Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 274096 words

Chapter 24 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1382

Ads at the middle of Article

Ko damuwa bai yi ba, da Fudail ya dauke ta.


Akan fuskar shi zaka Fahimci ai damu ba, amma a cikin ran shi kuwa bakin ciki ne da kishi kamar ya rufe Fudail da duka, amma ya matse. Bayan sun gama shiga da ita cikin gidan,


"Na shiga uku! Wannan yarinya zata kashe ni." Ya faɗa a sanyayye, kamar me rad'a.


Sunyi kokarin ta farka amma barci ya dauke ta, dan haka suka fito, dan dole Fudail yayi musu sallama ya bar kauyen zuwa wajen garin.
Yana tafiya amma gabaki daya nazarin abinda ya faru yake, anya Mehran bashi ya kawo mata dauki ba, toh amma me yasa bai damu ba? Kawai ya share batun baki daya.


..... Bayan tafiyar shi ne Baban Mahlika yace mishi.
"Sultan zaka iya shiga ka duba ta"
Tabe baki yayi tare da share batun kamar baya gurin, har yamma lokacin da aka yi sallah isha Fudail ya dawo, suka kafa hira. Duk da yana lura da yadda take mishi kallon kurilla ba.


Ganin kallon yaki karewa ne ya d'aga mata gira daya,
"Ahhh" na fada duk suka zuba min ido,
"Lafiya!"
Idanun yana kan shi baki sake nace musu.
"Babu!"
Cigaba aka yi da hira, aka Cigaba da hira, can idanun mu ya kuma sarkafewa da juna, kyafta min idanu yayi. Da sauri na juya baya, ina juyawa ya d'aga min giran shi dukka biyu.
"Wayyo Allah na!"
"Lafiya suka tambaye ni a razane tare leka inda nake zaune.
"Wani abu ne da yake yawo a kafana!"
Nan aka shiga dubawa, muna hada ido ya sake min murmushi,
Haka suka gama niman basu samu ba. Tsakanin shi da Allah yayi ta manna min hauka, kafin kace kwabo kasa nutsuwa. Baba ne ya fahimci abinda Mehran yake min dan haka ya mike tare da mana sai da safe. Fudail ne yaki mik'ewa dan bai san meke faruwa ba, sai da Baba ya kira shi tare da bashi Shawaran ya bawa Sultan guri. Yana ganin babu kowa daga Ni sai shi.
Lumshe idanun shi yayi tare da kurawa wutar idanu.


Ganin babu abokan hira yasa nima na mike zan bar gurin, dole ta gaban shi zan wuce. Ina zuwa gaban shi ya saka min kafa, zuɓewa nayi a jikin shi. Fuskar mu tana kallon juna. Da sauri na fara kokarin sauka daga jikin shi. Kara matse ni yayi yana kallon cikin idanuna.


Ganin zai azabtar dani da wannan idanun shi ruwan zaiba, ya sani dukar da kaina tare da dunkule hannuna a kirjin shi.
"Mehran!"
"Hmm!"
"Sake ni kar wani ya ganmu"
"Ahmm"
"Don Allah ka sake ni kar wani ya ganmu naji kunya"
"Kunya?!"
Ya tambaye ni, d'ago kai nayi tare da kallon shi, aikuwa abinda nake gudu ne ya faru, domin idanun mu yana haduwa da juna, take naji kamar an daki gabobbina, ya sake lokaci guda na ji kamar bani da wata kuzari a jikina, kwanciya nayi a jikin shi, tare da sauke wata irin ajiyar zuciya.
"Karfe biyar, na asuba ina jiranki!"
Yayi maganar kamar me rad'a.
"Humm! Ina zamu je!"
Matse ni yayi. Nace.
"Ouch!"
Bakin shi ya kai kunne na, tare da sake min wani irin numfashi. Cusa kai na nayi kirjin shi ina shaƙar kamshin turaren shi.
"Meehraan!"
"Amaaahhhh!"
Yaja sunan kamar yadda na ja nashi.
"Don Allah ka daina haramun ne, mace baliga da namiji baligi suka haɗu, na ukun su shaidan ne!"
"Hmm!"
Ƙoƙarin mik'ewa nake amma kamar wacce a ke manna ni da jikin shi na kasa koda motsawa, a hankali ya mike tare da ɗaukata, bai zame ko ina ba, sai masaukin shi dani.
" Meehhh"
Kallona yayi tare da isa bakin kofar Masu kula da kofar suka bude, shiga yayi dani a falon me dauke da kilishi ya..... *Ya dai dan kurma🤔☹️😏*


```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 34


A hankali ya shimfida ni a saman kilishin sannan ya koma gefe yana me cire takalmin kafana, d'gowa nayi ina kallon shi. Lumshe idanun shi yayi tare da Cigaba da cire min, sannan ya mike ya nufi inda wutar itaccen yake ci, yana me zare kayan jikin shi.


Tagwayen ajiyar zuciya nake saukewa, gyara wutar yayi sannan ya dawo kusa dani ya zauna. Tare da kurawa tagar dakin ido, tashi yayi tare da sake labulayen, sannan yayi irin kwanciyar sarakuna, yana wasa da gashin kai na. Kallon shi nayi bai kalle ni ba,. A hankali barci yayi gaba dani. Kusan har tsakiyar dare yana zaune a gurin, juyawan da nayi ne ya sashi kallon yadda na farka, mik'ewa nayi tare da tattara mayafina, na nufi ban dakin dake cikin dakin shi nayi alola sannan nazo na fara sallah nafilla. Har kusan karfe uku ina sallah.


Ina idarwa na kwanta, sai lokacin na lura da shima yayi barci, a dan takure. Shiga dakin nayi da lallubar na dauko bargon shi. Juyawar da zanyi naga mutum a duhu, ihu na ware zanyi ya rufe min bakina, tare da cewa.
"Tafi can!"
Ajiyar zuciya na sauke sannan nace.
"Wallahi ka bani tsoro daga yau kayi sallama kafin ka shiga guri."

Share ni yayi ya koma bakin gadon shi ya shiga cire kayan shi, da sauri na juya mishi baya, ban daki ya nufa, ya kwara ruwan sanyi.


Dakyar ya fito, yana rawan sanyi, ina tsaye sake da baki lokacin da naji yana watsa ruwan sanyi a jikin shi, kamar wani gungumen dutse ya jibgu a gadon shi, lokaci guda.
Girgiza kai nayi tare da cewa.
"Toh kashi nayi wallahi bazan iya wanka ba, balle kai."


Rufa mishi bargon na fara yi, ya fisgo hannuna na fada kirjin shi.
"Sanyi!"
Ya fada tare da kaduwar sanyi hakoran shi suna dukar juna, janyo Ni yayi sosai, har cikin bargon, niman yadda zai rabu da sanyin yake.
"Meehhh!"
Hancin shi ya shiga gogawa da nawa, lokaci guda ya fara ƙoƙarin shigewa jikina yake, wani irin azzabbrn tsoro ne ya shige ni. Sabida yadda yake wurgi da kayan jikina zaka rantse da Allah, wani abu yake son yi dani, nan kuwa rage sanyin shi yake son yi, a hankali ya rabani da kayan jikina, sai dan abinda nake daure kirjina( wato kamar yadine kamar towel, shine madadin bra.) Shigewa jikina yayi tare da boye fuskar shi a wuyana zuwa kirjina, goga fuskar shi yake kamar zai shiɗe.


Tausayi ya bani, ban san lokacin da na rungumo shi ba, tare da kifa kan shi a tsakanin kirjina da wuyata. Dakyar barci ya dauke shi, kamar yaro karami haka ya shige min, kasa barci nayi ina kallon shi, tare da tunawa da Noman da Airan, hawaye ne ya shiga zuba min daga cikin idanuna, sakamakon tuna kanwata da masoyina. ina gurin har aka kira sallah farko, tashi nayi a hankali na zare shi daga jikina.
Na nufi ban daki nayi tsarki da alola, sannan na tsince kayana na saka, kafin na gabatar da rakatul firj.


Ina idarwa na gabatar da sallah asuba, na jima ina addu'o'in. Kafin ya motsa tare da kallon yadda haske yake shigowa dakin.


Ji nayi a jikina yana kallona, dan haka ban juya ba ne Cigaba da Addu'a, ina idarwa na mike tare da dauke sauran kayana da suke kasa na fara saka, sannan na janyo matashin dake gefen shi zan d'an kwanta, zubur ya mike zaune,


Jan kwarjallen shi yayi tare da gyara zaman shi ya sauka daga gadon, ya nufi ban daki can ya fito tare da kallona yana jiran na nuna mishi kayan shi, ban kula shi ba sai dai nasan ana sanyi dan haka na duba mishi wata ƙatuwar rigarshi,.tare da sauran kayan shi takalmi da hula.


Kallona yake ina ajiye mishi, ban san ya taho har inda nake ba, sai da na d'ago kai na, kawai Naji bakin shi a goshina. Da sauri na d'aga kaina ina kallon shi.


B'ata rai yayi kamar bashi ba tare da, daukar kayan shi zai saka na fita na bashi guri.
~~
Tunda Baba yace ya basu guri ya nufi makwancin shi, bai iya kwanciya ba, kawai dai yana tsaye a jikin taga, yana kallon su. Bai taba sanin so zai mishi illa har haka ba sai yau, hawaye yaji yana sauko mishi daki daki.


Yana tsaye har Mehran ya dauki Ikram, suka shige basu yana tsaye a gurin har asuba, sannan ya tafi sallah. Yana masallaci a zaune Baba yace mishi.
"Kayi hakuri da zanen ƙaddara, ta zana ka a cikin su. Amma ba yana nufin zaka sami hakan ba, dashi ta dace."


"Baba baya sonta! Ni nafi dacewa da ita, bana son na rasa ta." Ya faɗa a raunane.
"Zaka rasa ta ai! Kuma mafi girman rashin ma kuwa, kayi hakuri gaskiya."


Daga haka bai kuma magana ba, har garin ya fara haske. Yana fitowa masalaci ya hango su, zasu shiga daji. Kirjin shi ne yayi nauyi, yana kallon su har suka kulewa ganin shi.


Kasa hakuri yayi yabi bayan sun, sai da suka yi tafiya me nisa sannan suka tsaya a bakin wani guri me kamar tsuni (Mountain)


Gatarin shi ya dauka tare da shiga daji ya saro itaccen da zasu zauna, sannan yazo ya hura musu wuta, tunda suka zauna a bakin tsunin yake cikin yanayin farin ciki, ba zaka tab'a fahimtar haka ba, dan fuskar tana nan a turnike, kallon yadda take kallon wutar bakinta yana motsi yayi.


Yanayin bakin burge shi yake, dauke kai yayi tare da d'aga kan shi yana shaƙar iska, kallon hanyar da suna biyo yayi, bai ga alamar kowa ba, sai dai kuma lokaci zuwa lokaci yana jin alamar kamar ana kusanto su.
"Ke dawo nan!"
Ya faɗa mata haka, da sauri na dawo kusa dashi, kallon yadda ganyayyekin bishiyar da muke zaune yake saukowa ne, can kuma ya lafa, zaman mu a tare ya haifar mana da wani irin kusancin sosai domin muna gogan juna.


Mun jima a haka babu wanda yake iya ko motsi, d'an gogan kafadana yayi na d'ago kai da sauri zan lalle shi, fuskar mu ya haɗu da juna, idanun shi cikin nawa, da sauri na rufe idanuna, murmushi yayi tare da shafa fuskar na. Janye daga jikin shi nayi tare da mik'ewa, sai ji nayi kamar an wurgo dutse daga sama, dib ya sauka a tsakanin mu.


Baya nayi tare da kallon katon halittar birin da ya diro gaban mu, juyawa yayi yana kallona, tare da wangale baki ya fasa ihun da dajin sai da ya amsa baki daya, a razane na toshe kunne na. Tab'a shi Mehran yayi.


A fusace ya juya yana huci, kallon juna suka yi tare da juyawa dukkan sun, suka kalle ni.
Sabida ba fara ƙoƙarin juyawa da gudu, gatarin shi ta zare a cikin rigar sanyin shi, yayi kan birin suka kaure da azzabbrn fada.
"Karki yarda ki gudu!"
Tabbas rayuwar duniyar nan cike yake da al'ajabi, domin kuwa Mehran ya kafe ya nace, yana fada da biri ne sabida ya nufi kan Ikram, dan haka cikin hauka da fusata birin ya juya ga Ikram wacce take kokarin boya a bayan bishiya.naushi daya yayiwa bishiyar ya zube.


Nan kuwa Mehran ya kuntatta rayuwar shi da sara, ihu yayi tare da dukar kirjin shi, duk yadda yaso guduwa tare da niman tsira da rayuwar shi Mehran ya hana, sai da ta kai birin nan ya fadi akan gwiwata shi ya zube a gurin, sannan Mehran ya kyale shi, kallo yayi lokacin da ya haura saman birin ya tsaya, tare da goge jinin da yake diga daga goshinsa zuwa kan hancin shi.


Ni wallahi tsoro ma ya bani, na fara ja da baya, yarda gatarin yayi tare da mika min hannun, sai ji nayi anyi sama dani.. "Aamahhhhh!"
Ya kwala min kira, yana kallon yadda biri suke wasan kura ni, ihu nake ina niman daukin amma ina juyawa yayi da mugun gudu, ya koma gurin kayan mu.


Yana zuwa ya dauki kwari da baka, ya kuma shigowa dajin da gudu, daga nesa ya daidaici birin da yake rike da ni ya sake mishi kwari har uku, timmmm ya fado daga sama. Aikuwa suka kuma fusata gashi nan dai suna ganin shi dan mitsitsi sai tarin bala'i ya kuntatta rayuwar su, ya hana su sake, haka yana harbin su yana binsu da takobi, bai cika son fada da takobi ba. Amma matukar ya dauki takobin toh kuwa zai raba mutum biyu ne.


Duk wannan fadar da ake akan Idanun Fudail yana son yaga gazawar Mehran, amma abu ya ci tura asalima kara tunzura shi hakan da suke yi yayi.


Birai dai ganin Mehran yayi musu mugun barna yasa suka fara gudun ceton ran su, tare da barin gurin, dakyar Allah ya kwace su, bayan sun kai Ni karshe tsunin. Wanda kasan shi yake dauke da wata irin ruwa me gudana, (spring water) ko nace korama.

Ganin haka yasa shi zuwa da gudu, tare da wutsar da kayan fadan yana mika min hannun.
"Zo nan! Karki damu ina tare dake, da dad'i ko ba dad'i."


"Baka da tausayi, ji yadda kake ta kashe dabobbi, haka idan da mutane ne suka kawo min farmaki haka zaka kashe su. Mehran ka kyale Ni nayi."
"Karki sake ki fada domin kankara ne a cikin ruwan."
"Ka tafi bana son ganin ka!"
Ban san ya aka yi tsantsi ya akwashe Ni ba.
"Meehraan!!!!!!"
Da gudu ya biyo bayana, tare da kara kaifin gudun shi, har ya kasance yaci mani, kafin ya riko ni, mun fasa ƙanƙarar da ta rufe saman ruwan baki daya.


Muka fada cikin ruwan, me masifar sanyin, riko hannuna yayi tare da kamo ni mika fada kokuwar fitowa, dakyar muka fasa wani gurin, sannan muna fito waje, kallon yadda nake numfashi yayi, ya fitar dani wajen baki daya, daukana yayi tare da sakani a kan kafadar shi, yaga zan takura mishi dan haka goyani yayi. Ya nufi kauyen dan yabi bakin gaɓar kogin ne har cikin kauyen, da azabar gudu.


Koda ya isa dani na suma, karb'a na Baba yayi. Tare da bashi wani ruwan magani da zafi, yana sha shina ya yanki jiki ya fad'i. Murmushi Baba yayi yana mamakin wannan kurman Kaunar.


D'aga shi yayi zai kwantar dashi Fudail ya shigo fuskar shi a turnike, yana kallon Mehran. Tsana da kishi ne suka cika mishi zuciya, tare da kallon yadda muke yi wani irin Fayau.
"Ina suka shiga ne? Dajin mun nan akwai hatsari fa"
"Fada yayi da birai domin yayi musu barna, sosai domin ya kashe babban su, sannan ya kashe su bilhaki."


"Alhamdulillahi! Biran nan sun dame mu, bamu isa muyi noma ba zasu lalata mana, matan mu suka tafi korama diban ruwa, suyi lalata dasu, yaran mu maza idan suka tafi kiwo su kwakule musu idanu su kashe dabobbin mu Sultan Mehran rahama ne a gare mu Allah ya turo shi. Domin tun zuwan shi yake bata kashi da duk wani abun da zai cutar da al'ummar Musulmi. Allah ya bashi tsawon rai yadda zai mulki SAMAIND cikin adalci."


Dakyar ya iya furta "Amin" tare da zuba makaman Mehran, tunda ya kawo ni, nake sume. Shi yayi farka, kuma ya damu sosai. Amma Ikram babu alamar farkawa, tana kwance sai yadda aka yi da ita, shafa kanta yayi cikin tashin hankali ya kalli Maman Mahlika.
"Zata kai Yaushe bata farka ba?"
"Iya wa'adin da Allah ya nufa zata farka."


Kura Ikram idanun yayi cikin damuwa, a hankali ya nufi kanta yana shafa fuskarta. A ranshi kuwa tambayar ta yaƙe.
*Me yasa ba zaki farka haka ba! Me yasa ba zaki takaita barcin nan haka ba? Ina tare dake! Ina kuma tsaye a tare dake! Zan tsaya miki a zahiri da bad'ili. Bilqisul Ikram*


Ya faɗa tare da sumbatar goshinta, yana me jin kamar zuciyar shi zata buga. Motsi kafarta yayi a hankali ta kuma motsawa, ya zata gizo take mishi dan haka ya dauke kan shi, ganin da gaske tashi za tayi ya sashi dauke kai kamar bai ganta ba....
#Mai_Dambu
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

*Wannan shafin naku ne Aunty Mamieh Mom Imam, da MOM Sayyid and Noor 😒😏 Me za ayi da basamuden kun nan*
Page 35


Tarin da nake hade da aman ruwa ya sashi fita daga dakin ma, Baba ne ya shigo yana mamakin halin shi kamar bai damu ba, sai da ya gama bani kulawa sannan yace min.
"Kina jina?"
"Eh!"
"Yawwa sannun taso muje!"
Haka na taso jikina a sanyayye ga ɗan karen sanyin da nake ji, bayan ya nuna min yadda zanyi amfani da ruwan wanka da yadda zan sha, ya fita.


Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads