Header Ads
Showing 177001 words to 180000 words out of 274096 words

Chapter 60 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1402

Ads at the middle of Article

niman ka" a hankali ya juya tare da kallon Bhaiq, sannan ya tashi tare da bin bayan shi. Suna shiga ya zauna a gaban Sultan Mu'allim da Wazir. Shiru duk suka yi sannan Sultan yayi gyaran murya yana faɗin.
"Kaje ka tawo da ita"
"Toh Atta mun gode." Daga haka ya juya ya bar gurin su, yana kara godiya. Bayan fitar shi Wazir ya kalli Sultan."ina ganin me zai hana ka hakura da wannan hadin da zaka yi ka barta ta akan zab'in ranta, tunda shi Rahil yana da masoya babu amfanin a tirsasata yin abinda bai dace ba."


D'ago kai yayi sannan ya sake wata wadatacciyar murmushi kafin yace mishi. " Koda Rahil bai ce yana sonta ba, bana jin zan barta ta auri wani bayan shi, tunda kuma yace yana sonta sai naji faduwa tayi daidai da zama, abinda nake buƙata ne Allah ya kuma biya min bukatar, dukkan su mallakina ne!"
"Allah ya huci zuciyar ka, ba wai ina nufin wani abu bane, sai dai idan har aka bata wanda take bukata haka kamar karin daraja ce ga masarautan mu, Yar mu tana auren Sarkin Samaind ka duba abinda idanun basira mana."


Lashe bakin shi yayi tare da sunkuyar da kanshi yana wasa da furfuran kanshi, sannan ya kalli Waxir ya sake wata ƙaramar murmushi yace mishi.
"Eh na hango katin ci-gaba amma bana jin a raina haka wata masalaha ce, babu cigaban da zata kawo ma, sannan babu wani abinda zai bayyana mana na cigaba dan tana auren Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran! Kawai haka ba wani abun azo a gani bane dan babu wani Cigaba da za a ce an samu dan kawai tana auren Sarkin Samaind!"


Shiru Wazir yayi yana kallon yadda Sultan Mu'allim, kasa yayi da kan shi ya kuma cigaba da cewa.
"Sultan akwai matsala domin Ikram bata son shi da Aure a matsayin d'an uwan ta dauke shi, kuma haka ba zai tab'a kawo zaman lafiya, ido da ido kuke wariya akan ta, kuna nuna mata dan ita mace ce, ba zata zab'i abinda take so ba, sai shi?


Haka zai sanya tayi ta mishi kallon ya fita daraja a gaban ku, sannan haka zai sanya tayi ta jin ina ma bata dawo gare ku ba, ban san yadda zan gaya maka kuna cusa k'iyayyar ku a zuciyar ta ba, amma tabbas babu adalci a tsarin ku."


Shiru yayi sannan yana nazarin abinda Wazir ya faɗa.


...
Ina zaune sai gashi ya shigo, kallona yayi sannan ya sake murmushi yana faɗin.
"Bilqisul Ikram!" Dauke kai na nayi ina murmushin bakin ciki, takowa yayi har ina nake zaune. Durkusawa yayi tare da kifa min mari, sannan ya d'ago kai na, tare da yana kallona. Murmushi yayi sannan yace min.
"Baki isa ba! Kinyi kaɗan Ikram marina kika yi? Idan da kin dake ni, yanzun baki isa ba."


Tofa mishi yawu nayi tare da kallon shi har cikin idanun shi. Share fuskar shi yayi tare da wani irin murmushin takaici. Mikewa yayi sannan tare da cewa.
"Ku kunce hannun ta, tare da kawo min ita shashina." Ya faɗa tare da ficewa daga dakin, tunda suka kunce hannun, suka tasa keyana har shashin shi, tunda nake da Mehran bai tab'a nuna min karfi ba, bai tab'a kawo min farmaki ba, yau sabida soyayyar shi Rahil yake nuna min karfi. Tunda na shiga ya saka ni a gaba da bala'i, domin karfi da yaji ya fara kokarin keta min rigana. Dakyar na kwaci kaina, yana ganin haka ya kuma shake ni tare da matse min nonuwa na, kuka ne ya kwace min tare da kallon shi.
"Me yasa kake son lalata min rayuwa? Tunda nake da Mehran bai tab'a kawo min hari ba, kullum mutuntani yake tare da girmamani, na kwana a daki daya da Mehran na kwana a jikin Mehran hannun shi bai tab'a isa cinyata ko kirjina ba, bai tab'a kawowa a ranshi zai iya amfani da karfi ba. Yau d'an uwana yake son keta min mutuncina sabida nace bana son shi!"


Murmushi yayi sannan ya mike tare da ture ni, ya nufi ban dakin shi yana ji kamar zuciyar shi zata fita, bai dan me yasa yake jin babu dadi akan Ikram ba, kuma ba kome ya janyo haka ba, sai dan yadda take nuna soyayyar Mehran a sama da kome. bata tausayin shi kamar yadda take nuna mishi da, yanzun ga baki daya ta tsane shi sabida Mehran, da zai ga Mehran tabbas sai ya kashe shi. Ya tsani Mehran ya tsani rayuwar shi. Kuma Insha Allah sai ya raba ta da kimarta koda kuwa ba zai same ta ba.


Kafin ya fita na tashi tare da ɗaukar alkyabar shi na saka, sannan na nufi shashin mu. Tunda na shiga na zube a tsakar dakin na sake wani irin kuka me mugun cin rai, ina tuna Mehran. Ga baki daya naji na tsani kai na, me yasa a daren da nake duba shi ban bashi kai na ba, koda kuwa ace haka zai janyo min jifa ranar Amarcina.


Kuka ne ya kuma kwace min, shigowar Ruwaida da Izmah ya sani juyawa ina kallon su, zama suka yi sannan suka ce min.
"Abinda kike babban Abin kunya ne, ace yau kina kuka akan SO, WALLAHI ABIN GORI KIKE AIKATAWA UWAR DAKINA DON ALLAH KARKI KUMA ZUBDA HAWAYEN KI SABIDA SO"


Dafa kafana Izmah tayi sannan tace min.
"Kiyi hakuri Ikram!"
Rintsa idanuna nayi.tare kifa kaina akan cinyar Izmah tana shafa min gashina, sallamar Ruwaida tayi tana kallon yadda nake zubda kwalla.
"Ikram ki daina kukan nan, kiyi hakuri Insha Allah idan Mehran ne rabonki zaki mallake shi idan kuma ba rabonki bane shi Allah ya sassauta miki halin da kike ciki."


Haka tayi ya rarrashina, har barci ya dauke ni. Gyara min kwanciya tayi tare da jera min matashin a kaina. Kallon Ikram tayi cikin damuwa, tana tuno abubuwan da suka faru, a baya tabbas wannan kadai ya ishi me hankali fahimtar hikimar Ubangiji, duk wannan zafin yanzun duk babu. Sai sanyin da tayi gabaki daya ta zama wata iri mara amfani. Bata iya fada bata iya rigima babu zafin rai babu kome sabida so tayi watsi da kome.


~~~
SAMAIND


Kimanin wata daya kenan, kallon juna Jasrah da Mahlika suka yi cike da mamaki, jin likitan masarautan yana tabbatar musu da cikin da Azizatul Nissah take dashi. Saka su mutuwar tsaye. Shi kan shi Mehran kura mata ido yayi. Tabbas ya kwanta da ita tun daga lokacin da ya sha maganin ba sau daya ba ba sau biyu ba.


Yasha Narjis ta kawo mishi ita, amma kuma bai tab'a kawowa a ranshi zai mata cikin ba. Domin idan ya tuna duk abinda yake da ita bawai yana mata yadda zata ji dadi bane yana mata yadda zata wahala ta gudu ne ya sami abinda zai kafa hujja dashi sai ga cikin shi ya isa kafa hujja. Wani irin yanayi yake ji na gamayyar damuwa ko tashin hankali.


Kallon Azizatul Nissah Fudail yayi domin ya fara gajiya da tashin hankalin da yarinyar ta Kunno mishi wanda shima yasan laifin shine da ya gayawa Mehran wancan lokacin da yaci Ubanta amma yanzun ko ya faɗa zasu kira shi da d'an dakin Ikram ne, shi yasa ya zuba mata ido, yana kallon yadda take kokarin daurawa Mehran cikin da bana shi ba. Babu babban wawa sai shi.


Yayi kuskuren barinta da cikin bai gayawa Mehran ba, da ya gayawa Mehran da kome bai faru ba, kuma dan kayan haushi ko Sultanah Fazilatul nisa bai gayawa,.yaja bakin shi yayi shiru dan wauta.


"Sultan MEHRAN! Muna taya ka murnan samun Magaji Allah ya sauki Amirah Azizatul Nissah lafiya ta haifa mana Yarima."


Cikin karfin iko da mulki tace musu..
"Insha Allah sai dai Na haifi Sultan Abdus Samad Aamaan Mehran, na biyu."


Kallonta suka yi tare da kauda kansu, idan. Suka ci-gaba da tsayuwa zata iya saka su fidda abinda yake ransu. Dan haka suka juya tare da barin d'akin, suna mata fatan Alkhairi. Zama yayi a kusa da ita yana kallonta.
"Ya jikin naki?" Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Da sauki, ina son cin abinci amma ina tsoron kar a bani guba sabida kishin rashin samun damar daukar cikin ka."


Mikewa yayi tare da barin d'akin, murmushi tayi sannan ta shafa cikin Jikinta, kallon Fudail tayi da ya kura mata ido, tabbas badan kar yayi abinda zai sanya Mehran ya kullace shi ba, da yayi ta dukar cikin jikinta, har dai ta mutu. Amma a halin yanzun kana tab'a cikin kamar ka sayi mutuwa je da hannunka,domin Mehran ba zai tab'a barin ka a raye ba.


Amma kuma taya haka ya faru? Cikin a sanin shi na Nawwas ne, kuma sai gashi ya juye tare da komawa na Mehran,.kuma babban damuwar shine meye ya faru ranar da ta fara kwana da Mehran.


----
Kallon ta Sultanah Hoyam tayi sannan tace mata.
"Kamar Ya Azizatul Nissah tana da ciki? Kina nufin yayi tarayya da ita ne! Ko kina nufin."


Zuɓewa Mahlika tayi tare da rike hannunta cikin juna jikinta yana rawa tace mata.
"Sultanah! Duk abinda kike tsammani haka ne". Ture kayan gabanta tayi tare da cewa.
"Na aike ki ne ki zo ki gaya min matar da suke kewayen shi.tana da ciki ne?


Meye amfanin abinda na baki kina saka musu a shayin su? Wato ga sakarya nan bata san me take yi ba, Yanzun meke tafiya a harem?"


"Kiyi hakuri abinda ke faruwa babu dad'i domin dai ta kwace duk abinda ake yi, sannan kuma ta hana kowa shigowa shashinta. A takaice dai hatta abincin da zasu ci sauran matan daga gare ta yaƙe.".


Sake wurgi tayi da kayan marmarin gabanta.
"Wani irin hauka kika yi ne? Me kika aikata min haka? Baki da hankali da zaki bari kome ya koma hannunta, ni kuma nawa aikin fa?"


Sake damke hannunta tayi iyaka razana ta razana, amma bata iya ko tari ba, domin Sultanah Hoyam ta isheta riga da wando, dan haka ta sunkuyar da kanta, sannan tace mata.
"Ki gafarce ni!"
"Tashi ki fita!" Ta daka mata tsawa. Da sauri ta mike tare da barin d'akin, ta nufi harem.


Ajiyar zuciya ta sauke yafi sau uku. Sannan ya nufi Harem, tunda ta nufi hanyar gidan, take jin kamar zuciyarta zata buga, tana shiga tayi karo da Rubina babban baiwar Azizatul Nissah.


"Ina kika tafi? Toh muje zaki yabawa aya zakinta, tunda da zaki fita baki gayawa Sultanah Azizatul Nissah ba. Wato anje kitsa munafunci ko?"


Bata ce mata kome ba, har ta shiga gurin Azizatul Nissah, kanta a sunkuye. Tana shiga ta tsaya daga bakin kofar shiga d'akin.
"Da izinin waye kika fita daga Harem?"
Shiru tayi tare da wasa da warwaron hannunta.
"Kinawa Ikram Aiki ne?" Da sauri Mahlika ta d'ago kanta, tare da girgiza kai tana faɗin.
"Me kuma zanyi mata bayan bata nan!"


"Ki min shiru! Koda yake ba mamaki kinawa Jasrah aiki ne ko? Toh zo nan." Durkusawa tayi a gabanta, tare da matsawa kusa da ita.


Babu tausayi ta shiga marin Mahlika, sosai fa tun yarinyar tana jurewa har ta kasa jurewa, bata fasa ba, shigowar Mehran ya sata sauke hannunta da ta d'aga, zata kuma marin Mahlika.
"Meye haka?"


"Sultan MEHRAN! Abu ta kawo min da guba, wai ikram ce ta bata sakon duk lokacin da ta sami labarin ina da ciki ta zuba min nasha." Ta faɗa tare da sake kuka.


Wangale baki yayi tare da kallon su, kara kallon Mahlika yayi yasan yace mata.
"A sanina baki shiri da Ikram meye gaskiyar abin da ta faɗa?" ...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


5


Jikinta ne ya dauki rawa, tana kallon sharri kiri kiri. Amma bata da ikon kare kanta, kallon ta yayi a karo na biyu fuska babu alamar wasa yace mata.
"Ba dake nake ba?" Ya faɗa da dan karfi, haka ya sanya ta kuma rud'ewa tana zaro idanu.


"Sultan!" Ta kira sunan shi jikinta yana wani irin rawa."Fudail!" Ya kira sunan Fudail ko rufe baki bai yi ba, sai gashi shigo d'akin.
"Yawwa bawa Fudail ka tafi da ita,.ka kuma tabbatar ka hukuntatta, domin tayi yunkurin zubda min cikin jikina ko Sultan Mehran" ta ambaci sunan Mehran tana kallon shi.


Dauke kan shi yayi tare da zama ya kasa cewa kome.
"Zaku iya tafiya!" Ta kuma fada, tana murmushi. Matsowa tayi kusa dashi, ta zauna tana me sake mishi murmushin jin dadi.
"Sultan MEHRAN! Kaga ikon Allah baka ta samu haihuwa ba sai a kaina, kuma." Juyawa yayi yana kallonta,.kafin ya dauke kanshi yana me jin b'acin rai akan yanayin da yake ciki.


Haka tayi ta damun shi da magana, ganin yaki kulata yasa ta mike tare da barin d'akin, bin bayanta yayi da ido, ita kuwa tana fita bata tsaya ko ina ba, sai Shashin Sultanah Fazilatul nisa, tana tare da Shairah da Narjis, suna tattaunawa ta shigo.


Murmushi tayi sannan ta nemi guri kusa da Sultanah tace mata.
"Nazo ne ki albarkaci jikanki da yake cikin mahaifana"


A matukar mamaki suka kalle ta, bakin su sake.
"Sultan MEHRAN bai gaya miki bane? Ai wata biyu da suka wuce ya..."


"Toh ya isa!" Inji Shairah, ya daka mata tsawa.
Gyara zaman tayi cikin fusata tace mishi.
"Kai waye? Bawa dan daudu, ni zaka dakawa tsawa? Lallai kana son na saka a maka koran kare."


"Ya isa haka, me kike bukata?" Inji Sultanah Fazilatul nisa. Tana kallonta,
Dariya tayi sannan tace mata,
"Bana son a kuma barin Mehran yayi mu'amala da wata mace! Sannan bana son ana shiga shirgin shi. Idan da hali a fita hanyar shi. Domin nice Magajiyar sarauta nan gaba, Uwar Yaron shi da yake kwance mahaifana!"


Ta mike tare da zaga dakin tana murmushin mugunta, tana faɗin .
"Mugun hukunci zai tabbata a kan wanda ya Kuskura ya shiga lamarin Mehran. Zan gyara mishi tunanin shi da nazarin shi, kar na kuskura naji mugun labarin akan haka, a sanar da matan da suke dakon ya kwana dasu."


Tana gama fadar haka ta bar dakin cikin jin dadi tare da jin ta isa domin ta kaftawa Sultanah Fazilatul nisa kashedi kuma hakan zai taimaka mata, domin idan ba haka ba tana ji tana gani sauran matan da suke hareem zasu iya daukar cikin Mehran.


Koda ta fita, kallon matan da suke hutawa tayi, sannan ta zauna tana gyara gashin kanta, tana murmushi. Baiwarta Rubina ta kalle matan gurin ta shiga musu bayanin cikin Azizatul Nissah, take Jasrah ta mike tana faɗin.
"Karya ne, baki isa ki"


"Kawo min ita nan" inji Azizatul Nissah, babu musu aka kawo ta, jefata aka yi a gabanta, mik'ewa tayi a hankali, tare da kallon ta. Murmushi tayi sannan tace mata.
"Kika ce me?"
"Kar..." Kifa mata marin da tayi yasa ta had'iye maganar da zata yi.
"Rubina, ki zane min ita." Inji Azizatul Nissah wai a zane Jasrah.


Duk sauran matan hatta Sakeenatu binti Abu Waqqas, sai da jikinta yayi sanyi, domin tunda take rayuwa bata tab'a tsintar kanta cikin mugun yanayi ba, sai da ta shigo cikin Samaind. Akan idanun su, aka zabe Amirah Jasrah irin mugun dukar nan da babu wanda ya isa yayi maka ita sai mugu.


Shafa Jelar gashin kanta tayi tana faɗin.
"Ya isa haka, ba ita ba hatta ku idan kuka kuskura kuka d'aga min murya zan ba kowa kyautar hukuncina, ku dauke ta ku kaita shashinta."


Cikin wani irin tsoro da fargaba tabbas Azizatul Nissah ta shirya fuskarta kowa kuma a cikin wannan yanayin, ta gaya musu ciki ne da ita, dan haka kar kowa ya taka shashin Sultan Mehran sai da izinin ta. Gyada mata kai suka yi. Domin babu wata hanya da zasu mata bori.


----
"Meye ya hadaki da ita har ta sako Ikram a maganar ta." Fudail ya tambayi Mahlika.
"Kawai sharri take son yi mata, kuma tasan a halin da Mehran yake ciki na kewar Ikram zai iya tsanar." Rike bakinta tayi tana kallon shi.


Murmushi yayi sannan yace mata.
"Karki damu. Yanzun me kike ganin zaki yi?"


Shiru tayi sannan ta sunkuyar da kanta kasa, tana me jin kamar tace mishi zata koma Madinatul Mah, sai kuma ta d'ago kai tana faɗin.
"Babu abinda zanyi."
"Ni kuma zan sakaki aiki" ya faɗa mata yana leka hanyar, a hankali ya matsa tare da gaya mata abinda yake son tayi mishi, zaro idanu tayi sannan tace mishi.
"Zanyi amma da sharadin. Zaka hada ni da sultan Aamaan!

Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ba zan iya hadaki dashi ba, mutum ne me ra'ayin kanshi, idan kika sami damar ya gayyace ki toh idan kuma baki samu wannan damar ba, ina me tuna miki aikina da na baki. Sultan MEHRAN yana cikin kewar Ikram ne ko yayya aka tunzura shi zai iya aikata wani abu bayan haka."


Yana gama gaya mata haka ya juya abin shi ya barta a gurin. Shiru tayi na wani lokaci kafin ta bar gurin tana jin itama zata tsayawa kan.
......
A can cikin gidan kuwa, kallon Juna ake tsakanin Sultanah Fazilatul nisa dasu Shairah. Kura musu ido tayi kamar tana son gano gaskiyar abinda Azizatul Nissah ta faɗa, sai kallon su take kamar tana hango abinda.


"Ina Mehran? Maza ku nimo min

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads