Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 274096 words

Chapter 3 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1341

Ads at the middle of Article

a kirjin Hoyam, suka shiga mata dariya suna dukarta, kafin kace me sun mata taron dangi, sun mata dukar Bala'i.


"Ranki shi dad'e, uwar bayi. Alima ta daki Hoyam fa" da sauri suka kalli Juna da Shairah, tare da Narmin da take gurin a tsaye, bata jira abinda za ace ba, ta wuce da sauri zuwa ban ɗakin, ta sami Hoyam akwance ta suma, Alima tana murmushi, tare da kai mata duka, a cikinta tana faɗin.
"Jaka! Ke har kin isa ki mallaki zuciyarshi, toh na aiki lahira kafin na sami Sultan kowa ma na mai dashi bawa na."


Ture ta Narmin tayi lokacin da Narjis ta shigo, ta kuma kifa mata mari.
"Lallai kina cikin azabar da tafi ta wuta Bala'i. Maza ki saka kayanki kafin Sultan Abdus Samad ya nime ki."


Da sauri aka shirya Hoyam, aka fitar da ita zuwa shashinta sannan aka kira masu kula da lafiyar matan shashin, kafin kace me, maganar ya yadu har Chamber Sultanah. Tayi farin ciki, amma kuma ta danyi shakkar abinda Alima tayi, dan haka tasa aka kama Alima, tun kafin Sultan yaji labarin. Sai dai abinda basu sani ba, kawai sai ganin Sultan aka yi yazo Chamber din Hoyam. Ganin halin da take ciki. Ya fusata shi ainun.


Dan haka ya saka aka kawo mishi Alima, kallonta yayi sannan yace mata.
"Meye kika aikata?"


Zubewa tayi a gaban shi tana kuka, tare da kallon Narmin.
"Sultan na cancanci mutuwa, amma kafin nan ina son na fadi wacce ta sani aikata wannan ta'asar," ta kuma rushewa da kuka.sannan ta fito da sisin gwal, a cikin wani san karamin jaka, ta zuba.
"Sai da nace miki Narmin ba zan iya ba, kika sani na dake ta, toh gashi kin sani zan sadaukar da Rayuwa ta. Sultan Narmin ce ta sani."
Cikin tsananin tsoro Narmin ta zaro idanu waje, sannan tace.
"Kiji tsoron, Wallahi ban aikata kome ba"


Kafin kace me, Narmin ta faɗa cikin maganar, kallonta Sultan yayi sannan ya nuna ta hanyar fita, tare da saka masu tsaro su tafi da ita, ita kuma Alima a mata bulala talatin ladar aikata abinda aka sata, ita kuma Narmin kar a mata kome sai an gama bincike,


Hoyam kuma kulawarta ya koma hannun Narjis, tare da Shairah. Dan haka duk abinda zata yi kar a takura mata. Bayan an gama shara'ar, Sultan ya tafi da ita shsshin sa taci abinci sannan yace daga lokacin da ta ji yunwa a shashinsa zata ci abinci, kuma ta amince.


---
"Amma, Shairah baka tunanin akwai wani abu a kasa, taya Alima zatayiwa matar da muma mun same ta da aikinta haka?"
Inji Narjis.
"Yau naga abinda ya fi zare tsayi, Yo ku mata kaidin ai sai a hankali, kawai tayi haka ne sabida dalilin kanta, tayu kuma sakata akayi, tayi kuma ita tasaka kanta."


Kus-kus suke maganar, har na wani lokaci, sannan suka isa shashin Sultanah, kallonta suka yi ranta a b'ace.
"Waye a cikin ku ya saka Alima aiki?"
"Sultanah tuba muke, amma babu wanda zai saka Sultanah aiki akan wani dalili mara hujja,"
Inji Shairah,
"Kuma kawai anyi haka ne dan a rushe Yardan mu ne a ranki."


"Toh waye? Waye ya sakata aikata haka?" Ta faɗa da karfi.
Shiru suka yi, tare da sunkuyar da kansu, suna jiran hukuncin da ya dace da.

**
Istanbul.
Daular Umayyad
Salmanu Abul Hassan Bin Abrad.
Shine Sarkin wannan daular, kuma ana mulki bisa ka'ida da adalci, sannan su masarautan basu da fitina da tashin hankali, bayan haka kuma basu da magadar mulkin, sabida basu tsarin Magajiyar sarauta, wato (Empress Mother of King) kenan.


Tattaunawa suke akan Taron da suke halatta duk shekara, a babban hakwatar musulinci da take garin baghdad. Sannan Sarki Abul Hassan tana son isar korafin shi ne akan yadda Daular Abbasid, suke kwashe bayi karfi da yaji, sannan kuma suna kai hare haren wulakancin ga talakawan da suke iyakar su, daukar Umayyad basu da tashin hankali. Domin suna yin kome tsarin addinin Musulunci ne, shi yasa talakawan da suke wajen iyaka suke ta dawowa cikin daular.


**
Daular Abbasid.
Kukan da take mishi ya tsaya mishi a ranshi, rike hannun shi tayi tare da cewa.
"Sultan Narmin ba zata tab'a sawa a cutar dani ba, don Allah ka sake ta ni na yafe matar ina bukatar ta!"
"Toh bar kuka haka, zaa saketa, sannan ki kula"
Gyada kai tayi, tare da mikawa ta shiga ban daki tayi wanka, zata fito shima ya shigo."


Dan haka suka kuma komawa cikin ruwan wankan wanda aka janyo mishi kamar wata korama, a cikin ban dakin shi...
Tana fita, ta nufi shashinta, sannan ta koma gurin Sultan, ta sha ruwa. A hanyan da zata gidan tsaro, suka bangaji juna da Alima, ai kuwa ya ta yanki jiki ta fad'i. Tana shure shure.


*Shin wacece ta fadi Hoyam ko Alima*
BANI DA SALO! Amma ina da chakwakiyyoyi🤫🤨
#Paidbook
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1030677648?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=UAFVn6IqJPyhet8kdMafauzI6wppA5jaY51yBCvSwl%2FcN4uLk7Q7lAmpMHMD0fir5Z6QacntpbxI11YFe%2Fi%2BDwUpDABGp7ATfdvnLZHFieJDX6S1r%2FtPBG4sMaCfMkGe
*_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*


_The Historical_
~BOOK ONE~


Bismillah Rahamani Raheem


Page 4...


A razane Hoyam take kallon Alimah da ta yanki jiki ta fad'i. *Me take nufi?*
Kafin ta bawa kanta Amsa, Alimah ta danna wani irin ihu da yaja hankalin masu kula da shsshin su, shigowa da gudu.
Jini ne ya b'ata inda take da jikinta, kuka take tare da nuna Hoyam.
Wani irin tsoro ne ya kamata, dan dole ta zuba mata ido, haka Narjis da Shairah suka saka Bayi mata suka dauke ta.


Ita kuma Hoyam aka tasata keyarta, zuwa gidan Yarin, domin ta aikata laifin zubda cikin jikin Alimah. Kafin kace me har sun ririta alamarin zuwa babban al'amarin da har ya kai kunnen Sultanah.


Take tasaka aka kamo Hoyam, aka kai ta Fadar Sultan, aka fadi abinda tayi aka kuma kambama al'amarin da yana cikin tsinuwar da aka yiwa masarautar akan Sarki ya b'oye.


Dole aka tura Hoyam horo me tsannanin na tsawon sati biyu. Tare da hukuncin ba zata kuma zama babban shashin ba, sai kebantaccen shashin dake wajen masarautan, a can zata yi wa'adin da aka diba mata.


Wannan abun da suka yi yayi mugun fusata ta, dan haka tana kallon Sultanah irin kallon sai na miki kwatankwacin abinda kika min, sai na rama sama da abinda kika min.



Bayan tafiyar Hoyam, Sultanah Fazilatul nisa tasaka aka kama Alimah, tare da dauketa cikin masarautan baki daya, tare b'atar da ita baki daya.


Bayan sun mata wulakancin na fitar hankali, aka mata barazanar kada ta kuma dawowa cikin masarautar idan ba haka ba, zasu kashe ta.
*
Bayan an rufe Hoyam, bai hana Sultan Abdus Samad zagawa gurin Hoyam yana rage daren shi a gurinta har ta gama kwanakin da aka diba mata.


A hankali kome yake tafiya har bayan wata biyar, aka sami labarin Hoyam tana da ciki, wannan shine dalilin da yasa aka dawo da ita cikin masarautan sannan aka bata shashi me girma irin na Sultanah Fazilatul nisa.



Tunda Hoyam ta sami cikin ta shiga bada wani irin umarni wanda shi kanshi Sultan. Ya kasa magana akan haka, emirate councilors sun so dakatar da ita, sai ya kasance Sultan ya bata kariya,


A hankali cikinta na girma matsalolin masarautan na kara girma, har cikin ya isa haihuwa.


Wata daren ƙaramar sallah ta haifi Yaronta namiji kyakyawa dashi, tun da aka d'ago mata yaron ta ganshi, aka kuma fitar dashi gurin Sultan, ya mikawa babban Limamin masarautan, yayi mishi huduba. Bayan Sultan ya gaya mishi sunan shi.


**
Tunda aka fara shagalin suna sai da akayi sati Daya ana abu daya, sannan aka tsagaita.


Matsalar da aka fara samu, shine Sultanah Fazilatul nisa, tana masifar kawo tarnaki akan Aamaan, wanda har ya kaita tayi tuntuben harshen cewa.


"Tunda ka zaɓe ta sama dani, sai naga bayanka har ita ɗin." Akan wannan furucin, sai da aka dakatar da mahaifinta, wanda haka ya fi mishi sama da ace baiwa ce ta kori yar shi daga cikin gidan da yake saka ran shine zai mulke ta nan gaba.


Haka Hoyam ta cigaba da baza mulkinta har ta kai, ta sauke wasu gwamnoni na cikin yankunan kasar, ta dauko yan ƙabilar ta, ta daura. Kasancewar itace mahaifiyar Crown prince yasa babu wanda ya dakatar da ita sai Sultan.


"Hoyame! Bana son kina shiga sha'anin mulkin na, nasan d'anki shine zai zama sarki anan masarautan, dan haka ki bar shiga harkokin cikin masarautan!"


Cikin kirsa da kisisina, tace mishi.
"Toh shugabana, duk abinda ka bukata haka zanyi, tuba nake ya shugabana!" Yadda take maganar tana matse kwalla yana cikin abinda yake masifar sosa mishi rai, dan haka ya rungume ta, yana gaya mata sabida akwai masu Niman bayan su ne, idan aka ce yau tana shiga harkan mulkin shi tabbas zasu ga gazawar shi.


Shi kuma baya fatan samun haka, kafin kace kwabo Sultan da Hoyame, sun lula wata duniya na daban.
***
"Amir Ansas! Baiwar Sultan tana min kama da wani anan masarautan." Inji Amir Fujai,


"Bani daya na fahimci haka ba, ba kowa bane sai Ghanim, wannan Mutumin.."


Da sauri yayi shiru, tare da juyawa yana kallon Inuwar mutum ya juya da sauri, take yasa aka bi bayan mutumin babu shi babu dalilin shi.


*"Hmm! Ina sane da abinda yake faruwa, amma kuma taya kuke ganin zamu kawo karshen Abdus Samad, sannan taya zamu iya samun damar mulkin kasar nan bayan shi kanshi yana da magaji, sanan itama Hoyam din ba kyaleta zai yi ba"


Kallon Abdul Mannan suka yi sanan suka ci-gaba da cewa.
"Dole zamu bada damar canja wurin da kome, amma Sultan kan dole mu idda aikin mu akan shi, koda taimako ko babu taimako, sannan.yadda aka wulakanta mana mahaifi dole mu tsaya domin kare mutuncin shi."


Haka suka bar wannan batun tare da tsayawa ka'in da na'in, kowani kusurwa na masarautar kowa burin shi ya zama shine magajin Izzah, dan anyi Mamakin yadda Sultan Abdus Samad yakai wannan lokacin. Ba tare da an sami matsala ba.


Sanan kuma wani abun da ya d'aga hankalin mutanen da suke harin karagar, ba kome bane. Sai wayen gari da akayi Sultan Abdus Samad yana maida duk wani kundin tsarin mulkin ƙasar tare da da saka sunan Aamaan shine sarki na gaba.


Tare da maida wasu abubuwan da ya kasance nashi izuwa na Hoyam da Aaman. Babu wanda ya saka baki ko ya nemi dakatar da Sultan, sai dai daga kulawar da ake bawa, Hoyam da Aaman. Sultan ya gayyace Yan uwan shi a wani liyafa.


Wanda ya bayyana Hoyam a matsayin Matar shi da zai aura, wannan shine mafi kololuwar tashin hankalin.


"Na gabatar muku da ita ne domin kuwa gobe Insha Allah zan aureta, kuma itace Sultanah Hoyam."
Kallon shi suke cikin fusata, amma babu wanda ya isa bayyana fushin sa, tare da gabatar da b'acin ranshi bisa ra'ayin shi. Amir Kaisan yace.
" Ya kai d'an dan uwana, kasan kuskuren da kake cilla rayuwarka ciki kuwa?


Wannan shawarar bata dace da wannan tunanin ba, kayi min afuwa amma tabbas akwai abinda Hoyam take nufi da ta shigo rayuwarka! Ita din Y'ace ga Ghanim, mutumin da ya ciyar da Sultan Aamaan dan uwana, tare da matar shi Sultanah Sajiyah guba, ga ta nan tambaye ta.?"


Juyawa yayi yana kallon Hoyam,. wacce kwalla ya shiga zuba mata. Dakyar ta bude baki tace.
Sultan! Baka yarda dani bane? Kai ka sayo ni, kuma ka..."


" Ya isa tashi kije zan zo yanzun."
Tana tashi ta rungume D'anta tana kallon su baki daya, sannan ta lashe bakinta, hawaye na zuba mata. Tabar gurin.


Tunda ta tashi aka fara cacar baki tsakanin Sultan wanda shi kan shiru yayi musu, duk abinda suke fada ana jin su, karshe haka suka mishi barazanar zasu kashe shi, idan bai dakatar da auran Hoyam ba. Fita yayi daga cikin su ya dawo shashin Hoyam, a daren ranar ya rubuta takardan dakatar da duk wanda ya gayyata aka ci abinci dashi.


Haka ya kwana zuciyar shi babu dad'i.
Sannan wani abun da zai baka mamaki, ya washi gari yana tashi bayan an dakatar da mutane, sai ya bawa Hoyam damar tayi magana, tunda ake a tarihin masarautan ba a tab'a cin zarafin emirater councilors ba sai a wannan lokacin.


Haka suka yi hakuri tare da ɗaukar abinda yazo musu, dole suna shiga kyakyawan shiri akan Sultan da Hoyam.


Wai akace wanda ya shirya ya shirya wanda bai shirya ba dole ya fadi, domin an daura auren Sultan da Hoyam, wanda ya sanya Sultanah Fazilatul nisa. Haukacewa kamar ba me cikakken lafiya ba.


Abu goma da ashirin, an dakatar da mahaifinta, sannan ana cikin wannan yanayin aka kuma bankad'o wani abinda ta aikata, wato koran Alimah daga masarautan. Da kuma saka Alimah yiwa Hoyam sharrin ta zubda mata cikin karya.


Wannan abun shi ya kara dagula mata lissafi, Domin Sultan ya bawa Hoyam damar tayi duk abinda ya dace. Amma banda kisan kai. Dan haka tace.
"Zunubin da suka aikata zai kawo su gabbar da za'a hukunta su" wannan abun da take yana masifar burge Sultan Abdus Samad.


Abinda yayiwa Sultanah ba wani abu bane sai haramta mata shiga duk wani abinda ya shafi cikin masarautar kasancewar ta yar magajin sarauta yasa aka d'aga mata hukuncin. Aikuwa Sultanah ta fusata tana faɗin.
"Sai na kashe ka Abdus Samad, tunda kasaka wulakantacciyar Baiwarka ta wulakantani.


Insha Allah matukar ina raye sai na kashe ku. Sai na tozarta ku, sai na dasa muku bakin ciki a rayuwarku, ke kam wallahi ki kiyayye abinda zan miki, domin zan sanya miki bakin cikin da yafi guba illa," da ace Sultanah Fazilatul nisa ta san Illar abinda take cewa, da tai hakuri ta kyale su.


Dan haka suka fitar da ita tana, ihun tare da ɗaukar alwashin sai ta girgiza masarautan baki daya.


Sam haka bai dame su ba,, domin a hankali Hoyam ta juya kome ya koma nata, ya dawo karkashin kulawar ta, sai da takai ta kawo Sultanah Hoyam ita ke umartan Sultan wanda shi kuma ya fara goce mata. Haka ya matukar girgiza mata zuciya domin bata kawo hakan zai tab'a ta ba.


--- bayan wata biyar Sultan ya fara rashin lafiya, wanda ya haɗa da tarin jini, abinda na daga mata hankali kenan, domin ana kiyayye abincin shi da na shanshi. Asalima baya cin abincin kowa sai dai ya girka da kanshi.


Hoyam aka fara zarga, shi da kanshi ya wanke ta, domin tunda yake da ita bata tab'a ko dafa ruwan zafi ba, dan haka ya wanke ta Sosai. Duk da ta kasance da tana jin haushin sa amma haka bai tab'a sakawa ta cutar dashi ba.


Haka ya cigaba da jinya, wanda aka yi nasarar fahimtar an kawo mishi kyautar wasu kayan alfarma a jikin su aka sami gubar, dan haka aka fara binciken mutanen da suka kawo kayan ba a same su ba. Dakyar Allah ya kwace shi daga wannan gubar.


Yasha jinya sosai, lokacin Saman yana da shekara daya a duniya.


Dan haka suka dauki soyayyar duniyar nan aka daura mishi.
Gefen yan uwan Sultan da ita kanta Sultanah suna shan alwashin kashe ahalin sultan Abdus Samad. Dan haka cikin murdaddiyar yanayi aka wayi gari. Tare da kama Sultanah Fazilatul nisa a dakin Sultan da katon wuka.


Hannunta duk jinin shi, tayi mishi kisar gilla, wanda ya fusata Hoyam da ta rasa mijinta, take aka fidda Sultanah daga cikin masarautan, sannan wani abun da ya daurewa kowa kai yadda take rantsuwa wallahi bata kashe shi ba.


Ba ita bace tayi kisar, itama ta samu bai cika bane tayi kokarin cire wukar amma ba ita bace.


Lokacin da aka fara bincike, masu tsaron kofar shi sun tabbatar da ita ce ta shiga. Dan haka babu wanda ya shigo kafin ita, amma sam taki yarda..dole aka kaita haramtacciyar Fada aka ajiye ta, tare da Alimah da Narjis da Shairah,.


Wacce itama aka samu itace tayi sanadin kawowa Sultan kayan da yake da guba, Sannan aka rufe kundin tarihin su..


Ranar da akayi jana'izar Sultan ranar Hoyam ta canza duk wani tsarin masarautan, aka yi garambawul da wasu abubuwan, ta kwaso kabilar ta. Ta watsa su cikin tsarin mulkin masarautan.


Sannan Yan uwan Sultan da suna ki mishi mubayi a, suka mata. Sannan tare da goyan bayan mulkinta.


Bayan sun yi haka da wasu kwanakin aka tsinci gawarwakin su, sakamakon zasu yi juyin mulki, Dakarun Sultanah Hoyam suka bude musu wuta.


***
Birnin Kisra.
Babbar kasa ce da suka shahara a harkan sihiri da tsafi, dan haka suke Baje kolin baiwar su. Guri babban bokan kasar Amir Hood da Amir Kaisan tare da Fujai, suka zube a gaban shi.


Dariya yayi sannan ya kalle su, sanan ya nuna su sa yatsa.
" Ba zaku tab'a mulki ba, ba zaku tab'a dakatar da wanda ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads