Header Ads
Showing 96001 words to 99000 words out of 274096 words

Chapter 33 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1391

Ads at the middle of Article

yake kusan yakai girman dakuna uku.


Murmushi tayi tare da cewa.
"Shigo mana! Sultan MEHRAN!"
"Hmm!" Yace kasan makoshinsa, fita suka yi sannan ya shiga, kitchen ɗin, kallon shi tayi sannan ta cigaba da cewa.
"Wannan abincin shine Sultan Abdus Samad yake so! Naso da na rayu kusa da kai na koya maka cin shi!"


Kallonta yayi sannan ya cigaba da kallon yadda take girkin, cikin kwarewa, idanun shine suka shiga ciko da kwalla, yana tuna Yarinyar da take hana idanunta barci sabida shi.yau ta tafi tabar shi! Ajiyar zuciya ya shiga saukewa akai akai, tare da dafe ginin Kitchen din wato inda suke ajiye kome na aikin.
"Da zafi mutumin da muke kaunar kasancewa dashi yayi tafiyar bazata da rayuwar! Sultan kana son Baiwar ka ce?"


Wani irin ajiyar zuciya yake saukewa tare da dafe kirjin shi yayi yana kallon..
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


06
Kallon shi tayi yadda yake kokarin sake kwallar da ta cika mishi idanu.
"Karka sake naga kwallar Bahashimin ya sauka kasa, karka sake naga kwallar Jinin Abbasiyyah ya sauka kasa, idan har jinin dake yawo na Abdus Samad ne toh baka isa naga kuka akan so ba, karka yarda naji duniya ta kira min kai lusari! A koda yaushe buri daya gare ni, Duniya da mutanen Samaind su ambace ka da Shan Sultan Mehran, yau kukan akan so! Me akayi tukun. Idan Ikram rabon kace zata dawo domin Ina sonta har cikin jinin jikina. Idan ba rabonka bace zaka sami matar da zata so ka."


"Ba zata dawo ba!"
Ya faɗa kan shi a kasa, dan yanzun yake jin yana da wacce zata taya shi kuka da murna, kiran nasabar shi yasaka shi jin wani irin yanayi a ranshi.
"Akan wani dalili ba zata dawo ba?"
Ta tambaye shi, hankalin ta yana kan majuyin abincin,
"Sabida sun kashe ta, ita da mijin da zata aura"
Sake abincin tayi tare da kallon shi sannan ta kuma rike abincin, bakinta na rawa.
"Ina Fudail?"
"Baya nan na aike shi"


Wani irin tausayin shi ne ya tsaya mata a ranta, dan haka ta dauke kanta tare da Cigaba da aikinta.
"A gaban mutane dari uku da wani abu,. Suga Sultan Mehran yana kuka don kewar masoyiyar shi?


Na taso inda ake boye so da jin dadi saboda girma da Darajar gidan da ka fito, Shan Sultan Mehran zai iya alaka da baiwa amma bai sama tilas sai ya zurfaffa tunanin shi akanta ba.


Duk da nasan kai namiji ne, kuma zaka bukaci mace a gefenka bana son kayi kuka dan so! Kayi kuka dan suwaye suke tare da kai,kayi kuka dan al'ummar da suke kasar ka.


Karka zurfaffa tunanin akan goben ka, sabida ita din na al'umma ce, kayi tunani da kyau. Ikram ka rasa ba kome ba, dan haka ka dauki haka a matsayin jarabawar ka, karka sake so ya illata lafiyar ka."


"Ammyn ba so bane! Shak'uwa ce, shi yasa na." Wani irin murmushi tai sannan ta juya tana cire abin hannunta, tare da kallon shi.
"Ni kamar uwace a gare ka, tunjiya nasan kana cikin yanayin damuwa, amma na kyale ka sabida ka samu nutsuwar zuciya."
A hankali ya kalle ta a sadadde, sannan ya mai da kanshi kasa, kafin ya juya zai fita.
"Kayi wanka, yanzun zaka karya."
Tsayawa yayi kafin ya fice daga kitchen ɗin, kwalla ta goge kafin ta nufi, waje ta karasa aikin ta, tare da kiran bayi suka tattara, abincin kallon Mahlika tayi sannan tace mata.
"Ya Alima take?" Sake bowl din hannun tayi tare da juyawa a tsorace, tana kallon ta.
"Ki biyo ni d'akina "


Tun da suka shiga dakin kanta a sunkuye, har Fazilatul nisa tayi wanka, ta fito tana shiryawa kanta yake sunkuye, tana gamawa tace mata.
"Baki gaya min ya take ba?"
Zuba gwiwar ta, tayi a kasa tare da sake kuka.
"Don Allah Sultanah Fazilatul nisa kiyi min rai!"


Murmushi tayi sannan tace mata.
"Taya zan miki rai bayan duk wanda zai kusanci Mehran ina sane da fansa yazo dauka a rayuwar shi? Da yau na kashe Alimah bayan nasan da hadin bakinta aka so watsar dani waje, ai da ba a haife ki ba.


Meye nufinku? Kunzo daukar fansa akan laifin da aka yi shi domin tsira da rayuwar ta, Hoyam ta sakata ture ta, domin kawai su kirkiro rigima a tsakanin su."


Sake fashewa da kuka tayi tana me kara kallon Sultanah Fazilatul.
"Sultanah wallahi duk abinda kika sani zanyi."


Murmushi Sultanah Fazilatul tayi sannan tace mata.
"Meye shirin ku anan gidan?"
Jikinta ne ya dauki rawa, sama da can baya.
"Ba zaki gaya min bane ko sai na saka an muku yankan rago dukkan ku!"


Cikin kuka take fadan abinda aka saka su, tare da wulaknta darajar Mehran, mugun aikin da aka sasu ba karamin abu bane, lumshe idanun ta, Fazilatul tayi. Uwace kawai zata iya daukar nauyin tashin hankalin D'anta.


Murmushi tayi sannan tace mata.
"Idan na saka aka kashe ki, kamar na bawa makiya dama su kalubanci Mehran ne, idan na barki a raye su din da suka turo ki sune ajalinki.


Itama Mahaifiyarki da take ta faffutikar, ganin ta turo ki hmm cutar dake zata yi domin amfanin dake za ayi idan bukata ta biya zaki sha mamaki."


Nuna mata Hanyar fita tayi, jikinta a sake, sabida bakin cikin abinda take ji take gani, Alhamdulillahi tana tare dashi ko babu kome zata zame mishi garkuwa.


Fita tayi ta nufi dakin da ya kwana, ta kira shi yana zaune ya kurawa guri guda ido, zama tayi sannan tace mishi.
"Kayi hakuri!"
Wani karamin murmushi yayi wanda bai kai Zuci ba, ya ce mata.
"Nagode!"
"Taso muje ka karya;"
Babu musu ya mike suka fita dashi.
---
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Yanzun ta ya aka yi gobara ta cinye Y'ata da jama'ar ta?" Take ya fara wani irin girgiza, kafin ya fadi.
Jasrah itama kuka take tare da ihu, Goggonta.
Dakyar aka fitar dasu daga filin gidan da ya kone murus, ana kai shi gidan shi ya sake murmushi, tare da cewa.
"Kome ya kammala min"


Dariya suka saka shida Jasrah tare da kamanta abinda suka yi a gaban jama'a, suna dariya tare da cewa ai an yarda dasu.
~~~
Bude idanu nayi ma ganin a saman rumfa, da sauri na duba naga Izmah, ajiyar zuciya na sauke tare da shafa kanta, ina faɗin.
"Duk wuya duk rintsi sai na baki garkuwa!"


"Sarauniyar barci, kin farka?"
D'aga labulen nayi sannan na ce mishi.
"Eh amma yaushe aka dauko mu?" Dariya yayi sannan yace min.
"Karki damu da haka? Zaki ji kome a hankali."


Mika min abinci yayi na kalli abincin sannan naki dauka!
"Kina tunanin ko na saka guba ne?"
"Ai nasan ba zaka zuba guba dan ka kashe ni ba, aiko dan cikar Muradin ka zaka barni a raye."


"Toh tunda kin yarda da haka kici mana!"
"Zanci kai, Abokiyar tafiya ta nake tunanin bata cin abincin irin wannan"
"Toh yayi kyau. Tunda haka ne bari akwai wani nama sai ki bata."


Murmushi nayi sannan na cigaba da cin abincin.
"Ban san sunan ka ba, lokacin sallah yayi?"
"Taya kika san lokacin yayi."
Murmushi nayi mara sauti sannan nace mishi.
"Ka duba sararin samaniya, rana ta raba tsakiya."
"Toh Malama!
Haka muka yi ta musayan kalaman har muka iso garin, kallona yayi sannan yace min.
"Daga yanzun zan miki aika kuma zai zo har inda kike, domin nayiwa Amir Rahil alkawarin zan kawo mishi sabuwar baiwa, kiyi amfani da wannan damar ki kashe min shi.


A sanyayye yadda kowa ba zai kawo hakan ba a ranshi, ina son kiyi aikin nan da wata uku, ki shiga jikin shi yadda babu wanda zai iya fahimtar kome."


Gyada mishi kai nayi, sannan muka shiga cikin birnin da ake kasuwanci, kamar ba gobe. Gaskiya garin yayi min kyau, dan haka ina kallon shi har aka nufi gidan sarautar kasar damu.


"Karki manta kiyi abinda ya kawo ki karki yi tunanin fadawa wata damuwar da zata saka mu hadu a fada."


Gyada mishi kai nayi, tare da jin son garin da yanayin garin yana shiga na, sai da muka ratsa wani gida, muka ci abinci, sannan muka nufi fadar kasar.


An shiga damu, har cikin fadar musamman yadda muka yi shiga na tukurun bayi, muna zuwa muka zube a gaban wani dattijo, wanda yake buga mulki kamar me,


"Amir Sulaiman, har ka dawo daga tafiyar da kayi?" Wani a gefen zubewa gaban Mutumin sannan ya ce mishi.
"Sultan Mu'allim na dawo daga tafiyar da nayi, da fatan zaka saka amshe ni hannun biyu biyu"
Ya faɗa cikin taushin murya.


Kallon shi wasu daga cikin yan fadan suka san halin shi, kallona suke, sannan wasu suka dauke kansu.
"Yarinya daga wani yanki na duniya kike?"
.kallon shi nayi sannan na sunkuyar da kaina, domin ya bani damar magana.
"Daga yankin Afirka ta Tsakiya."
"Meye sunanki!"


"Salwah!"
Kallona suka yi kafin suka ce, min.
"Ita kuma wannan wadar ba?"
"Jasmin"
Na fada a takaice, ina me sunkuyar da kaina.


"Ku kaita shashin bayi kafin a kaita inda zata zauna. wato shashin Sultan Rahil"
"Yanzun za ayi yadda kace"
Haka suka tasa keyar mu, har shashin bayi, muna shiga suka shiga mana dariya, ban yi mamaki ba, sai dai ita Izmah sai ya zama kaman cin zarafin ta suka yi..dan haka na rike hannun ta.


Nuna mana inda zamu zauna akayi sannan aka bamu abinci, na saka hannu zamu, fara ci wata cikin yan matan dakin, tana sanye da jan kaya. Ta kai min duka.
Ban kulata ba,. Na turawa Izmah abincin cikin tsoro ta fara ci, sake kawo min dukka tayi na buge kafarta tare da kai mata duka, sai da kashin kafar yayi tsawa.


"Wayyo Allah! Kafana!"
"Ba rigima nazo nima ba, kowa dan haka ku shiga hankalin ku, nasan halin ku na bayi, dan haka kar wata ta kuma d'aga min murya. Dan zan karya kasusuwan ku!"


"Toh mafadaciya! Sake mata kafarta, ki shirya a kaiki shashin Amir Rahil."
"Toh!" Na sake kafar sannan muka fara cin abincin, muna gamawa na mike tare da nufar hanyar ban daki nayi wanka da alola, ganin na fito zan gabatar da sallah duk sai jikin su yayi masifar sanyi, suka shiga kallon juna ina idarwa nacewa Izmah.
"Muje na taimaka miki kiyi wanka!"
Haka na taimaka mata tana gamawa na fito, nuna mata gurin kwanciya nayi sannan nace mata.
"Ke Yar masunta, duk wacce tayi miki shirme kiyi mata yadda kuke watsawa kifi koma a ruwa. "
Da sauri matar ta leko tana kallona, cike da mamaki rabonta da taji murya irin na shi kusan shekarar ashirin da biyar kenan, ajiyar zuciya ta sauke sannan na fito ina tafiya tana waige na. Har muka fito shashin,.wato akwai wata dabi'a da Abba yake yi, a duk lokacin da ya shiga damuwa, zaka samu ya kai hannun shi baya, yana tafiya. Wannan dabi'ar nakanyi lokaci zuwa lokaci.


Amma ban maida shi ya zama abin dogara na ba, kawai yau na tsinci kai na dayin haka ne, aikuwa ina yi naga abun mamaki, domin duk inda muka wuce Ni ake bi da ido. Da gudu wani mutum yazo ya janyo Ni bayan wani lungu. Zuɓewa yayi a gabana, tare da cewa.
"Ban san ki ba, amma tabbas jinin Ahalin Mu'allim yana yawo a jikin ki, wacece ke?"


Kallon rashin fahimta nayi nashi sannan na juya tare da nufar matar, har muka isa gidan da zata kai ni.


Babban gidane me dauke da manyan dakaru, a hankali na shiga bin bayanta na sami dakarun gidan dukkan su a tsaye, wai ana wasa da Amir Rahil. Sai ihu suke suna tafa mishi.


Shi kuma ya rufe fuskar shi da farin kyale yana niman su, ashe ita matar ta koma gefe, dan laifina a katse wannan haukar.ni kuma ban lura ba, sai ji nayi an kamani tare da sake wata zazzakar murya kamar ba namiji ba.
"Ahah na kama waye?"
Hmm, mara mutuncin kawai sai ji nayi ya kai hannun shi kan nonona ya matsa tare da dumbular shi. Har cikin raina naji zafin abin ban san lokacin da na murɗa hannun shi tare da buga shi da kasa sai da ya fasa wata irina kara, sake juya kan hannun nayi zan karya.
Suka samun takobin akan wuyana.
"Kin san waye kika daka?"
Zubur ya mike tare da zare idanu, yana me cire kyallen a fuskar shi, sannan ya kura min ido.
Gefen bakin shi yana fidda jini, sauke wata irin numfashi yayi, tare da kallon yadda nake fusace.
"Durkusa! Ki bashi hakuri kafin a hukuntaki!"
"A'a barta kawai, a gaban waye ta kayardani? Shin kun gani ne?"


Girgiza mishi kai suka yi sannan ya fashe da dariya kafin ya kira su dukkan su duka koma baya tare da cewa.
"Kunsan m....
Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


07
"Toh tunda babu wanda yaga lokacin da ta makani da kasa a manta batun, kuganta sai kace wata namiji, dan haka muje muji meke tafe da ita."


Ya basu hannu suka tafa, sannan ya zo inda nake tare da goge jinin bakin shi yana faɗin.
"Hmm! Zan miki afuwa sai kin bani hakuri?"
"Hakuri?"
Na kuma tambayar shi, kallon masu tsaron shi yayi sannan ya kane musu ido, yace musu.
"Ko ba haka ba?"
"Eh ki bada hakuri sai mu kyale ki"
Ganin suna b'ata min lokaci nacewa matar.
"Ko zaki taimaka ki kai Ni shashin yarima Rahil!"
Cikin wani irin jin dadi ya gyara kwalar rigar shi, tare da kallon na ya nuna min kanshi da hannun shi yana faɗin.
"Gani nan"
Kallon shi nayi cikin mamaki nace mishi.
"Kai?"
"Baki yarda bane?"
Ya kuma dawo min da tambayar yana gyara hannun rigar shi, alamar shine fa, takaici ya sani cewa.
"Toh yanzun naji nayi laifi kayi min afwa"
"Na miki! Amma da sharadi!"
Kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Name fa?"
"Zaki nuna min wani abu ne me laushin da na tab'a."
Suke fuskana nayi tare da kaiwa kafarshi wani mugun taku, sai da yayi ihu. Sannan na kyale shi.
"Baka da da'a ne? Ina mace kana tambayana abinda ka tab'a a jikina ai sai a rena ka" na fada mishi kasa kasa.


"Kuma haka ne fa," yana kallon mutanen shi. Sannan ya gyara muryan shi yana faɗin.
"Wacece ke? Kuma waye ya turo ki?"


Da sauri matar tazo sannan tace mishi.
"Sunanta Salwah daga tsakiyar Afrika, Amir Sulaiman ne ya kawo maka ita"


"Salsabila! Sunanta daga yau. Dan tafi dacewa da sunan. Sannan mu shiga daga cikin gidan."
Ya faɗa tare da goya hannun shi a baya, abun sai ya bani mamaki da dariya, wato shima yana yi, share batun nayi har muka shiga cikin gidan, muna shiga muka sami ana ta aiki, haka yayi ta bin bayin yana make musu duwawun su, tare da zuba musu dundu a baya.


Da zafi amma haka suke dariya, ya kai kan wani dattijo kenan na buge ganin shi sai da ya saka kara.
"Toh kuma meye nayi miki?"
Ya faɗa a shagwaɓe, har idanun shi yana kawo kwalla,


"Wannan abun da kake babu kyau rashin da'a ce, Allah bai baka mulki dan ka wulakanta rayuwar wasu ba, Allah ya baka ne dan ka sama abun tausayawa a gare su ka Fahimta?"


Fuuuu ya wuce abinshi yana kuka. Kallona suka yi dukkan su, tare da cewa.
"Mun gode!"


Share su nayi tare da nad'e hannuna a kirjina ina kallon gidan, yadda suke aiki. Babu juyawa ina tsaye har sai da yamma tayi sannan ya fito sanye da kananun kayan mutanen ketare.
"Ke zo nan" ya kirani.
Ba musu na isa gaban shi, kallon shi nayi sannan yace min.
"Don Allah yaushe zan fita daga wannan yanayin? Ni ina son nayi rayuwa kamar kowa amma kullum Kaka rufe Ni yake yi! Kisan sabida me?"


Kallon ko ina yayi sannan yace min.
"Sabida yaran Kaka Uku maza kashe su ake yi, An kashe Kawuna Almustapha! Sannan an kashe Me bin shi Abubakar! Sai Abba na sa ake kashe shi a shekara goma da suka wuce. Kuma sabida mulki ne, don Allah dube ni fa, ina son nayi rayuwa kamar kowa amma an hanani, Kinga kisan yadda zaki yi mu fita cin kasuwan dare don Allah!"


Ya faɗa a shagwaɓe, kamar zai min kuka.
Kallon shi nayi tare da hango yar tusar jakin da yake kunnen shi sak da na Abba na. Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Ban san yadda zaka fita daga gidan nan ba, kayi hakuri Amir Rahil!"


Kamar ya saka kuka haka ya kalle ni, sannan ya dauke kanshi kafin can ya sake min kuka. Har da ihu, share shi nayi tare da juyawa na fita daga gidan. Na nufi hanyar gidan da nafito.


Ina juya labarin da ya bani.
"Zaki iya tafiya da kome yadda kike so! Idan ma zaki iya shiga jikin shi duk ba laifi, amma maganar gaskiya bana son aikina ya wuce wata uku."


Juyawa

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads