Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 274096 words

Chapter 14 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1355

Ads at the middle of Article

raye Babu wanda ya dace da Askandariya sai Banafsha." Ta faɗa a sanyayye.
---
Muna shiga cikin gidan, aka wuce damu ban daki. Wanka muka yi tare da tsayawa a layi, saka mu aka yi muka zare mayafin da muka rufe jikin mu, sannan aka shiga duba mu sama da kasa. Tare da bincike jikin mu.


Wato zunzurutun binciken har da bakin mu aka duba, ana ware mu. A hankali layin yazo kai na. D'ago kai nayi na kalli matar. Bayan ta duba kasa na. Gyada kai tayi sannan ta bude bakina tana kallon bakina zuwa daso rina, farcen hannuna ta kalla. Tare da kallon cikin idanuna.


Siririn yatsar kafana da dunduniya ta, gyada kai tayi sannan ta koma gefe tana magana da yar uwarta, zani suka bamu muka daura. Sannan suka bawa kowa shedan shi da zai tsaya akan aikin shi. Ni kuma suka kalle ni tare da cewa.
"Gaskiya ba zaki zauna a cikin mu ba, sai dai zamu kai ki gurin Sultanah Hoyam ta ganki."


Gyada kai nayi sannan suka saka mu a gaba har zuwa shashin Sultanah, tunda muka doshi shsshin kamshi yake dukar mu, har muka shiga dakin. Muka tsaya kan mu a sunkuye,
A hankali suke gabatar mata da mu, tare da kiran sunan mu.


Yadda suka bata bayani akai na, ga kuma ciwon da yake fuskana sai yace musu.
"Ku kaita haramtacciyar Fada, domin bana son Yarona na ga fuskarta mara kyan nan hankalin shi ya tashi. Jiya an kai mishi Husna ya korota, sabida baya yi abinda ya dace ba.


Yau ku gaya musu su san abinda ya dace, idan yana wanka toh ku tuntube shi ko yana bukatar taimakonku gurin cude mishi bayan shi, idan kuma ya fito toh a kula da inda ya saka fuskar shi da idanun shi. Bana son ya kuma korafin ba a kula dashi ba."


Tana gama fadar haka ta nuna mana kofa, muka fita. Duk sauran an nuna musu inda zasu yi aiki nice dai aka kai ni haramtacciyar Fada, a hankali na shiga cikin gidan. Babu kome sai tarkacen tsohon sarki, dan haka ina shiga suka kalle tare da tambayar ta.
"Daga ina kike? Meye ya kawo ki nan?"
Kallon shigar jikina nayi sannan nace musu.
"Daga wancan gidan nake aka ce nazo nan nayi muku yan aikace aikace."
"Toh bakar fata! Mun muna me konannen fuska, an tab'a gaya miki idanun ki sak yake da ya maje, Shairah fitar min da ita tsoro take bani!"


Inji wata budurwa a cikin gidan, kallo daya nayi mata, na dauke kai, dan har gaba ta tsaya. Murmushi kawai nayi, zata kuma takawa na saka mata kafa, duk basu lura ba. Haka ta hantsila ta fadi. Mik'ewa tayi cikin fusata.
Ta kawo min duka, na kauce ta daki iska.


Sake kai min duka tayi, nayi maza na bata guri ta fadi, cikin jin haushi da takaici, ta kuma juyawa zata kai min duka na saka mata kafa, ta fad'i. Har sai da ta fasa hancinta.


"Ni kika fasawa hanci?"
Cikinin fushi ta dauki kwanon cin abinci na tangaran, ta kwada min na kauce tare da dukar hannun nata, sai da suka zube a kasa na koma gurin da nake tsaye na tsaya, sake mik'ewa tayi taja wuka tawo kai na.
"Ya isa haka! Ke mafadaciya daga ina kike?"
Sai lokacin na d'ago kai ina kallon matar da take fitowar, wacce mulki da izza suka taru akan fuskarta, kwayar idanun ta kuwa cike yake da fusata. Kwarjini tayi min, dan dole na sunkuyar da kaina.


Tana isowa gabana, ta d'aga kai na tayi tare da kallon kwayar idanu.
"Meye sunanki?"
"Ikram!"
"Hm! Me suka turo ki kiyi a cikin wannan gidan?"
"Sun bukaci nayi aiki kawai!"
Na bata amsa a takaice,
"Yayi kyau! Shine kika aika abu mafi kuskure?"
"Bana jure cikin mutunci bane"
"Kenan idan aka tab'a ki zaki fusata?"
Sake sunkuyar da kai nayi, sannan nace mata.
"Eh toh ya danganta da irin tab'a ni da zaki yi!"

Kallon wasu mata tayi sannan tace mata.
"Ku nuna mata abinda ya dace Narjis"
Gyada kai tayi sannan ta nuna min hanya. Muna barin gurin tayi murmushi.
"Me ka Fahimta?"
"Fusataciya ce!"
Gyda kai tayi sannan tace mishi.
"Baka fahimci abinda ka gani ba, amma dole ta zama iya tawa ce."


Jinjina kai yayi sannan ya kuma shiru.
** Tunda suka yi faɗa yake jin babu dad'i, sai da ta kai barci Barawo yake ɗaukar shi, wani masifaffen kewar Ikram yake cika mishi zuciya.


A hankali ya fito daga cikin jirgin ruwan, anan ya sami Nawwas a tsaye. "Kai ma kana cikin yanayin damuwa ko?" Juyawa Nawwas yayi tare da dauke kan shi yana kallon taurarin da suke sararin samaniya kafin yace.
"Me zai sanya ni shiga damuwa?"


Jingina yayi da jikin wani gwafa, sannan ya kurawa Nawwas ido, tare da sauke ajiyar zuciya yana lashe bakin shi cikin wani irin yanayi na daban.
"Ina kaunar Ikram! Toh amma ka amince ta tafi a baiwa?"
"A'a karka dauki haka a matsayin son kai!"
"Nima ban ce kana da son kai ba, amma duk abinda kake kauna baka mishi rikon sakainar kashi!"


Dan lasar bakin shi yayi tare da kallon ruwan.
"Ban sadaukar da ita ba, dan son zuciya ta ba, sai dai haka da nayi zai sama min zaman lafiya da al'umma ta."
Gabaki daya Nawwas ya gundura da surutun shi, ko yace soki burutsin shi, dan haka ya ki amsa mishi, asalima share shi yayi daga maganar baki daya, domin ya tsani renin hankali.


Haka yayi ta gaya mishi yadda yake jin babu dadi rabuwa da Ikram, shi kuwa Nawwas ji yaƙe kamar ya rufe shi da duka, cikin mugun takaici ya juya tare da barin gurin, ya mishi sallama saboda barci da yake ji, kuma ba kome ya saka shi jin barcin ba sai sututun Sultan Abrad,


Tunda ya shiga cikin dakin, ya kwanta ringingine, abubuwan da suka gabata ya shiga dawo mishi, tun daga ranar da ya daukota har zuwa lokacin da ya shiga cikin dakin Abrad yaga yadda gadon kwanciyar su, ya hautsine ranar Dakyar yayi barci, dan ranshi yayi mugun b'aci sosai.ga kishin da ya cika mishi zuciya.
...
~~~
Tunda na fahimci gidan da nake na shiga hankalina, domin sau dayawa ina fuskatar cin fuska da tozarci, daga masu kirana da me idanun mage, sai masu zagina da bakar fata.


A hankali na fahimci larabawa suna da mugun kyamar bakin fata, domin ido da ido. Suke guduna, abu daya ya kwance ni shine ina daka yan banza.


Sauri nake zan tafi gidan da nake aiki, yan matan bayi biyar suka tsare min hanya.
"Ke me idanun mage mummunan dake mara fasali, kaskantacciyar baiwa. Sai munci ubanki."


Kura musu ido nayi, sannan na dauke kai na zan wuce. Suka kuma dawo dani gaban su. Kallon su nayi sosai ina kara tuna ta yadda zanci Ubansu a tsanake.


Hango mu da fadawar masarautar suka yi, take suka kore mu, na wuce gaba abuna, Ashe yan iska suna biye dani, har nayi nisa, suka sake tare ni, kasancewar gurin babu mutane, nad'e hannun rigana nayi, tare da falfalawa da mugun gudu, aukuwa jakuna suka biyo ni, a wani bayan lambu muka tsaya, nayi tsalle na karyo itaccen bishiya.


Na fara gyarawa, tare da kallon su, dariya suka saka tare da nuna ni.
"Ke bakar fata! Kina nufin Mu zaki daka da bulalar hannunki?"
Murmushin Mugunta nayi musu, sannan na wullar da bulalar ina me durkusawa ina basu hakuri.


Yan iska, sai ga shi suna dariya, zasu dake ni,


Kamar yadda suke tsammanin zasu min, sai labarin ya sha banban, domin kuwa Hango Sultan Mehran suka yi da gudu suka bar gurin, tun kafin ya iso mutanen shi sun taso min, tare da korana kar na bari ya ganni.


Barin gurin nayi ', dan sun nuna zasu iya dukana....
~~~
khartum.


Babban birnin Sudan, kallon Juna suka yi shida Sarwat. Ba kome yasa suka kalli Juna ba, sai.yadda suka ga ana sayar da mutane, d'ago kan da Noman zai yi ya hango wani mutum,. yana ƙoƙarin gudu, da gudu yabi bayan shi, tare da niman kama shi.


Karshe dai garin gudu suka fada cikin ruwa, aikuwa Noman ya shake shi.
"Me yasa kake gudu? Meye nufinka!"


"Ko zaka zaga duniyar nan da niman Ikram ba zaka tab'a samun ta ba, domin tayi maka nisan da bazaka iya cimmata ba,"
Inji Mutumin,


Sake shi Noman yayi cikin tashin hankali da kaduwa, kurawa juna ido suka yi. Idanun shi ya cika da kwalla, a hankali ya shiga fitowa daga cikin ruwan, tausayin shi Mutumin yaji, yace mishi.
"Me yasa ba zaka bincike ni da karfin tsiya ba?"
Cak Noman yayi tare da juyawa yace.
"Akan me zan maka da karfi sai ka gaya min? A'a Allah yana sane da abinda kai min, dan haka wallahi babu kome."


Ya juya zai fita, abin shi cikin wani irin yanayi mutumin yace mishi.
"Ban san inda take ba, amma da alamu tana yankin larabawa ne!"


"Nagode sosai!"
Daga haka ya bar cikin ruwan, ya koma inda yaga ana cinikin bayin, inda shima ya nemi a saye su, dakyar aka sami mutanen da suka saye su. Sannan suka bar Gabbar tekun Sudan.


~~~
SAMAIND
Wata uku


A hankali nake ganin yadda ake koyar da Jasrah, ita ke koyawa nice nake dauka. A hankali suke daura mata litattafai akanta, sai sun gama shirya mata zai zube,


Kallona Matar da nake mata kallon Mahaifiyar Jasrah tayi.
A hankali ta yafato ni, na isa gabanta,
"Shairah ka gwada shiryawa Ikram mu gani!"
Babu musu ya shiga daura min littafan akai na, tare da kallona yace min.
"Zaki saka hannunki a k'ugun ki, sannan d'ayan hannun ki cigaba da juyawa,tafiyar a sanyayye ake yinta, babu amfanin zafin nama."


Lumshe idanuna nayi sannan na kalle shi, muka Cigaba da tafiya, suna kallona.


Wasa wasa matar nan tayi bala'in janyo ni jikinta, tare da sakawa ana koya min, dab'iar masarautan, tare da nuna min wasu abubuwan da ya fara bani tsoro. Domin sai da ta fahimci abinda Abrad ya saka min fuskana, ta saka aka cire min, sannan ta nuna min rufe fuskar kawai ya wadattar,


~~~
A hankali ya farka daga barci, kallon wasu kyawawan yan mata yayi, tare da dauke kan shi. Gyara kwanciyar shi yayi, tare da lumshe idanun shi, idan yana kaunar ganin yan matan nan ya mutu a kwance, ya tsani ganinsu. Amma Ammuh ta dage mishi lallai sai ya mu'amalantu dasu.


"Sultan Mehran! Ruwan wankan ka yana."
Tab'a wani abu yayi a jikin gadon shi, sai Darakshan ya shigo har cikin ɗakin,kallon shi Mehran yayi tare da juya mishi baya, kad'a keyar yan mata yayi, suna fita ya mike zaune.


Tashi yayi tare da nufar ban dakin, shiga wanka yayi ya jima yana fama da mulki a cikin ruwan, kafin ya fito.


Ya shirya cikin kayan sarauta, sannan ya nufi shashin Sultanah, tun da ya shiga ya sami yan mata suna rawa a gabanta sanye da wasu kaya masu kama da tsirara, zama yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Barka da safiya, Mehran!"
Bai tanka mata ba, sai ma kara sunkuyar da kan shi da yayi, zuba mishi abin karyawa tai sannan ta zuba mishi ido.
"Mehran! Dama akan gwamnonin nahiyar nan nake son ko zaka dakatar da su,ka kwaso wasu."


Bai kulata ba, amma kuma bai fasa cin abincin ba, shiru tayi kafin ta cigaba da mishi bayanin yadda zai tafi da mulkin shi. Cikin mugunta da zalinci, kar yaji tausayin kowa, ya hukunta duk wanda yake da hannun a kawo mishi harin bazata. Yana gamawa ya mike tare da goge hannun shi, zai fita yace mata.
"Hmm!"
Sannan ya fita, jimawa kadan Fudail ya shigo, tare da ce mata.
"Sultanah Hoyam, Sultan Mehran yace kar a kuma tura mishi yan mata castle din shi, idan ba haka ba zai sanya mu sare kan su."


"Amma akan me zai..?"
"Umarnin da ya bamu kenan idan muka kuma ganin wata mace."
*Allah ka jikan Iyayena😭😭😭😔🤲🏽*
Book dina kudi ne
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM



Page 21.


Sake baki tayi tana kallon shi, kafin ta tattaro sauran kuzarinta tace mishi.
"Akan wani dalili zai ce haka?"
"Baya da ra'ayin mata ne, idan kika cigaba da turo su zasu mutum ne, dan haka ayi hakuri da turo su."


Daga haka ya fita, shi kuwa Mehran yana fada, an kawo karshen binciken harin da aka kawo mishi lokacin da ake bikin bashi sarauta, wata uku da suka wuce.
Kallon Magatakardan masarautan yayi, sannan ya cigaba da kallon hanyar waje. Ba kome yaja haka ba, sai yan mata guda shida da aka turo su, suyi rawa.


Tunda suka shigo ya dauke kan shi, tare da kallon Darakshan. Dakatar da yan matan yayi tare da koran su.
Ana ƙoƙarin gabatar da wanda suka kai mishi hari, kawai sai gani aka yi fadar ta cika da hayaki. Kafin kace kwabo an kwace takardan da aka kawo na bincike.


Murmushi yayi sannan ya mike zai bar fadan, ya saka Darakshan ya nimo mishi mutanen da suka yi binciken. A sirrance bayan sun fita daga fadar.


Cigaba da tafiya, yayin da abubuwan al'ajabi suka shiga faruwa, a kowani ɓangare na masarautun larabawa, musamman akan yaki da cinikin bayi.


A cikin wata na shida da zuwa masarautar na sami horon zama daya daga cikin amirorin masarautan, musamman yadda Sultanah Fazilatul nisa take nuna min ni din kamar lu'ulu'u ce me daraja, dan haka kar nayi wasa da damata.


Duk wannan Kawata min duniyata da take min sam baya burge ni, kawai gida nake son komawa. Na gaya mata kai na, a sunkuye.
"Zaki koma gida, amma kafin nan so nake ki shiga cikin wancan gidan,idan kika shiga toh kin gama min kome, zaki iya tafiya gida."


Gyada mata kai nayi, sannan wani abun da basu sani ba.tun da aka kawo ni, ba zan ce waye ba. Amma da zaran karfe goma sha biyu yayi na dare,za a tashe ni. Daga nan zan fita. Ban san waye ba, dai amma koya min yaki yake na fitan hankalin. Bai tab'a min magana ba, amma yana bani horo na fitan hankalin.


Horon da yake bani irin horon da ake bawa maza ne, domin idan muka gama da takobi, horon dambe yake koya min.


Karfe uku nayi zai juya yayi tafiyar shi,nima kuma na koma bangaren mu na bayi, dan haka na sami horo ta kowani fanni,


Matsalata guda daya ce shine tsangwama ta da suke da baka, takai ko wanka muka shiga niman hanyar tozartani suke, dan haka na sami Sultanah da maganar abinda ake min.


"Toh karki damu, zaki bar cikin su ma." Gyada mata kai nayi sannan na bar gurin na cigaba da abinda nake, ina halkance da abinda Jasrah take min, ban tab'a jin haushin ta ba, sai ma dauke kan da nake mata.


Bayan na bar dakin mahaifiyarta, shiga tayi cikin damuwa tace mata.
"Amih! Me yasa sai Ikram."


Mika mata hannu tayi sannan ta karasa jikinta, tana faɗin.
"Naka sai naka, dadin zama sai bare, barta tayi miki aikin da Bazaki iya ba, sauran kuma ki karasa. Akwai abin da na gani a tare da ita idan ta gama miki aikin zata bar miki sauran."


Murmushi tayi sannan ta cigaba da gaya mata irin taimakawa da Ikram take mata. Dan haka karta d'aga hankalin ta.
~~~
Wato akwai abinda ake kira ƙaddara, idan Allah yaso haka sai ya faru bata tare da kowa ya fahimci haka ba. Sau dayawa mutane sukan iya shirya kome dan cikar Muradin su, amma sai kaga Allah ya shirya nashi tsarin sama da nasu.


Haka ce ta faru, Sultan Mehran zai fita rangadi, dan haka suka shirya Dawakai kusan dubu goma tare da mahayan su, daga can gefe keken dokin shi ce me dauke da wasu irin Dawakai masu shegen kyau..farare kal kai, masu gashi har kafar su kamar an saka musu, dawakan manyan ne daga yankin turawa aka kawo mishi.


Ana ƙoƙarin saka keken tsakiyar mutanen na, Dawakai suka fara ihu da bori, lokacin Ni na fito zan wuce haramtacciyar fada. Shi kuma yana ƙoƙarin shiga cikin keken, na hango wata irin maciciya, tana kokarin karasowa inda kafar shi take,abinda ya saka sauran dawakan ihu tare da gwara juna,


Saura kiris ta sare shi, ban san lokacin da na iso tare da fisgo shi ya fado kai na ba. Haka muka zube kasa, dawakan suka. Shiga gudu.


Kallona yake ido cikin ido, zuciyar shi tana wani irin bugawa har ina

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads