Showing 240001 words to 243000 words out of 274096 words
Chapter 81 - DAULA BIYU Complet Document .txt
zan hana ka ba."
Rike hannuna yayi cikin na shi sannan ya matse a hankali, yana murza yatsuna hannun.
"Ikram ni na dace dake, karki manta zan zauna dake a duk yadda kike, Ikram ina tsananin kaunar ki"
Rike hannun shi nayi cikin nawa tare da kura mishi ido, ina hango iyakar gaskiyar shi. Dauke kai nayi tare da cewa.
" Nasan kana sona, amma ya aka ji idan ka taso daga sahara me matsanancin zafin rana, sannan kuma kana murnan zaka tsallake kana hango koramar ruwa, kana isa ka sami ruwan an hanaka sha. Ya zaka ji? Toh haka ka shiga tsakanin mu."
Mikewa nayi zan shiga ban daki yace min.
"Zan iya hakuri dake har zuwa lokacin da zaki soni amma Tabbas zan aure ki. Kuma zan zauna dake."
Cak na tsaya sannan na juya ina kallon shi, kafin nace mishi.
"Zaka zauna da ni Tabbas zaka ƙunshi bakin ciki, domin zan zame maka kamar ramin maciji ne, kowani motsi kayi da dafina zaka motsa, bana son mu kai ga haka shi yasa nake gaya maka illar haka." Na shige abuna.
Shiru yayi tare da jin babu dadi a ran shi, amma kuma babu yadda ya iya, dole haka ya saka kai ya fice daga d'akin. Tunda na shiga ban daki na fashe da kuka, tare da zama a gurin ina kuka, Tabbas na san yana sona, amma haka bayana nufin zan iya rayuwa da shi bane, Mehran shine zab'i na, Rahil dan uwana ne shi. Ban shirya zama dashi a matsayin abokin rayuwata ba.
A hankali na fito daga ban dakin ina sauke ajiyar zuciya, tare da zuɓewa a jikin gadon dakin ina jin kwalla na zuba min.
Mehran shine zab'i na, shi din farin cikina ne..idan ana iya musayar so ba zan tab'a musayar Soyayyar shi ba, ina mugun son shi, a lokacin da ba zai min amfani ba. Lokacin ya gama kure mana, dan haka na had'iye kukan tare da kifa kai na a jikin gadon, ina jin wani irin kewar shi.
***
Takowa yayi har gaban gawar da masunta suka dauko shi daga ruwa. Babu abinda ya sami gawar, kamar bai jima da mutuwa ba, sai hasken fatar da yayi irin fari fauu din nan. Kallon gawan Nawwas Fudail yayi sannan yaja mayafi ya rufe kafin yace.
"Wannan gawar shugaban dakarun daular Umayyad ne, dan haka ba zamu binne shi ba, sai mun san ta yadda aka yi gawar ta wanzu a cikin yankin mu."
"Toh shugaba!" Suka amsa mishi.
"Kwanakin Baya mun ga lokacin da ya shiga wata jirgi, tare da a yarin daga nan ne na shiga jirgi na, na haura saman Teku, daga nesa na hango lokacin da ake jefa wani a cikin ruwan amma ban sani ba ko shine ba."
Gyada kai Fudail yayi lokacin jin da yaji bayanin wani mutum da yaga lokacin da Abrad yasa a wurga gawan Nawwas a ruwa. Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Toh babu kome zamu bincika." Gaba yayi sannan dakarun suka ɗauki gawar a makara, suka nufi cikin garin SAMAIND da shi.
.....
Kallon Mehran Azizatul Nissah tayi tare da toshe bakin ta, tana me fashewa da kuka, da gudu ta nufi hanyar da zai sadata waje,
Bin bayanta yayi sabida karta tab'a lafiyar cikin jikinta, zuɓewa tayi a gaban gawar tana kuka da ihu, sabida yadda ta ga gawar shi bata kawo hakan ba a ranta, dakyar Mehran ya d'aga ta, ya koma da ita, sai da aka gama bai bincike sosai, kafin aka nad'e gawar aka mishi jana'iza.
"Zan tafi gida, ina ganin babu wanda yasan da labarin mutuwar shi don Allah karka hanani." Shafa kanta yayi tare da maida gashin ta baya, yana me jin tausayinta a ranta, sannan yace mata.
"Ba yanzun ba sai kin haihu." Wani irin kuka ne ya kwace mata, bata san lokacin da ta kuma sake kukan ba, ta rike hannun shi tana faɗin.
"Toh taya zasu sami labarin mutuwar shi."
"Zan aika da sako a gaya musu. Insha Allah" sake rungume ta yayi, ta kuma narke Mishi kamar wacce take cikin tashin hankali na gaske. Haka yayi ta rarrashinta, domin kuwa baki daya ta birkice mishi. Kwana biyu tsakani idan ka ganta zaka Dauka jinya tayi nan kuwa dauke hankalin shi tayi da makirci kamar mutuwar ya dake ta. Duk da kuwa ta kadu da mutuwar amma ba wani jijjiga ta ba, sabida cikin jikinta kar yace dai kwace abin shi, ko wani dalili da zai fito ya fadi gaskiyan cikin nashi ne, Tabbas akwai matsala domin haka zai iya janyo yakin da za a rasa rayukan al'umma, sannan itama bata tsira ba, kisar wulakancin za a mata a gaban jama'a. Dan haka mutuwar Nawwas yazo mata a gaɓɓar da ya dace, dan haka bata ga abinda zai wargaza mata lissafin ta ba. Shima Mehran duk ya damu, domin a tunanin shi da gaske take, dan haka duk ya shiga damuwa duk da yana cikin damuwa, amma sai ya tsinci kanshi da tausaya mata sosai, har yakan zauna yana b'ata lokacin shi akan ta, ita kuma haka sai ta narke tayi ta nuna alamar bata ita fa tana kewar gida, dan haka ya taimaka ya kaita ko da yayya ne yan uwanta sun san yadda take ji gashi babu wanda ya san da mutuwar sa ita.
Dan kar ya samu damar da zai nufi gurin Sultanah Fazilatul, yasa ta baki daya ta kawo mishi yanayin da take ciki, yana fita sallah zata ware, ko kuma tayi ta kuka, asalima ta hana shi ko zuwa fada, domin yana fita zata saka rigima haka zai dawo matan da suke dakon shi kuwa haka suke jin babu dadi ga zafin kishinta da suke ji.
Wata idan ka nutsu zaka Fahimci burin Azizatul Nissah, bukata take ta dauke hankalin Mehran baki daya, haka da sauran suka gani yasa su hade kan su, suka tsayar da shawara. Akan su shiga jikin Sultanah Fazilatul nisa, sai aka yi rashin Sa'a an sami munafukai a cikin su. Wato Sakeenatu binti Abu Waqqas, ta rubuta wasika ta bawa baiwarta mesuna Munirah ta kaiwa Azizatul Nissah.
Ita kuma da ta tashi hada rigima sai ta sauya tsarin labarin tare da kwafe wani ta saka wani abu na daban. Sannan ta bawa Baiwarta me Suna Unaizah takai Fada. Inda Sultan Mehran yaƙe, tare da shaidawa duniya cewa tana dauke da juna biyun shi.
Shiru Fadar yayi sannan magatakardan ya cigaba da karanta wasikar kamar haƙa.
_Sultan Mehran a halin da nake ciki ina dab da rasa rayuwata, ba dan kome ba sai yadda Fazilatul nisa! Tasa Matan da suke Hareem su dake ni! Sultan MEHRAN ka kawo min a gaji domin zasu kashe ni da goyan bayan Matar da kake mata kallon Mahaifiyarka, tare da amintacciyar baiwar Ikram_
Wani irin lumshe idanun shi yayi tabbas, yana bukatar ya dakatar da Sultanah Fazilatul nisa, amma yana jin wani irin girma da darajar ta a ran shi, shi yasa yake kasa murza mata kome, dan haka ya mike ba tare da yayi musu magana ba, ya nufi cikin gidan.
Kallon juna suka yi manyan Fadar.
"Kanwar Abrad ce ta samu damar daukar cikin shi? Lallai akwai abinda yake shirin Faruwa, idan har muka dake wata daga wata daular ta haihu da Mehran har abada mulki ya fita hannun Daular Abbasiyyah! A barar da cikin"
Dariya Sultanah Hoyam tayi sannan tace musu.
"Cikin ba zai tab'a zuba ba! Sabida shi kanshi cikin zan bukaci na tsaya kan shi kamar yadda na tsaya akan uban dab haka babu batun zubda jinin Mehran"
"Amma!"
"Na yanke kuma ya yanku, babu wanda ya isa ya sauya min ra'ayina, ko kuma dole kubi abinda nace." Ta fadi haka tana mik'ewa daga kujeran ta.
Bin bayanta suka yi da ido, Tabbas sun dibo ruwan dafa kansu dan haka su san abinyi domin kuwa har da hannun yaransu a cikin abinda aka turo, wani irin hukunci Mehran zai dauka akan Yaran su?
Kuma me yasa ya ajiye FAZILATUL a gidan sarautar? Duk basu da amsar tambayoyinsu dole shi ne zai basu.
"Toh ya zamu yi idan da hannun Yaran mu a ciki!" Inji Mir Umdatuddawla,
"Sai mu maida laifin kan Fazilatul nisa, ai tafi su hankali, kuma sunanta ya fara fitowa kan nasu, dan haka karka damu sune zasu kwaci kan su."
Daga haka suka watse daga fadan.
----
Lokacin da Mehran ya shiga cikin gidan, Ya samu Sultanah Fazilatul nisa tana kokarin shiga tsakanin su Jasrah da Azizatul Nissah, sakamakon fadar da suke yi, wanda dama can tana cike da ita akan zaneta da ta saka aka yi, dan haka ta same ta da bugu, a bangaren Azizatul Nissah itama abinda take bukata kenan Mehran yazo ya same su a wannan yanayin, sabida ta sami damar sharrin da ta kulla musu.
Tana ganin shi ta yanki jiki ta fadi tare da rike cikin jikinta.
"Wayyo Allah na, wayyo cikina, wayyo Mehran"
Ga baki daya ta birkice mishi tare da murkusussu, kallon Sultanah Fazilatul nisa yayi, cikin matsanancin b'acin rai.
"Anneh! Sad'akata ce kika sa Jasrah ta sake ta da cikina?"
Zaro idanu tayi waje tana faɗin.
"A'a Aamaan akan me zan saka su dake ta? Me tayi min da zafi haka da zan tab'a lafiyar ta."
"Ya isa! Ki tattara ki bar cikin fadar nan ko kuma."
"Sultan MEHRAN!" Fudail ya kira sunan shi da karfi.
"Karka hana shi, bar shi ya kore ni barshi ya tura ni waje saboda Azizatul Nissah."
Sanyayye ta juya zata bar falon, amma ba haka Azizatul Nissah taso ba, taso idan ya kore ta yasa a kaita gidan horo, b'ata fuska tayi sannan tace.
"A haka zaka kyaleta, ba ka hukunta ta ba, bayan so take a kashe ni itama Jasrah hukuncin. Da ya dace da ita kenan, sannan a nuna musu matsayina."
Kallonta yayi tare da kai hannun shi kan cikinta yace.
"Fudail ka kama Anneh,. A kaita tsohon gida ta zauna a can kar a hada da masu kula da ita, a barta ita daya, Jasrah kuma a kaita gidan horo."
Daga haka ya mike tare da Ɗaukar Azizatul Nissah, kura musu ido Fudail yayi, a ranshi yana cewa.
*Ikram itace kawai zata iya dakatar da wannan wulakancin* sannan ya raka Sultanah Fazilatul nisa yana bata hakuri, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Karka damu, tunda Ikram ta bar gidan nan na fahimci babu me iya tankwara Mehran bayan ita, Azizatul Nissah kuma tayi amfani da cikin jikinta ta juya mishi tunani, amma nayi mishi Uzuri."
"Yanzun babu abinda za ayi Ikram ta dawo?" Ya tambayi Sultanah Fazilatul,
"Itama danginta suna kaunar ta, babu wanda zai so ta shigo wannan rayuwar." Ta faɗa tana share kwalla.
Haka ya takata har gidan, sannan ya dawo ya tasa keyar Jasrah. Bayan Mehran ya kai Azizatul Nissah d'akinta, lallab'a ta ya shiga yi har tayi kamar ta fara barci, kallonta yayi sannan ya mike zai bar dakin ta rike hannun shi.
"Sultan MEHRAN! Shin kana kaunata?" Kura mata ido yayi sannan ya zare hannun shi cikin nata, sannan yace.
"Ina Sonki mana, koda abin cikin jikinki."
"Me yasa ba zaka kaunace ba?"
Murmushi yayi sannan ya shafa kanta, bayan ya mike zai fita.
"Ko har yanzun wancan Yarinyar da maza suka gama hawa da sauka akan ta kake kauna? Amma kuma taya zaka gayawa Al'ummar ka Ikram ta tab'a aure har ta kwanta da wani namijin? Koda yake ai baka san yadda akayi kome ba, domin Yayana ya sha kwanciya da ita ni ganau ce ba juyau ba....
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
7...
"Ya isa haka!!!" Ya daka mata tsawar da sai da dan cikinta ya juya zunzurutun fusata, jikin shi yana kerma ya nufe ta kamar zai rufeta da duka.
"Kika sake raina ya b'aci dake, ba zai miki kyau, wallahi sai na baki mamaki. Sai na wulakanta ki a cikin Masarautan nan, sakarya me kike son nayi miki? Ita nake kauna. Ita na fara sani, ban damu ba ko mazan duniyar nan zasu kwanta akanta abinda na sani kaunarta dani gaskiya ce, babu karya a cikin shi. Idan na kuma jin Kinyi irin wannan haukar zan baki mamaki."
Daga haka ya fita ya barta, ita a tunaninta Mehran irin mazan nan ne da zaka. Sarrafa su cikin tsarin da ka gindayawa musu sai ya nuna mata shi baya cikin mutanen da zaka tanada domin bukatar kanka.
Mehran da Ikram ba tasha ta da a tare da shi ba, duk da kuwa suna kaunar juna Kamar ya, murmushi da farin ciki ne suka rufe ta, kamar zata tashi sama. Ta jefe tsuntsun biyu da Dutse daya, ta sanya shi ya kori Mahaifiyar shi da Jasrah ta kuma cusa mishi jin haushin Ikram, kenan babu amfanin da ba zai mata ba,. Dan haka daga yau tayi ta sanya shi cikin wani yanayi kenan. Kiran Rubina da Unaiza tayi tare da basu silallar zinari akan suje su watsa a ko'ina na farkon da bayi mata suke zama.
Tana murmushi, suma cikin farin ciki suka fita suna watsawa. Kallon juna Sawda da suka baiwar ta me suna Atika, cikin yanayin damuwa tace mata.
"Uwar d'akina, kamar fa anyi haka ne dan a tinzira zuciyar ku."
Murmushi tayi sannan tace mata.
"Karki damuwa, dan haka saka ido ki ga yadda za ayi ta."
Mik'ewa tayi tare da barin gurin, ta nufi waje, a hankali take tafiya har ta hango Sultan MEHRAN a can yana zaune. Fudail yana tsaye a gefen shi. haka ma Sarwat shima yana gefen shi. A nutse ta isa inda suke, kallon su tayi tare da musu alamar su basu guri.
Zama tayi a daya daga cikin kujeran dake gurin na alfarma, a hankali ta zubawa fuskar shi idanu. Kallon ruwan da aka kawo mishi bai sha ba, ta mike da kanta ta zuba mishi tare da mika mishi. Amsa yayi tare da dauke kan shi, sai da ya sha sannan ya cigaba da rike kofin ruwan.
"Uwa irin Fazilatul nisa, ba zata tab'a yunkurin abinda zai tab'a ɗanta ba, tunda mutanen duniya suka fahimci karfin Abbana yana tare da Ummina suka saka shi a gaba sai sun raba su, amma kasan me? Uwa irinta ake alfahari da ita, domin duk abinda aka yi domin a raba tsakanin su, Allah bai yarda ba sai da shida kanshi yayi ikon shi da ita.
An yiwa mahaifiyar mu kome domin itace Kwarkwarah shi da yafi kauna, amma kuma lokacin zuwa lokacin ana batun matsayin irin na sarauta sai gashi an cilla rayuwarta cikin hatsari, Mahaifiyar mu, ta badda rayuwar ta ne ta hanyar da aka so ta kashe Abban mu, sai ta amshi gubar tasha, kafin ta rasu ta rubuta cewa. Ita bata yi haka dan kowa ba sai dan Ni da Abba na, don Allah kar ya tura rayuwata kamar yadda ita ta tura rayuwarta. Sultan MEHRAN ban baka labarina dan kayi ta kallona ba, na baka labarina ne sabida Sultanah Fazilatul nisa da kasa aka rufe ta a wani gurin.
Duk wanda yake tare da kai yasan kana kewar Ikram, amma sabida zurfin ciki ka iya b'oyewa domin fusakarta Al'ummar ka, Sultan MEHRAN ban biyo ka ɗan na cusa maka b'acin rai ba, na biyo ka ne, dan na tuna maka mahaifiyar ka bazata tab'a ganin bayan ka ba. Amma kayi hakuri Insha ALLAH ba zan kuma maka shishigi ba." Daga haka ta mike zata wuce, riko hannun ta yayi tare da kallon yadda take kokarin barin gurin.
"Zauna!"
Zama tayi tana kallon shi, sake shanye ruwan yayi sannan ya mika mata tare da cewa.
"Kara min!" Ta kuma zuba mishi ya shanye, sannan ta kuma zuba mishi ya shanye, kafin yace mata.
"Ban taso da kowa ba, haka nayi rayuwa cikin kaɗaici da bani umarni nayi kaza nayi kaza."
Shiru yayi tare da lumshe idanun shi kafin ya bude a kanta, yana faɗin.
"Lokacin da ta shigo rayuwata ta sha wahala sosai, ta sha ukuba, ni kaina nasan na bata azaba da hannuna, amma kuma ta tafi ta barni da ciwon da ba zai tab'a warkewa ba, ya zaki ji idan aka ce miki abinda kake matukar kauna bai da inganci?"
"Idan har kaunar nakewa abun taya zan damu da batun mutane, Sultan Mehran karka daka ta mutanen duniya haka suke su kashe kashe ka, da ranka ba abun damuwa bane."
Tagwayen ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon ta, sannan yace mata.
"Anneh! Tasan ita ta haife ni ta cilla rayuwata cikin gararin? Laifin Anneh yana da yawa, domin Ikram ce ta sani fahimtar kome akanta, shin zan iya yafewa Anneh, ta kashe mahaifina sabida mulki ni kuma tana son ta kashe abin da za a haifa min taya zan iya dauke kai na akan abinda ta aikata?
Hada baki tayi da ku zaku kashe abin cikin Azizatul Nissah fa, Kinga kuwa dole naji babu dad'i."
Cike da mamaki take kallon shi sannan tace mishi.
"Wallahi bana son zama a cikin wannan masarautan amma sanin cewa nan ne zaman lafiya na, ya sani amincewa na zauna da kai. Na rantse da Allah wanda babu wani sarki sai shi, Sultan Mehran, Anneh bata tab'a tunanin tayi maka haka ba, bari kaji abinda ya faru."
" Bana son jin kome, tashi ki tafi kawai" ya faɗa mata, babu musu ta mike tare da mishi sallama.
Cikin