Header Ads
Showing 207001 words to 210000 words out of 274096 words

Chapter 70 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1412

Ads at the middle of Article

ya kira shi da Mehran! Dan haka kadangarun bariki bani da lokacin da zan b'ata akan shi ina kishi.


Duk macen da bata had'a zakuna a gabanta suna yaƙi akanta ba. Sunanta lusara jakar mata macen da ta isa da kanta take haɗa zaratan maza! Ko yau Mehran bai isa yace na biyo shi dan soyayyar shi ce, kudirina ya kawo ni gare shi bayan haka bani da wani abin da zan ce nazo daukar daga gare shi."


Ina gama gaya musu haka, na fita tare da barin su a gurin suna mamaki na, nauyin da yake raina na sauke tare da jin nutsuwa a raina, sannan na Barsu da kallona. Har muka b'ace.
"Ne yarinyar nan take nufi? Wato duk cikin mu babu wacce zata iya kiran shi da Mehran."


Inji Sawda,
"Ga alamu nan, dukda nasan na tab'a haduwa dashi amma ban sami zarrar kiran shi da Mehran ko Aamaan ba, amma kiga ita yadda take kiran sunan shi gaskiya Sultan Mehran ya bata dama dayawa." Inji Yasmin.


Jasrah bata ce musu kome ba, amma kuma a hankali take fuskarta abinda suke tattaunawa, ita dai tasan ko kwanakin da tayi a dakin shi bata iya d'aga kai ta kira sunan shi ba, a iya kwanakin da tayi bata da wani sabon abu da zata iya nunawa nacewa yana tare da ita, domin duk zamanta a dakin babu abinda ya haɗa su. . Sai tausa da bashi ruwa da wasu labarai har ta cika kwanakin babu abinda zata ce gashi ya faru a tsakanin su.


Shi kuma dan ya tuzira Ikram ya bawa Jasrah damar zama wani abu a jikin shi sannan yace ta iya da bakinta ta nuna cewa kome a tsakanin su ya faru, sannan ya tara mata manyan gwala-gwalai ya sallame ta dashi tare da bata wani babban daki wanda ya kusan kai na Ikram girma. Duk yayi haka ne dan ya tinzira ikram, kuma ya yi nasarar haka, domin kuwa ranar da tafito take farin ciki tare da habaici.


Kasa barci Ikram tayi, kuka kuwa dannewa tayi tayi, a cikin daren sau uku tana zuwa turakar shi yana cewa ace yana aiki ne ta tafi sai ya sami lokaci zai kirata.


Har yanzun yau da yaki sauraronta, tana jin zafin haka balle kuma da ya kamata da laifin zuwa gidan Abrad. Shi yasa yaji ta bashi haushi baki daya, yaji ya tsane ta baki daya, baya kaunar ganinta koda wasa, amma kuma haka bai hana shi jin tashin hankali da damuwa ba, domin kuwa yana jin ba zai iya hakuri ya rabu da ita ba,.idan ya tuna abinda take aikatawa sai yaji kamar ya cire zuciyar shi ya huta domin kuwa yana zaune kalau ta haɗa mishi tashin hankalin da bai taɓa kawowa a rayuwar shi ba.


......
Koda muka isa dakin Sultanah, Narjis ta gaya mata abinda matan suka min. Murmushi tayi sannan tace mana.
"Ita ikram kallon su tayi bata ce musu kala ba?"
Sunkuyar da kai kasa tayi tare da rike hannunta tace mata.
"A'a ai tana da kaifin basira ta gaya musu abinda ba zasu iya ba koda zasu shekara dubu da Sultan Aamaan Mehran"


"Hmm!" Tace tare da kallona ta nuna min guri na zauna, shayi ta mika min. Na amsa cikin nutsuwa tare da cewa.
"Nagode!"
Kurb'a tayi tare da kallona. Ina juya kofin a hannuna, nakasa sha. Kallon fuskana tayi tayi. Ganin yadda damuwa da firgici ya cika kanshi tam. Murmushi tayi sannan tace min.
"Baki son komawa gida ne?" Da sauri na d'ago kai tare da kallonta, sannan na maida kaina kan kofin nace mata.
"Ina son komawa!" Shiru nayi nakasa koda furta kalama daya ne.
"Gaya min meke faruwa?"ta kuma tambayana,
"Laifi na mishi wanda har ta kai ya tsane ni a duniyar shi!" Na faɗi haka ina jin kamar na fashe da kuka.
"Kina son shi ne?"
Da wani irin sauri na d'ago kaina, girgiza mata kai nayi sannan nace mata.
"Kallon Ɗan uwana nake mishi ban tab'a jin son shi ko kaunar shi a rai na ba."
Na fadi haka kamar zanyi kuka.
"Wato keda shi kuna kokarin kashe junar ku, wannan lafazin zai iya tab'a darajar ku keda shi. Amma babu damuwa, Allah yasa hakan itace mafi alkhairi. Amma ki sani zamu yi kewar ki ni da sauran mutanen cikin gidan nan!"


A hankali na mike tare da mata godiya sannan na fice daga dakin. A hanyar d'akinta muna hadu ni zan fita shi kuma zai shigo. Kallon juna muke tare da kasa furtawa juna koda da kalmar sannun ce, karshe sai gashi mun tsincin kan mu da kasa bawa juna hanya idan ya kuma gefe nima zan koma gefe,.


.idan ya tsaya zan tsaya karshe ture ni yayi gefe ya shige abin shi ina kallon shi. Wannan wacce irin rayuwa ce haka? Meye nayiwa Mehran da ba zai yafe min ba yake bani wahala har haka? Zan tafi zan yi nesa dashi yadda zai gane bani da laifin da yake zargina, amma tabbas Mehran ya zalince ni sosai. Babu kome Allah zai bayyana gaskiya koda bana tare dashi. Duk tsawon lokacin da na dauka, da fansar da nace zan dauka na ƙasa daukar haka sabida Mehran yau gashi sabida abin da yake da yakinin bai faru ba, ya kirani mazinaciya, karuwa, datti,shara, bolar kowa.


Share kwalla nayi tare da barin kofar d'akin, na nufi hanyar da zai fitar dani, Fudail muka ci karo.
"Ikram yanzun ɗan uwanki yake ta niman ki kamar wani karamin Yaro." Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Rahil rigima!" Har zan wuce yace min.
"Kiyi hakuri! Kishi yake damun Sultan Mehran, amma kece rayuwar shi."


Ganin shi muka yi a gaban mu, jikin shi yana kerma.
"Waye kake magana akan shi? Ni Allah yayi min tsari indai ni ne, wannan itace rayuwata? Kishinta nake?" Riko hannuna ya yi tare da jana zai kai ni cikin Kwarkwarorin shi ya tozartani. Sai ji nayi an rike hannuna, tare da fisgo ni. Dukkan mu a tunanin mu Fudail ne. Amma abinda mamaki Amir Rahil ne.


Cikin b'acin rai,.wanda tunda nake ban tab'a ganin shi ita ba. Fuskar shi har wani jajja jjaa tayi. Ya karasa takowa gaban Mehran ya. ya janyo ne jikin shi tare da sakala hannun sa a kafadana, yana kallon Mehran.


"Ba zaka wulakantatta ba, matukar ina raye. Muje Salsabila ke kadara ce me tsada baki yi wannan arahan nan da za a tozartaki ba. Dan haka muje cikin Zuri'ar mu kiga yadda ake kaunarki. Mulki yake yawo a jininka shi yake yawo a jininta. Ya zaka ji idan na gaya maka ita kanta Sultanah ce a kasar Masar!


Ya zamani idan mace maka ita Sultanah ce a Merocco. Dan haka karka tozarta ta, domin zan iya sare hannunka." Ya faɗa mishi yana kallon cikin idanun sa, juyawa muka yi tare da fita daga gidan baki daya. Kukan da nake rikewa ne yazo min, sosai nayi tare da kifa kai na a kirjin shi.
Har muka isa masaukin su, anan ya ajiye Ni a dakin shi, yayi ta min hira tare da bani labarin abinda zai sani da dariya. Nayi kokarin koran b'acin rai da damuwa, akan fuskana amma a zuciyata kawai ina jin babu dadi. Dan haka nayi ta biye mishi muna ta hira har ya ga nasake ina dariya.


Tausayi ya bani sabida yadda yake nuna min so ba karya bane, kaunar da yake min yana shimfiɗe akan fuskar shi. Dan haka yake kokarin sai ya sani dariya kota halin k'ak'a.


~~~
Har suka bar gidan yana tsaye kamar gumki, idanun shi jajjur. Dan ji yaƙe kamar an tafi mishi da zuciyar shi, niman faduwa yake. Fudail ya rike shi. Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Sultan MEHRAN! Kayi kuskure babba. Duk abinda za a gaya maka akan Ikram bai dace ka dauka ba, sannan itama kanta taje taji meye ya faru har ka tsane ta haka.


Mehran ko yanzun haka Nawwas yana jiranka zai maka bayanin abinda ya faru, amma ka sani sai ka cire wannan tsanar da kake mata, tare da fahimtar wacece ita. Sai ka haɗa abinda ya gaya maka da mahaunin hankali matukar kace ba zaka yi haka ba, tabbas yanzun ka fara nadama, domin zaka yi ta kuka har karshen rayuwar ka......
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


38


Kallon Fudail yayi cikin damuwa, amma kuma idan ka kalli yadda ya ɓoye haka zaka iya rantsewa har da Allah babu kome a ranshi, Mehran yana cikin mutanen da Allah yayi musu baiwar ɓoye damuwar su, zai yi wuya ka zauna dasu su ka gane akwai damuwa a tare dasu dan yana da irin zurfin cikin nan ne wanda idan ba shi yayi magana ba ba, ba zaka yi yarda ba.


Sannan yana iya ɓoye abin a ranshi ba tare da ya gayawa kowa ba, yayi ta cin shi ba tare da kowa ya fahimci haka. Ko Fudail yana saurin d'ago shi ne ta hanyar tsananta binciken motsin shi. Wannan d'anyen halin nashi ba karamin damun Sultanah FAZILATUL gani take kamar da gayya yake k'in faɗa mata, ita bata damu da kanta ba, koda wani zai iya gaya mishi. Amma fir yaki nuna damuwar shi sai dai ya rufe kanshi a daki yayi ta zaman kunci.


Duk lokacin da ya shiga wannan yanayin, kowa yana shiga damuwa. Shi yasa basu son Ikram tayi nesa da shi. Kuma da alamu haka ce zata faru, tunda ya kasa furta kalmomin da ya dace, gashi nan danginta zasu tafi da ita.


Juyawa yayi yana kallon waje. Kalmomin Abrad ne yake yawo a kunnen shi.
_Ko mijin da ta aura ba zai iya cewa shi ya dauke abinda kake hari ba! Ka tambaye ta ni na fara kwanciya da ita! Ni na bude idanun ta. Ni na nuna mata yadda namiji yaƙe_


Rintsa idanun shi yayi tare da jin bakin ciki dama da kullum, ji yaƙe kamar ya cire zuciyar shi ya huta, ga baki daya ya tsani kanshi da Abrad ina ma da yana da damar kashe Abrad tabbas sai ya kashe shi.


"Sultan!" D'aga mishi hannu yayi tare da cewa.
"Bana son ganin shi."
"Amma wannan kuskure ne kake tafkawa, kana kuskure ne babba. Me yasa ba zaka Fahimci yarinyar nan ba? Me yasa ba zaka gane meke faruwa ba, Idan abinda kake zargi haka ne me yasa ba zaka ajiye shi a wani guri na daban ba, kake kuntatta mata da hanyar da bai dace ba! Gaskiya baka mata adalci ba. Shi kenan Allah yasa haka shine mafi alkhairi ga sakon daga Fada Amir Hood ya baka auren jikar shi. Amma sai nan da wata uku zuwa huɗu. Tunda sun sami labarin Ikram an mata bai ko da Amir Rahil. Allah ya tabbatar da alkhairi."


Daga haka ya juya tare da barin d'akin, tunda ya fara magana bai juya ba, har sai da ya bar dakin sannan ya juya yana kallon kofar tabbas yana son ganinta. Yana son jin meye ta sauke shi. Yana son ganinta kome dare ba zai ya fita da rana tsaka ba, dole ya fita cikin dare ya isa gare ta. Amma kuma meye makomar shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da dauke kanshi kasa. Yana shafa kan shi tare da murmushi.


~~~
Kasa magana nayi ina kallon yadda Sultanah Amrah take kallon Nimrah, mayar da Nimrah baya nayi. Sannan na tsaya a gaban ta, nace.
"Kiyi hakuri Ummyn, bata da laifi. Kuma nasan ke me adalci ne."
Dakatar da ita tayi ta hanyar d'aga mata Hannun, tare da kura mata ido.
"Ban ce zan mata kome ba, amma ina tsoron abinda Mahaifiyarta tayi mana ne, domin ba lallai bane ta fahimci abinda ta aikata."


"Insha Allah, Nimrah ba zata aikata kome ba, wallahi ki yarda dani bata da wannan tunanin a ranta ban dai sani ba, amma babu wannan karsashin a ranta."


Haka nayi ta lallab'a Sultanah Amrah kafin ta sake jiki, tana kallona daga lokaci zuwa lokaci. Musamman idan ta fahimci na shiga yanayin damuwa,.sai ta ce min.
"Kina son zama da Mehran ne?"
"A'a nafi son zama daku."
"A'a Ikram bamu shiga hakkin ki ba?"
"A'a" nace tare da mik'ewa zan bar dakin domin na tsani hirar da zata kawo min zancen Mehran. Shi yasa bana son zama koda su Izmah ne domin rabin hiran su akan shi suke min.


A waje na hadu da Rahil ya kawo Abrad, dan haka ban yi mamaki ba, dan nasan yazo gaida Ummyn ne, har cikin gidan ya shiga suka gaisa, sannan suka shiga tattaunawa akai na, wanda duk hiran akan yadda ake shirya min tarb'a da bikin da za ayi mun ni da Rahli.


Bai ce komai ba, amma daga yadda ya rasa nutsuwar shi har ya gama hiran da ita, muna zaune a harabar masaukin. Zama yayi a kusa dani tare da zuba min ido. Dauke kai na nayi daga gare shi sannan na cewa Rahil.
"Ina son zan sha madara! Amma bana son bayi su kawo min" na fada cikin sakakkiyar murya.


Mikewa yayi tare da cewa.
"Zauna ki huta mata na, ba zata tab'a wahala ba. Domin ita din sarauniya ce zan kawo miki." Ya faɗa tare da nufar hanyar cikin gidan. Gyara zama nayi sannan na kalle shi.
"Kayi ƙoƙarin raba ni da Mehran, ka dasa mishi k'iyayyana. Sai dai kayi kuskuren mafi girma domin kuwa kayi abinda ba zai tab'a barin ka ba, daga yanzun daga wannan lokacin ka fara boya, kayi ta gudu karka tsaya.


Domin tsinin takobin shi sai ya huda kirjin ka. Ka fara gudu karka tsaya inda zai same ka. Nayi danasanin fadawa hannunka, domin babu wanda ya kashe ni da rayuwata sama da kai.


Babu wanda ya lalata min rayuwa sama da kai. Sannan sauran da yarage kazo zaka lalata min su! Meye nayi maka da zafi? Meye na tsare maka da zafi haka? A sanina ka auri Kanwar Mahaifiyata toh meye kake son daga gare Ni? Amma masu iya magana since idan ajali yayi kira ko ba'a ciwo za aje."


Daga haka na mike , rike hannuna yayi cikin zafin rai na tsinka mishi mari sannan na wuce abuna, duk akan idanun Amir Rahil ne, ina shiga ya zuba min ido.
"Meye ya haɗa ki dashi? Meye Matsalarki dashi? Yau zan dakatar da shi."
Gudun kar a kuma aikata abinda Ya faru yasani rike shi tare da kallon shi nace.
"Karka damu. Ya wuce na koya mishi yadda ake mutuntawa."


Murmushi yayi tare da mika min madaran muka shiga zaga gidan, wai duk sabida kar na saka damuwa a raina.


"Wai dama an miki baiko da wancan basamuden ne?" Kallon shi nayi tare da murmushi kafin nace mishi.o
"Eh amma kuma sawun giwa ya badda na Raƙumi ba" shima kallona yayi sannan yace.
"Ban gane ba?"


Murmushi nayi a karo na biyu, sannan nace mishi.
"Zaka gane mana." Dariya yayi sannan yace min.
"Amma kuma"
"Amma kuma me?" Na tambaye shi,
"Amma kamar kuna son juna da wancan basamuden?"
"Me ka gani?"
"Kin dawo min da tambayana"
"Kamar ya?"
"Kamar yadda na gani da idona"
"Lallai kayi kuskuren"
"Banyi kuskuren ba sai gaskiyar da na hango."
Kasakai nayi ina kallon shi.kafin nace mishi.
"Babu wata soyayya a tsakanin mu, kawai kana ganin haka ne amma ban ga!"
"Da gaske baki son shi?" Ya tambaye ni, tsayawa nayi ina kallon shi. Tambayar da yayi min iya gaskiyar shi ce, amma kuma bana jin zan bashi amsar wannan tambayar dan haka na juya tare da barin shi a gurin, bakin ruwan da yake gudana a gurin na isa sannan na zauna tare da saka kafana ina nazarin maganar da muka yi da Rahil. Zama yayi kusa dani, sannan yace min.


"Kiyi hakuri da sakaki surutu da nayi, sai dai kowani mutum me hankali da sanin ya kamata zai so ya ajiye irinki a gefen shi ko badan mu'amalar aure ba, ana bukatar mutum ya ajiye mace irinki na farko zaki bashi garkuwa, na biyu zaki bashi farin ciki a rayuwar shi, na uku kuma..." Murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Sai nan gaba zaki Fahimci abinda nake nufi"


Girgiza kai nayi sannan na juya tare da kallon cikin ruwan, ina jin babu dad'i domin Allah ya gani son Ƴan uwantaka nake mishi ba son kauna na aure ba, kuma ba zan iya bijirewa iyayen mu ba, tunda abinda suka yanke kenan. Amma ko ya ya bai kamata su zartas da hukuncin haka ba, idan suka yi dubi da ni bakuwa ce a cikin su.


"Ikram ko na takura miki ne?" Ya tambaye ni cikin damuwa,
"A'a baka takura min ba, sai dai kana da hawa kai" na fada ina kallon shi,
"Toh kiyi hakuri! Ban san yadda zan nuna miki farin cikin da yake raina bane, amma kuma ina jin nutsuwa a zaman mu nan."ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai ya bani tausayi, tabbas akwai matsala domin nasan dai ba zan hada maza biyu ba, amma kuma yadda Mehran yayi min ban ji dadi ba, dan haka na juya ina wasa da ruwan.


Kasa hakuri yayi tare da zama kusadani kamar zai shige jikina, kallon shi nayi kafin nayi magana ya jingina kan shi akan kafadana, tare da riko hannun na, yana me matsawa a hankali.


...... Ya saba da ganinta tana sintiri dan haka yau da bai ganta ba, duk sai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads