Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 274096 words

Chapter 27 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1386

Ads at the middle of Article

ta zama wakiliyar shi baya barinta sakat, duk wani abinda zai rubuta ko zai kafa doka itace ke rubutawa, wani lokacin idan aka turo sako ita ke karanta mishi, tunda ya fahimci haka kawai sai ya tsiro mata karatun dare, wato tsofin Littafin masarautan shi take karanta mishi yasa a kwaso. Gashi babu halin ta gaji zai tsiro da masifa da tsaki tare da mita, har dai ta dawo kusa dashi wai dan karta yi tunanin Noman ne, haka bai ishe shi ba, dai da ya tabbatar ya saka mata dokar bata fita wajen masarautan.


Lokacin da aka turo yaran Gwamnonin Yankunan SAMAIND, itace tayi mishi hira yana zaune tayi ta zance dashi, gaba daya ya dauke kan shi kamar shi ya rako ta, ba ita bace ta raka shi lambun ba, haka yayi ta juyata son ran shi kuma ba zaka tab'a jin ya rarrashi ta ba, asalima nuna mata yake duk abinda zata yi dolen tane. Kuma dokar shi ce.


~~~
Oman.
"Matukar Noman ya ci amanar mu, toh tabbas zamu kashe shi har lahira, Sannun kanwata kinyi aikin da muke bukata, idan da mune muka saka shi yaje can ba zai yarda ba, amma da kika kawo hikimar hakan kome ya tafi yadda ya dace....
Washi na gaji.
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM


Page 38


"Sai na Fahimci ashe bazan iya wannan b'arnan ba, domin Mehran ya d'aga muryan shi sabida ke? Ya kuma ragewa Hoyam matsayinta tare da rage na mahaifina. Ikram na Fahimci kin yin min abinda ban ma saka ki ba, Nagode sosai. Amma ki sani baki gama aikinki ba, domin akwai mutanen da sun shigo domin daukar fansa da laifin da nayi akan Mehran."


Hawaye ne ya zubo min tare da rike hannunta, bakina ya gaza furta kome kallon ta nake a hankali ta cigaba da cewa.
"Sun dauke Jasrah na kawo ta ne domin tayi min aikin da kika yi sai na fahimci bata da bushewar zuciya irin naki.


Bata da kome bata da kwarjini da kamala, bata da nutsuwar zuciya da ruhi, na san nayi laifi masu girma, tun daga ganin ki na fahimci kece zaki share min kuka na, amma ban tab'a sanin cewa kina da naki rayuwar ba, na zata idan kika zama makusanciya da shi zai sanya ki manta kome da kome ki fuskanci wata rayuwa, sai na Fahimci ba haka ba.


Mehran yana rayuwa ne ba tare da yasan me yake yi ba, Mehran yana rayuwa ne ba tare da ya gane halin rayuwa ba, amma haduwar shi dake ya sanya fahimtar darajar da Allah yayi mishi. Shairah, zo ka mata bayanin yadda zata fahimta."


"Ba zan fahimci sakon da zata shiga bayan wanda zuciyata take ciki, don Allah karki kara labta min azabar da nake ciki. Me yasa sai ni? Me yasa ba zaki zabi wata tayi miji aikin ba sai ni? Wato mareniya wacce bata da gata da galihu na shigo tsakanin ku kuna gwara kai na, meye nayi muka haka ne?


Me yasa na fito karamar ahali, shin kuskure na ne ko Kuskuren kaddarata ce, me yasa kowa yake son cillani wata rayuwa na daban, meye laifin rayuwata?"


Na fada da karfi ina kuka, tare da shasheka, na rasa Uwa na rasa Uba, na rasa kome nawa, sai yau kalaman Ummina yake dawo min da tace.
```Bilqusul Ikram! Duniya tana da fadi da yawa, ƙaddara mace ce da ba a san me zata haifar ba, ina ji a jikina bai zama dole na amfanar da gaba ba, amma tabbas rahamar Ubangiji yana bibiye da rayuwar wanda yayi imani dashi
Karki manta! Halayyar da dabi'u suna tafiya ne kunnen doki, gashi ba zan kai ba balle nace zan so ki rayu kamar sarauniya! Zan so naga yadda zaki amshi karfin mulkin```


Ajiyar zuciya na sauke tare da kallon kasa, hawaye na zuba min, abinci ta ajiye min da kanta tare da zama a gabana, wanke hannun tayi sannan ta fara diban abincin wanda aka dafa shi da nikekken nama, tana bani a baki hawaye na zuba min, itama haka. Tare da kallon yadda idanuna suke zubda kwalla.
"Ya kamata na cire wannan abun ki huta kema, ki rayu kamar sarauniya! Kinsan me ake kira da mulki? Ki zama sarauniya yana nufin ki adana darajar ki da budurcin ki ga sarki ne! Ina son ranar da ya amshi budurcin ki ya zama itace ranar da za a kiraki Sultanah Bilqisul Ikram Mustapha, ina son wacce ta iya fitowa daga yankin gabashin sahara ta mulke fararren fatan wannan yankin.


Ina son izzar da nake hangowa da ikon nan ya tabbata akan ki, zama Magajiyar sarauta ba abu ne me sauki ba, idan har zai zo da sauki toh ina rokon Arzikin kar a tab'a kimar yaron can! Kar wani namijin ya kusanci nahiyar shi, ba dan Ni ba, ba dan na isa ba, ina rokon a kare budurcin shi domin cikar muradin mu, so nake ki wargaza."


"Hmm!" Na fara dariya ina kallon ta, tare da cewa.
"Na wargaza rayuwar su, ki wargaza nawa. Bayan nasan kome akan ku ahalin Abbasiyyah, cin amana yafi yankan takobi kaifi a cikin zuciyar ku, cin amana yafi kome faruwa a cikin gidan nan..
Wata goma sha daya nayi ina zaune daga nan zuwa nan har na isa shashin Sultan Mehran, yau kice zaki min farar dabara."


"Akul Ikram! Kamar yadda zuciyar ki take cikin kauna da bege haka itama nata zuciyar take kwana da begen shi, taya hakan zai kawo karshen rikicin masarautan nan? Sultanah Fazilatul nisa ce a gaban ki kike gaya mata maganar da tafito bakin ki?"


"Toh d'an daudu idan ban gaya mata ba, bari na tashi nayi rawa saboda ina murnan kun kashe min rayuwa? Jinka dan an haife ni a karamar ahali zai hana na kasa kwatar kai na ne? Tab kayi kad'an ka kasa," na faɗa.


A madadin naga fusace ko fushi sai murmushi nake gani me hada da zubar hawaye, tana me mika min abincin. Kallon ta nayi sannan nace mata.
"Kuka kike?"


"Hmm! Eh"
"Ni ne da kuka bake ce da kuka ba."
Murmushi tayi bata kuma ce min kome ba. Har ta gama bani abincin sannan tace min.
"Tun ranar da aka kawo ki na sami labarin irin halittar ki! Koda suka mika ki ga Hoyam nayi fatan ta dawo dake waje har akawo min ke? Idan har irin halittar jikinki Mehran zai samu. Cikin rayuwar shi tabbas sauran tarkacen da ake shirin zab'a mishi su. Sunyi asarar babba. Ni nan zan shawo kanki yadda zaki rike duniyar shi, ki zama kece a ranshi ko a ina ne!"


Daga haka ta bar falon, tare da kallona.
"Ni budurci na da Ni kaina, na Noman ne"
Cak ta tsaya sannan ta juyo ta sake min murmushi, kafin ta wuce abinta.
Ihu da bori nayi ta musu, tare da ture kome, babu wanda ya kuma bi ta kai na, wato ga mahaukaciya.
~~~
Duk wanda yake tare dashi sai ya fahimci, halin da yake ciki, duk wannan kuzarin da mulkin babu, sai dai ya koma musu wani irin masifaffen mutum, d'an kuskure idan aka aka mishi zai saka a kai mutum gidan horo,


Mutumin da yabar giya, sai gashi ya dawo da shan giya sama da ruwan shan shi, a hankali Sultanah Hoyam ta shiga turo mishi yan mata, a duk lokacin da yake buge zata saka a kawo mishi mace, amma dake har cikin ranshi bayan son haka bai tab'a afka musu ba, haka zai gama shaye shayen shi, har ya yayi barci babu abinda yake hada shi da mace. A duk lokacin da ya farka zai zauna yayi ta kallon kanshi a madubi, Sabida tashin hankalin da yake zuciyarshi.


Kasawa ne ace macen da take karkashin kulawar shi wani namijin ya zo ya dauke ta, Zubewar mutuncin shi ne da na daular shi, sannan kamar watsawa kanshi kasa yayi a ido, me zai cewa Mahaifiyar shi, idan ta mishi gorin wani namijin ya kwace mishi macen da take karkashin kulawar shi?


Me zai cewa mutanen fada da kowa ya gama sanin ya kawo tane dan tayi goggaya dasu, me zai cewa Fudail da ya raba tsakanin su, lallai akwai tashin hankali a gaba kadan.
Tunda ya saka aka kai ta kebantaccen shashi, da kanshi ya shiga fita niman Noman.


Baya tashi fita sai dare, haka yake bin gidan baki, kullum sai ya fita, a irin haka, har ya isa wani gidan baki dake wajen gari.


Suna cikin hira, ya shigo gidan. Kallon shi suka yi tare da cewa.
"Waye kai?"
"NOMAN nake nima?"


Mik'ewa yayi sannan yace mishi.
"Gani nan"
"Ko za muje waje?"
"Toh!"
Fita suka yi Sarwat zai bisu Noman ya hana shi.
"Ka zauna babu wani abinda zai faru."
Yana fadar haka ya bi bayan Mehran, har waje..yana tsaye, a hankali ya nufa gaban shi..
"Gani nan!"
Shiru yayi yana kallon shi, meye noman ya fishi da har Ikram ta zabe shi akan shi? Tab'e baki yayi sannan ya cigaba da abinda yake, kan shi a kasa yana wasa da gashin kan shi, cire mayafin fuskar shi yayi tare da d'ago kan shi, yana kallon Noman.


Maza irin gurjiya, ba gaba da gaba ba, ko ta bayan sai an shirya, ja da baya yayi, cikin nutsuwa da mamaki tare da sauke kan shi ƙasa.
"Kana bukatar gabatarwa ne?"
"A'a Sultan Aamaan Mehran! Bana bukatar gabatarwa, Abinda yake gurin ka nazo amsa."


"Ko?" Ya faɗa a sanyayye, yana kallon Noman.
D'ago kai Noman yayi yana kallon shi, yana girmama al'amarin mulki, yana ji a bakin mutane yana da Izza, yau gashi ya gani da idon shi, domin kuwa maganar ma ya kasa bashi lokacin shi yayi magana.


"A bisa adalcin da zan maiay, shine zan saka gobe a kawo maka kyauta na musamman, daga dangin zinari, lu'ulu'u, da wasu abubuwan bukata, ka bar min ita! Kayi tafiyar ka duniyarka, idan ta nutsu zan kawo ta taganku. Ita din muradina ce."


"Gaskiya wannan adalci bane, ba zan iya fansar da soyayyar mu akan kananun abun duniya ba. Kabani ita na koma da ita, kamar yadda tazo." Inji NOMAN,
.ware idanun shi yayi tare da kurawa noman, a hankali ya dage takobin shi.


Tare da zare ta daga kubenta, a hankali yace.
"Da alamu zan aika ka inda ba zaka dawo ba."
. "Idan har akan Ikram ce tabbas sai da na rasa rayuwata."


Cikin fushi da fusata tare da d'aga takobin, aikuwa aka fara iska, me ƙarfi tare da alamar garin zai iya samun ruwan kankara ko kuma dusar ƙanƙara.
Azzabbrn yaki ne ya sarkafe a tsakanin su, kamar zasu hallaka juna.
---
A firgice na farka sakamakon mafarkin da nayi Noman yana yaki da Mehran, ina tashi ban Nime izni ba, nayi ficewa ta tagar gidan.
Gudu nake sakamakon iskar da take kad'awa, shashin Mehran na nufa, da Fudail na hadu.
"Ina Mehran?"
"Ya fita niman Noman?"
Hannuna dukka biyu na saka a bakina, tare da kallon shi. Na kasa magana, da gudu na juya ya rufa min baya, haka muka yi ta zaga gidajen baki har Allah ya nufa muka isa wajen gari.


A jikin wata itacce na tsaya ina maida numfashin da ya taso min, fada suke na tare da jima junan su ciwo. Walkiyar da aka yi ne ya sakani ganin yankar da Noman yayi mishi a hannun shi, shi kuma Noman a gefen kirjin shi, jini na zuba musu, duk da shi Mehran yana tsaye ba tare da ko layi kamar Noman da yayi taurin kai yana son kare martabar SOYAYYAR SHI.

Shiga tsakiyar su nayi bayan sun kawowa juna mummunan sara.
"Ya isa! Noman karka manta ina tare da kai, ina sonka amma bayana nufin zan Barka ka hada dantse da Sultan MEHRAN ba, shi din kamar Yaya ne a gare ni, kuma Uban gidana ne."


