Showing 57001 words to 60000 words out of 274096 words
Chapter 20 - DAULA BIYU Complet Document .txt
gefen shi wanda yake dauke da kayan ciye ciye, a hankali ya motsa bakin shi kamar me fama da ciwon baki yace.
"Da sauki!"
Kallon shi suka yi, sannan suka sunkuyar da kansu. Gyaran murya Amir Hood da Mir Umdatuddawla yace.
"Sultan Aamaan Abdus Samad, mun tawo baki daya ne mu baka hakuri da!"
D'aga musu hannu yayi sannan ya kalle su daya bayan daya sannan nuna musu kofar fita, kan shi kwance saman matashin kujeran.
A hankali suka yi ta mik'ewa daya bayan daya, suna fita, karshe dai ya rage shi daya a falon, fitowa nayi ina ƙoƙarin shiga kitchen, bin bayana yayi da ido, ganin yadda na b'ata kayana da jini ya sashi dauke kai, bai ce min kome ba, har na gama abinda zan yi na fito na koma dakin, tasowa yayi tare da shigowa, wai zai gaya min abinda ya faru da jikina shine ya tako har inda nake tsaye, sai ji nayi an wurgani gado, na tashi da sauri. Ya kuma mai dani tare da zama a bakin gadon ya janyo kafana, a hankali ya ture ni ta daya gefen kyakyawan zanin gadon ne ya b'aci da jini, yana ganin na Fahimci haka ya mike tare da barin d'akin.
Saka kai na nayi a tsakanin cinyoyina, na rufe idanuna sa karfin tsiya. Ina sauke ajiyar zuciya. Tashi nayi na shiga wanka nayi sosai sannan na gyara jikina, ina gamawa na taso tare da nufar kitchen na daura mishi gasheshen nama sai madara da nayi gyaran shi. Na kawo mishi.
Tunda na kai dakin yana zaune tare da kallon yadda na gyara gadon tsaf, zama yayi ya fara cin abincin a hankali. Tunda na gama ya nutsu na fita daga dakin.
~~
Tunda Sultanah Hoyam taga ya sami sauki, ta shiga aiko mishi yan mata tsalla-tsalla. Wai suzo su dauke mishi kewa, sai dai abinda ka kasa Fahimta akan shi yan matan baya barin su, su shiga min dakin, sai dai kuma zai fito falo dasu ya zare kayan shi ya kwanta suna mishi tausa, dake Allah ya taimaka bana jimawa a cikin hailata, kwana hudu ne, lokacin ana sallah saura kwanaki ƙalilan za ayi.
Bana son kwanakin tahajjun ya wuce ni ne, ranar da nayi tsarki ranar na fara sallah tahajju, idan ina karatu bawan Allah nan dawowa yake falon ya zauna har sai na idar sannan yake komawa dakin shi, sake kwanakin azumi zanyi dan haka yana ganin ina sahoor, bai ce min kome ba, sai gyara kwanciyar shi da yayi tare da lumshe idanun shi, yana son kyawawan dabi'unta.
Ibadarta ya zarta tunanin shi, tana da kokari akan kome, sai dai matsoraciya ce na kin karawa, yana son mace me kokarin irin na Ikram.
Kaf kwanakin da nayi ina ibadana, tare dashi muka yi domin tsakkanin shi da Allah ya saka idanun shi akan ibada na, kasa hakuri yayi tare da kiran Fudail.
Shiru yayi tare da kasa cewa kome, sannan.yace mishi.
"Kasan wani irin abu yarinyar nan take yi? Shi ba waka ba shi ba hira ba, meye shi? Sannan idan karfe sha biyu da rabi yayi tana wani abu, da d'aga bayanta dama.
Haka idan karfe uku da rabi yayi toh ba zata kuma kula Ni ba sai tayi abin, Fudail ina cikin damuwa?"
Kasa yayi da kan shi tare da cewa.
"Mehran ba kome take ba sai ibada."
"IBADA?" Ya tambaye shi tare da kura mishi ido, sannan yace mishi.
"Kai kana yi ne?" Gyada mishi kai yayi alamar eh,
"Me yasa Ni bana yi?" A dimauce Fudail ya zuba mishi ido, shi kanshi ya hangi firgici da tambayar da yayiwa Fudail din.
Shiru yayi a gajiye sannan ya juyawa Fudail baya, yana sauke ajiyar zuciya.
"Mehran!" Dakatar dashi yayi, bai kuma magana ba, haka Fudail ya fita,
---- Ina gyaran kifin da Darakshan ya shigo min dashi, akan zan dafawa Mehran, na nutsu bakina yana ambaton sunan Allah, shigowa yayi cikin madafin ya tsaya a kaina, ban d'ago ba amma kuma hakan bai min dadi ba, kasa jurewa nayi ina kallon shi. Kafin nace mishi.
"Ko wadanda ba musulmai ba, idan zasu shiga gurin musulmai suna faɗin, Amincin Allah ya tabbata a gare ku. Wai me yasa kake haka ne?"
Haka kura min ido yayi, sannan yayi kasa da kanshi, jikin shi a sanyayye ya fita daga cikin madafin, bai zame ko ina ba, sai shsshin Mahaifiyar shi. Kura mata ido yayi cikin wani irin rauni yace mata.
"Waye Ni?"
"Mehran ban gane ba?" Ta tambaye shi akan tambayar da yayi mata.
"Waye Ni?" Ya kuma tambayar ta,
"Ka nutsu ka min bayani me kake nufi da haka?"
Hawaye ne ya shiga sauka daga cikin idanun shi yana kallonta, bakin shi na rawa, yace mata.
"Me yasa bana sallah?"
Wani irin bugu zuciyarta yayi cikin tashin hankali a zuciyarta tace.
*Kai Na shiga Uku na lalace! Wannan shaidaniyar Yarinyar sai ta t lalata min rayuwa Ya zanyi?*
"Yanzun Mehran akan sallah ne kazo ka tsitsiye Ni?"
Ta faɗa fuskarta a daure, tare da niman guri ta zauna, sannan tace mishi.
"Zauna muyi tsayayyen magana."
Ba musu ya zauna, cikin hikima da dabara ta shiga kawo mishi abinda ba shi bane, tare da gaya mishi, wacece Ikram sannan ta gaya mishi ai surkulle take. Dake Uwa ce, kuma tana da hangen nesa dan haka tayi ta b'ata Ikram a hankali cikin dabara sai da ta cusa mishi rashin yarda akan Ikram kuma ta zauna ta gaya mishi abinda yasa take jin ba dad'i akan zamanta a shashin sa, dan haka ya kore ta, idan ba haka ba zata kawo mishi rudani.
Sai dai kuma kasa yarda yayi daga abinda ya faɗa yana kallonta cikin nauyin harshe yace mata.
"Fudail yana yi"
"Toh munafukai ne, kuma suna son ganin bayan ka ne, idan baka manta ba, lokacin da baka da lafiya haka suka yi ta cin Amanar ka, idan kuma karya ne ka tambayi Darakshan Fudail da Ikram suna mummunar alaƙa. Yanzun ma idan da zaka shiga gidan a bazata zaka same su."
Ita lallai dole so take ta raba shi da Ikram, musamman da Darakshan ya kawo mata tsegumin Fudail yana son Ikram kuma yayi alwashin ko za a kashe shi ba zai tab'a barinta ba. Kurawa Mahaifiyar shi ido yayi wanda ya zaro su kamar zasu diro kasa,ji yaƙe kan shi yana wani irin yatsuna kamar an zuba mishi tsutsa akan shi. Sunkuyar da kai yayi bai ce kome ba. Amma hatta gashin jikin shi a mike suke.
Dan haka ya tashi daga inda yake zaune ya saka kai zai fita, tace mishi.
"Mehran kayi ƙoƙarin karkade munafukan da suke jikin ka, idan har Fudail yanayin sallah tabbas shi da Ikram bayan ka suke son gani, idan kuma kaki toh ba makawa."
"Ina ruwa na?" Ya tambaye ta, cike da mamaki take kallon shi, yadda lokaci guda ya gwaleta, ya sa kai ya fice, idan ka kalle shi sai ya baka mugun tausayi, domin yayi laushi sosai, kuma a iya kan fuskar shi zaka karanci yana cikin tashin hankali da damuwa, duk inda ya gifta gaishe shi ake dakaru na bin bayan shi, cikin nutsuwa.
Fuskar shi ma'abociyar kwarjini da haiba ta fito fess, kana ganin shi kaga wanda yake ji da mulki da izza, amma yau jin amintattun shi. Suna ha'intar shi yasa shi jin babu dad'i, ba zai iya kashe Fudail ba haka ba zai iya kashe yarinyar da yake jin dadin sauraron muryan ta ba. Amma tabbas zai iya raba su, cikin sauki zai haramtawa Fudail shiga shashin sa har abada, har ya iso kofar da zata sada shi da falon sama yaji Muryan Ikram.
"Kai jinka ina zaune ne anan abisa jin dadin rayuwa ta? Toh ina nan ne dan babu yadda na iya, ina nan ne sabida fansar rayuwar kanwata, ina nan ne domin kanwata. Iya adadin lokacin da na diba ya cika tabbas ko bai zo min ba zan koma mahaifata, Idan masoyina yazo Tabbas ba zaka kuma gani na nan ba."
"Amma kuwa wannan masoyin naki sunan shi gawa! Domin wallahi na rantse miki da wanda rayuwata da mutuwata take hanun shi sai na kashe duk wanda ya kuskura ya keta Alfarmar Mehran! Duk wanda ya kuskura yazo nan da sunan yazo daukar ki, bayan kina kasar mulkin Mehran sai na raba kan shi da gangan jikin shi.
Dan haka ke mallakin Sultan Aamaan Mehran ce, babu wanda ya isa ya kusanci inda kike balle ya tafi dake k..."
Gyaran murya yayi bayan ya shigo falon yana kallon mu, munyi cirko cirko,. Dauke kan shi yayi tare da wuccewa abin shi. Murmushi Fudail yayi tare da sauke wata Boyayyen ajiyar zuciya, tabbas yasan nadan Allah ya mishi baiwar iya fahimtar ana kusa dashi ba da ya tafka kuskuren da ba zai tab'a barin shi ba.
Lokacin da Mehran ya iso bakin kofar, yaga alamar wani yana bakin kofar, dan haka bai dakatar da Ikram ba, sai dai shi ya sauya kalaman shi. Fita yayi daga gidan. Burin shi ya cika dama abinda yake son gani kenan Mehran yaji Ikram tana da wanda take so.
Tunda ya shiga dakin shi ya kwanta, tashi yayi zubur. Tare da kaiwa da komowa, wato tana da yakinin akwai wanda ya isa ya keta Alfarmar shi yazo ya dauke, ya ga shegen da ya isa ya shigo har sansanin shi ya dauke ta....
Littafin nan na kuɗi ne.
Allah ya jikan Iyayena
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Yadda yake huci sai ka rantse da Allah, an zo daukarta ne nan kuwa zunzurutun rigima ce kawai yake damun shi. Kamar wanda aka mintsine shi ya fito daga dakin, kitchen ɗin ya nufa tare da kallon bayan ta, yadda yan k'ugun ta da mazaunanta suke juyawa a hankali. Ikram ba ta bata da cikakken halittar jiki, bata cikin jinsin sirarra ko irin lutayen nan.
Sannan ba za a kirata ramammiya ba, daidaigwargwado tana da jiki me kyau, musamman k'ugun ta, kirjin ne dai sai a hankali, domin a shafe yake, yan nonuwan kamar na me kirgan dangi. Amma kuma kamar wanda aka dasa su daga kasa, a cike suke tam daga sama ne zaka dauka babu su. Sannan rashin kulawa da abinci me gina jiki ya taimaka matuka gurin boye cikar halittar jikinta, k'ugunta ne zuwa mazaunin ta, kamar wacce aka hura abu ko aka mata dashen shi.
Domin idan ka nutsu zaka ga har wani motsawa suke, tunda yake bai tab'a kare mata kallo ba sai yau, bai tab'a ganin mace me diri irin ta ba, wannan halittar shi ya kad'a mishi hankali lokaci guda, had'iye yawu yayi cikin b'acin rai, ya juya tare da barin gurin.
Ya ga shegen da ya isa ya shiga mishi iyakar kasar shi domin daukarta. Haka yayi ta aiyanawa a ranshi, dan haka a washi gari ya maida Fudail fada, sannan ita kuma ya zuba ido akanta, yana kallon iya gudun ruwanta.
Gefe guda ya dawo da mugun halin shi, idan tayi mishi abu zai kai mata mangari ko ya tad'e ta, ta fadi, wani irin zazzafar k'iyayya ce ta Kuma haihuwar kanta a tsakanin su, wanda ta kai Itama Ikram din ta fara rama abinda yake mata, ai kuwa yace bai iya ji ba, azaba kuwa babu iya ka. Kuma babu halin ta fita ko ina, tana cikin gidan.
---- watan shi takwas da bashi mulki aka fara turo y'ay'an gwamnonin yankunan hudu nan, akan zasu yi zama dashi na tsawon wata hudu idan suka fahimci juna, sannan za ayi bikin su bayan wasu wata hudu masu zuwa, wato wata takwas zasu yi suyi suna nazartan tsarin mulkin ƙasar da yanayin cikin gidan.
Dan haka aka shiga kwaskwarimar masarautan baki daya, tare da dawo dashi asalin tsohon shsshin Mahaifin shi.
----
Yau naji a raina ina son bisa sarewan Uwaisul Qarni, dan haka na tafi d'akina bayan na gama abinda zan yi na fara busawa, a hankali duk da bawai ina fahimtar abinda nake busawa ba, amma kuma ina jin wani irin kewa da son kasancewa da yar uwana, ina busawa hawaye na zuba daga idanuna. A hankali dakin ya fara wani irin sanyi da kad'a iska me dad'i,hade da sanyin kamar nadamina.
Lumshe idanuna nayi ina kara bisa sarewar, ina kuma yi tare da hango Airan tana dariya tare da gudu da wani dan karamin rago suna gudu a tare.
"Barka dai magajiyar sarauta" da sauri na bude idanuna, tare da zuba mishi. Murmushi yayi sannan ya kuma cigaba da tasbihin da yaƙe yi,. Kallon gurin nayi tabbas ina dajin nan ne.
"Baba yaushe nazo nan?" Na tambaye shi bayan na koma kusa dashi, dariya yayi min sannan yace min.
"Ai kin bisa sarewa kuma Insha Allah zata kawo ki har nan da yardan Ubangiji. Nasan kina cikin kaɗaici bayan kaɗaici, gashi kin fara aikin da ya dace amma kuma kina zubda ladar ki"
Kallon shi nayi tare da sake baki sannan nace mishi.
"Wani irin aiki na fara kuma na ke zubda la.."
"Kin fara ai! Kuma kin gama gina kome a cikin aikin ki, saura ki jira lokacin da Cigaban shi zai zo miki, don Allah ki taimaka ki saka shi ya san waye shi ? Ki taimaka ya san halin da al'ummar kasar shi suke ciki, baki san wani abu ba.
Aamaan na biyu sunan yana mulki ne amma ba shi yake mulkin ba wasu ne suke mulkin, Jikata ki taimaka ya san inda yake ya kuma san waye yakewa Hidima. Don Allah ki taimaka. Koda zaki na fuskarta wahala a tare dashi ki tabbatar yasan abinda yake yi, akwai mutumin da ya kama kafin ya kwanta ka jinya, amma an kubutar dashi bayan an fitar dashi sun nemi kashe shi dan kar ya tona musu asiri sai dai Allah bai basu Sa'a ba, guguwar ƙaddara tana zuwa gare ki, don Allah ki tsaya ki bashi kariya."
"Baba ka sani a duhu wallahi, duk na rude na kasa fahimtar kome."
"Da Sannun zaki fahimci abinda nake nufi, yanzun dai ki taimaka ya fahimci alkibla." Kura mishi ido nayi tare da cewa.
"Me yasa sai Ni?"
"A duk lokacin da tafiyar dare ta kama fatake, abu uku yake zuwa mishi! Na farko namun daji! Na biyu yan fashi! Uku ina zai saka kafar shi babu hasken farin wata babu fitilar da zata taimaka mishi. Toh dole ya hakura da tafiyar ko ya tsaya ya kwana a gurin ko kuma yayi taradda aradu da fadin kai! Bilqisul Ikram dole ki zame mishi fitilar makafi!"
Wallahi duk sai na rud'e tare da zuba mishi ido, ga baki daya na rasa abinda yake nufi, kamar zanyi kuka nace mishi.
"Baba don Allah me kake nufi? Don Allah ka min bayani"
Dariya yayi sannan yace min.
"Ko na miki filla filla ba zaki tab'a yarda ba, sabida rashin adalcin da zuciyarki take miki."
---
"Sultanah, har yanzun babu wani abu daga Ikram!" Inji Shairah.
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Babu wani abu, aikin da na saka ta take min, kuma nasan zata dawo min da Alkhairi nima kuma zan mata kyautar alkhairi."
"Mama, don Allah a kashe ta, bana kaunar ta. Bana son ganin ta, wallahi gani nake kamar ba zata." Wani irin kallo Sultanah Fazilatul nisa tayiwa Jasrah, cikin b'acin rai nuna mata hanyar dakin ta, babu musu ta nufi hanyar d'akinta.
Babu wanda ya kuma magana, sai ma shiga hankalin su da suka yi, domin har yanzun babu wani sako daga Ikram sai suke ganin kamar zata ci amanar su.
---
Jikina wani irin rawa ya dauka tare da jin sanyin ya lullube ni,
"Don Allah karka bani abinda ba zan iya dauka ba, wallahi bani da yancin."
"Zaki iya tafiya! Domin na gama abinda zan iya miki, taimako gkg yi tare da jahadi."
Girgiza mishi kai nayi, zan yi magana na tsinci kai a dakina. Wani irin gumi ne yake karyo min, a hankali na koma na kwanta da baya, ina sauke ajiyar zuciya. Wannan wacce irin ƙaddara ce ta shigo min babu sani na.
Bayan yan kwanaki, Mehran zunzurutun rashin yarda ya mai dani Jelar shi, eh toh dai yanzun haka dai tun jiya aka kawo min kaya daga kasar roma, kallon kayan nake wata irin doguwar riga ce, sai kallon kayan nake ina kuma kallon shi, a hankali.
Buga min kofar dakina aka yi na mike tare da buɗewa, Rakshan na