Showing 174001 words to 177000 words out of 274096 words
Chapter 59 - DAULA BIYU Complet Document .txt
wani mahayi da aka turo shi.
Dan haka garin ya kasance kamar ana bikin sallah, wani irin biki ake me cike da shagali. Haka muka isa har fadan, inda aka muka yada zango a falon Sultan Mu'allim. Mika min hannun yyi. Da sauri na isa gare shi. Ina isa na zube gwiwata a kasa, kai na a bisa kafadar shi, na sake kuka me cin rai. Takaici yasa Rahil fita a gidan.
Kuka nake wanda idan ka tambaye ni ba zance maka ga abinda aka min ba, amma kuma a cikin raina, ina kuka ne domin na rasa Mehran. Yadda nake kukan ya sashi sake murmushin jin dadin. Sannan ya shafa kai na, yace.
"Kiyi hakuri! Haka muke tsara miki baki rayuwar. Da karen layi gwara Zakin gidanka koda kuwa zaka zane shi da bulala ne, kiyi dan mahaifanki da kanwarki. Ba akan ki da soyayyar ki ba. Mun rigada mun yanke kuma al'adunmu sun sha banban da kowane, mukan iya binne abinda muke so! Mukan iya boye abinda muke kauna, matukar hakan zai bamu damar fuskantar matsalar.
A tsarin mu, bai zama dole mace ta samu abinda take so ba, matukar zata bawa Mulkin mu. Gudunmawa dan haka na zab'i ra'ayin shi sabida ki bashi gudunmawa. Yanayin ku yayi daidai da mulkin, abinda ake bukata domin mulki kin hada, dan haka ki amshi Rahil a matsayin abokin rayuwar ki."
Hawaye ne ya shiga zuba min, na kasa magana tare da sunkuyar da kaina, domin yayi min kwarjini. Haka aka fitar dani har dakin Bilqisul Ikram, tankwarata. Shafa kaina tayi sannan ta kira amintattun bayin ta, suka shiga dani ban daki. Aka hada min wani irin ruwan wanka tare da turaruka masu dadi. Sai furen kamshi da wanka aka watsa a ruwan, sannan suka shiga cudani. Hawaye na zuba a idanuna. Shi kenan na rasa Mehran. Na rasa Jarumina, me yasa tun tuni ban amsa mishi ba. D'ago kai nayi sannan nace a raina.
_Toh amma ai bai ce yana sona Ba? Toh amma kuma ai duk abinda yake min duk na soyayya ce! Kishi da zafin rai akai na duk abinda masoyi ne kaɗai yake yin shi! Toh Ni me yasa na shiga zab'en? Kenan bawai na shiga dan shi bane sai dan ina son shi?_
Kwalla ne ya zubo min, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, haka suka taimaka min nayi wanka na fito bayan sun bani wani yadi na lullube jikina, tare da fitowa daga ban ɗakin, tunda na fito suka shiga shafa min wani abu kamar mai kamar sabulu, ina zaune ina kallon su. Kwallar da nake sharewa a kai a kai, yasa Bayin suka shiga rarrashina, kamar dama jiran su nake na fashe da kuka. Hannun daya daga cikin su ta saka min a bakina.
"Abin kunya ne babba ga Sultanah Balkisu Ikram aji cewa babbar Yar D'anta na farko tana kuka akan SO kinsan yadda muke boye kalmar a ran mu kuwa? Toh koda kuwa zaka rasa ranka akan sone yana da kau kayi hakuri da shi, idan baso kike mulkin kasar nan ta gagari Amir Rahil ba.
Don Allah ki hakura da Sultan Aamaan Mehran. Mun san yadda kike son shi, amma duk wanda zaki gani a cikin masarautan nan yana da tab'on soyayya, dan haka karki sake a Fahimci zuciyarki tana ga wani da namijin domin abin kunya ce ga Kakarki."
Haka suka kashe ni da magana tare da nuna min illar abinda nake aikatawa, nayi kuka da sunan Allah kuma nayi bakin cikin zamowa ta, daya daga cikin ahalin babban gida. Ina ji ina gani ranar aka mai dani kamar wata yar tsana, zunzurutun wanke nan shafe ne. Ana gyara min jikina. Har kusan tsakiyar dare a sannan nayi wankar karshe tare da sallah na kwanta,. Ranar barci na zance kacokan mafarkin Mehran nayi tayi. Ina kuka ina kome haka zan farka naga bayin nan suna rarrashina.
..... Washi gari ina farkawa kafin nayi sallah asuba, suka bani madara dafaffiya,, sai da na wanke baki na shanye tass, sannan na shiga wanka tare da Alola ina idarwa, aka kuma kawo min yankanken y'ay'an itacce, wanda aka zuba madara da zuma na shanye shi, ina ji suna faɗin.
"Kirjinta muke son ya cika kafin zuwa bikin su." Shiru nayi domin bani da bakin magana sai yadda suka yi dani...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
03
Wato ma'ana bani magani suke tare da abinci me gina jiki, duk abinda suke idanuna a rufe suke, bana budewa wani lokaci haka zasu yi ta magana ina jin su, bana tanka musu, idan suka gama min kuwa a gurin nake kwanciya. Ina kuka duk taurin zuciya ta da taurin kai na, sai da ya kai komi kashin b'acin rai kuka yake sani.
Rabona da Izmah kuwa sai dai na shafe kwanaki goma kafin aka barta ta shigo min dakina, lokacin da ta ganin sai da ta firgita, tana mamaki.
"Ikram! Baki da lafiya ne? Kinyi kyau amma kuma kinyi mugun rama, meye yake damunki? Me aka miki? Don Allah gaya min"
Zama tayi a jiki na, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, nace mata. "Izmah Mehran nake son gani" kamar wacce aka dasata, haka take kallona. Bakinta yana rawa tace min.
"Sultan MEHRAN?" Ta kuma tambayana, gyada mata kai nayi tare da rushewa da kuka, rike hannuna tayi tare da kwantar da kaina a kirjinta.
"Ikram!" "Don Allah Mehran;" na katse mata abinda zata fada, duk sai ta rasa abinda zata ce min, ta kuma bude baki zata yi magana, Amir Rahil ya shigo cikin ɗakin, yan mata na biye dashi. Mikewa tayi zata fita na rike hannun ta.
"Kiyi hakuri zan jira idan ya fita zan shigo muyi Magana."
"Wacce magana zaku yi? Ai akan wancan Jahilin da ya kasa miki uzuri ko? Ko akan Abrad da ya gama da budurcin ki? Kinga Ikram. Ina Sonki shi yasa zan dauki duk abinda ya same ki, amma kika Kuskura kika shigo da Mehran yake ko Aman yake? Wallahi Billahi azim, zan kashe wannan abin" ya nuna min Izmah, sauka nayi daga gadon na zube gwiwata a kasa, tare da rungumo Izmah, ina kuka nace mishi.
"Kayi hakuri! Ba zan kuma maganar shi ba, amma karka tab'a lafiyarta. Idan nice na amince." Na fada cikin kuka, murmushi yayi tare da nunawa Izmah kofa ta fita, tunda ya shigo inda nake ya d'ago ni. Kallon kayan jikina yayi yadda ya fitar da surar jiki na. Nayi kyau na fitar hankali. Duhun fatar da nake dashi ya washe nayi wani irin haske me ban mamaki.
Matsalar kawai rashin nutsuwar da bani da shi ne ya janyo min rama. D'ago kai na yayi tare da kallon fuskana. Kan shi ya kawo da sunan zai hada bakin mu na kauda kaina, murmushi yayi tare da cizon kunne na, rike rigar shi nayi tare da jin saukar kwalla daga idanuna. Na bakin ciki dan Allah ya gani bana son shi a mijin aurena, a dan uwan na dauke shi amma bai Fahimci haka ba, yayi ta shige min.
"Ai da wancan banzan ne ba zaki na kuka kamar karamar yarinya ba, dake baki kaunata shi yasa kike kuka. Ikram me yasa baki sona? Ni dan uwanki ne kuma zan iya bada rayuwata domin."
"Ba zaka iya, shi daya ya bada rayuwar shi domin ni, don Allah." Dama abinda yake nima kenan, kuma ya samu. Dan haka banyi wani abun da zai nuna mishi jin dadi ko bakin ciki ba, na dai rufe idanuna. Ya gama sumbatar bakina, sannan ya janye daga jiki na, ganin har lokacin idanuna a rufe suke, ya sashi fita daga d'akin yana murmushin jin dadi.
Haka rayuwar mu yayi ta tafiya, ina zuwa shashin Sultan Mu'allim, yana bani wasu abubuwan da ya zama mallakar mahaifina, tare da wasu kyautattakar, haka zan dawo shashin Sultanah Balkisu Ikram, na zauna, shima sabida wancan wahalallen nake haka, idan a d'akin ta, domin yana shigowa zata kore shi. Haka ya sani tarewa a d'akinta, duk da kuwa d'akina na kallon nata ne, haka akayi ta gabatar min da y'ay'an gwamnonin nahiyar, tare da manyan mutanen ƙasar.
Har zuwa lokacin Mehran shi yake da kaso mafi girma a zuciyata, na kasa cire shi a raina. Na sha tambayar kaina me yasa lokacin da nake tare dashi ban ji haka ba, sai da bamu tare? Wannan amsar har yau na kasa bawa kaina amsa. Kullum da wannan nake kwana nake tashi.
"Ciki abincin mana!" Kallon Sultan Mu'allim nayi tare, sunkuyar da kaina, na tsakuri abincin na kai bakina.
"Rahil yace min har yanzun baku fahimci juna ba?" Sunkuyar da kai nayi tare da kasa kai abincin bakina.
Ajiyewa nayi zan mike yace min.
"Zauna."
Komawa nayi ka zauna, tare da damke hannuna, jikina yana rawa.
"Kar na kuma jin labarin kinyi magana akan SULTAN Mehran! Idan kuma hakan ya faru, zamu kashe baiwar da kike kauna, domin idan bamu fito miki a asalin mutane ba zaki kunyata mu. Bamu son muyi miki dole shi yasa muka baki damar ku fahimci juna. Nan da wata biyu muka baki ki fahimci waye shi idan ba haka ba."
"Taya zan Fahimci abinda kuke so? Bayan ni din ba mallakarku bace, ni bana son lusari." Dukar tabirin yayi tare da kallon Sultan Mu'allim.
"Atta kana jin abinda harshenta yake faɗa." Kallona yayi sannan ya kuma maida kanshi ga Ikram.
"Haka zaki zauna dashi domin baki da mijin da ya wuce shi."
Mikewa nayi zan bar gurin Rahil ya taka rigar jikina, karar yagewar jikina, naji kallon shi nayi ban san lokacin da na wanke shi da mari ba, sai da ya firgice. Tabbas yayi kuskuren babba, amma kuma marin da tayi mishi shine mafi girman wulakanci da aka tab'a mishi. Shafa fuskar shi yayi sannan yace.
"Atta! Marina tayi."
"Me yasa ka taka mata rigarta? Matar da zaka aura bata bukatar tilastawa, kasan tana da wanda zuciyarta yake so kai kuma ka same ta ne a sama. Karka sake haka ya kuma had'aku."
Juyawa yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Ke kuma za aka kaiki gidan horo."
"Atta!" Ya kira sunan Sultan Mu'allim, murmushi yayi sannan ya d mishi.
"Idan na yanke hukunci ko kaina bana saurarra dan haka, Bhaiq kazo ka tafi da ita."
Ban yi gardama ba dan haka na amince aka tafi dani.
"Atta don Allah."
"Matar da zaka zauna da ita ta mare ka, me kake tunanin nan gaba zata aikata? Dan haka ka bari a nuna mata girmanka da darajarka."
Jikin shi a matukar sanyayye ya bar gurin cin abincin, bai tsaya ko ina ba, sai gidan kakan shi na gurin Uwa wazir. Zama yayi cikin nutsuwa sannan ya gaishe shi, tare da yin shiru. Kasa magana yayi yana kallon yadda Rahil din ya nutsu, kafin ya ce mishi.
"Ina jinka!"
"Dama dama dama.."
"Ka nutsu kayi min magana!"inji kakan shi, nutsuwa yayi kafin ya fadi abin da ya kawo shi. Da kuma dalilin da yasa aka rufe Ikram. Kallon son kai yayi mishi,
tsantsan domin kuwa banda son kai babu abinda ya hango a maganar Rahil.
"Tun lokacin da ka bayyana soyayyarta a ranka na gaya maka cewa ka rabu da ita, amma fir ka kiya, sai ma goyan bayan da kasamu daga danginka, ba wai Ikram nace bata sonka kai ne baka dace da rayuwarta ba, ai duk wanda yaga yadda ta bar kasar nan bayan ta gama maka aiki har ta kai da ta nuna ita ta mutu zaka fahimci akwai soyayya a cikin tafiyarta, amma zuciyarka dake a rufe take kaki yarda akan lallai ita kake buƙata
"
"Amma kuma taya gida bai koshi ba za a dauka akai waje? Taya ina sonta zan kyaleta ta tafi yanki mafi hatsari da ganganci da rayuwa? SAMAIND cike take da rayuwa da mutuwa! Kuskure daya idan mutum yayi mutuwa tafi kome sauki a rayuwar shi. Uwa uba zunzurutun makircin da yake cikin masarautan. Kaka nazo ne domin niman hanyar da Ka fidda ikram, idan ba zan samu ba na hakura nayi tafiya ta"
Kallon shi yayi na tsawon lokaci kafin yace mishi.
"Ta yaro kyau take bata karko, Ba zan daina gaya maka ba Ikram bata dace da rayuwar ka ba, Ka barta tayi rayuwarta da wanda take SO Ni dan taimaka maka, amma ba zan tab'a tilasta mata ba,.kuma ba zan mata dole kamar yadda kuka mata ba, zan bata goyan baya ta auri wanda take so."
Mikewa yayi cikin fushi zai fita, har ya isa bakin kofar kakan Yace.
"Kai ake bukatar ka zama sarki, idan har baka san yadda ake sadaukarwa ba yaushe zaka yiwa Al'ummar ka adalci? Ita saboda jarumtarta ake bukatar ta a jikinka, me yasa ba zaka zama jarumi ba kamar ita? Amma karka tilastawa zuciyarta yake cike da kaunar wani. Domin kana ji kana gani zaka yi danasanin rayuwa."
Fita yayi daga cikin gidan, ya nufi can babban shashin. Inda ta zube a gaban Sultanah Balkisu Ikram.
"Me yasa bani da Sa'a? Me yasa kowa yake min kallon mahaddami? Ni ne ban dace da Ikram ba ko ƙaddara ta ce bata dace da ita bane? Sultanah a tunanina ni Maraya ne, samun Ikram ne ya sani fahimtar ni me galihu ne, me yasa Ikram ta sani nake jin ni ba kome bane?
Me yasa a kullum nake jin nayi son kai? A duk lokacin da na kalli Ikram sai na dinga jin a raina nayi son kai sama da kome a rayuwar mu, tunda ta dawo cikin gidan nan ban tab'a ganin ta dauki takobin domin kare kanta ba, me yasa?"
"Sabida zuciyarta tana wani guri na daban, kaunar da take mishi ba boyayya bace, yadda take kuka akan shi ya tabbatar min ita din ba kowa bace a fagen SOYAYYA! Zai yi wuya ka hada soyayyar da Jarumta, amma kuma ana ana iya hada soyayya da yaki koda kuwa haka zai bada damar a shafe alkarya guda! Akan soyayya tana iya haifar da juyin juya halin a cikin masarautan! Akan soyayya akan iya shayar da sarki guba domin cimma manufar Soyayya! Irin soyayyar Ikram da Mehran! Idan ba ayi takatsantsar gurin nuna musu bambanci rayuwa ba, dole dayan su yayi rayuwa dayan su ya mutu?
Soyayya ce ta shiga tsakanin zubda jini! Kasancewar dukkan su sun kasance, a cikin lambu. Ba zance shine ƙayar ba amma tabbas haka ya nuna min cewa soyayyar su kamar fure ne cikin ƙaya. Gashi da kyau amma kuma haka za a hakura da shi,.idan kuma ka nace kana so. Ba makawa kayar zata illata ka. Idan kuma ka hakura dole haka zaka ji ranka ya raya maka soyayyar furen da take ciki ƙaya. A halin yanzun..Ikram ta kasance fure cikin ƙaya ce.
Duk inda Mehran yaƙe yana faffutikar ganin ya iso gare ta, idan ma shi bai isa gareta ba, ita tana kokarin isa gare shi"
"Taya bayan tana gidan bada horo? Haka ba zai yiwu ba
" Ya faɗa tare da kallon kakan shi.
"Zai yiwu mana, kai abinda ka sani kenan. Ita kuma abinda ta sani zata aikata. Kayi hakuri da Ikram domin ita zuciyarta tana ga Mehran..kai ma ai akwai shukrah da take sonka me yasa ba zaka hakura da Ikram ba?"
Ka sake yayi yana kallon kakar su, kafin yace mata.
"Me yasa kika ce haka?"
Gyara zama tayi sannan tace mishi.
" Kai anan gabaki daya cikin masoya da dangi kake, Mehran kuma cikin makiya yake rayuwa, da ace yana cikin dangin shine da suke kaunar shi ba zata tab'a komawa gare shi ba"
" Amma kuma ai dan daukar fansa ta koma gare shi. Domin rama abinda yayiwa Nu'man."
Dariya tayi sannan tace mishi.
"Waye ya gaya maka k'iyayya ce ta kaita gare shi? Duk wanda ya gaya maka ta koma ne domin rama abinda yayi mata toh yayi karya, soyayya ce ta maida ita da ɗaukar fansa ne ba zata tab'a amsar tayin shi ba, da ɗaukar fansa ne ba zata tab'a yarda ta amshi ragamar auren shi ba, kasan inda ake kurman Kaunar! Toh ka zuba ido zaka ce na gaya maka Allah ya bamu nisan kwana"
"Yanzun Nanna duk soyayyar da na mata ya tashi a banza Kenan? Na sota iya so babu algus me yasa na rasa ta? Soyayyar ta nake mata babu cutarwa a cikin shi amma me yasa ba zan same ta ba? Don Allah Nannah ki taimaka min na same ta. Dan itace abokiyar rayuwa ta...."
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
04
Murmushi tayi tare da ɗaukar ruwan da yake gabanta ta kurb'a, sannan ta dauke kanta kana ta cigaba da cewa.
"Ba zan ce ka hakura da ita ba, domin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, wayallah kayi nasara wayallah kuma ka fadi wannan shine abinda zan gaya maka."
"Amir SULTAN yana