Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 274096 words

Chapter 15 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1364

Ads at the middle of Article

jin haka a kirjina, hannun shi dukka biyu suna kan dukiyar shanuna, a hankali na zare hannun shi, tare da ture shi na mike da gudu domin har zuwa lokacin Dawakai basu bada daman da mutanen shi zasu iso gare shi ba, da gudu nayi ta shiga tsakanin dawakan na bar gurin, bin gurin yayi da ido, yana jin wani abu yana mishi yawo a kwantar shi, kamar wanda aka saka mishi wani abu. Lumshe idanun shi yayi tare da cigaba da kwanciyar a gurin, dakyar Darakshan ya iso inda yake, suka mishi kawanya. Tashi yayi zaune tare da cusa hannun shi cikin tsakiyar kirjin shi, yana kuma jin sautin bugun zuciyar shi, tare da fitar numfashinta a kan fuskar shi.


Mik'ewa yayi a sanyayye kamar wanda kai ya fashe mishi a cikin shi, tunda ya shiga cikin gidan ya kwanta bai ce musu cikanku ba, bai kuma ce ga abinda zasu mishi ba. Amma idanun shi a rufe suke. Jikin shi kuwa a mace take.


Ba zai iya bada labarin abinda ya faru ba, amma tabbas yana da yakinin akwai abinda yake bibiyar shi, musamman lokacin da yaji ta ambaci wata kalma ya kasa fahimtar Meye haka yake nufi, *Ya Rabbi*
Me ye haka? Sake shiga cikin damuwa yayi tare da kara shigewa jikin kilishin da aka shimfid'a mishi a falon yayi.
---
Tunda na samu na bar gurin da gudu,.nake jin zuciyata tana wani irin bugawa, tsoro da firgici suka taro min a guri guda, fuskar shi tana cikin Sulken yaƙi, wato hular baka ganin kome sai hancin shi da yar bakin shi ruwan hoda.


Ƙwayar idanun shi har wani ratsi_ratsi yake na alamar ja, "amma ai ba a kai na ya fadi ba, toh taya aka yi na ya juya kasa Ni kuma na koma saman shi,alamar nice na fadi akan shi?"


Sake shiga rudani nayi sanin da nayi dai nice na taimaka mishi amma taya? damsshin da naji a wuyana ya sani shafa gurin, "jini?" Na fada da karfi ina me tsalle gefe guda, toh ta ina jinin yazo. Duba jiki na, na fara ina mamaki. Kafin kace me na sake shiga rudani.


..kai karshe da na Fahimci cutar da kai na nake sai, na manta da batun na nufi gurin aiki na, amma maganar gaskiya na wuni a ranar suku suku, ba dan kome ba, sai dan yawan jin sautin bugun zuciyar shi a dodon kunne na.


Tunda na shiga cikin gidan suka fahimci, akwai abinda yake damu na, amma zunzurutun zurfin ciki na, babu wanda ya isa ya san me suka kyale ni, ina gama share musu ko ina na juya zan fito, Mamar Jasrah tace min.
"Yau zamu yi darasi akan Budurwan Masarauta, amma manta kawai, zaki gane anan gaba"


Nasan tana son koyar dani, amma Ni ban ga dalilin haka ba.


Yadda take warware min sirrin cikin gidan sarautar ya bani tsoro da Mamaki, dan haka zunzurutun tsoron da yake cikin labarin ya sani ji kamar zan mutu na dawo, sai da muka kusan wuni tana bani labarin yadda aka kafa daular da yadda kowa yake kokarin sai ya kafa haramtacciyar ra'ayin shi a cikin daular.


.... Sai bayan magarib na baro gidan, na gaji sosai. Dake ban tab'a fita cikin dare ba, ban san yadda masarautan yake ba, ashe suna sake wani katon kare me sufar kura, shafa gefen cikina nai,.tare da dauko sarewa na. Sam na sha'afa na saka a bakina kenan naji gurnannin abu a bayana.


Da sauri na juya tare da kallon shi, haushi yayi min. Naja da baya, ya kuma min haushi naja da baya. Cikin wani irin zafin nama, muka kasa a guje, bina yake ina kaucewa yana bina ina kaucewa, sai da ya kusan kamo Ni na kwace.


Yankar wata yar lungu nayi, kawai sai ji nayi kamar an d'ago ni sama,turus karen yayi, nima zunzurutun tashin hankali ban fahimci me ya faru ba, sai da na bude idanuna na kalle ni a tare da wani mutum,dake akwai duhu bana hango kome saboda fuskar shi tana lullube cikin duhu, nima nawa fuskar tana lullube.
Hannun shi a k'uguna, a hankali ya hade jikin mu, wanda ya haifar mana da bugun zuciya lokaci guda, yana rungume ni ya sakewa karen nan, wani abu, wanda yasa karen faduwa, zunzurutun rashin mutunci sake ki yayi daga saman yayi tafiyar shi, haka na fado kusa da karen da ya suma, na tsallake zan wuce. Juyawa nayi tare da d'aga kai na.


Shima yana tsaye amma bai juya bayan shi ba, tafiyar shi ma yake kokarin yi.


A hankali na juya tare da barin gurin, da sauri na nufi shshin mu, tunda na shiga na Fahimci akwai sabin bayin da muka samu. Ban kula kowa ba kai na a sunkuyar zan wuce.


Shan gabana aka yi, sake ratsa gefen ta nayi ta kuma shan gabana, daga can gefe ina hango Narmin tana kallon mu, kai hannun tayi.zata cire min mayafin fuskana, nayi maza na dake hannunta.
"Mahlika karki tab'a ta, ki rabu da ita"
"Narmin ba zan iya ba, duke min hannu tayi, bakar fata tana da izza har haka." Ta tako har gabana, tare da kai hancinta zata min isgilanci, sai kuma ta shako kamshin turaren da taji shi, bayan shigarta Falon Sultanah Hoyam, har take tambayar Narmin ko zata sato mata turaren Sultanah nan ne, dan kamshi yayi mata.


Kwaɓe ta Narmin tayi tare da gaya mata wannan turaren SULTAN Mehran ne, ta kuskura tayi hauka sare kan ta zai yi. Dan haka ta shiga hankalin ta, amma kuma kamshin Turaren ya zauna cikin kwakwalwar ta, wanda ya haifar mata da daukacin kaunar shi.


Kallona tayi kirjinta na wani irin bugawa, cikin fusata ta kai min duka dan ban zaci haka daga gare ta ba. Faduwa nayi can gefe,
"Narmin wannan yar yarinyar naji kamshin turaren Sultan Mehran a Jikinta a gidan Uban waye ta samu?"


"Sultan Mehran?"
Kafin kace me, dama suna jin haushina tuni suka tara min fadawa, aka dauke ni zuwa shsshin Sultanah Hoyam, ita kanta taji kamshin dan haka ta tashi tare da sakawa a riko ni har shashin Mehran. Tunda muka shiga baya kusa, haka ta haura sama,can sai gasu tare yana sanye da wata rigar shan iska. Kallon mu yayi tare da mutanen da suka riko ni, sannan ya zubawa Sultanah Hoyam ido.


"Mehran! Taya akayi yarinyar nan ta sami turaren ka? Abu yaja ana ta kanannan magana." Dauke kai yayi kamar bada shi take ba, tana kuma tambayar shi ya juya ya bar mu a gurin, cikin takaici da bakin ciki, tasaka a kai ni can wani gidan Horo me suna Darul Azab...
. Bayan tafiyar mu ne tasaka aka kawo mata Mahlika.
"Kinyi abinda ya dace, dan haka ina son ki saka ido akan kome na motsin yarinyar, dan in har ta sami kusanci dashi a bayan fage yake nan. Kema bana son kusancin ki da Mehran kasancewar ban yarda da kowa akan shi ba. Kinji Ni?"


"Eh na ji ki Sultanah."
"Zaki iya tafiya!"
"Nagode Sultanah"


Wannan littafin na kuɗi ne..
*Allah yajikan Iyayena 😭😭*
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 22
Tana da fita ta sake murmushin mugunta tace.
"Lokaci yana zuwa Sultanah Hoyam."
A hankali take takawa, tana nazarin abinda Mahaifiyarta tace mata.
"Narmin itace makamin mu, sabida itama tana da ciwon Sultanah Hoyam, idan muka rike ta zata bamu hadin kai.


Burina ki sami kusanci da Sultan Aamaan Mehran, yadda zaki yi abinda babu wnada ya tab'a yi, amma karki sake Abban ki yasan cewa akwai cin Amana a cikin tafiyar domin ba zai yarda ba, kuma zai iya dakatar dake abinda zaki yi."


Murmushi tayi a karo na biyu, sannan ta nufi hanyar shsshin su.


~~~
Tunda aka kai ni, darul Azab, wanda yake cike da zalinci karkashin kulawar wasu maradai mara imani da mutunci, ya sani shiga cikin tashin hankali, domin kuwa wani irin nau'in azaba suke bawa kowa. Suna da wata bulala me dauke da wasu irin allurai a jikin shi, dan haka suka shiga zane ni dashi.


Har sai da nayi laushi, haka suka kyale ni, washi gari suka tashe ni da ruwan zafi, aka daura sabon azbtuwar.


.. tunda gari ya waye FAZILATUL take saka idanun akan zuwan Ikram babu ita babu labarinta, har zuwa rana anan ta tura darda ya tafi niman ta, sai hangota yayi a tsakiyar masarautan an saka bayi suyi ta jifarta da d'anyen tumatiri, da sauri ya koma ya gaya mata.


Bisa al'adar idan aka gama mata wannan uƙubar, zasu kuma yanke mata hannun sabida tai sata, dan haka ta rubuta wasika izuwa ga mutanen gari tare da gaya musu, irin nauyin Uƙubar da Sultan Aamaan Mehran yake ganawa mata da bayi, bayan kowa yasan halin shi dan luwadi ne.


Kasancewar an cika ana kallon Ikram har aka watsa musu takardun, basu Fahimta ba, lokacin da suka fahimci sakon da yake jikin Takardan, aikuwa talakawa suka shiga bore, tare da kunce Ikram, sannan suka juya al'amarin satar izuwa cewa.
Ya kamata zai yi luwadi da ita ne, ita kuma garin gudu ta shafe kamshin turaren.

Dan haka lokaci guda, maganar ta zama wutar daji, tare da zama babban al'amari. Talakawa sun fusata ai nu, dan haka suka ce ko ya fito ya kare kanshi ko kuma ya sauka a kujeran mulkin.


*Wani irin tashin hankali nake kuma fuskanta ne? Wani irin bala'i ne ya ke kuma tunkara na? Me yasa sai Ni? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun*
Wadannan sune abinda yake yawo a raina, duk da sun kwance ni, na kasa tafiya. Sakamakon yagewar da tufafin jikina yayi. Ina durkushe a gurin.


....
"Wannan wani irin rashin daraja ne? Idan kasan zaka yi kazamar rayuwar ka, sai ka..."
Cikin zafin nama aka hango kan Mir Jazib, yana tsalle gangan jikin shi yana birgima jini yana ambaliya a cikin fadar.


Takarkarewa Sultan Mehran yayi ya kwatsama musu ihu, sabida yadda yake jin zuciyarshi tana ci da wuta. Idanun shi Jajjur ya nuna su da yatsa yana huci.
"Ku dauko min ita!"


Ya juya tare da barin Fadar zuciyar shi tana ci bal-bal-bal. Ina sunkuye naji an dauke ni cak, tunda suka dauke ni basu ajiye ni ba, sai a katafaren shashin sa, wanda yake dauke da kamshin turaren da ake bala'i akai. Tunda suka ajiye ni, jikina ne yake rawa sakamakon hango shi da nayi tsaye tare da juya min baya, yana daure da kwarjalle. Dakin kuwa kwalbar turaren ne a fashe a ko ina. Juyawa yayi tare da kallona idanun shi da fuskar shi abin tsoro ne. Domin sunyi jajjur.


Shiga ban dakin yayi tare da barina a gurin, dan haka ban yi karambanin kome ba, na kwanta sabida zazzaɓin da yake cin jikina. Tunda na kwanta a gurin nake gani dishi dishi, ba zan iya tantance abinda ya faru ba, sai dai na farka ne a wani daki karami a dai cikin castly ɗin. Tashi nayi a hankali na ga maganin tare da abinci. Tashi nayi na fara ci, sannan na lura da ban daki na shiga nayi alola da wanka na fito.


Ina idarwa daya daga cikin mutanen shi ya shigo min, kallona yayi ina ƙoƙarin saka mayafin fuskana, takowa yayi gaba na, tare da kai hannun shi zai tab'a ni, na kaiwa hannun duka.
"Me zaki boye a fuskar ki? Baki san har jikinki na gani ba."
"Kayi kuskuren ganin jikina, amma yanzun zaka biya ladan ganin da kayi."
Wani irin karar da muke kama gashin kaina na dauka, tare da suka Mishi yana kaucewa, wani irin azazzaben fada muka kama a cikin d'akin, tunda yaga jikina wallahi sai na fasa mishi idanun shi.


Aikuwa Allah ya bani Sa'a na soka mishi tsinken, a saman idanun shi, tare da kai mishi wata irin duka, ihu Yasaka tare da kiran Fudail ya kawo mishi dauki, duk da na sha duka amma haka bai hana Ni jin dadi, na tsinka mishi jijjiyar saman idanun shi ba. Shigowa Fudail da Darakshan suka yi, suna kallon yadda gashi kaina ya lullube fuskana.
"Ke wacce irin mutum ce da bata jin magana?" Inji daya daga cikin mutanen.
"Rashin darajar ku ya janyo haka, idan baku kyale ni ba, wancan lusarin dan daudun sai na burma mishi wuka ta cikin shi ya bullo ta bayan shi. Ko kuma ta alkalamin shi ya fito ta duburar shi."
Fitar da shi suka yi, sannan suka koma gurin Sultan Mehran suka gaya mishi. Da hannun yayi musu alama, su fitar da Ita, dan haka suka fita da sauri abun su, kai ta shsshin bayin suka kuma yi, tun daga ranar ban kuma samun rashin mutunci ba. Sai dai kuma an sauya min aikina daga can haramtacciyar Fada, zuwa cikin Fadar.


Inda nake kawowa manyan fadar abin sha da naci, wannan shine aikina da kuma dalilina na zama cikin masarautar. Idan akwai Abinda yake min ciwo yadda suke kai min duka a ɗuwais dina,.duk da kuwa dattawa ne babu matashi sai shi da masu kula dashi.


Bai tab'a kallon haka a matsayin cin mutuncin ba, kawai abinda ya sani ya zab'i a tozartani sama da abinda nayi mishi.


Yau na kawo musu abin sha, watsarwa suka yi tare da finciko ni, Mir Rahil yana ƙoƙarin kai hannun shi cikin rigana, na daki makogaron shi, take numfashin sa ya tsaya cak. Caaaa dakaru suka min da takobin, zare na jikin Mir Rahil din nayi, tare da jan layi.


Mamaki ne ya kama kowa a gurin.
"Ke ki ajiye takobinki!"
"Ba zan ajiye ba sai na kashe wancan kazamin me wanka cikin datti."


Aikuwa yaki ya barke a tsakanin mu, me shegen tashin hankali. Kafin kace me na jikata mishi dakarun fadar, ina kallon shi dukda na gaji sosai, abinda ya kwace ni a hannun su zafin nama, a duniyar yaki zafin nama itace sama da kome, durkusawa nayi akan gwiwata, dogare da takobin ina huci.


A hankali ya mike tare da zare takobin shi, ya tako gabana.
Da ace nasan waye a gaba na, da har duniya ta tashi ba zan so na kuma hada karfin dantse da wannan basamuden ba.
Mik'ewa nayi tare da tattara gashin kai na, na mai da baya, sannan naja kafana baya tare da jan layin. Na mishi alama ya taso idan ya shirya.
Gyada kai yayi tare da sake murmushin takaici. Yau da mace zai yi fada. Bari yaga wani irin horo ta samu. Sai dai kashhhh Fudail shi ya sha gaban shi tare da kawo min mugun sara kamar zai rabani gida bi.

Tunda muka fara gwabza yaki tsakanin mu, muke jin kamar zamu kashe junan mu, dukda wutsiyar raƙumi tayi nesa da kasa, sannan abin kunya ce a gare shi faɗa da mace, shi yasa Fudail ya amshi fadar tare da fadawa musu maganar da yayi matukar tasiri a ransu.
"Ba zamu tab'a barin Sultan Mehran yayi fada da yar karamar kiyashi ba"
Dan haka tunda muka fara, ko kwarzanin shi banyi ba, sai ma kare kai na da nake, domin Idan ya kawo min sara, ji nake kamar da mutane dari nake fadar, yarda takobin nayi tare da kallon shi.
"Me kika taka?"
"Idan ka shirya!"
Da nasan cewa bala'in da zan tarowa kai na, haka ce da ban yi yunkurin juya fadar zuwa dambe ba.
Domin lokaci guda nayi dana sanin yafi karfin kwando dubu, domin dukar kawo wuka Fudail yayi min. Koda ya juya, babu sultan Mehran a cikin fadar. Daukata yasa aka yi, suka kai ni can Shashin bayi.

Sai da na kwana uku, kafin na warware kamar jaka. Ina zaune aka watsa min kaya.
"Ki saka zaku je can babban majalisar Sultan zaku sanya su nishadi."
"Ba zanje ba."
"Zaki"
"Toh naga mai kai ni!"
"Idan baki kije dan Allah ba zaki dan azabar shi."
Lashe bushashen lebbena nayi sannan na shirya ba daura wata mayafi kai, cirewa suka yi tare da daura min wata jigidan zinari wanda kana motsa zaka ji karan har cikin kanka. Kafana ma haka da ko ina, kayan da na saka yar karamar buje ce, me tsagu har tsakanin cinyoyina, sai dan karamin dan kamfe da yake makale da shi. Kirjin kuwa dama akwai wani yadin da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads