Header Ads
Showing 108001 words to 111000 words out of 274096 words

Chapter 37 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1381

Ads at the middle of Article

bayan sun mata fyade da tsohon cikin."


Kofin da Mehran yake rike dashi na tankarar sai da ta tsage tare da soke mishi hannun shi, yana diga da jini.
"Suka wulakantatta, abinda ya saka bawan Allah nan kasa koda motsi, domin sunce zasu koma kan Babbar Yar shi da karamar, haka aka yi ta kokarin daukar mataki ya hana, sannan yace ya barsu da Allah, zai bi musu hakkin su.


Bayan rasuwar ta da abin cikinta ne ya auri baiwarta, tun daga lokacin bai da kwanciyar hankali, ana haka wata rana ya fadi a gurin kiwo, "


Haka ya basu har labarin yadda aka dauko Ikram akan lafiyar kanwarta.
_Ce maka akayi sabida jin dadi nake nan! Rayuwata bata nan! Ina raye ne sabida kanwata da yau zan sami duniya da kome na cikinta tace tana bukata zan bar mata koda kuwa ace abinda nake so yana cikin shi! Ka kyale ni ba zan zauna ba!_


Kusan abinda yake yawo kenan aransu dukkansu uku. Wato Sultan Mehran da Sultanah, da Fudail.
"A ranar da ta bar garin Allah ya amshi rayuwar Airan, wanda zuwan mu ne Noman ya gaya mata, bayan nan ba zance ta san abinda ya faru da Mahaifiyar ta ba."


"Zata sani! Kuma zata bi hakkin jininsu. Idan ta kyale su sun cutar da ita, dan haka dole ta rayu, dole tana bukatar rayuwa a duk inda take zata so taya nisan kwana"


Kallon Fudail tayi tare da kallon Hannun Sultan Mehran, da sauri ya dauko kayan aiki ya fara duba mishi hannun shi. Kallon Sultanah yayi sannan yace mata.
"Ina bukatar zuwa gezira!"
Kallon shi tayi cikin murmushi sannan tace mishi.
"Ina zaka? Daukar fansa abinda aka mata? Indai har zaka iya haka toh ka fara bincikar waye ya kashe Mahaifin ka, idan har kayi haka zaka iya zuwa gezira."


Daga hakan ta mike tare da barin gurin.
~~~
Ji nayi an watsa min abu kamar raga, suka dauke ni sama aka nufi hanyar wani gida dani, watsa Ni suka yi a kasa.


Fita nayi daga cikin ragar, tare da kallon su, nace musu.
"Ni bana son fada, don Allah ku kyale Ni!"
"So muke mu baki abinda wancan sakaran ya kasa baki."
Dariya na kwashe dashi sannan nace musu
"Idan har kuka iya cire koda rigar jikina, nayi alƙawarin da kaina zan kwanta kuyi ta hawa kai na kuna sauka, idan kuma nayi nasara kareraya ku."


Dariya suka kwashe da shi, sannan.
"Kai ku cire mata kayanta tsaf ku miko min ta"
Kai na a sunkuye, badakaren ya miko hannun shi, murɗe hannun shi nayi tare da juyawa nayi tare da karya hannun, sannan na naushi hakarkarin shi.


Faduwa yayi tare da jijjiga kamar me farfadiya, mik'ewa nayi domin ina durkushe. Na tsaya ina shafa hannuna, sannan na musu alamun su tawo. Haka muka yi ta dasu..sannan na karya hannun Yazeed da Yasir, Samir kuwa targada mishi kafa nayi. Sannan na juya na bar gurin.


Ina shiga gidan mu na bayi, sai ga dakarun.
"Ke!"
"Kayi kasa da muryan ka sabida mutane suna barci, muje!"


A hankali na fita tare da binsu, har gidan da aka kai ni, ina zuwa na samu kujeru biyu babu masu shi, daya kuma Rahil ne jikin shi yana rawa.


Ina zuwa na dafa kafad'ar shi, ina lura da yadda ya sauke ajiyar zuciya.
"Ke wacece?"
Kallon Amir Sulaiman nayi, sanan nace musu.
"Zan gaya muku wacece ni, amma shi wannan ku sallame shi. Idan ba haka ba. Zan iya samun kai cikin rashin nutsuwa."


"Ke!" Amir Sulaiman ya saka min tsawa, takowa nayi har gaban shi, tare da shafa fuskar Yasir, tare da kai fuskana kan ma shi.
"Kasan me? Da ace babu yarjejeniya, da na karya kashin wuyar wannan da yake cewa a kwab'e min kaya yayi yadda yake so dani, tarbiyyar da kai mishi kenan?" Wani tab'e baki nayi sannan nace mishi.
"Yadda kuke farautar Rahil ya sani fara shakku akan ku, dan haka ku zuba min ido ko ku rufe idanunku."


Daga haka na riko hannun shi muka bar gurin, har mun isa baki kofar na d'ago yatsar hannuna nace musu.
"Kar a kuma tab'a min shi, domin zan iya samun damar kashe kowa"


Sannan na fita dashi tare da kallon shi, kai hannun shi yayi tare da rungume ni, ina jin sautin bugun zuciyar shi.
"Nagode" ya faɗa hawaye na zuba daga idanun shi. Tausayi ya bani na rungume shi. A hankali na cire hannuna a jikinshi muka tafi gidan, har cikin gidan shi na raka shi. Zan fito. Yayi maza tare da riko hannun na.
"Ki zauna anan!"
Ya faɗa min cikin dakewa, tare da zuba min idanun shi. Haka kawai sai.naji yayi min kwarjini. Dan haka na zauna. Ya nufi ban daki bai fito ba, sai kawai yayi ta tsalla ihu.
Da gudu na shiga. Dariya ya saka min tare da cewa.
"Toh zoki taimaka min"
"Baka da hankali"
Na juya zan fito.
"Wayyo Allah!"
Da sauri na juya, "subhanallahi!" Na fada tare da juyawa da sauri nayi, ina jin takaicin wannan Iskanci tare da fita daga ban dakin. Koda ya fito ina tsaye, zama yayi tare da cewa.
"Zoki goge min kai na;"
Wato na lura da Rashin mutuncin shi wani yakewa, dan haka ina zuwa kusa dashi na zabga mishi naushi.
"Wayyo Allah na, kiyi hakuri!" Ya faɗa kamar zai yi kuka, hmm na ce tare da juyawa zan fita ya finciko ni, na fado kanshi.
"Baka san ina d'aga maka kafa bane?" Juyar dani yayi. Kallona yake tare da lumshe idanun shi.
Kanshi ya kai wuyana nayi maza na kai hannuna wuyar shi.
"Kisan abinda nake ji akanki?"
"Don Allah!" Fada muryana na rawa, janye hannuna yayi tare da kallon cikin idanu, murmushi yayi tare da kallon yadda nake zare ido, hancin shi ya kai kan nawa yana gogan nawa.
"Don Allah kabari!"
"Har yanzun baki sona" gabana ne ya fadi,
"Kayi hakuri! So daya tak nayi kuma na binnewa me shi, zuciyata da ruhina yana gare shi, bana jin kome akanka shi daya nake jin tasirin kwayar idanun shi, shirun shi shine Yaren shi a gurina, na manta da shi amma zuciyarta yana rike da dabi'ar shi. Kishin shi akai na a bayyane yake, ban san fuskar shi ba, amma kaunar shi dawammamiya ce.....
```BOOK one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```


#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: Monday-March-2021
*FURE cikin ƘAYA*
_CIGABAN DAULA BIYU_
BOOK TWO


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


12
Ganin yadda kwalla ke cika a idanuna yasa shi girgiza min kai tare da cewa.
"Kiyi hakuri! Ba zan iya barin ki, ki subuce min ba, dole nayi abinda zaki zama nawa har abada."
Cikin wani irin sauri yake kokarin rabani da kayan jikina, riko fuskar shi nayi, sannan nace mishi.
"Me yasa kake ganin kamar zina itace saukakkakiyar hanyar da zaka same ni? Me yasa kake ganin kamar idan har ka kwanta dani ba zan guje ka ba, zan zauna domin rufawa kaina asiri? Karka manta ni zuwa nayi nan kasan dalilin zuwan nawa? Baka sani ba, daga ganin mutum a jikin ka har ka bashi zuciyarka, toh kashe nazo yi!" Na fada da karfi.

Cikin wani irin tsoro da tashin hankali, ya kalle ni. Tare da sake ni. Yana kallona ilahirin jikin shi rawa yake, tare da nuna ni da yatsa.
"Meye nayi miki?"
"Sani aka yi! Dan haka karka yi tunanin soyayya tana cikin abinda ya sani nake zaune da kai, ganin ta kowani kusurwan gidan sarautar ku ana niman ranka ya sani bincike inda zan Fahimci meye matsalar su.


Hakan ba zai sakani samun damar binciken ba sai na tsaya a bangaren ka, shine dake kai banza ne ka fada soyayya dani, ka kiyayye kanka domin Ni zan kashe ka ne" na fadi haka ina mik'ewa daga gadon, tare da gyara jikina na fita, ina jin yadda yake kuka ya bani tausayi dan haka na fita daga gidan.


---
Duk wanda na tambaya meke faruwa, basu bani amsar asalima tsoron tambayar suke, sannan abinda na fahimta, yaran Sultanah Balkisu Ikram sune kusan sadaukai a cikin masarautan, kuma basu nan a raye, dan haka na yanke hukuncin tun karar Sultanah Balkisu Ikram, sai da na bari dare ya raba, sannan na shiga hawarawa katangar gidan sarautar, ban tsaya ba. Har sai da na isa bakin kofar shashin ta, sannan na dake kafadar masu tsaron kofar. Sannan na shiga, a hankali har cikin dakunan sai a wani daki can na same ta, zaune akan abin sallah.


Tana kuka, tsaye nayi cak ina kallonta, tare da jin kukanta har cikin kokon raina, a hankali na taka har gaban ta, ya cire mayafin dake kan fuskana na zauna a gabanta.
"Me yasa kike musu kuka?"
D'ago kai tayi tare da share kwalla tace min.
"Barka da zuwa! Amma me yasa kika zab'i shigar dare?"


"Ya akayi kika san zan zo?"na tambaye ta, murmushi tayi tana share kwalla, tun da aka ce Sulaiman ya kawo mace da Rahil ya bukata, naji a raina babu makawa zaki bukaci gani na,


Idan da namiji ne tuni yayi abinda ya kawo shi, dan nasan ya kawo ki ne ki kashe Rahil, sai dai zuciyar mace ba irin na namiji bane, mace tana da taushin. Ban san sunanki ba?"


"Bilqisul Ikram Mustapha!" Cikin wani irin sauri ta d'ago kai tare da rawan jiki, tace min.
"Matso na ganki!" Tana kai hannunta fuskana, alamar bata gani, shafa fuskana take son yi dan haka na matsa kusa da ita.


"Ina iyayenki?" Ta tambaye ni, "sun rasu!"
"Daga ina kike?"
"Gezira!"
Ajiyar zuciya ta sauke, sannan tace min.
"Me kike bukata a cikin wannan gidan?"
"Me yasa suka kashe miki Yaranki?"
Hawayen da suke zuba tare da tuttukowa daga idanunta ya sani fahimtar kome.
"Yanzun me kika fahimta akan Sauran dakunan?" Na tambaye ta, girgiza min kai tayi sannan tace min.
"Kasancewar nice matar shi ta farko, kuma yar kasar Habasha, kuma ina zuwa ban jima ba, Yayan shi Sultan Khabir ya rasu, sai aka bashi sarauta, ganin haka ne yasa yaran shi suka fusata me yasa ba zaa bawa Mahaifiyar su magajiyar sarauta ba(Which mean Empress)


Sai suka fusata har itama Ummu Kulsum din taji babu dad'i, su kuma sunyi nazarin gidan da tafito ne, ba wasu bane kuma idan aka basu magajiyar sarauta, basu da Addini dan haka suka zab'i Mu'allim, lokacin ina goyon Cikin Almustapha, anyi rikici karshe aka tsayar da magana idan ta gana takaba zata aure shi kuma ya amince.


Sanin cewa musulunci bai haramta ba yasani saukar da kaina, har Allah ya sauke ni lafiya, lokacin na haifi Almustapha, a hankali sai mutum suka fara kokuwar ganin ai tunda na fito a cikin gidan da suke da karfin mulki a nahiyar Afirka, dan haka suka fara bani goyan bayan a bani Sultanah, shi kuma Sultanah ana iya samun shi ta karfin mulki,. musamman idan kin hada nasaba da manyan masarautu a jininki, sai Allah ya sanya aka fada abin daidai kai na. Kuma aka duba tarihin kasar mu, babu kowa nawa da yayi bauta, mulki aka haife mu muka taso cikin shi.


Dan haka suka bani, tun daga lokacin aka fara farautar rayuwar Almustapha, har na haifi Abubakar, sha'anin mulki dole sai kayi takatsantsar, dan haka duk ta yadda naga mijina zai kauce ina tsaya mishi domin ina da ilimin addini sosai, shima kuma haka, Ikram. Har na haifi Aliyu, ana samun matsala a cikin gidan nan sai da na haifi Raziyana, na sami sauki lokacin Mu'allim ya auri Baiwar shi. Itama ta haifi yara maza Abdullahi da Abdul Rahman, anan aka zafaffa k'iyayyar da ake acikin masarautan.


Cikin hukuncin Ubangiji, sai gashi yarana sune Jarumai ko yaki aka tafi sune suke dawowa da tuta, tun Almustapha yana da shekara sha biyar ya fara fita yaƙi, kuma ya jagoranci yaki na fitar hankali, har ya kai matakin shekara ashirin da biyar, su uku suke fuskarta yaki, kowacce iri ne, Allah yayiwa Almustapha baiwar iya fahimtar lamarin yaki, yayinda Abubakar yayi tafiya har kasar ruma, yayi ilimin yadda ake sarrafa, nakiya, shi kuma Aliyu ya kware a iya leken asirin abokan gaba, yara Uku sai suka zama kaf nahiyar Afirka su ake kwantaccen dasu.


Idan suka fara yaki har saka maza gudu suke."
Murmushi tayi wanda ya fidda mata yan lub'anta, sannan ta cigaba da bani labarin.
"A hankali yarana suka kawo ka, Ana cikin nima musu auren Yar Daular Askandariya, aka wayi gari ya tafi farauta daga nan ba a kuma ganin shi ba sai kayan aikin shi. Muna cikin wannan halin Abubakar da yayi tafiya zuwa kasar Sham, a hanyar dawowa ya rasu, Kinga bude wancan akwatin, zaki ga rubutun su kowa ya iya Rubutu, kuma sun ajiye min tarihi."


Haka na bude tare da daukowa naga sunan Almustapha, gabana ne ya fadi. Sakamakon ganin rubutun Abba na,.kallonta nayi ina jin hawaye na zuba min, tabbas akwai ranar da na tab'a ganin shi yayi rubutu, sannan ya juya zoben hannun shi wanda yake da wani abu a bayan shi ya kunna wuta ya kona bakin abun ya manna a jikin Takardan. Sai daga alamar wancan da na gani a gurin shi.


"Bayan mutuwarsu, dan haka Muka kama Aliyu muka aura mishi yar gidan Abu Ayyub, shekaran su goma sha biyu, aka kona su, Allah ne ya nufa Rahil zai yi nisan kwana, aka samu baban shi ya fidda shi daga cikin gidan, ya turo shi waje! Har yau ba a san suwaye suka musu kawanya ba."


Fesar da kukan nayi sannan nace mata.
"Me kike so nayi musu?"
"A hukunta su idan an same su, idan kuma ba a same su ba, Allah zai hukunta su."


Mikewa nayi sannan na taku daya biyu, nace.
"Idan aka musu shara'a a fada, zasu sami sassauci, hukuncina dai dai take da hukuncin Shari'ar Muslunci. Idan ka kashe a kashe ka idan ka tab'a a tab'a ka, matukar jini Ya tsaga dole hukuncin ya haura kansu."


Ina gama fadar haka na fice daga cikin gidan, na nufi gidan Sulaiman, ina shiga na shiga sumar da dakarun shi, har na isa cikin dakin shi, yana kwance nayi kwance kwance na zuba Mishi duka akan cikin shi. Da gudu ya farka.


"Yau nazo na ji bayanin daga bakin ka, saura sati biyu na gama abinda ya kawo ni, idan kuma kayi karya, zan datse kofar numfashin ka."


"Wai Ni kam wani irin masifa ce ya sani kwaso ki?" Ya fada yana dukan kanshi.
"Waye ya kashe Almustapha da yan uwanshi." Zaro ido yayi sannan ya rufe bakin shi. Yace min
"Kasancewar kin tab'a Bala'i zan gaya miki, amma zaki mutu"
"Karka damu, a jini na yake wasa da mutuwa,! Gaya min"


"Almustapha nina fitar dashi daga kasar baki daya na kai shi iyakar kasar nan bayan mun shiga Algers, domin Amirah Raziyana tana son zama mace ta farko da ta mulki kasar nan, ba zata tab'a samun damar haka ba, dole sai takawar da yayunta, Ni da Almustapha mun taso abokan amana, ba zan iya gani a kashe shi babu dalili ba, dan haka koda na kai shi Algers sai na samu nayi mishi dalilin da ya manta da kome nashi amma kafin nan ya gaya min cewa. Ko bude ko bi jima zai dawo, idan bai dawo ba Allah zai kawo jinin shi.


Dan haka ina jin haka na buge kanshi ya fad'i, sannan na yiwa bayin shi barazana da zan kashe su. Sanan daga baya na hana shi da wani mutumin da shi kanshi Almustapha bai sani ba, yayi ta bibiyar rayuwar shi, har aka ce min ya sauka a gezira. Amma ban tab'a zuwa ba, wannan shine zunubin da na aikata, sai Abubakar kuma, Babu ruwan mu a cikin mutuwar shi, domin an hanya tasaka aka kashe shi wannan kan ba ita daya bane har da Abdullahi, Mutuwar Aliyu ma haka har da su. Domin Umma da ta ga lallai Mulkin gidan ya koma kishi a tsakanin zubda jini ta hana mu shiga cikin maganar gidan.


Bayan haka toh mun fara jin ƙishin ƙishin, Sultan zai yi murabus, kuma ana zargin Amir Rahil zai bawa, shine na kawo ki."
Kukan da nake ya kura min ido.
"Wacece ke?"
"Bilqisul Ikram! Yar Amir Almustapha Mu'allim! Idan na kashe ka na b'ata kome, zan Barka a raye domin Rahil kuma, zan dawo kamar yadda nace, .maka amma zan karasa aikin da azo yi sai dai ba gawar Amir Rahil bane, gawan mutanen da suka yi wanka da jinin Ahalina zan bar su. Domin akwai sauran aikina."


Juyawa nayi na fita daga gidan, nayi kuka nayi danasanin kuntatta mishi, ashe dan uwana ne,nake ta bashi azaba, shi yasa suka ki bashi tarbiyyar sarauta...


Haka har na isa gidan, ban kuma kwanciya ba, domin a duk lokacin da na kwanta bana iya barci, sabida Rahil gani nake kamar ina rufe idanu na zasu far mishi.


....
A hankali har kwanakin da za ayi gasar ya shiga zuwa, kamar na san ana shiri a kaina, ranar na dauke shi har gidan Amira Raziyana, tun da Samir ya ganni,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads