Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 274096 words

Chapter 5 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1340

Ads at the middle of Article

gamawa na dauki kayan da sauri na dawo gida, dan a tsora ce nake da gurin, kasancewar nasha samun labarin an tare yan mata a gurin an musu Fyade, sai abin ya bani tsoro.


* Ikram Almustapha, shine cikakken suna na, mahaifina makiyayyi ne, kuma bakin Balarabe ne, kasancewar muna da alaka da larabawa, yasa dabi'ar mu sak da bafulatanin daji, sabida kakana da ya haifi Mahaifiyata Yazeed Balarabe ne na kasar meroccon,


Dan haka Mahaifiya ta fara ce sol, mahaifina ne bakin fata, mahaifiyata ta rasu sakamakon dogon nakuda, ta barni da kanwata Airan, sai ni Ikram. Bayan rasuwar ta ne ya auri Mamma me sunan Kanwal, tunda ya aurota matar nan ta daka rayuwar mu, uku ta kuntatta mana, amma a haka muke rayuwa.


Mahaifin mu yana da hakuri, tare da kauda kai. Shi yasa matarshi take cutar mu, sai dai yace min.
"Kuyi hakuri, Allah zai duba maraicin ku, Ikram Insha Allah ba zaki gushe ba, sai Allah ya duba miki rayuwar ki, duk inda kika yi Allah sai ya kare ko da karfin ikon shi. Kayu hakuri Allah zai albarkaci rayuwar ku."


. Wannan shine kalaman shi a kullum, lokacin da Baffa ya aureta yana da dabbobin shi, amma daga baya duk ya kare, ba tare kwashe su tass.


Mu biyu Baffa suka haifa shi yasa yake nuna min lallai duk wuya duk rintsi kar na sake na rabu da Airan.


--- koda na dawo na shanya kayan, na duba madafi babu abinda zamu ci sai guntun tsakin alkama, ita na watsawa ruwa ba wanke tare da hada wuta na turara shi, bayan na samu yayi..na juye mana, wani kwano na dauka me dauke da maikon mai.
Na zuba mana a cikin na juya, tare da ɗaukar kwanon na kawo daki, a hankali na shiga hurawa Baffa ina bashi.


Sai da ya koshi, sannan na raba mana, nida Airan muka ci sauran. Tare da kallon ta, dan abincin babu yawa, kawai sai na tsame hannuna na bar mata, nasha ruwa na kwanta.




Noman Anwarulkharim, shine sunan saurayi na, mahaifin shi ne hakimin garin mu, Noman shine d'a na uku, a gidan su. Yana da yayu mata biyu da kanen biyu,


Babbar Yayar su, Malikah, Ajeebah, sai shi. Kanen shi, Quraibah, Saghirah.


Noman yana da ilmin addinin musulunci, da kuma ilimin duniya, domin duk cikin yankin mu babu wanda ya tab'a fita wata duniya yayi karatun su, sai shi.


Duk da dai daidai gwargwado ilimin addinin mun iya kuma muna yaki da jahilci. Noman malamin mu ne a makarantar masu jan kunne, duk da a lokacin mun iya Rubutu da karatu, a yanzun haka na kusan hada Alqur'ani, a gefe guda. Ma ina da ilimin litattafan addini, burin Baffa na kenan. Dan yace min Mahaifiyata, tana kamata ta haɗa Alqur'ani, dan haka nima nayi ƙoƙarin haka.


Shi kuwa Noman wanda nake yawan kiran da Sayyid, mun hadu ne a wani hatsarin da ya kusan faruwa dani, matasan larunga, wasu irin matasa ne masu shegen rashin kunya da rashin mutunci, sannan sun addabi kauyen mu, bamu isa fita kiwo babu namiji ba, duk inda zamu dole mu sami rakiyar namiji, domin idan suka kama mace suna cin mutuncin ta ne, na fitan hankalin, toh ranar tun asuba Mamma ta kore ni kiwo, ina fita bakin rafi lokacin matasan sun tawo ayari guda, dan haka suka shiga ƙoƙarin rabani da mutuncina, har Allah ya kawo min shi,


Tun lokacin nake kokarin b'oye kaina, amma ya nuna min shi bai san kome ba, sai so. Ya nuna min so ne yake tare shi, dan haka abinda yazo min dashi kenan, kuma nima na amshe shi a matsayin mutumin da ya dace da rayuwar.


Duk da matar Mahaifina bata kaunar shi dani.


Wannan shine tarihina, a hankali na juya, na saka hakarkarina.
"Ikrammmmmm!"
Baffa ya kira sunana.
Da sauri na mike daga kwanciyar da nake na nufi gurin shi.
"Baffa gani!"
"Ruwa nake so zan sha!"
Juyawa nayi na fita daga dakin, na dibu mishi, d'aga kan shi nayi na bashi ya sha, har zan cire ya kuma maida kanshi.


Naji tsoro ya kamani, kallona yayi dukda hasken dakin na aci balbal ne, haka ya kura min ido.


Kiftawa yake yana kuma kallona, abu yake son fada amma ya kasa, cewa kome.


Kallon kwayar idanun shi nayi na fahimci akwai abinda yake son fada, amma bani da yancin Sanin abinda yaƙe cikin ranshi.
#Mai_Dambu#Paidbook
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜


_The Historical_
~BOOK ONE~


Bismillah Rahamani Raheem


Page 7....


*SAMAIND*


Kallon Khabir tayi babban hannun Damarta, ta gyara zama tace mishi.
"Hmm!"
Zuba gwiwar shi yayi a kasa, sannan ya kai hannun shi kirjin shi yace mata.
"Sultanah, mun daidaita dasu. Har sunyi mana kyautar bayi, masu yawa. Akan ki huce!"


Dauke kai tayi tare da mik'ewa daga inda take zaune, ta nufi gaban tagar da yake hango mata haramtacciyar fada.


"Bana jin haka da kuka yi da wata alfanu, ina ji a jikina yarda zai haifar da cin amana!


Kafin kai nasan halin mutane da yawa, dan haka karka yarda ka ci Amana ta, ya kuka yi da Abrad?"


Jikin shine yayi sanyi sannan ya sunkuyar da kai. Muryan shi na rawa yace mata.


"Sultan Abrad zai badda Kanwar shi!"
Ya faɗa a tsorace,
Ta dauki lokaci tana share hannunta, sannan ta koma mazaunin ta,ta kalle shi.
"Idan na kashe ka, zasu zuba idanu akai na, idan na Barka zasu kuma jin wata magana daga gare ka?


Dan haka kayi tafiyar ka, idan zaka fita ka dauki wancan sakon ka tafi dashi."


Jikin shi na rawa ya zube a gabanta.
"Abinda kika ce shi zanyi"


Mik'ewa tayi tare da cewa.
"Ka kula da harshenka, domin zai iya kai ka, hanyar da ba zata dawo da kai ba.


Kuma bana son na fahimtar da kai wacece ni"
Tunda ta shiga shashin duk masu kula da lafiyar shi, har dasu Darakshan da Faduil. Kallon shi tayi na wasu dakikai, sannan ta debi abincin a cokali ta kai bakin shi.
Buge hannun ta yayi, sannan ya dauke kan shi akan Abincin.
"Aaman!!!"
Kamar da dutse take magana, yaki ko kallonta.
"Me yasa baka amsar tayin da ake turo maka, dukkansu bayi ne babu."


Mik'ewa yayi tare da, gyara zaman alkyabar yayi cikin wani shegen miskilanci, wanda ya zame mishi kamar rayuwar shi ce, zai bar shsshinta
"Aamaan ko baka da lafiya irinta maza ne?"
Cak ya tsaya sannan ya gyada mata kai, alamar eh.
Daga haka ya bar shashin, Indai haka ne toh tabbas akwai matsala ta wani gefe,. Wani ƙasaitacciyar murmushi ta sauke lokacin da hasashenta yazo mata dai dai dan haka a ranta taji ba zata iya daukar nauyin kula da lafiyar shi ba, dama tayi kokarin tasan ko yana da matukar bukata ga Y'a mace ne, sai kuma ta Fahimci shi irin mutanen nan ne da basu cika damuwa da mace ba, ko da yake ai baida lafiya ce ta kawo haka.
Tunda ya shiga babban filin da yake hawa na biyu na castly din ya shiga juyi tare kallon Fudail.
Takobi ya dauka tare da yin kan Fudail, da azabben sara, cikin wani irin zafin nama..ya goce.
Cikin mugunta da mugun nufi ya shiga kaiwa Fudail sara da suka..


Tun yana gocewa har ta kai baya iya gocewa sai kare kanshi yake,
"Sultan Aaman mun tuba Mehra"
Cak ya tsaya, tare da cillar da takobin yana huci. Kallon kwari yayi tare da ɗauka. Cikin b'acin rai ya dauki bakar ya haɗa.


Tare da sakewa inda yake koyan horo, yi yake yana kuma yi, idanun shi sun yi jajjur. Kalmar da Mahaifiyar shi ta gaya mishi ne yake kara azazzlar shi.


Bai san dadin abota ba, kallon kowa yake da wata zuciya duk cikin su bai yarda da kowa ba, sai Darakshan. Domin yasha ganin shi yana yawan shiga damuwa, yazo yayi ta mishi magana, kuma har yau bai tab'a ko da cewa Darakshan sannu ba,, duk abinda yake cikin, matukar zai gan shi a gurin sai yaji ya sami nutsuwa a ranshi, domin dukkan su masu kula da lafiyar shi,. Darakshan ne ya iya mu'amala da shi.. a hankali ya juya da a sanyayye kamar wanda ya rasa lakar shi ya haura saman gidan shi. Kallon juna suka yi, tare da sunkuyar da kai.
Babu wanda ya isa yayi magana sabida ko tari ba ayi a cikin gidan. Magana me tsayi basu yin shi, sai dai hiran kurame.


Kasancewar manmallakin gidan baya son hayaniyar mutane, idan kaji hayaniyar mutane, toh wasan takobi ake anan ne zaka samu yana sarrafa takobi kamar wanda ya kware a filin daga.


Tunda ya haura zama, ya koma tagar dakin shi, ya zauna yana kallon yadda rana take tafiya zata fadi yamma.


Bai tab'a ganin yadda ake rayuwa a waje ba, shi kawai abinda ya sani ya zauna a sama, sai idan ya najin nishadi ya dauki takuba.


Lumshe idanun shi yayi tare da buɗewa, ya sauke ajiyar,. Sauke kanshi yayi kasa, yana kallon tsohon fadar da ba a amfani da ita, har ya nuna alamar babu wanda ya damu da ita. Kallon wasu tsuntsaye yayi ya ga sun nutsu suna shawagi, kallon su yake yadda suke rayuwar su, sai yaji haka yayi mishi dad'i ina ma da zai sami sabon rayuwa, tabbas zai yi yawo kamar yadda yake so, shi mutum ne da yake son rayuwar bude ido, kisan shi.yana zaune a guri daya ne,


Amma da ya sami damar fita kamar kowa tabbas zai zama wani abin alfahari a gurin shi


**
Haramtacciyar fada.
Kallon kanta take a jikin wani tsohon madubi, me dauke da yanar gizo da kura. A hankali ta taka har gaban madubin.
"Sai da soyayya ake iya cin Amana, idan babu soyayya babu wanda zai yarda da wani! Shairah, madubin nan yana faffutikar ganin ya tuna min gobe na! Shairah har yanzun da sauran lokaci ko? Tabbas zan rama shekaru talatin da biyar suna cike da zuciyar da aka yasar da ita ?" Inji Sultanah Fazilatul nisa,
Sunkuyar da kai yayi sannan yace mata.
"Ya shugabana, duk abinda kika ce haka za ayi, amma ki cigaba da tausar zuciyar ki."


"Narjis! Kinji abinda Shairah yace, wai na kara hakuri anya zan iya." A hankali narjis ta kalli. Darda,


"Zaka iya shigowa."
A hankali ya shigo, cikin nutsuwa ya nufi kusa da Sultanah Fazilatul nisa.
"Sultanah kome ya tafi yadda kika tsara."


Rabonta tayi murmushi tun ranar da aka kawo ta dakin.
"Insha Allah, sai na fanshe bakin ciki na, sai na murza mulkina. Sai na hana kowa suku ni."


Dariya take tare da kallon su, tana dariya tare da zama tace.
"Ku dauki gwala-gwalai na ku raba a tsakanin ku, ku dauki kome na mallaka, ku kai cikin garin ku rabawa al'umma.


Kuyi kyauta da sutura ta, ku kwashe kayana, ku raba karku bar min kome, Burina da muradina ya kusan cika, Alhamdulillahi."


Zuba gwiwar ƙasa tayi, tare da fashewa da kuka. Tayi kuka ta kuma, tare da komawa gefe ta cusa kanta a tsakanin cinyoyin ta. Ajiyar zuciya take saukewa, sannan ta cire kanta, tana kallon su tace musu.
"Wallahi ban kashe Sultan Abdus Samad ba."


"Sultanah mun zan ba zaki kashe shi ba." Share kwallar tayi da bayan hannunta, kamar yarinya ƙarama tace.
"Toh me yasa baku gaya musu."
"Sultanah idan muka gaya musu ba yarda zasu yi ba, kuma karshe hukuncin kisa zasu yanke mana."


Gyada kai tayi, sannan tace.
"Zaku taya ni wannan yakin?"
"Sultanah zamu tayaki matuƙar ya kama daukar fansa ce, bayan haka ba zamu iya taimaka miki da abinda ya wuce haka ba "


Kwalla ne ya zubo mata, tayi ta gyada kai tana share kwalla, kafin tace.
"Har raba ni da dangina suka yi"
"Allah zai baki dama akan su."


Haka suka yi ta rarrashin ta, tare da bata baki.

*Damascu*
Yau kwana uku kenan, yana zaune a fadar shi, kallon shi Sheikh Saiful Badarr, ya gyara zama sannan yace musu.
"Karku ha'incin masarautan Samaind, sabida sun fimu karfin mulki, sannan koda aka ce zamu gwabza yaki dasu mune a kasa, ku basu abinda bakin ka ya faɗa, tunda kace Almirah Azizatul Nissah zaku basu."


Dakatar dashi Sultan Abrad yayi, da sauri.
Yana kallon mutanen fadar.
"Bahhas ka tabbatar yau kun dauki ayari zuwa Andulus, karku manta ku zab'a mana mace mafi daraja, karku damu da tsannanin kyau, kawai ku nima musu wacce zata jure duk wata wahalar su."


"Insha Allah, Rabbi."
Haka suka juya zasu fita, yace musu.
"Karku manta ku nimo musu wacce zata zame mana fansa ga kanwata. Tun bayan mutuwar Dariya bana fatan kanwata da Y'ata su kuma fadawa Matsala."


"INSHA Allah."
Mik'ewa Sultan Abrad yayi, tare da barin fadar, yana shiga cikin gidan sarautar ya wuce dakin da Kanwar shi take, ya same su tare da yarshi, suna zaune sai hira suke tare da yar shi, a hankali ya shiga cikin dakin, yana jin duk wata nutsuwa yana sauko mishi.


Wato da ya Kuskura ya sake Kanwar shi ta shiga cikin wancan gidan, akwai matsala domin kuwa zai rayu cikin bakin ciki da tashin hankali har karshen rayuwar shi. Shi yasa da wancan me rufin fuskar ya kawo shawara ya amince.
"Abbi!"
"Yaya!"
Murmushi yayi sannan ya tako gaban su da sauri, ya rungume su. Dariya suka saka tare da kara rungume su.


"Almirah!"
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Yayana, naga farin ciki da bakin ciki a fuskar ka?" Ta tsura mishi ido, zama yayi kusa da ita, sannan ya bata labarin abinda yake faruwa.


"Amma da baku amshi tayin wancan mutumin ba, idan ya kasance shi din munafuki ne fa?" Ta tambaye shi tana kallon shi.
Shiru yayi sannan ya sunkuyar da kanshi kasa, kafin yace mata.
"Mafita nake nima! Kuma ba lallai bane idan aka tura baiwar a sami biyar bukata, ki bani haɗin kai don Allah karki bari wani abu ya dame ki..."
Mu hadu a next page Insha Allah..
#Mai_Dambu
#Paidbook
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1032132293?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=a7uCjjAvUSJSKPRj92lkHRqYhhrfYA3lHRyw28GFKsPFnIgz2LhKAsyWyZ%2FT4tyTFv%2FZXjTsoXVfLCBqiF0Z9D8z7QeQxtX2I1QXt6H6fQgMzsSw37mphWhiwp71eIKk
🐾ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜🐾


_The Historical_
~BOOK ONE~
Mai_Dambu


Bismillah Rahamani Raheem


Page 8
2in1
"Ba mafita ka nima ba,"
Zuba mata ido yayi sannan yace mata,
"Mafita ce, domin suma basu bukatar Y'a! Baiwa suke nima, idan aka basu Y'a zasu wulaknta ta, amma baiwa a wulakance zata rayu"


Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Allah shi ya halicce mu, sannan a cikin zukatar mu ya sanya mana, juriya da hakuri. Ita baiwar wata rana Allah zai."


Mik'ewa yayi tare da shafa kan Yarshi, ya bar d'akin dan matuƙar ya cigaba da sauraron ta,zata iya sanya mishi karamin ciwon kai. Fatar shi mutanen da ya tura Andulus su kawo mishi abinda yake son kare martabar Daular shi.


***
GIZERA


Haka yayi ta kallona, sannan ya riko hannuna cikin nashi, yace min.
"Ikram! Airan!!!" Hawaye ne suka shiga sauka daga idanuna, sannan na rike hannun shi.
"Ikram Airan"
Juyawa nayi na kalleta, tana barci a saman tsumar mu, cikin kwanciyar hankali.
Ajiye shi nayi tare da kofin ruwan, na juya na nufi gurinta, tashinta nayi.


Koda na tashe ta, muka dawo gurin shi, kallon mu yake tayi, hawaye na zuba mishi. Ita dake barci yaci karfinta, haka ta jingina da jikina. Hada hannun mu yayi da ita, tare da cewa.
"Insha Allah, sai kin zama mace mafi daraja a duniya!"


Daga haka ya lumshe idanun shi, hawaye na zuba mishi, juyawa yayi ya kwanta, a hankali yake sauke ajiyar zuciya. Wanda yake nuni da cewa yana jin jiki. Kwantar da ita ayi a kan gwiwata,


A haka muka kwana, da asuba na mike tare da dibo ruwa. Nayi mishi alola, duk yadda naso ya tashi yaki, wani irin tashin hankali nake ji yana cika min rai, da gudu na nufi dakin Mamma, na burmu. Kwance na same ta da wani mutum.
A firgice suka farka, tare da kallon na suna rufe jikinsu.
"Yar mijinki ce?"
"Eh Jonah!"
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Kina da kayan dukiya kike b'ata lokacinki?"
Wani irin rawa jikina ya dauka,
"Mamma Baffa baya motsi fa"
Na fada ina ja da baya sabida yadda mutumin yaƙe kokarin riko hannuna, da gudu na fita.
"Allah ki duba abinda nace, yarinyar zata yi cire ki a halin talaucin da kike cikin shi?"


"Amma taya?" Inji Zariya!
"Ta hanyar sayar da ita, a kaita babban birnin kasar nan, tayi aikatau."
"Sayarwa kuma? A'a sai dai na baku kuna biyana kuɗi"


Matseta yayi sannan yace mata.
"Karki damu, za ayi haka."


Jin Ihun mun yasa mutumin banzan ya bar gidan, da sauri tare da niman hanyar tsira, yana fita ta samu ta shigo, daga nan ne fa ta fahimci, mutumin da take wulakantawa ya ya koma ga mahaliccin shi. Sai lokacin ta samu damar saka hannu a kai ta fasa ihu.


Tare da fitowa waje tana kururuwa, Kafin wani lokaci zuwa sallah asuba, har an shirya Baffa.


Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads