye kayan yakinki da Mehran ba? Ko kin fi son kullum kina ganin shi cikin damuwa ne?"
"Kashe min miji yayi fa?kuma na yafe mishi?"


Kura mata ido yayi, da zata ga halin da rayuwarta yake ba zata so d'aga hankalin ta akan Mehran ba, sam bata cikin nutsuwa baki daya, matsalar jinin da ta zubda ya fara bibiyarta, bai ce mata kome ba, sai Addu'o'in da ta tofa mata a cikin ruwan sha, ya mika mata.
"Karki sake yunkurin cutar dashi! Idan kika Kuskura kika d'aga hannu domin cutar da shi,, ina me baki tausayin abinda zai biyo bayan, domin kina gab da zama mara amfani."
Murmushi nayi tare da bude baki zan ce mishi. Wani abu kawai ya kalle ni tare da shafa fuskana,. Komawa nayi na kwanta, ban farka ba sai kusan azhar, nayi wanka da alola, nayi sallah azhar.


Ina idarwa na juya tare da kallon Izmah da Nimra, suna musu.
"Yawwa Ikram, nace ba kin hadu da sarakunan larabawa babu iyaka wani sarki ne yafi burge ki da mulkin shi? Ni dai nace ina ga Sultan Mehran yafi sauran,"


"Ni kuma nace mata na tab'a ganin Amir Rahil, sau daya a wani tafiyar mu aikin hajji."


"Duk cikin su babu wanda ya kai Mehran d'an Abdus Samad kyau da jarumta, sai dai mugu ne na gaban kwantaccen" yadda nake gaya musu halin Mehran da haduwar shi. Yasa su sake baki tare da cewa.
"Amma taya kika iya rike dabi'ar shi haka? Sannan kuma karki manta da cewa makiyinki ne fa?"
Wayo kunya ne ya kama ni, wato jiya inda Mehran ya kai ni ya sani kasa Fahimtar kome sai halin shi da nagartan shi. Na kasa fadar laifin shi, dan haka na juya na kwanta ina cewa.


"Ba shi nake magana akan shi ba, Ni akan Amir Rahil nake magana," na fada.
"Wai daga baya kenan, yarinya kin amayar da abinda yake ranki."


"Bana son shashancin, ki fita bana son ganinku." Dariya suka saka min, sannan suka fita ni kuma na shiga jin babu dadi meye zanyi da mugu, haka na wuni cikin daki da dacin rai.


.....Bayan kwana biyu.
Ga baki daya Sultan Mehran ya kasa samun nutsuwa, burin shi dai ya fito gari ya ga Ikram, dan haka ya shirya cikin shigar badda kama, shida Fudail suka fito garin.


Haka suka yi ta bin gidajen baki da suke wajen gari, har Allah ya kawo shi gidan da Ikram take, suna can wani gidan da babu alamar akwai mutane a gidan, daga bakin kofar shiga gidan ya hangota zaune tayi tagumi. A hankali ya shiga cikin gidan bata sani ba. Dai dai fitowar Izmah.


"Kana niman wani ne?" Ta tambaye shi. Cire rigar jikin shi yayi da badda kamar da yayi ya kalle ta, sannan ya juya ga Ikram da bata san dashi ba ma.
"Yallabai kai ne Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran?" Ta faɗa bakinta da muryan ta yana rawa, kamar zata fashe da kuka,karamin murmushi yayi mata sannan ya kalli Ikram da bata san suna yi ba.
"Barka da zuwa Yallabai ka shigo gidan mana"