Juyawa nayi tare da kallon Mehran, na sunkuyar da kaina ba.
"Kayi hakuri! Yayi laifi da ya tako har sansanin ka domin farauta. Sai dai kuma kasan cewa, idan me guri yazo dole me taburma ya nad'e, kayi hakuri."


"Ba zan yi hakuri ba, sai dai ki sallame shi, idan ba haka ba ajalin shine ya kawo shi daulata."
Yana gama fadar haka ya juya tare da barin gurin, kallon Mehran nayi tare da juyawa na isa gurin da Noman yake kokarin faduwa, na rungumo shi, tare da sake kuka me cin rai ina cewa.
"Me yasa ka fara tinkarar shi da yaki? Waye ya gaya maka cewa shi din gama garin mayaki ne? A cikin wannan lardin Noman don Allah karka kuma wannan kasadar."


"Ba zan tab'a bar mishi ke ba ba, wallahi ba zan Barki ba, wallahi ko mutuwa zanyi sai na tafi dake, dan haka ki koma ki shirya akan idon shi zan tafi dake, wannan shine magana ta"


*Toh fa 🤔☹️ inda ba kasa nan ake gardaman kokuwa*
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```


#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 39
_Daga wannan Pagen din insha Allah wanda zai zo shine karshe!_


Taimaka mishi nayi ya mike tare da kai shi dakin shi, muka shiga bashi taimakon gaggawa, saboda yankan da aka mishi, har jinin ya tsaya, sannan na lalle shi tare da Mik'ewa zan fita yace min.
"Me yasa min fuskar ki?"
Shafawa nayi sannan na ce mishi.
"Babu kome!"
Gyada kai yayi sannan ya koma tare da kwanciya da kanshi yana fadin.
"Kar ki manta da tafiyar mu,"
"Insha Allah! Sai da safe!"
Na juya tare da ficewa daga dakin, ina fitowa waje na hango Fudail.


A hankali na karasa gare shi, sannan muka nufi cikin garin.
"Me yasa ba zaki iya tafiya ba, ga damar tafiya amma ba zaki tafi ba! Ko kina tsoron Mehran ne kar ya saka a kashe ku?"
Kallon shi nayi na wasu dakikai, sannan na cigaba da tafiya na, tare da kallon gabana.


"Haba Wakiliyar Mehran, me yasa ba zaki amsa min ba?" Ya faɗa cikin raha da Tsokana,
"Tausayin MEHRAN nake ji! Shi ya hana ni tafiya, da tun tuni nayi tafiya ta."
"Ko kema kina son shi ne?"
"Ko kana kishin shine?"
Na fada ina murmushi tare da tsare shi da ido, fisgo ni yayi tare da hadani da jikin wata bishiya, yana kallon fuskana da nake kallon shi babu tsoro.
Kan shi ya sunkuyar zai hada da fuskana nayi maza na kare hakan tare da kai mishi duka.


"Ni ba kazama bace! Na haɗa jiki da shugaban ka, kuma na hada da kai wannan shine kolokuwar cin fuska da mutuncin Aamaan." Na fisge kai na, tare da mai da hankali na akan tafiyar da muke.


Duk yadda yaso su fahimci juna taki asalima kamar bada ita yake ba, ga shegen kwarjinin da tayi mishi.
....
Koda na shiga keb'entaccen shashi, na sami Sultanah Fazilatul nisa a zaune tana kallona, bata ce min kome ba, har zan wuce tace min.
" Me yasa kike rusa shi daga kasa? Abinda kike aikatawa zai ja a dakatar dashi na tsawon shekaru uku zuwa goma.


Abinda kike bukata ba zai samu ba, idan har kika sake kika bar masarautan nan, tabbas Aamaan zai iya fuskarta tsigewa daga muqaminsa. Tare da mai dashi daya daga cikin masu jiran gado.
Don Allah Karki janyo min abin kunya da tashin hankali, sannan zai fita daga cikin gidan sarautar har sai ranar ya dawo da martabar shi. Duk da ba laifi bane hukunci ne laifin da ya aikata, na girmama Baiwar shi sama da dattawan Fada.


Don Allah Karki saka ni asarar duk faffutikar da nayi, domin zasu mai dashi wancan fadar da yake wancan dajin ne. Gashi bai da goyan bayan gwamnatocin shi.


Bai da goyan bayan mahaifina bai da goyan bayan Hoyam, kuma ba lallai bane sauran mutanen fada su taimaka mishi, don Allah Karki ja min asara biyu."


Kura mata ido nayi tare da kallon yadda take cikin tashin hankali, sannan nace mata.
"Wai ke meye Matsalarki da Shine? Ina ruwanki dashi ne? Meye nufinki akan shi Ni kam ma zargin ki nake, Wacece mishi ke?"
Wani irin rugugi garin yayi tare da sake wata irin tsawa, wanda ya haifar da walkiya me shegen haske, tare da haska ko ina,cikin d'aga murya tare da izza me hade da iko tace min.


"Nice Mahaifiyar shi!" Wani irin tsawa aka kuma bugawa me shegen ƙarfi wanda ya saukar da wani irin ruwan sama babu kakkautawa, ta tako gabana tare da kallona.
"Tun daga lokacin da kika iya dukar Jasrah a cikin gidan nan, maganar Uwaisul Qarni ya tabbata zaki zo taimakona!" Da sauri na kalle ta tare da sake baki na.
"Kinyi mamaki ne? Bayan na tabbatar dake ma kin san shi? Ba abin mamaki bane, haka bai wadatar dake ba, sai da kika yi mata duka ta kasa koda amsar kanta. Sannan Ni nasan cewa ke ba daga karamar ahali kika fito ba, amma bansa daga wani ajalin kike ba.


Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads