Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 274096 words

Chapter 4 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1344

Ads at the middle of Article

shirya yaki ba, amma zaku iya samun damar shiga tsarin mulkin ta karkashin kasa, shima lokaci ne zai baku damar haka.


...kai Fujai da Kaisan, mutuwa zaku yi irinta wulakanci da kaskanci, kai Kuma zaka yi dogon zamani, amma bakin ciki zai kashe ka.


Kamar yadda ake mutuwa a cikin sahara idan ruwa da guxirin suka kare, haka idanun kowa zai bude, shekara bayan shekara zata bayyana kanta, babu alamomi ta, amma tabbas wannan mulkin mallaka zaku rasa shi, za a shafe kome zai zama tsarin Ubangiji shine sama da kome.


Kamar yadda kuka zalinci kanku haka kome zai zo, ya faru...


Acct: 0472282105
Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK! +2347035133148 zaku iya tura shaidan ta Number Zahran Adda Ramlat,
#Paidbook₦200 nafi son ta bank, katin mtn 300₦
#Mai_Dambu.
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1031122018?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐾*_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*🐾


_The Historical_
~BOOK ONE~


Bismillah Rahamani Raheem


Page 5...
"Karya kake mushiriki! Karya kake Azzalumin mutum, Ni ba zan yi mutuwar wulakancin ba, nawa Amir Hood ya biyaka? Ni zaka kalla kace mutuwar wulankanci zamu yi?"


Murmushi kazugumin bokar yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Kaisan ka haifi d'a namiji! Amma ba zai hana ka mutuwa ba, haka kai ma Fujai."


Hawaye ne ya zubo daga cikin idanun su.
"Mafi yawancin ku, zaku mutu ne da tabon cin amanar juna, ku kiyayye abinda kuka aikata, kai ma Hood baka tsira ba, domin gwara su mutuwa zasu yi, kai kuma kaskantacciyar rayuwa zai ayi har lokacin da zaka sami damar sarrafa abubuwan da dama, zaku iya tafiya."


Silalar zinari suka bada, sannan suka bar gidan, zuciyar su cunkushe da tashin hankali, musamman Fujai da Kaisan, da zaka tsaga jikin su, zaka samu babu jini sai zunzurutun tashin hankali. Babu abinda suke tunawa sai bayansu. Wato yaran su, tashin hankalin da yake nukuskusa zuciyar su ba a fada.


Amma tabbas suna tsorace da abinda zasu je su tadda a gida ba. Dan haka suka kalli Amir Hood.
"Tabbas daga yanayin da muke tinkarar Daular mu, na Fahimci akwai tashin hankali a cikin shi.


Duk da bamu san meke faruwa ba, amma don Allah ga Yarona da baida Uwa sai ni ne Ubanshi nine Uwar shi, na haɗaka da Allah ka sanya min ido akan rayuwar shi."


Inji Kaisan yana zubda hawayen bakin ciki, haka ma Fujai ya bada d'an shi da matar shi. Suna kuka suna kome haka suka iso birnin Samaind, suna shiga kofar masarautan, aka zagaye su. Tare da kama Amir Kaisan da Fujai, aka tafi dasu. Shi kuma Amir Hood aka wuce dashi fadar Sultanah.


Wacce take zaune bisa kujeran mulkin masarautan. Yana shiga ya zube a gabanta, yana cewa.
"Rayuwata da kome na mallakar ki ce Sultanah Hoyam, kiyi duk abinda kike so koda kuwa sare kaina zakiyi ina shirye na sadaukar da numfashina domin ki"


Sai da tayi shiru na wasu dakikai, kafin ta tsura mishi ido, sannan tace mishi.
"Kuskuren ku daya ce, na bincike akan wanda ya shirya yaƙi? Dan haka ba zan hana walwala ba, domin barin makiyi a raye shima wata nasara ce da Ni'imar rayuwa, zan Barka ka rayu a cikin yanayi mafi kaskanci, ga dai mulkin ina kanyi amma babu wanda ya isa dakatar dani.


Dan haka kuyi hankali dani, domin zan iya shafe dukkan larabawan wannan daular na zuba kabilata"


D'aga haka tayi alama da hannu a dauke shi ya bar mata fada.


Da wannan damar Sultanah ta cigaba da mulkinta, har tsawon shekaru masu yawa cike da zalinci da azabtar da duk wanda yaki mata mubaya'a, sanan ta kuma kange danta da kowa, domin ko cikin mutane bata barin shi ya shiga ita ke tare dashi.
***
Aaman na da shekaru goma, aka gina wata (castly) kamar gidan sama ne kamar me, mafi girma da tsawo, wanda ita kanta Sultanah tayi shine sabida D'anta, ta kuma yi nasarar nisanta shi da al'ummar mutanen kirki. Sai ma wasu Yara irin shi aka kawo Darakshan da Kuma Fudail, duk da an kawo su, iya kansu. Akan abinda zai yi ne ba yaki, bayan nan basu da hurumin shiga koda babban falon shi. Kuma duk da kasancewar su a cikin gidan bai saka ya kalle su a cikin masu sanya shi farin ciki ko abokan hira ba.


A hankali ya tashi cikin kaɗaici sosai, bai da abokin tarayya bai da abokin hira, ya tashi cikin wani irin miskilanci da mugunta, domin an zuba mishi dakaru sama da dubu dari shida masu kula da lafiyar shi, sannan a gurin ake bashi horon yaki na fitar hankali.


Domin an cire mishi wata shashi na musamman, domin horon yaki. Yana da shekaru sha tara, aka fara mishi gwajin lafiyar shi na d'a namiji ta hanyar kawo mishi yan mata, masu rufaffen fuska, yana kwanciya dasu.


Shi kan shi daga lokacin ba zai iya tuna me ya faru ba, amma sam bai da ra'ayin kasancewa da mace, bai san yawan yan matan da ya kwanta dasu ba. Sai dai kuma wani abu da ake zargin shi musamman Sultanah Hoyam. Wato mahaifiyar shi.


Shine idan aka kai yan matan, haka zai a fita dasu, dan wani lokaci yana gaya musu bai da lafiya, ya fara wannan salon ne daga lokacin da ya hadu da yarinya take gaya mishi don Allah kar ta mata kome ita makauniya ce, satota aka yi, itace yarinyar da ya kyale ta, bawai dan yana tausayin ta ba, sai dai wani irin yanayi da yake jin yana cikin koshin lafiya ya rasa macen da zai kwanta da ita, sai miskiniya.


Haka kawai ya saka kyamar kwanciya da Yan matan, daga karshe aka fara zargin ko yana luwadi ne, kuma masu kula da lafiyar shi basu tab'a ganin shi da namiji ba.


Haka Ya tashi babu abinda ya sani sai mugunta, domin kuwa idan aka kawo mishi matan, hana su shigo mishi turaka yake.


***
Bayan shekaru talatin da biyar,


"Wai ku nan zaku iya ja ne da Sultanah Hoyam?"
"Khabir baka da hurumin magana akan Iyakokin mu, ku sa kuke da lusarin magajin sarautar ku,sannan ita kanta Sultanah Hoyam din wacece ita?


Ko ance muku bamu sami labarin irin mulkin mallaka da take yi bane? Dan haka karka fara shiga iyakokin kasar mu, sannan bakin haure da suke shigowa ba zamu dakatar da su ba, sabida son zuciya irin naku, idan kuna son mu tsaya akan ra'ayin ku, ku sauke mace a mulkin ku"


"Zulushimalain! Karka gaya min maganar banzan kai waye kai." Cikin fusata fadawan daular Umayyad suka far musu sai da suka kashe su, sannan suka bar Khabir.
"Ga sako nan! Ka kaiwa wancan Yarinyar, ka gaya mata mun shirya tsaf domin kare kasar mu, idan ta kuma ihu kamar kare zamu mata kisar gilla."


Bayan sun gama suka sari cinyar shi tare da daura shi bisa raƙumin da tarin dukiya, suka kuma hada da Zungurerren takardan cin mutuncin da fusatar zuciya.


Lokacin da magatakardan masarautan ya fara karanta lafuzan da aka rubuta a takardan, wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyar shi da ruhin shi, zuɓewa yayi tare da fashewa da kuka yana fadin.
"Kaicona na shiga uku na lalace, me yasa suka rubuta abinda ba zan iya karantawa ba, na tuba shugabana kiyi min rai ki karamin nisan kwana."


"Hmm!" Tayi mishi alamar ya cigaba da karantawa, haka yana rawa tare da makarkata, yake karanta labarin yana zubda hawayen, har ya gama karantawa.mikewa tayi tare da barin dare bata ce kome ba.


Sai da aka kwashi kwana goma ana zubawa Sultanah ido akan abinda zata aikata, kawai tasa aka tura musu da sakon.
*Ya kai karamin mutum! Kazo daulata ka bani hakuri tare da durkusawa a gabana, Ni kuma Sultanah Hoyam Ghanim zan maka afuwa na yafe maka! Rashin bin abinda nace zai iya zama tashin hankali a dukkan Daulolin guda biyu*


Wannan wasikar kaskancin da aka tura ga Sultan Abrad, yayi masa zafi domin bai san abinda ya faru ba, kawai shima ya saka aka rubuta mata na cin zarafin ta tare da bakakken magana da har suka kira ta, da koriyar macijiya.


.... Wannan dalilin ya saka aka fara shirin yaki, inda Sultanah ta shirya dakarun miliyan uku da dubu dari tara,. Lokacin da yan leken asirin Daular Umayyad suka sami labarin, take suka tura. Aikuwa dole hankalin mutane ya tashi aka korafin babu yaƙin da za aje kodan Albarkacin mutanen da suke zuwa niman mafaka, Sultan Abrad ya duba maraicin su ya nime sulhun.


A take ya shiga niman taimako yankunan jazziratul Arab emirate, su bashi hadin kai domin yakin da Sultanah, duk suka ki, karshe Sarkin Yeman Abul Hassan shi ya turo mishi da wasikar cewa ya nime sulhu.. dan haka ya shiga niman hanyar da zasu dai-daita. Dan haka ya shiga niman.mutanen da zasu tsaya mishi.


Karshe Amir Abdul shakoor na kasar Dubai, shi ya gayyace su, tare da wasu sarakunar larabawa, aka shiga tabirin sulhu, dakyar aka samu Sultanah ta sauko dake ta tura wakilanta ne da yadda zasu ja, kafin aka yarda. Suka dai daita inda suka nime Abrad ya bada Kanwar shi Azizatul Nissah. Bayan nan kowa ya kama gaban shi.


Hankalin Sultan Abrad ya tashi ainun, domin baya kaunar ya bada Kanwar shi, dan haka sukayi ta tattaunawa.
"Bamu da zab'i! Bamu da iko! Dole mu dakatar da Iran, zubda jinin ya isa haka, Jama'ar mu!" Ya karshe maganar a raunane yadda zai fahimtar da kai yana cutuwa daga halin da al'ummar shi take ciki.
Cikin nutsuwa mutum min da yake gefen shi ya sunkuyar da kan shi yace.
"Allah ya taimaki Sultan Abrad! Ina gani ka basu ƙanwarka tayu a kawo karshen rikicin dake tsakanin masarautu biyu!"


Watsar da kayan dake yake gaban shi yayi, tare da rintsa idanun shi kan mutumin da yayi maganar cikin tsawa yace.
"Murad kayi hauka ne? Ka haukace ne? Toh bari na gaya maka, wannan yarjejeniya ce idan baka sani ba, ba zan tab'a daukar kanwata Almira Ashnah na bawa wancan Mahaukacin ba!


Kasan me suke nufi idan muna son a janye yakin dake tsakanin mu? Na basu kanwata su mai da ita baiwa, akan me zan taso daga daulata nazo nan Dubai nimar baiwa da zata dace da gidan mu.


.... Ruwanka ka zab'a min kyakyawa! Ruwanka ka barni na zab'a da kaina. Amma ka tuna Daular Larabawa sunki taimaka mana, sabida kowa yasan kasar Farisa da fitina.!"


Daga haka ya saka kai zai fita, aka kwankwaso kofar dakin. Kallon Murad yayi, da sauri ya buɗe kofar dakin wani mutum sanye da kaya fuskar shi a rufe ya shigo dakin.


Kallon Juna suka yi da Sultan Abrad, shi kuma ya kalli Murad ya fita da sauri, har yana tuntube.
Rufe kofar yayi sannan ya zuba mishi ido.
"Har yanzun baku nime hanyar sasantawa da kasar Farisa ba ko? Toh kuwa yaki zai ci kasar ku, dubanin dukiyoyin dake cikin masarautar zata lalace, kasa zata sha jini. Sannan mata zasu zama zawarawa, yara zasu zama Marayu. Bamu son ƴa me yanci!


Baiwa muke nima! Baiwa muke so! Idan kuka bamu ƴa ba zata iya zama shiru ba, bamu bukatar sarauniya a cikin masarautan, sarki kawai ya ishe mu!"


Mik'ewa mutumin yayi zai fita, Abrad ya rike hannun sa, cikin damuwa.
"Ka taimake ni! Idan ban sami baiwar ba ya zanyi! Wallahi bana son azubda jini a daulata!"


murmushi mutumin yayi sannan yace.
"Ina da wani dan Safara a nahiyar Afirka yanki yammacin su, akwai kyakkyawan mata a gurin, amma ba asalin kyakyawa muke bukata ba, domin bamu son soyayya ta tsaga tsakanin zukatar mutanen masarautan."


Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke, sannan yace mishi.
"Toh! Waye shi?"
"Yana kasar Andolus! Shaibaan. Dan kasar Saudiyya ne,"
Cikin yarda da ƙaddarar su, Abrad yace.
"Yau ashirin ga watan Agustan, Insha Allah kafin watan goma na wannan shekarar, zan turo muku ita cikin daular ku.


Indai haka zai kare zuciyar da take cike da kaunar Juna, nayi alƙawarin haka."


Ya faɗa tare da jaddadawa akan shi abinda yake da Muradin faruwar shi.


Bayan fitar mutumin da basu san fuskar shi, take suka fara hada shirgin su, tare da jin sun rabauta daga wannan yanayin.


Dan haka suka nufi daular su cike da kwarin gwiwar abinda zasu iya aikatawa.
**
Gezira Sudan.
Wata karamar gari ce, wacce take tsakanin blue sea, gari ce da a da can baya ake kiran ta da. Jazira, daga baya aka maida ta gezira, mafiya yawancin mutane yankin makiyaya ne, masu kiwon shanu da rakumai, kasancewar garin yana tsakanin ruwa ne, kuma ga shi ana hidimar cigaba ga lambuna da kuma inda makiyayya sune kiwon su. Babu tashin hankali sai yawaitar Arziki da cigaba, dan wani lokaci idan akwai tashin hankali babu Cigaba da ake samu.


..... Watsa min ruwa yayi na sake murmushi, tare da kallon shi, girgiza kai nayi ina wanke tufafin Baffana.
"Ikram!" D'ago idanuna masu kalar ta mage nayi na kalle shi,
"A duk lokacin da na kalle ki tsoro kike bani"
Mai kai na nayi tare da cigaba da aikina.
Dawowa yayi gabana ya amshi wankin hannuna,
"Ikram! Ina ji a raina wata rana zamu kasance tare, amma bana jin zamu yi tsawon rayuwa a tare."
Nan ma ban kula shi ba, sai da na gama dauraye kayan na nafi gurin shanya.
#paidbook
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/970384685?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=l43AacEqBsPiLlYx5dhUheB%2F6jOni0C%2FxhyeNcS9TpekWSOB8YCl6xXvPHaqW4bRGWROavXnJPdrwFm8rAjS2tmZwTvI3QQgXPSh3Q6sUDHNdzt%2FH%2BdwCgongFSjFBz5
ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜


_The Historical_
~BOOK ONE~


Bismillah Rahamani Raheem


Page..6
Sake shan kaina yayi tare da cewa.
"Zuciyata tana yawan bugawa idan na kalli kwayar idanun ki! Ina ji a raina ban cancanci."
"Noman!" Na ambaci sunan shi a sanyayye, kafin na cigaba da aikina.
"Ikram!"
"Me kake so nace? Ina kowani abu ne dan kare kai na kimar mahaifina, baka ga yadda Matar shi ta mai dashi ba? Ina ma zan iya goge zanen ƙaddara ta da kake hangowa! Ina ma zan iya fuskarta Gobena da kake hangowa.


Banda sakewa na baka kai na shine abu mafi muni da Zubewar kimata,Noman kai ne mutum mafi kusanci da ni, don Allah ka bar azabtar da ruhina"


Amsar kayan yayi a hannu na, tare da kallon cikin idanun ta.
"Sirrin kyanki yana cikin kwayar idanunki, ba kowani cikakken mutum bane zai fahimci ainihin sirrinki, Ikram ina miki kaunar rai da rai ne, wallahi na rantse da Allah babu macen da zan iya sadaukar da rayuwata akan ta ba sai ke!"


A hankali ya tako gabana, har numfashin mu yana jauraya da juna, yana kallon cikin idanuna.
"Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki, da ya halicce mace mafi kyawun idanun a cikin wannan nahiyar tamu, Ikram kina tattare da sirri na musamman."
A hankali ya lallubo hannuna, ya kai saman fuskar shi.
"Ba dukkan mutane suka san meye So ba, so yana karewa. Amma kaunar da nake gani cikin kwayar idanun ki, ya ishe ni."


A hankali na zare hannuna, tare da amsar kayan hannun shi, na bar gurin. Tare da tattara kayan baki daya. Ina tafiya yana bin bayana. Tare da wakokin yabo da wasu baitoci..
(Yawwa toh wallahi zanyi waka. Kar kuma ce muryan ba dad'i 😻
_So da kaunarki ya mamaye zuciya da ruhina_


_Mafarkin zuciyata ke ce!_
_Muradina taki ce_


_Kece kaunar zuciyata_

_Ruwa da iska, dare da rana_ da kaunarki nake kwana_


_Abar kaunata... Kin zame mini farin wata na! Farin ciki na, maganin bakin ciki na_


_Murmushinki maganin bakin cikina! Dariyarki maganin kuka na!_


_Abar kaunata ki kaunace Ni Ko zan samu daman kiran kaina namijin Soyayya_


Juyawa nayi ina dariya, sannan nace Mishi.
"Kana da kyan hali, kana da dadin mu'amala, kana da kyakkyawar alaka da mutane.


Rayuwata fansa ce ga rayiwarka! Amafin rai a ji dadi, amfanin numfashi na, fansan ranka, murmushin ka magogin bakin cikina, Rayuwata da duniya ta zan tattalin shine domin ka, Mu gina rayuwar mu da kaunar mu, har karshen rayuwar mu"


Haka kawai naji kwalla na zuba min, tare da kara yawan shi. Takowa yayi tare da kallona.
"Idan akwai abu mafi daraja da nasamu kece, na same ki a lokacin da nake bukatar ki."


Saka hannun yayi tare da gogen min kwalla, da sauri muka juya sakamakon kirana da Airan take.
Da sauri na dauki sandar da nake kiyo dashi, tare da kora tumakan da na tawo dasu, tare da wankin Baffa.
"Noman sai mun hadu a makarantar dare."


Da sauri na bita, tare da koran dabbobin.
"Airan lafiya."
Tana haki,
"Baffa!"
Da gudu muka rufa hanyar gidan mu, muna isa muka same shi a kwance, cikin kazamta domin ya b'ata jikin shi.

"Mamma baki ga ya b'ata jikin shi bane?" Cikin wani irin kallo.tace min.
"Na gani, kawai ban gadama na gyara shi bane."


Haka na fito jikina sabule, na koma dakin shi na saka Airan, ta kawo min ruwa a wani katon mazubi, sannan na shiga goge shi, tare da kwashe kayan ta fito, taga garin ya fara duhu,kwalla ce ta zubo min, ina kallon yadda garin.


A hankali nake tafiya har na isa bakin rafin na fara wanke kayan, ina

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads