Header Ads
Showing 228001 words to 231000 words out of 274096 words

Chapter 77 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1350

Ads at the middle of Article

kallon yadda take kokarin barin gurin.
"Zauna!"
Zama tayi tana kallon shi, sake shanye ruwan yayi sannan ya mika mata tare da cewa.
"Kara min!" Ta kuma zuba mishi ya shanye, sannan ta kuma zuba mishi ya shanye, kafin yace mata.
"Ban taso da kowa ba, haka nayi rayuwa cikin kaɗaici da bani umarni nayi kaza nayi kaza."


Shiru yayi tare da lumshe idanun shi kafin ya bude a kanta, yana faɗin.
"Lokacin da ta shigo rayuwata ta sha wahala sosai, ta sha ukuba, ni kaina nasan na bata azaba da hannuna, amma kuma ta tafi ta barni da ciwon da ba zai tab'a warkewa ba, ya zaki ji idan aka ce miki abinda kake matukar kauna bai da inganci?"


"Idan har kaunar nakewa abun taya zan damu da batun mutane, Sultan Mehran karka daka ta mutanen duniya haka suke su kashe kashe ka, da ranka ba abun damuwa bane."


Tagwayen ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon ta, sannan yace mata.
"Anneh! Tasan ita ta haife ni ta cilla rayuwata cikin gararin? Laifin Anneh yana da yawa, domin Ikram ce ta sani fahimtar kome akanta, shin zan iya yafewa Anneh, ta kashe mahaifina sabida mulki ni kuma tana son ta kashe abin da za a haifa min taya zan iya dauke kai na akan abinda ta aikata?


Hada baki tayi da ku zaku kashe abin cikin Azizatul Nissah fa, Kinga kuwa dole naji babu dad'i."
Cike da mamaki take kallon shi sannan tace mishi.
"Wallahi bana son zama a cikin wannan masarautan amma sanin cewa nan ne zaman lafiya na, ya sani amincewa na zauna da kai. Na rantse da Allah wanda babu wani sarki sai shi, Sultan Mehran, Anneh bata tab'a tunanin tayi maka haka ba, bari kaji abinda ya faru."


" Bana son jin kome, tashi ki tafi kawai" ya faɗa mata, babu musu ta mike tare da mishi sallama.


Cikin damuwa ta nufi hanyar barin gurin, kallon Fudail tayi sannan tace mishi.
"Yaki saurarona, ban san me haka yake nufi ba, dama haka yake da kafiya?"
"Rashin Ikram ce ya kuma mai dashi zuwa haka"
"Tana ina ne yanzun?"ta tambaye shi.
"Tana can Merocco, ana shirin bikinta da Amir Rahil, dan uwanta ne" ya bata amsa,
"Toh amma haka zamu zuba ido muna kallon shi babu me iya tankwara shi akan abinda yake aikatawa? Ni yanzun idan nace zan tafi can, zai yi wuya ya barni na tafi amma don Allah kayi wani abu, sannan a kaiwa Anneh bayinta domin jikin girma da damuwa zai mata yawa, idan aka kai mata mutane tana jin motsin su zata rage damuwa."


Gyada mata kai yayi sannan yace mata.
"Toh ya zamu yi da Mehran idan ya fahimci mun kai mata bayi?"
"Karka damu, zan gyara kome Insha Allah. Sannan ka sami lokaci ka bani labarin Ikram, tayu na dauki wani abu daga cikin halayyar ta."


Gyada mata kai yayi sannan suka yi sakayi sallama, ta bar gurin. Cike da gamsuwa. Idan baka iya kuka ba aka ce uwarka ce bata mutu ba, dan haka Sawda tayi amfani da wasu dabi'a tare da bin bayan Mahaifiyarshi domin samun kusanci da ita.


Tun daga ranar ta maida gurin shi gurin hirar ta, dukda tana yawan mishi shirme haka yasa shi jin zai iya sawa a dawo da Mahaifiyar shi, tunda itama Sawda tayi kokarin ganin ya fahimci gaskiya, sanan itama tana kokarin zuwa har inda Sultanah Fazilatul nisa take, tana zama da ita.


~~
Kallon kakan shi yayi wanda ya haifi Mahaifiyarshi, kafin ya shiga wasa da kofin shayin da aka bashi ya cigaba da cewa.
"Insha Allah zan yi yadda kace, sai dai zuciyata ba zata ji dadi ba,"
"Ka gwada Rahil zaka sami nutsuwa, kuma itama zata girmama al'amarin ka, zata kuma gane kai mutum ne me nagarta, amma idan ka nuna mata kai Kanka kake so zayi wuya baka samu tangarda da ita ba! Amma kayi nazari da kai."


Kai kofin shayin yayi sannan ya kurba, mik'ewa yayi tare da cewa.
"Zan koma"
A hankali ya mike tare da barin gidan kakan shi, wani irin tausayi ya bashi, yana son Ikram amma kuma shi a nashi tunanin ya hakura da ita, badan kome ba, sai dan yadda tazo jiya ta gaishe da kakan da ya kalle ta sannan tace mata.
"Bilqisul Ikram! Ya batun shirye shiryen bikin ku, naga anata tura sakon gayyata"
Matse hannun ta, tayi tare da sunkuyar da kanta sannan tace mishi.
"Ana kan shirin."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ke baki shirya bane"
Matse hannunta tayi kamar zata karya shi.
"Ina kai"
Kura mata ido yayi sai ya fahimci bata son maganar auren ne baki daya, dan haka ya jefeta da tambayar da ta sata d'ago kai.
"Shin ko kina da wanda kike so ne? Bamu sani ba"
Da sauri ta d'ago kai tana kallon shi sannan ta kuma maida kanta kasa,.kwallar da take kokarin dannewa ne ya shiga sauko mata, a hankali ta saka bayan hannunta ta goge. Murmushi irinta manya yayi mata sannan yace mata.
"Share hawayen ki, kinji kiyi hakuri da abinda muka zab'a miki,.Insha Allah zaki yi farin ciki."
Gyada kai tayi tare da mik'ewa zata bar falon, duk sai yaji babu dad'i musamman yadda ta kasa rike kukanta, dan haka yake ji ba mata adalci ba, dan haka yake ganin koda anyi auren zasu ta azabtar da juna ne ta hanyar amfani da k'iyayyar juna, shafa gemun shi yayi, dan yasan auren kan babu fashi. Kamar anyi an gama ne ma.


.......
Kallon sakon gayyatar Masarautan SAMAIND yayi, sannan ya ajiye shi a gefe kafin yace.
"Zanje da kaina naga meye Mehran ya fini dashi"


Dan haka ya mike tare da nufar cikin gidan, yana shiga ya wuce dakin kakan shi wato Sultan Mu'allim, zama yayi sannan yace mishi.
"Ka tura na ko ina amma ni zan kai na SAMAIND tunda ta zauna a gurin Sarkin Daular, ka ga kenan zamu gayyace shi."


Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Allah ya jikan Iyayen ka, ina son yadda kake nuna jarumtar nan,.dan haka ka shirya gobe Insha Allah ka kai mishi!"


Gyada kai yayi sannan ya mike tare da yin sallamawa kakan, dakin Ikram ya nufa, ya same ta ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta, tayi wani mugun kyau da cika, shi kanshi sai da yaji a aran shi ya dauke ta ya boye ta shi dayan shi. Sai kace Yar tsana, birkitotta yayi yana sumbatar goshinta.


A hankali ya saukar da kanshi zuwa wuyarta.
"Ikram me zan gayawa Saurayin ki domin zan kai mishi sakon gayyata na bikin mu."

Ban san lokacin da na d'ago da mugun sauri ba, nace.
"Mehran? Gurin shi zaka?" Sharr hawaye ya fara zuba, kamar yadda nake tsammanin, kasa tabuka kome nayi, na lumshe idanuna..ina jin wani irin kuka yana zuwa min, shi kuwa abinda yake son gani kenan, dan haka ya zame ni cikin lumana ya fara jagwalgwala ni, rike hannun shi nayi tare da cewa.
"Don Allah,.karka min haka duk tsawon lokacin da na kare kaina, bai isa ba sai lokacin da ya rage taki kadan kace zaka kutsa min."


Janye jikin shi yayi sannan ya sauka a gadon, tare da fita zuwa dakin Sultanah Balkisu Ikram, sun jima suna hira kafin yayi mata sallama. Tunda ya fita nake kuka. Domin yau nake jin wani irin kewar Mehran, ban tab'a sanin cewa na haukace akan Mehran ba sai da yace min zai tafi gurin shi, naji kamar na cire zuciyata na bashi ya kai mishi, haka Izmah da Nimra suka shigo min itama kallona take, tare da cewa.
"Naji wai Amir Rahil zai tafi SAMAIND, amma zan bashi sako ya kaiwa Fudail."
Gyada mata kai nayi, sannan na juya musu baya na kwanta ina ajiyar zuciya, har barci ya dauke ni, ban farka ba sai da dare ya raba sannan na nufi ban daki nayi alola, sannan nazo na gabatar da sallar nafilla, na jima i a gayawa Allah kuka na, ina kuma niman a gaji a gare shi, kwallar da nake danne su, suka zuba min, tabbas so masifa
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


02


Kaiwa yake yana komowa, tsabar yaji haushin abinda ya faru. Jin cidan hadari tare da rugugi ya sashi zare ido cikin takaici da bakin ciki.
"Duk irin zaman da muka yi da.". Bude kofar shi da aka yi yasa shi had'iye sauran maganar da da zai yi, ya zubawa kofar ido. Shigowa tayi tare da ajiye mishi ruwa. Sunkuyar da kai tayi cikin girmamawa tace mishi.
"Sultan MEHRAN gashi."


Kallon ta yayi tare da tuna abinda Abrad yayi mishi dan haka ya a nufi ruwan bai ce mata kome ba, ya dauka ya shanye tass. Ya ajiye kofin kafin ya zauna yana kallon ta.
"Me yasa yayi min haka?"
Kallon shi tayi a razane tare da ja da baya, tana girgiza mishi kai.
"Ni."
"Tambayar ki nake zaki dawo min da tambaya na" wani shegen tsoro ne ya lullube ta, tare da zaro idanu waje, jikinta yana rawa. Tabbas duk rayuwarta da tayi bata tab'a ganin wanda iya tsawar shi abar firgita ce kamar Mehran.


Shin dan ya kasance Shugaba ne? Koko dan ya kasance Zaki ne kisabo, wallahi ita har tsoron had'a idanu take dashi. Ganin taki fita ya sashi fahimtar akwai abinda take buƙata, bai tsaya da tunanin shi ba, yaji marar shi kamar an daure mishi. Wani azazzaben sha'awar kasancewa da mace ya taso mishi. Kura mata ido yayi ganin yadda take kallon shi. Komawa yayi saman kujeran ya zube yana sauke numfashin sa.


A hankali ta tako gaban shi, tare da tsayawa tana kallon yadda yake lumshe idanun shi, wato shi ba zai kira mace ta taimaka mishi ba, ya gwammace koda zai mutu ne gwara ya mutum, zare kayan jikinta tayi suka zube a kasa. Sannan ya taimaka mishi suka shiga d'akin.


A wannan lokacin shi kanshi idan ka tambaye shi wani hali yake ciki bai sani ba, amma tabbas yaji a ranshi yana kwance da mace. Sai dai har yau kamar can baya da yaki matan dan kanshi ya kyamaci haka a ranshi. Duk da kyamar bai hana shi buga mata isa ba. Ya kasance ta da iya karfin shi da lafiyarta, tun tana kallon haka a matsayin abin da bai kai ya kawo ba, har ita da kanta ta fara dukar shi tana kuka.


Shi kuma wai yayi haka bane dan lafiyar shi, haka ya faru ne dan abinda ta bashi ya sha, shi yasa ya rasa tunanin shi ya hake mata Sosai. Komawa gefe yayi tare da kwanciya rub da ciki. A hankali barci me nauyi ya dauke shi. Kallon shi tayi sannan ta mike a hankali. Bata tsaya wanka a dakin shi ba, ta saka kayanta tare da fita daga d'akin bayan ta ajiye mishi wani tambarin da zai iya wargaza mishi kome har karshen rayuwar shi.


~~~
Sai da ruwan nan ya kare tsaf akan Fudail ya shigo Masarautan, koda ya shiga shashin sa ya nufa yayi wanka da ruwan zafi sannan yana wankan tare da murmushin abinda Mehran yayi mishi bai wani damu can ba, sabida ko shi aka yiwa haka iya hukuncin da zai yanke kenan.
Dan haka babban abinda yake shirin akan Azizatul Nissah ce.


~~~
Munyi tafiya me nisa wanda muka bar yankin Farisa sannan muka nufi kuduncin jazziratul Arab, anan muka yada Zango. Tunda muka tsaya aka gama shirya mana tantin mu. Na shiga gurin Sultanah Amrah, na zauna duk da ba hira muke ba, amma kuma haka yana sani jin kamar ina tare da Ammyn na ne, dan haka bayan munyi sallah na kwanta a gurin, ita kuma ta cigaba da abinda take, lokaci zuwa lokaci tana kallon yadda nake barci.


Hawaye ne ya zubo mata, ta girgiza kai sannan ta cigaba da aikinta, tana tuna abubuwa dayawa akan yaranta da mulki yasa ta manta da su. Tabbas mulki matukar baka nemi Izni Allah akan shi ba, zai iya kai ka ya baro ta,


Kamar yadda ya kaita ya baro ta, sai dai ta wani gefen zata iya godewa Allah tunda akwai Ikram da Ilham, Yar gidan Abrad. Murmushi tayi bayan ta shafa kanta, tana me jin kewar Yaran ta.

... Zan iya cewa barcin da nayi me cike da gajiya da mafarkai marasa kyau da dad'i, karshe dai haka na farka da sunan Mehran. Da gudu Rahil ya shigo tantin. Da sauri ya iso gabana, fadawa jikin shi nayi ina haki. "Me ya faru?" "Mehran!" Na fada kamar zanyi kuka. Juyar da kan shi yayi. "Ba zaki daina kwadayin ganin shi ba?" "Karka raba ni da shi, zuciyata halittar shi ce." Matse bakina yayi idanun shi cike da kwalla. "Ni kuma sabida ke aka halicce ni, ina sonki Ikram. Nasan idan ba zama daya muka yi ba, ba zaki daina kwadayin shi ba" ya faɗa bayan ya cire hannunsa a bakina, kokarin hada bakin mu yake na kawar da kaina. "Meye kike nufi? Ba zaki." Ture shi nayi tare da mik'ewa, ya kuma tasowa yana kallona. Kamar zai yi kuka yace.
"Meye yafi Ni dashi? Meye na rasa da ba zaki amshi tayi na ba, wallahi yau sai na dasa miki kaunata a ranki." Fada sosai muka yi da Rahil domin ya kafe sai ya fahimtar dani yadda yake sona. Ni kuma na rantse ba zan yarda da wannan tunanin na shi ba haka muka gama dakyar na kwaci kai na.


Sam na kasa nutsuwa a raina, domin kuwa, haushina yake ji kamar ya kashe ni, bayan fitar shi Sultanah Amratu ta shigo, fadawa nayi jikinta ina kuka. Tare da cusa kai na a jikinta.
"Zuwa yanzun ya kamata ki cire Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran, a ranki domin kwanaki ƙalilan zaki kasance matar Rahil. Don ki daina tunawa da sultan Aamaan."


Kallonta nayi baki sake, kafin na sauke idanuna kasa, ina kuka.
"Ummyn!" Yatsar hannunta ta saka min akan bakina, tare da girgiza min kai.
"Kowa yasan cewa kece kwarin gwiwar shi, ki taimaka ki sauko ayi kome cikin ruwan sanyi."


Hawayen da nake tarewa suka daga cikin idanuna, na kasa magana baki daya sai kallonta nake.
"Tsarin masarautar mu, cike yake da kawaici da YAKANA karki yarda ahalin Mahaifinki su fahimci kin sayar da zuciyarki ga wanin su. Domin haka tilin abin kunya ce gare mu!"


"Toh dole ne sai na rayu cikin mulki? Me yasa ba zaku gan.." d'aga min hannun tayi tare da kallon, yadda bakina yake rawa. Kifa kai nayi a tafin hannuna, na fashe da kuka. Ina girgiza kai,


Tashi tayi tare da bar min tantin kuma ta hana kowa shigo min, domin tana ganin matukar suka shigo min zan iya tsarewa. Gurin yan uwan Baba na, ta nufa suka tattauna. Anan suka ajiye shawara ita zata wuce Asakandariya su kuma su wuce dani can Merocco. Idan ita mace ce mai rauni tausayina zai iya sakawa ta bani abinda nake so.


Su kuma ahalin mahaifina babu wannan yanayin a tare dasu, dan haka su tafi dani. Bayan ta dawo ne, take kallon yadda na kifa kai ka a saman gwiwar kafana.
"Zaku wuce Merocco."
Da sauri na d'ago kai na, zanyi magana ya juya min baya bata bani damar ma tambayarta ba, ta cigaba da abinda take, ni kai na nasan ba zan iya tababa da ita ba, amma kuma ya kamata su fahimci abinda nake so. Bayan mun huta aka kuma tadda tafiyar. Ina ji ina gani ta tafi da Nimrah.


Ni kuma muka tafi da Izmah, bayan mun sha kuka. Tunda muka dauki hanya, banzan can yake wani shige min. Ko kallon shi banyi ba, har muka wuni a hanyar, dab Magarib muka shiga garin, wanda tun kafin mu iso labari ya iso musu muna kan hanyar mu, sakamakon wani mahayi da aka turo shi.


Dan haka garin ya kasance kamar ana bikin sallah, wani irin biki ake me cike da shagali. Haka muka isa har fadan, inda aka muka yada zango a falon Sultan Mu'allim. Mika min hannun yyi. Da sauri na isa gare shi. Ina isa na zube gwiwata a kasa, kai na a bisa kafadar shi, na sake kuka me cin rai. Takaici yasa Rahil fita a gidan.


Kuka nake wanda idan ka tambaye ni ba zance maka ga abinda aka min ba, amma kuma a cikin raina, ina kuka ne domin na rasa Mehran. Yadda nake kukan ya sashi sake murmushin jin dadin. Sannan ya shafa kai na, yace.
"Kiyi hakuri! Haka muke tsara miki baki rayuwar. Da karen layi gwara Zakin gidanka koda kuwa zaka zane shi da bulala ne, kiyi dan mahaifanki da kanwarki. Ba akan ki da soyayyar ki ba. Mun rigada mun yanke kuma al'adunmu sun sha banban da kowane, mukan iya binne abinda muke so! Mukan iya boye abinda muke kauna, matukar hakan zai bamu damar fuskantar matsalar.


A tsarin mu, bai zama dole mace ta samu abinda take so ba, matukar zata bawa Mulkin mu. Gudunmawa dan haka na zab'i ra'ayin shi sabida ki bashi gudunmawa. Yanayin ku yayi daidai da mulkin, abinda ake bukata domin mulki kin hada, dan haka ki amshi Rahil a matsayin abokin rayuwar ki."


Hawaye ne ya shiga zuba min, na kasa magana tare da sunkuyar da kaina, domin yayi min kwarjini. Haka aka fitar dani har dakin Bilqisul Ikram, tankwarata. Shafa kaina tayi sannan ta kira amintattun bayin ta, suka shiga dani ban daki. Aka hada min wani irin ruwan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads