Showing 120001 words to 123000 words out of 274096 words
Chapter 41 - DAULA BIYU Complet Document .txt
ba zai iya amai ya lashe ba. Ba zai iya juyawa maganar shi baya ba, ba zai iya kallon tsabar idanun jama'a yace musu yarinyar da tayi aure da wani yake so, waye zai fahimci ainihin sirrin shi? Ita daya ce mahaukaciya kawai, ta lalata mishi kome sannan tayi nesa dashi!
"Amma wannan hukuncin da ka yanke ba." Juyawa yayi ya kalle ta, sannan yayi murmushi yana kallon yadda iska yake kad'a ganye, zata kuma magana ya juya tare da kallon ta, yana me nad'e hannun shi a kirjin shi.
Dole tayi shiru, amma kuma yanayin yadda fuskarta ta nuna kamar bata ji dadin abinda yayi ba.
"Sau dayawa muna iya sauya ra'ayin mu, sai bamu cika son tistawa ba." Ta faɗa a sanyayye,
Bai ce mata uffan ba, har ta gama magana, zata fita sai kuma ta tsaya tare da cewa.
"Bai zama dole ka dauki abinda nace ba, matukar aka san girma da darajar da ka bata a zuciyar ka, tabbas iya shi ya ishe makiyan ka, buga ka da kasa. Ba tare da sunyi amfani da wani makami ba. Da iya SOYAYYA aka salwanta da rayuwar sarakunan baya, dan haka karka zurfaffa abinda ba zai fidda kai cikin sauki ba."
Tana kai aya tayi fucewarta domin lallai ranta ya kai kololuwar ɓaci, kuma bata son ta nuna mishi haka har ya fahimta,. Sam bata kaunar dalilin da zai sanya ya fahimci bata kaunar yarinyar ko soyayyar da takewa yarinyar ya fita a ranta, sai dai kamar yadda ta sha fada a baya. Sarakunan daular kamar wad'anda aka musu tsafi da macen da suke so.
Idanun su rufewa yake basa ji basa gani sai sun tsinci, kansu a gaɓɓar mutuwa suke iya gane illar so. Ita kan tana tsoron kar wani abu ya faru dashi domin bata iya jin zata yafewa kanta.
Dan haka ko ta halin k'ak'a, sai ta dakatar dashi wannan makauniyar soyayyar da yakewa Ikram, tana tsoron kar soyayyar ya zama illa yadda ba zai iya dakatar da ita ba.
Tana shakkar kar makiya da kishi ya kai wasu amfani da Ikram domin cimma manufar su akanta da shi kan sa. Babban dalilin da take iya hangowa domin dakatar da wannan makauniyar soyayyar, ba kome bane matan da suke kokarin shiga rayuwata su da iyayen su ba kananun shu'umar ba ne.
Domin iya haka aka barsu da Ikram sun damata sun shanye kuma zasu iya mata dalilin da sai ta tsani kanta da shi kan shi Mehran din. Kai ina bata jin zata barshi haka ya tafi kamar yadda suka zalunci ta dole, su dauki alhakin ramuwar gayya, toh kuwa idan ta rama ba zasu yi hakuri ba zasu suce sai sun ga bayan shi.
Ji take kamar ta kumar ihu, domin bata da wata hikima ya tsaya mata cak!
"Narjis! Yanzun naga amfanin tsoron ki! Domin Mehran ya makance akan mace don Allah kiyi wani abu!
Bana son na rasa shi kamar yadda sarakunan daular suka yi ta rasa rayukansu, idan ta kama ma kar Ikram ta dawo daular nan don Allah kiyi wani abu ina son shi da Ikram amma kuma bana son ya mutu akan so, bana son na rasa shi a matsayina na Mahaifiyarshi zuciyata ba zata dauka ba,.kiyi wani abu nace."
Kasa magana Narjis tayi tana kallon kofar dakin, jikinta yana kerma, d'ago kai tai zata mata magana taga tayi mutuwar tsaye, juyawa tayi Mehran ta gani yana kallon su.
"Don Allah karka min mummunan fahimta, ka fahimci ni bawai ina nufin zan rabaka da Ikram bane."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Eh Toh ban ji kome ba! Ban kuma fahimci me kuke nufi ba, naji kina cewa a matsayin ki na Uwa ba zaki iya me ba?" Ya koma yana tambayar su, ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa.
"Alhamdulillahi! Toh yi maza jeka bada kai nake ba tunda baka ji ba, a bar maganar haka"
Bai ce mata kome ba sai murmushin da yayi, sannan ya saka kai zai fita yace mata.
"Ban tab'a soyayya ba, kuma bana jin yin shi. Amma akan wacce nake jingina rayuwata bani da dadin mu'amala!" Ya fadi haka tare da barin d'akin.
"Sultanah! Kina ganin kamar kuskuren ne idan kika Barsu a tare? Ko kina ganin zai iya dauke kai daga abinda zasu mata, ba zai iya hakuri ba akan abinda yake so ba, Don Allah Sultanah matukar Ikram zata zo karki sauya mata.
.. yau kina tare da d'anki ne saboda ita, yau idan kika juya mata baya babu wanda ya isa ya tabbatar mata da nutsuwar da zata samu. Addu'arki itacce zata sauya kaddarar su, don Allah karki bari abinda ya faru da sarakunan daular ya tab'a zuciyar ki."
Shiru tayi tana nazarin abinda ya faɗa da kuma wanda Narjis ta faɗa, kusan abu daya ne amma kuma ita Uwace. Taya zata dauki kasadar rabuwa da abinda ta shigo yaki domin shi. Zata iya mallakawa Ikram amma sauran matan fa? Idan za ayi duba na gaskiya zata iya cewa wa Ikram ta haifawa Mehran, ba sauran matan ba, dan haka zata yi kokarin ganin ta boye tsoronta ta maida Ikram wacce zata bi ra'ayin shi.
Sai ta nuna mata itace ta dace dashi yadda ba zata kullace shi a ranta ba, zata so soyayyar su ya zama wanda babu wani abu a cikin shi sai tausayi da kaunar Juna.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tacewa Narjis.
"Bani ruwa na sha"
Daukar ruwan ta yi tare da mika mata, tasha sosai kafin ta ajiye kofin tace.
"Bari na huta,"
"Toh Sultanah a tashi lafiya!"
Daga haka ta fita. Kasa kwanciyar ma tayi tana tunanin halin da Mehran yake ciki, yaki maida hankali akan abu daya, sam ta kasa gane shi wani irin mutum ne da baya nuna yanayi. Shi. Sai yaki ya fahimtar da kowa waye shi.
Sannan a haka ake bukatar bashi mata toh me zai musu? Ko baida lafiya ne? Anya kuwa? Kai haba toh me yasa baya bukatar mace? Da sabida mace daya ka zab'i zama na shekara goma! Kayiwa kanka iya ka da abinda zaka sami nutsuwa dashi. Kasa zama tayi ta kuma fito. Can back yard din ta koma yana tsaye tare da rike alkama yana kiran tsintsaye, yana watsa musu tsabar alkamar.
"Mehran!"
"Na'am! Anne!" Ya fada a hankali, da sauri ta kalle shi. Cike da mamaki bakinta yana rawa, tace.
"Ka kirani da Mahaifiya ce fa?"
Murmushi yayi sannan ya cigaba da abinda ake sam bai da wani karsasha ya gaya mata haka ne domin yadda take damuwa da shi, dan haka shima ya damu da ita.
Uwa ce kawai take iya damuwa da cutar D'anta, ba tare da taji labarin zai mutu ko zai rayu, shi tashi uwar Mantawa tayi dashi dan haka ya juya tare da zuba mata ido, kokarin maida kwallar da suke son zuba tayi tare da cewa.
"Shin baka da lafiya ne irin na sauran mazan?" Cikin wani azzababben kunya ya juya a hankali yana me ji kamar kasa ta tsage ya shige cikin shi. Yau yaji abun kunyar da ta dame shi. Dan haka yaki juya mata domin maganar ta sashi jin mugun kunya sama da kowani kunya, kai ko lokacin da Sultanah Hoyam ta tambaye shi bai tab'a jin kunya haka ba.
Kin juyawa yayi, tare da kin magana, gaban shi ta koma shi kuwa ya juyar da kan shi ta d'aya bangaren.
"Baka da lafiya ne kamar sauran mazan nake tambayarka? Kaki min magana"
Sunkuyar da kai tayi tare da kin d'agowa, ita kanta bata ga abin kunya ba, dan tana tambayar shine a matsayin ta na Uwarshi ba wai wani abu ba, amma sai yaki koda kallonta..dan haka tafito da sauri tana kiran Fudail da Shairah da Narjis. Duk suka hadu.
Kamar zata yi kuka take gaya musu abinda ta tambaye shi. Sake baki suka yi suna kallonta, kafin duk suka watsa kamar wanda ta watsa musu wani abun tsoro.
"Toh kuma ina zaku? Muna magana zaku gudu ai sai ku tsaya ayi maganar gaskiya!" Su kuma dalilin ganin Sultan yana tsaye ne yasa su guduwa, suna dariya. Wato idan ya fahimci Anne so take ta gayawa duniya dai...
"Kai Aamaan Mehran! Shin kana da ra'ayin maza ne?" Murmushi ne ya kwace mishi sannan ya tuna da tsohon zargin shi da ake cewa wai yana bin maza wato (dan luwadi) dan yaji yadda zata rikice, sai ya wani kalle ta, sannan ya sunkuyar da kanshi irin eh din nan.
Ihu ta saka tare da kiran Fudail, rike bakinta tayi tana kallon Mehran da Fudail, sannan tace mishi.
"Yarona Fudail! Gaya min shin Shugabanka yafi son mu'amala da maza ne sama da mata!". Kan Uba,. Da wani mugun sauri ya kalli Mehran, kashe mishi ido yayi tare da mishi alamar ya amince, da tambayar ta.
Cikin wani irin shauki da takaici kamar zai fasa ihu, ya kalle ta sannan ya dauke kan shi ya kuma duban Mehran, ya ɗan ciji bakin shi sannan yace mata.
"Labarin yana da tsayi, idan nace zan gaya miki zaki iya faduwa baki shirya ba, amma Sultan kan..... Sai godiya."
Ya faɗa ina cizon hannun shi. Dab'as ta zauna tare da cusa hannun ta cikin gashin kanta, taji kamar ta kurma Ihu, dan haka ta nuna musu hanya su bar mata falon bata son ganin su. Da wannan yanayin ya shiga dakin shi.
Ya zauna yana murmushi, haka kawai yake jin shi yau yayi nishadi, murmushi ya kuma a karo na biyu, yana tausayin ta. Amma bayana nufin zai bar musu rayuwar shi su gara mishi bane.
Dan haka ya kwanta a hankali barci me dad'i ya dauke shi.
A bangarori daban daban,.ana kan shirin za a turowa Sultan Mehran mata, dan haka suka maida hankali gurin koyawa Yaran su mata yadda zasu kwace Mehran, karsu bawa wasu damar rab'a ban shi. Idan kaga yadda suke gudanar da abin sai ya baka tsoro, domin shirin da suke zaka zata aure ne kuma duk kawai zab'e ne.
~~~
Askandariya.
Shiru fadar Sultanah Amrah yayi sakamakon yadda Waziriyar ta Nairah take bayanin abinda ta aikata, tana kuka. Ita kan Sultan Amrah bata iya magana ba, sai ma sunkuyar da kanta da tayi tana kuka. Tana tambayar kanta meye tayiwa Nairah da zafi haka?
Me yasa Nairah bata gaya mata mulki yake so ba? Da ace lokacin ta ce ita mulki take so wallahi da ta bar mata, akan mulkin banza ta rabata da Yarinyar da take kauna babu ita babu yar uwarta, duk sun rasu.
Hawaye ne ya zubo mata, sannan tace.
"Ba zan iya kashe ki ba! Nasan yadda kowacce uwa take ji idan ta rasa D'anta, a halin yanzun kuwa nasan kina cikin rashin Yarki dan haka babu hukunci akanki, kije Allah zai bi min hakkina indai na zalince ki babu abinda zai same ki, idan kuma ni kika zalunta, Idan nace ban yafe ba na rena iyakar shi ce dan haka Allah yasaka da Alkhairi zaman da muka yi dake!" Ta karshe maganar cikin wani irin kuka me hade da murmushi, domin iya haka kawai zaka Fahimci tana cikin damuwa...
#Mai_Dambu
200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641.. Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
19
"Me yasa baki Fahimci sabida ke take raye ba? Me yasa baki gane girma da kaunar da yarki take miki ba, sabida kina tare da shaidanun mutane irin Nairah binti Namdar, dan haka kamar yadda taci amanar mu, har ta kai da shirya juya mulki dole mu zartas da hukuncin mu akanta."
"Kyale ta Khadim! Kyale ta tayi rayuwa, kyaleta duniya zasu gaya mata abinda na gaza gaya mata" sannan ta fashe da kuka, share kwalla tayi sannan tace musu.
"Yar Joindah ta turo min sako, tace na tafi Merocco, naje akwai dangin mahaifinta a can me kuka gani?"
Share kwalla suka yi sannan suka ce mata.
"Duk yadda kika ce! Mu masu miki biyayya ne babu abinda zaki ce muce miki a'a!" Da wannan ta mike a hankali ta bar fadar, tun da tashiga d'akinta dariyar yaran ta, yadda suke gudanar da sha'anin su na farin ciki a, shi yake yawo a kunnenta.
Yadda suke wasa da matashi a dakin shi yafi komai mata dad'i, a hankali ta taka har gaban gadon da yau ya koma mata kamar yau aka kawo dakin, shashekar kuka ta ja, tana tuno yadda yadda Joindah ta maida kanta kamar namiji, hatta maganarta sai da ya sauya.
Idan ta dube hannunta ya koma mara taushi da laushi irin na mata, kafarta kullum cikin takalmin karfe yaƙe ko sau daya bata tab'a d'ago kai ta dube irin nasarar da Yarinyar ta samu ba.
Tasha ganin ta tana son yanke gashin kanta, amma ta hana ta, sai tace mata.
"Ummyn ni gashin addabar rayuwata yaƙe, shi yasa zan yanke amma bawai dan bai hana Ni rayuwa ne ba."
Zuɓewa tayi akan gwiwar ta, tana me rike kanta. Tana kallon yadda kome ya tafi yabarta, babu yaran da take mulkin domin su, babu Mijinta da ya bada rayuwar shi domin ita, kawarta Aminiyarta itace taci amanarta, duk Yardan da tayi da ita na tsawon shekaru, yau ta b'are, a hankali ta zame tare da kwanciya a kasa, hawaye na zuba mata.
Tana rufe idanunta, zata ji ihu da shewan yaranta, suna dariya da murna musamman idan Joindah ta tafi yaki aka yi nasara, haka zasu yi ta guje guje, har fada. Idan ka ga Joindah sai ka rantse namiji ne domin yadda take yanke sumarta.ya dawo iya dokin wuyarta.
Tana dariya, takaici take ji idan ta ga gashin a yanke. Har ta kare wata rana ta mata magana akan yanke gashin.
"Yanzun don Allah meye amfanin yanke gashin kanki? Me yasa kullum kike bukatar ganin raina ya b'aci, kefa mace ce?"
"Ummyn ni gashin ne yake damuwa, sannan ba a cikin gidan sarauta nake rayuwata ba, kai na wani lokaci sai nayi.wata daya ban saka mishi ruwa ba, muna can muna yaki da jama'a, toh Kinga kwarkwata da wasu kuraje damun kai na suke, amma Insha Allah ba zan kuma ba."
Ta faɗa tare da juyawa, sannan ta riko kunnenta.
"Karki damu! Duk lokacin da zaki yanke toh kina azumi uku!" Gyada kai tayi, hawaye na ya shiga sauka cur cuur. Dan ba zata iya daukar wasu tashin hankalin bayan wannan ba, ta rasa yaranta biyu.
Haka ta mike tare da shiga ban daki wanka tayi da alola sannan ya fito ta sallaci asuba, tana idarwa ta jima tana azkar da yiwa Yaranta da mijinta sai iyayenta addu'o'in, kafin ta koma ta kwanta sabida zazzafar zazzabi ya rufe ta, anan ta kwanta. Lokaci guda aka taru akanta bayan an fitar da sanarwar Sultanah Amrah babu lafiya.
Dayawa talakawan sunyi mata Fatan Allah ya bata lafiya, bayan sun ji zunzurutun cin amanar da waziriyarta ta mata, dan haka ba tare da sanin kome ba, suka shirya kashe Nairah binti Namdar.
~~~
SAHARA.
Kimanin wata biyu kenan, da shigar mu wannan gari me shegen bala'in tashin hankali, babban damuwata Nimrah, so nake ta koma Askandariya. Shi yasa nake kokarin na fidda ta cikin wannan yanayin.
Ita kuma bata da mutunci, rena min hankali take.
"Ke Wada! Zoki goge min bakina da nasha madara, matsiyata kun rabani da Mahaifiya ta, sai ta saka an sare min kanku"
Buge mata baki Izmah tayi tare da cewa.
"Allah wadaran iyayen da basu bawa yaran su tarbiyya sha-sha-sha kawai!"
"Ke Ni kike zagi?"
"An zage ki!"
Tasowa tayi zata nufi Izmah na tsaya a gaban su,
"Bana son rashin hankali! Da rashin sanin hakkin d'an adam, kiyi hakuri shikenan!"
"Zaki maidani garin mu?"
"Ba zan mai daki ba, sabida ina da burin ganinki kusa dani"
"Ke wacce irin rashin imani ne dake? Me yasa kika rabani da alkaeyata? Me yasa kika rabani da Mahaifiya ta, kin kawo ni cikin datti da tirbaya ina rayuwa kamar wata dabba, mutanen da basu kai tab'a ni ba, sune suke gogayyar tab'a jikina, meye nayi miki da zafi ne?"
"Nimrah! Ki nutsu ba ina nufin na cutar dake bane, kawai nayi haka ne domin gaskiya tayi halinta, idan kin gadama zaki iya tafiya yanzun haka zaki koma in..."
"Ikram!" Izmah ta kira suna na, da garaje,
"Izmah! Kyaleta ta tafi ko da ta koma kome ya kure, dan haka na gama shirya mata tafiyar tun wata daya da ya wuce."
"Taya?" Inji Izmah,
Murmushi nayi mata sannan ba nunawa Nimrah hanyar wucewa, rikon hannuna Izmah tayi, hawaye na zuba daga idanuna, rike hannunta nayi, goge kwallar fuskana nayi tare da cewa.
"Askandariya suna jiranki Nimrah! Kiyi hakuri da sauyin ƙaddarar ku."
Murmushi nayi domin nasan matukar ta shiga Askandariya toh tabbas sunanta babu. Domin har yanzun akwai masu fushi da fushin Sultanah, a hankali ba juya zuwa cikin gari.
"Yanzun meye ya rage mana a garin nan?"
"Hmm! Lallai kuwa wanda nazo nima har yanzun ina kan niman hanyar haduwa dashi." Haka muka shiga cikin garin, na