"Hmm! Nan ma ya isa"
"Ke! Tunanin me kike? Ga Sultan nan" kamar wacce take mafarki hana na farka ina kallon su, shigowa Fudail yayi ya zuba min ido. Kallon shi nayi tare da sake mishi murmushin jin dadin ganin shi.
"Yan uwan Fudail"
"Ikram kece a Samaind?"
Yayi kamar bai san abinda ya faru ba, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Gani nan Fudail" nan hira ya kwace a bakin su, tare da Mantawa da Mehran a gurin, wani irin hade fuska Mehran yayi tare da zabgawa Fudail harara,ya juya ya wabi b'ata rai. Yana kallon gidan, tare da cewa.
"Hmm!" Ya faɗa tare da fidda wani irin nishi, da sauri Fudail ya koma waje. Ita kuma makira tace mishi.
"A'a ka shigo gidan kaci abinci da ruwa!"
"Kai basamuden mutum! Jeka abunka bari muzo tare domin Sultan yana son hutawa a cikin gidan."
Izmah taja hannun shi suka fito daga cikin gidan, suka barsu a tsaye. Takowa yayi gabanta, tare da jan kumatunta yana fadin.
"Karki kuma mun abinda kika yi"
"Toh Ubana!" Buge min baƙi yayi, tare da kallon cikin idanuna, kasa nayi da kaina, tare da wasa da yatsuna,
*Duk ranar da na sami dama sai na aikaka garin da ba a dawowa*
D'ago kai na yayi tare da kallon cikin idanuna, sannan ya hura min iskar bakin shi me dauke da kanshi y'ay'an itacce.


*Me yasa ba zaki Fahimci abinda nake tare da shi ba? Me yasa ba zaki gane girman ki a zuciyata ba? Me yasa kike wahalar da zuciyar da bata dauke da sharri sai Alkhairi?*


Janye hannuna nayi daga gare shi sannan na dauke kaina zan fita, yayi maza ya riko hannuna, ya juyar dani, bayana yana kwance a kirjin shi, hannun shi ya sarkafe da hannuna ya manna akan cikina, tare da riko daya hannun ya saka akan cikina ya zarge ni a kirjin shi. Kanshi a bisa wuyana, yana sauke ajiyar zuciya akai akai.
_Na tsane ka! Bana son ganinka? Akan idanuna kace bani da daraja! Sannan ka kashe min Mijina! Mehran nice ajalinka, mutuwarka a tafin hannuna yake_


Na karshe da shashekar kuka, tare da kokarin fita a jikin shi.
"Ki gaya min meye laifina?"


Cikin fushi na kwace kaina, tare da juyawa ina kallon shi.
"Karka kuma takowa inda nake! Me yasa ba zaka gane bana son ganinka a rayuwata ba? Kai abin so ne? Waye ya gaya maka zan tab'a kaunar ka? Toh ko maza sun kare gwara na koma ga Allah babu mijin aure ka fita a rayuwata nace!!!"
Na daka mishi tsawa, ina kuka tare da zuɓewa akan gwiwata, ina kuka.
Shiru yayi sannan ya durkusa a gabana, ya riko hannuna..sannan ya kalle ni cikin damuwa kafin yace min.
"Gashi kiyi yadda kike so dani! Zanyi alfahari idan na mutu a hannun ki, zanyi farin ciki idan mutuwa ta ya zame miki karshen matsalarki! Amma ban miki alƙawarin koda ina raye zan daina bibiyarki ba, wannan shine alkawari na dake"


Kura Mishi ido nayi, na rasa gane wani irin mutum ne shi da bai damu da kanshi ba, sai dai ya kuntatta maka, banda kuntattawa me yasa zai kore Fudail ya kuma ce min na kashe shi salon yaja min magana..


*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


28
Kasa jure idanun shi nayi a cikin nawa, na kai mishi duka a kirjin shi, muryana yana rawa.
"Me yasa?"
Murmushi yayi sannan yace kai bakin shi saman kunne na, ya d'an kama da hakorin shi, rike rigar shi nayi tare da sauke ajiyar zuciya. Sake lasar kasan kunnen yayi na k'amk'ame shi tare da jin wani irin abu yana yawo a jikina kamar an watsa min tsutsa, kark'ada min harshen shi yayi a cikin kunne na, ji nayi kamar zan zube ƙasa, ya kuma rike ni sosai,
Mehran Mugu ne, ba fada dashi bane matsalar.


Kwana mita, domin a iya haka ya labtar da gangan jikina, ya kuma sani kuka babu fada babu zagi, hancin shi ya shiga gogawa wuyana, yana magana kasar makoshinsa.
"Ba fada zanyi dake ba, kuma ba zan hana ki faɗa dani ba, sai dai ki sani a shirye nake na bawa zuciyarki horon yaki akai na, a shirye nake nayi ta sanya ki kuka akan abinda ba zaki iya bujirewa ba. Tsaf na shirya yaki da zuciyarki har sai ta nutsu akan Abu daya, sannan zan kyale ki. Mara jin magana kawai." Ya fadi haka tare da hura min iskar bakin shi, wani irin kuka ne ya kwace min domin kafaffuna rawa suke, a hankali ya juya ni tare da saka harshen shi akan fuskana,


Yana lashe hawayen da suke zuba, tare da cewa.
"Ni zan saka ki kuka! Kuma ni zan lashe kukan nawa, duk abinda zai fito daga gare ki nawa ne!"
"Kyale ni, wallahi babu abinda zai zama naka ,Ni ba kara bace nice ajalin ka" na fada ina kuka.
"Bakin ki yana yawan magana, kuma ina tsoron maganar karta zame miki matsala, harshen ki kamaninki, don Allah ki rage yawan fadar haka. Domin ke baiwa tace."


Ture hannun shi nayi tare da kallon shi, kuka nake sosai tare da niman guri na zauna, murmushi yake, cikin jin Dadi. Allah ya gani yana son mace me jarumta, yana kuma son ganin mace tana kuka, cikin damuwa kara mata kyau yake balle Ikram da suka shekara uku basu hadu ba, zama yayi a kusa da ita, tare da matse ta a a jikin itaccen da aka yi gwafa da gidan.


Hannun shi ya saka tare da riko hannun na, yana kallon yadda nake kuka. Tare da kallon yadda nake shashekar kuka. Ita take kukan amma jin hawayen ta yake kamar narkakken dalma ake diga mishi akan zuciyar shi.


Kai hannu na ya kai kan kirjin shi, yana kallon yadda na sunkuyar da kaina, tare da kokarin zare hannun daga kirjin shi. Matso dani yayi jikin shi. Tare da d'ago kai na, yana goge min kwallar fuskana.
"Me kike so?"


Kallon shi nayi tare da kasa cewa kome. Bana iya kallon cikin idanun shi na tsawon mintina, lumshe idanun nayi kwalla suka kuma zubowa.
"Qurratulain!" Ya ambaci sunan daga kasar makoshinsa, yana ji kamar za a kwace mishi ita, gani yake kamar duk wani dakika na duniya kara nesanta shi ake da ita.
"Me kike bukata?"
"So nake na kashe ka" na bashi amsa ina kallon cikin idanun shi. Murmushi me zubin dariya yake yana kallo na, yana shafa fuska ta, tare da kai kanshi saman hancina.
"Har yanzun baki gaya min me kike bukata ba?"
"Na tsane ka"
"Anya kuwa?"
"Bana son ganinka"
"Da gaske?"


Kokarin ture fuskar shi nayi tare da sake mishi wata irin siririn kuka..
"Yau nayi nasarar saka Jarumar mata kuka ko?"
Mikewa yayi tare da kallon yadda take kuka, murmushi yayi sannan yace mata.
"Ban miki alqawarin zan rabu dake ba, domin zanta bibiyar ƙi" daga haka ya juya barni a gurin ina kuka, wanda idan da zaka tambaye ni me yayi min wallahi ban sani ba, kawai dai ina tare dashi kuma ban san lokacin da nake kuka ba. Hannun shi suna zuba cikin rigar shi. Fidda su yayi tare da shafa fuskar shi zuwa kan shi yana lashe bakin shi, sannan ya juya bai kuma magana ba, ya bar gidan. Sai da ya fita na sami kaina da yin shiru,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads