Showing 132001 words to 135000 words out of 274096 words
Chapter 45 - DAULA BIYU Complet Document .txt
juya, shi kuma ta shige cikin gidan, yana zaune a babban falon shi, sai ga Waziri. Da sallama, nuna mishi gurin zama yayi sannan yace.
"Sultan!"
"Wazir!"
"Na'am!"
A hankali ya warware mishi yadda suka yi da Rahil, shiru yayi yana sauraron shi har ya gama, gyara zama Waziri yayi sannan ya kuma kara nutsuwa, sannan yace mishi.
"Allah ya taimake ka! Sai dai kuma ina ganin kamar akwai tilastawa, domin idan tana da abokin rayuwarta ya zamu yi da ita? Ko zamu mata dole ne?
Ka ajiye shashancin Rahil, karka koya mishi kome ya nima zai samu, domin ba lallai bace ita ta amince ta zauna dashi."
"Zata zauna dashi mana, me yasa kake ganin ba zata zauna dashi ba. A iya fahimtar da nayi na gano itace kwarin gwiwar shi, idan tana kusa dashi, zai zama cikakken namiji, idan bata tare da shine zai kasance mara amfani, kuma a halin da na ganshi yana matukar kaunarta duk da yasan yadda muke iya boye soyayyar mu, amma ya kasa b'oyewa ya gaya min kaunar da yake mata. Don Allah karka karya mana gwiwar mu!"
Shiru Waziri yayi domin bawai baya son Ikram da Rahil bane , kawai yana hango yadda zata amshi tayin akan Rahil ne, idan kuma tana da wanda take so ya zasu yi tunda dai ai ba dole zasu mata ba.
Dan haka yayi ta mishi bayanin yadda zai fahimta amma son Rahil da tausayin shi na maraicin da ya taso ya hana Sultan Mu'allim hango kuskuren da zai aikata, dan haka wazir yayi shiru yana me binshi da toh, har ya gama bayanin shi, sannan ya sallami wazir.
Daga nan shsshin Rahil ya nufa, ya same shi yana cikin nishadi da annashuwa.
"Daka ce kana son yarinyar bata da wanda take sone? Karka so kanka matukar ka fahimci tana da abokin rayuwar ta, don Allah ka kyaleta karka mata dole, dan nasan matukar Almustapha ne ya haifeta ba zata tab'a tsallake umarnin Sultan ba."
Daga haka ya juya tare da barin shi yana kallon bayan Kakan shi ba gurin Uwa, shi yasa baya jin dadin shi domin sam bai sake mishi kofar da zai sake jiki dashi kullum cikin fada da tsangwama,kullum yayi abu yayi ta mishi fada kenan.
Tab'e bakin shi yayi sannan yace.
"Ina ruwana, koma waye Salsabila ta wace!" Ya fada kamar wani yaro karami, har da tura baki gaba.
Shida ba an bashi ita ba, toh koma meye su suka sani, Ikram tashi ce shi daya kuma babu shegen da zai kwace mishi ita. Har da bin dakin da harara.
~~~
Kowane bangare sun gama gajiya da niman Ikram domin Askandariya ma, tun wani yunkurin da Nairah tayi aka kamata tana gidan yarin, Sultanah Amrah tasha jinya sosai. Sannan ta saka aka tafi har Merocco, aka bincika mata kome akan dangin mahaifin Ikram, sai dai babu Ikram a can.
Abinda ya d'aga musu hankali kenan, suka shiga niman ta kamar hauka.
~~~
Yau shekara biyu da wata tara, sannan Wancan mugun ya fitar da mu, duk da mun sha wahala a cikin gidan yarin amma kuma sai da takai na rike shugabancin gidan baki daya, kuma yadda aka mana mulkin mallaka a cikin gidan haka muka yuwa kowa, tare a cin Ubansu. Shi yasa bamu lalace ba, dan da farko ne muka yi wata irin muni,
Toh da na fito a asalin tsagerancin sai gashi abincin mu daban da na sauran fursunonin,kome na mu sai da ya banbanta da na kowa, dan haka nasaka Nimrah da Izmah mike kafa suyi abinda ransu yake so, kuma sunyi babu abinda suka sani suna daga kwance aka musu wanki,tausa, abinci ma idan suka tashi sai suce a baki za a basu, Ni kuwa haka dad'i yake min.
Ina shimfid'a mulkina cikin Izza da takama, shi yasa yau da aka ce wai zamu fita, sai da mutane da da yawa suka yi kuka. Juyar da kai nayi sannan nace musu.
"Karku sani shauki domin wallahi ba zan muku kuka ba, kawai zanyi kewarku ne. Duk wanda muka mishi laifi ya yafe mana, saduwar Alkhairi. Mun gode sosai....
*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
23
Juyawa nayi a sannan nace musu.
"Kuyi hakuri! Haka Allah ya ƙaddara mana, Nagode sosai da zaman amanar da muka yi" duk da nasan mun yi zama mara daɗi a farkon shekaran da aka kawo mu. Amma daga baya kuma da na amshi cikin gidan sai gashi da kansu suke nuna min kuskuren su. Har ta kai suna kirana da shugaba, abinda na sani shine bana iya zalinci, kuma bana son naga anyi zalinci.
Amma kuma ko yaya ka tab'a wani da sunan zalinci nake jin haka a raina, dayawan su, ba yara bane manyan ne maza da mata, ƙalilan ne yara kangararu irina, lokacin da muka nufi fadar Aabis, yana hakimce a saman kujeran shi, kallon juna muka yi. Sannan yace min.
"Barka da fitowa! Ashe zaki ladabtu haka?" Murmushi nayi sannan na zauna cikin nutsawa,
"Waye ya gaya maka zan ladabtu cikin sauki? Kawai na zauna ne na huta kuma gaskiya gidan yarin akwai kulawa yadda ya dace, kai dai kawai abinda naso fahimta kananun tsagerun da ka ajiye a cikin gidan ya sani koya musu ladab."
"Har yanzu baki ji a jikinki ba?" Kallon shi nayi domin na fahimci bashi da mutunci.
"Hmm! Bana son na nuna maka yadda nake rayuwa, dan haka idan baka da abin yi zan tafi kuma idan Yaranka sun isa su dakatar dani!"
Na juya zan fita, suka sha gaban mu, maida su Izmah gefe nayi, sannan na gyara tsayuwa na, gatarin da na dauko a gidan yarin na fito dashi, na juya kamar yadda Mehran yake idan zai kai farmaki.
"Ku kyaleta! Dawo muyi magana dan na lura mahaukaciya ce ke!" Juyawa nayi sannan nace mishi.
"Daga turu nake" na bashi amsa,
Murmushi yayi sannan yace min,
"Mu shiga daga cikin gidan."
Haka muka wuce dashi, wani dakin sirrin shi muka shiga, anan yake bani labarin yadda ya tsira da shida Mahaifiyarshi, bayan kashe Sultanah tace ayi.
"Me kake bukata?" Na tambaye shi.
"Ki kashe shi! Domin nima ina da gadon sarautar SAMAIND"
"Toh duk buri daya gare mu, dan haka zan mishi yadda kake so zan kashe shi akan laifin mu, amma baka da labarin meke faruwa a can!"
"Eh Toh ina da labarin cewa, yanzun haka ana ƙoƙarin zab'a mushi mata ne, duk wacce ya zab'a sai ce bata mishi ba, ban san meye nufin shi ba."
"Toh ina ganin matar mutuwar shi yake jira gani nan tafe." Na fada mishi.
"Taya zaki shiga garin?"
"Dabara biyu gare ni, idan na shiga na farko da zamman kashe shi, shikenan. Idan kuma haka bai samu ba, zaka hada min tawagar da zamu tafi a matsayin matar da zata shiga zaben shi."
Kura min ido yayi sannan yace min.
"Amma kina da fikra!"
"Mhh!" Nayi mishi murmushin gefen baki, sannan nace mishi "tafiyar nan da kwana biyu, so nake na cimma matsaya kafin a gabatar da zaben zai iya kaiwa kwana nawa?"
"Dan da wata daya ba!" Ya bani amsa,
"Idan na kashe shi nan da kwana ashirin da bakwai, na gama aiki idan kuma ban gama ba dole na shiga wancan shirmen."
Na fada a hankali, kallon juna muka yi sannan yace min.
"Ya angama?"
"Eh ina tunanin haka!" Na bashi amsar.
"Zaki iya?" Ta kuma tambayana.
"Zan iya mana, duk da shi din ba gama garin mutane bane ba, kuma zai iya fahimtar wacece ni ba, sai na nime bakakken kaya domin kare kaina"
Da haka muka tsayar da magana, Aabis yasa aka shiga mana shirin da hidimar tafiyar mu, gefe daya kuma aka kai mu gidan da zamu zauna.
....
"Amma Ikram ba dai duk sabida wanda ya kashe miki miji kike wannan al'amarin ba?" Kallon su nayi yadda suka kafe ni da Idanu,
"Eh mana! Sabida yada zan dauki fansa ne" na fada ina me takaita maganar,
"Fansa akan mutum daya? Akan mutum daya zaki sayar da rayuwarki domin rama abinda aka mishi? Akan mutum daya zaki saka zuciyoyin mutane a cikin damuwa? Toh ko an ce miki Sultan Mehran d'an tsako ne da zaki iya watsa mishi hatsi me guba yaci ya mutu ko?"
"Wai Ni kam meye Mehran yayi miki da zafi? Gabaki daya kin sauya kanki kamar wata namiji, baki da aiki sai kisan kai, kuma abun haushi har yanzun baki ji kinyi kuskuren ba kullum."
Wanka na shiga na Barsu, sunata luguden lebbe, bayan na fito na gyara jikina, sannan na kwanta, ban ce musu kala ba domin yin maganar kamar kara tunzura su yake, haka ma shirun takaicin yake kara musu, dukkan mu muna hutawa aka kawo mana abinci, tashi suka yi suka ci.
"Gimbiya ga abinci"
"Na koshi!" Maida kaina dan d'agowa nayi ma basu amsa, gyara zaman suka yi, sannan suka cinye tass, kafin suka shiga niman kwanciya. Mikewa nayi na shiga ban daki nayi alola, sannan na fito na gabatar da sallah,.ina idarwa na kwanta a gurin. Tare da tambayar su.
"Ina abincina!" Zaro idanu suka yi waje, suna kallona. Murmushi nayi sannan na duba tiren nama na gani gashashe, kad'an naci sannan na kwanta, tare da juya musu baya.
~~~ Kwana biyu muka dauka sannan muka gama shirin tafiyar mu, SAMAIND a karo na biyu. Zan shiga Samaind cikin wani irin yanayi na daukar fansa. Tun da muka bar sahara, bana magana sai dai a yadda nake kokarin ganin na shiga nutsuwa na ne yake yawan damuwa. Domin haka kawai nake jin kamar bana bukatar fansa haka.
Zaman mu a garin Madinatul Mah ya sanya ni jikin mutuwar jiki, abubuwan da suka faru a can masu tsayawa a rai ne, bana jin zan kuma samun kyakkyawan damar da ya same ni a lokacin. Bana najin zan kuma jin yanayin da naji zama da shi a hankali, lumshe idanuna nayi ina hango wannan yanayin a idanuna.
Hannun Nimrah naji a cikin nawa, a hankali na bude idanuna. Da sauri na sake hannunta tare da wurga mata harara.
"Wannan wani irin Iskanci ne?"
"Dadi na dake fassara, dalla can ba dan wancan yanayin nake jin na miki magana ba."
"Kyale Ni" na fada mata, tare da juya kaina, na lumshe idanuna a karo na biyu, sannan na kwantar da kaina, a jikin keken dokin.
"Ki rabu da ita! Tana son yakar Mehran, amma kuma adilar zucuyarta tana tuna mata dajarar shi, mutumin da ya koya maka kare kanka, mutumin da ya roke ka, damar zama dashi mutumin da ya tsaya dom...."
"Kanin Ubana ne da zan d'aga mishi kafa?" Na tambayi Izmah,
"Idan baki d'aga mishi kafa dan adalci ba, kya d'aga mishi kafar domin raya kaunarku!" Kallon shegen bakinta nayi yadda ta iya zato gundumemmiyar magana haka.
"Kuma haka ne fa, Allah kasa naga waye Sultan Mehran din nan, naga yadda za a kwashe soyayya dashi har haka." Inji Nimrah.
"Amma dai ku yan iska ne? Ina ruwana da wani shi?" Na fada a fusace,
"Ba zaki gane bane, Kinga wannan bakinki? Wallahi idan kika Kuskura ya kama shi, hmmm wallahi na tausaya miki domin kuwa a mutunce zai cinye bakin babu wanda ya isa ya hana shi."
Toshe kunne na, nayi domin Iskancin su ya wuce tunani na, matukar zasu zauna toh wallahi maganar banza suke cirewa a bakin su, kuma karki tsammanin ba zasu iya fada bane.
Har muka yada zango, muna kwance a daki daya, abinci muka ci sannan muka fada hira. A hankali muna hira ban san ya akayi ba sai ji nayi bakina ya furta Uwaisul Qarni.
"Shine mutum na farko da na fara haduwa da shi, bayan na rasa kowa, daga shi sai Sultanah Fazilatul nisa, itama kuma dan Mehran ta bukaci ni,"
"Toh amma kuma shi Mehran fa?" Suka tambaye ni kamar hadin baki, iska na furza a hankali, sannan na kuma kallon su kafin na dauke kai na, akan su.
"Mehran! Aamaan Abdus Samad Mehran na biyu! Banyi tsammanin akwai abinda zan fada akan shi me kyau ba, mutum ne me mugun son kanshi da zuciyar shi. Mutum ne da baya hango cigaban ka sai Allah tashi. Idan na ce zan fada muku irin wahalar da nasha a hannun shi sai kun yi mamaki. Sai dai duk da haka, ya koya min fada da kuma tinkarar yaki.
Mehran ya ceto rayuwata sau biyu, ya kuma kare lafiyata, iya wannan yanayin kawai na tuna bayan shi bana tunanin kome akan mutumin da ya kashe min rayuwa ta, domin akan idanuna dakarun Samaind suka kashe min mijina a daren ranar auren mu, zuwa wayewan garin ranar. Ba zan iya yafe masa ba.
Ba zan iya yafe mishi ba, zan rama abinda yayi min dai-dai yadda yayi min." Na fada tare da jan mayafina na kwanta, kashe hasken tantin suka yi, a Sannun na soma jin wani irin sanyin yana shiga jikina. A hankali barci mara dadi ya dauke ni.
"Barka da zuwa! Yau Allah ya nufa kin tuna Ni?" A hankali na juya ina kallon shi. Ka rasawa kusa dashi nayi, sannan na zauna ina kallon shi. Kuka ne ya kwace min, bai hanani ba. Kuma bai rarrashe ni ba, haka nayi kukan har na gaji, mika min ruwa yayi nasha, tare da sauke ajiyar zuciya.
"Kinyi kokari da kika tsayawa ahalinki, amma don Allah ki tsaya mishi wannan lokacin"
"Kashe min miji yayi a daren me daraja a gurin."
"Shin kin yarda zai kashe miki masoyi? Shin kin amince Mehran zai hanaki farin ciki sabida ranshi? Kina mahauniyar rayuwa, idanun ki sun rufe da son ganin laifin shi. Mutum ne me takatsantsar akan al'ummar shi da kanshi. Ba gama garin maza bane masu aiki da mace. Kinzo a daidai lokacin da ake bukata, Mehran yayi zaman jiranki na tsawon shekaru uku, har yau yana nan bai cire tsammanin ganinki ba.
Dan haka idan kin gadama ki, saurare shi idan baki gadama ba ki kashe shi." Daga haka yayi b'acewar shi, Ni kuma ba farka ina jin sanyi sosai, tare da jin zuciyata tana girgiza.
~~~
Kallon shi Fudail yayi bayan gama mishi bayani akan rikicin da ya balle a fada yau, sai ga dattawan fada zasu daku.
"Akan me?" Ya tambaya tare da bude Alqur'an, yana dubawa.
"Wai akan Amir Hood yace musu Jasrah ce ta cancanci zama Matarka sauran yaran su, kuwa su tsaya a matsayin Kwarkwarorin ka, shine suka ce basu yarda ba, sai dai dukkan su. Su rasaka"
"Hmm!" Ya cigaba da abinda yake dan ba zai iya magana ba, yana gamawa ya kalli Fudail yace mishi.
"Anne ta sami labarin abinda ya faru?"
"A'a ban gaya mata ba" inji Fudail,
"Amma kuma me yasa?" Ya tambaye shi yana me kafe shi da fararren idanun shi.
Kwarjini yayi mishi, dan haka ya sunkuyar da kanshi, tare da cewa.
"Afwa!"
"Ka gaya mata yanzun!"
"Insha Allah!" Sannan ya juya ya bar falon, har yanzun Sultanah Fazilatul nisa fushi take da Mehran.
Duk da har yanzu bai gaya mata baya abinda yake zargan shi, amma ta kasa magana sai ma zuba mishi ido da Tayi, shi kuma hakan yana mishi ciwo, dan da yana cikin walwala da manta Ikram, amma yanzun fushin Sultanah ya saka shi jin kamar bayi da kowa a duniya, kuma baya iya jure kowani irin fushi, ya sha zuwa ya bata hakuri ya mata magana yadda zata fahimta karshe idan ya shiga dakin sai ya rasa yadda zai mata magana, ya wanke kanshi. Koda ya isa gabanta ma, sai ya rasa tacewa duk ta cika mishi ido. Shi yasa ya hakura da gaya mata gaskiyar ma tunda baya iya magana a gabanta.
Shafa kanshi yayi yana me jin babu dadi akan haka, dan ya gaji da shirun da take mishi. Ajiye Alqur'anin yayi tare da nufar hanyar d'akinta, ya same ta akan abin sallah, tana addu'o'in. Zama yayi har ya kai karshe, sanan ya kalle ta, ganin yadda ta share shi kamar baya gurin, ya sashi karasawa kusa da ita, ya riko hannunta cikin tsannanin damuwa, sannan ya bude bakin shi wanda yake ji kamar.....
*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
24
Ji yayi kamar an cika mishi iska a bakin shi, tare da rashin sanin madafa. Shiru yayi tare da sunkuyar da kanshi yayi tare da damke hannunta, haka ya tabbatar mata da hakuri yake son bata, amma sabida rashin iya mu'amala da mutane ya saka shi kasa ko magana, sai dai idanun shi da suka yi jajjur, jijjiyar goshin shi sun mike rad'a rad'a.
Had'iye yawun yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa, riko hannun shi tayi sannan ta kalle shi cikin idanu.
"Dole ka koyi rarrashi! Dole bakin ka ya iya fadar ayi hakuri! Wajibi ne bakinka ya iya fahimtar da mutane abinda basu Fahimta ba.
Aamaan dole ka koyi kula da mace, ba kana son Ikram ba?"
A bazata tambayar yazo mishi dan haka yayi maza ya d'ago kanshi