Showing 72001 words to 75000 words out of 274096 words
Chapter 25 - DAULA BIYU Complet Document .txt
Cire kayana nayi, sannan nayi wanka tare da wanke kayan tass, ina gamawa na nufi dakin na shafa mai sannan na same su, suna cin abincin ranar zama nayi na fara ƙoƙarin ci. Ruwan zafi aka mika min, na sha sannan na fara cin abincin.
---- wato Mehran tsakanin shi da Allah ya hana Ikram da Fudail haduwa, wai gudun kar su keb'e zai ce taje gidan shi, tayi mishi aiki kuma babu aikin, karshe zuwa yake ya sakata a gaba tana mishi karatun Alkur'ani. Har yayi barci tana ganin haka zata mike ta rufe shi da abu sannan ta juya zata fita zai ce mata.
"Banyi barci ba tukuna!"
Haka zata cigaba da zama har itama barcin ya dauke ta,yana ganin ta fara barcin zai zuba mata ido. Har sai yaga ta fara kokarin faruwa zai rufe nashi.
Idan kuwa sallah take, yana kallon duk yadda take, har ta idar, sai ka lura zaka Fahimci haka, idan baka lura ba, sai ka zata barci yaƙe.
A hankali suka cika wata daya cif, wanda ya kai watanin shi goma da zama sarki,. Zaman wata daya nan. Wani irin amayar da SO Mehran yayi a aikace amma a zahiran ce ya kasa furta kalmomin yabo ko burgewa, amma duk me hankali da tunani ya ga yadda yake ririta alamarin ta, sai ya fahimci yadda yake kaunarta.
Ana gobe zasu bar garin, mutanen garin suka shirya musu biki da dare, anata shagali da raye raye, haka yan mata suka jata bata so, amma haka ta shiga. Kura mata ido yayi tana rawa. Tare da dariya.
A karon farko da yaji tana tafiya a tsakanin zuciyar shi, kura mata ido yayi yana fadin a ranshi.
*Sirrintacciya na! Kinga yadda dariya yake kara Kawata fuskarki! Kin san girma da darajar farin cikin ki kuwa? Sirrintacciya na! Kin fahimci yadda kike haska dukkan Ni manta gurin? Idan da kin san da haka da murmushin ki sai tafi hasken farin wata kawa! Dariyar ki sai tafi iska kad'awa! Farin cikin ki sai tafi sanyin damina! Sirrintacciya na! Tayu wasu sun gaya miki sirrin kyanki! Amma Ni da nake tare dake zan iya gaya miki shi yasa.*
"Sultan ko zaka shiga cikin rawan ne?" Girgiza kai yayi tare da nuna alamun a'a, hango Fudail yana ƙoƙarin shiga filin. Ya sashi b'ata rai, ya mike babu shiri, haka ya shiga cikin rawan. Kamar wani mashiya ko sikago, yana tsaye yana kallon yadda take dariya da juyi, hannun shi ya kai zai riko ta, ta zille mishi. Sake kaiwa yayi ta kuma zillewa.
Saka mata kafa yayi ta tafi luuuuuu zata zube ya tare ta, suka d'an rankwafa, yana kallon cikin idanun ta, itama tana kallon na shi.
*Kai kan ban san wani irin mayye bane?*
Murmushi me sauti ya sake mata, tunda take bata tab'a ganin murmushin da tayi mata kyau, har kumatun shi yana lubewa ba sai yau, hannun ta takai gurin, tare da kallon shi, tsintar kanta tayi da sake mishi murmushin tare da lumshe idanun shi.
*Sirrintacciya na!!!*
*Heydar!!!*
Ta faɗa a ranta, can kuwa kasan ranta wani tunani ne yazo mata, lokaci guda ta kwace kanta zata fadi ya d'agata cak, ya dire ta da kafarta, dai dai lokacin da aka gama kid'ar haka sai ya bawa mutanen gurin damar tafa musu.
Wannan yanayin ya haifar mishi da farin cikin da ba zai tab'a Mantawa ba, a hankali na zare hannun daga gare shi na fita daga filin da gudu, bai damu ba, shi dai ya fito abin shi yana me zama a gurin shi. Baya son ya cika zakewa akan al'amarin Yarinyar nan, duk da zuciyar shi ta zab'e mata suna da sirrintacciyar shi.
Ya jima yana nazarin abubuwan da ya rasa na farin ciki, shigowar ta rayuwar shi ta bashi kome, d'agowan da zai yi ya duba yaga babu Fudail.
Da sauri ya mike tare da niman shi, zuciyar shi tana raya mishi suna can suka cin amanar shi, har hango su yake a idanun shi, yadda Fudail yake sumbatar ta, haka ya ficce a cikin mutanen ya shiga niman su. Can bayan gidan shi ya juyo muryan su, kamar fada suke ma ko meye yana zuwa kawai ya same shi kusa da juna, kallon su yayi bai san lokacin da zuciya ta kwashe su ba, ya tako tare da kifawa Fudail duka.
Sosai fa, sai da ya fadi. Cikin fushi Fudail ya mike tare da kallon shi, sunkuyar da kai yayi cikin nutsuwa yace.
"Sultan yarinyar nan bata sonka kabarta tayi rayuwar yancin."
Cakume wuyar shi yayi cikin fushi yana faɗin.
"Ka dube ni, ka dube ta meye zanyi da kaskantacciyar baiwa ta? Meye zanyi da mace mara daraja a gare ni? Mace me daraja ma ban jin tayi min ma ba, sai baiwar da kowani kare da doki yake ƙiyasta surar ta.
Ko matan duniya zasu kare ba zan tab'a kaunar wannan abun ba, domin bana kaunar mace irinta kazama mara tsafta." Sannan ya sake wuyar shi tare da kallona, idanuna suna kan shi. Ban tab'a ganin cin mutuncin irin wanda Mehran yayi min ba, had'iye yawun nayi sannan na bar gurin, ina barin gurin, ya kuma shure kafar Fudail yana fadin.
"Idan na kuma ganin ka da ita zai na kashe ka! Ita din mallakata ce. Babu wanda ya isa ratsa tsakanin mu."
Ya wuce abin shi, wannan abinda da yayi ya saka Fudail cikin takaici da bakin cikin mara iyaka, bayan tafiyar shi Baba da yake labe yazo ya d'aga Fudail yana faɗin.
"Na gaya maka ka fita harkan su, suna son junan su!"
"Baka ji abinda yace ba?"
"Kishi ne, idan ya nutsu ka saka ido ka ga yadda zai koma."
Tunda na bar gurin, kuka ne yake son zuwa min amma zunzurutun taurin kai naki barin shi ya saukar min, ina shiga dakin da aka bani na kwanta, tare da kara hasken fitilar dake gefen gadon akwai wani littafin dauka nayi tare da dubawa anyi rubutun da zallar bakin larabci.
*Zafin hawayen Uwa cike take da tartsatsin fansa! Kamar yadda Sultanah Fazilatul nisa ta cutar dake haka nima zan daukar miki fansa akan duk wani ahalin sultan Abdus Samad* jikina ne ya dauki rawa, a hankali na fara ƙoƙarin gano dalilin da Yasa Matar gidan bata cika sake min ba.
Shafi zuwa shafi nake karantawa, tare da yadda aka daurata zata je daukar fansa, daukar Littafin nayi na b'oye shi, sannan na kwanta, ina mamakin yadda aka yi babu wanda ya fahimci gidan da muke, wato mahaifiyarta tayi alaka da Sultan Abdus Samad, shine itama kuma suka zo da zummar alaka da Mehran domin daukar fansa mahaifiyarta.
"Ina ruwanki? Shi ta shafa, can da yawar su." Na fada da sauri, duk yadda naso cusa rashin mutuncin da wancan me kama da karas din yayi min na kasa,kuma na kasa barci, har asuba ina zaune kuma abun haushin dan b'atar basira ko sallah nafilla ban yi ba, haka na gama cika da batsewa na, na tashi nayi sallah asuba, ina zaune sai hararar gefe da gefe nake irin sune suka min laifi.
Koda gari yayi haske na shirya tsaf, na fito wai Mehran bai fito ba, Fudail yaje gidan wai kar a bude mishi kofa, dan haka muka zauna da Fudail muka yi ta hira, har da kyalkyalewa da dariya, sosai muka bude karamar dandalin nishadi, ashe mutumin yana kallon mu, wato shine ake mishi fatan mutuwa shi yasa babu wanda ya damu da lafiyar shi.
Ko a jikina, har sai da Baba yace min.
"Y'ata ki duba mana Sultan mana!" Ina ganin girman mutumin dan haka na tashi tare da nufar gidan, ina bude kofar yana zaune abun shi ko a jikin shi irin baku damu da rayiwa ta ba,
A hankali na tura tare da sallama, ko d'ago kai bai yi ba. Haka ya cigaba da b'ata rai. Ni ya gayawa magana, amma yau shi yake fushin da banyi ba, d'an dukawa nayi sannan nace mishi.
"Mu shirya ka fito ka karya sai mu."
"Na soke tafiyar!"
"Toh Allah ya kyauta." Na fada tare da juyawa zan fita, cike da mamaki nake kallon shi, kafin ya sunkuyar kan shi.
*Sirrintacciya Ni kika wulakanta! Sirrintacciya!!!*
A hankali na juya tare da kallon shi, sai kuma na fahimci yana cikin kaɗaici yana bukatar wani a gefen shi koda ba zai mishi magana ba, yana bukatar nutsuwa ko da kulawa ce, kasa fita nayi na tsaya a bakin kofar, da wutsiyar ido yake satar kallonta.
*Sirrintacciya!!! Kizo na sami nutsuwa!*
_Wato kai babu me gane alkiblan Heydar!_
Wani irin bugun zuciya naji dan dole naso juyawa amma na kasa, jan numfashi nayi da dan karfi sakamakon jin shi a bayana, ya sakala hannun shi a k'uguna ya bude kofar. A hankali nake sauke numfashin kamar wacce tayi mugun gudu.
_Heydar yaushe!_
*Sirrintacciya na!*
Juyar dani yayi tare da kallon yadda nake kifi kifi da idanuna, jikina yana kara sakewa sabida wani irin kasala da nake ji, d'ago kai na nayi, tare da bude baki zanyi magana, shima maganar yake son yi, amma baki na shi yana rawa. So yake yace wani abu. Amma ya kasa fahimtar kome akan haka, hannun shi ya saka a gefen kirjin shi.
Kallon juna muke a sanyayye, kamar me rad'a yace min.
"Baki ji"
Tsintar kai na nayi da gyada mishi kai babu musu.
Daga haka muka fito a tare, yana kallon yadda mutanen garin suka fito domin mana rakiya, yar karamar jawabi yayi musu, sannan yayi musu sallama.
Ya shiga keken dokin shi, Ni kuma aka baki doki, ina kallon Fudail muka shiga hira, muka dariya. Sosai muke hira, dukda hiran sama sama ne, bai hana Mehran yin magana aka dakatar da tafiyar ba.
"Shigo nan!"
Yabi Fudail da mugun kallo, tun da na shiga ya murɗe min hannu. Nake kokarin kwace kai na, sakani barcin dole yayi.
~~~
Bayan barin mu SAMAIND. Sunso kwarai su juya kan Zunnoon, amma yaki basu fuska dan Allah yayi shi mutum ne mai addini, shi yasa suka kasa tabuka kome. Dan haka kamar yadda suka shirya sai ya dawo haka kome yake tafiya.
Yau tun safe aka turo zai dawo dan haka kowa na garin murna yake, tare da gyara mishi fadar shi da turakar shi, idan ka gani zaka Fahimci akwai baki.
Ana kiran sallah la'asar muka shiga garin, kallon shi nayi nace mishi.
"Sultan kasan dayawa basu sanka ba,me zai hana ka hakura da keken nan, muyi badda kama kaji wani hali mutanen ka suke ciki."
Kallona yayi dan haka aka tsayar da Dawakai muka sake shiga duk da bawai shiga bane, cire kayan sarautan shi tayi ya dauko wata tsohuwar rigar Fudail ya saka, dan ya mika mishi, Ni kuma na gyara shiga jikina, muka sauka daga keken, suka yi gaba. Ni dashi da Fudail muka shiga garin da kafa, muna tafiyar kurame, kai Mehran mugu ne, hana Ni magana yayi ina ji ina gani, wasu manoma muka fara samu, daga kan su muka fara cin karo, tare da tambayar su halin da suke ciki.
Nan suka yi ta fade fade, wasu su fadi Alkhairi wasu su fadi sharri har da abinda aka musu,
Musamman yadda ake matsa musu da haraji tare da kwace musu amfanin gona su, kamar yayi kuka yadda suke bayanin, dan haka lokaci zuwa lokaci yana kallona, tare da dauke kai, har muka iso kasuwa, anan ne naga abinda ya kusan sani suma.
Domin idanun ya sauka akan....
Wannan littafin na kuɗi ne.....
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Page 37
A raunane ta kalle su, kafin ta juya ta bar falon, can lambu ta koma ta zauna, kallon juna Sultan Abrad yayi da Nawwas, sannan ya sauke ajiyar zuciya yace mishi.
"Wai da gaske kana son Ikram?"
Da mamaki yake kallon shi, abinda zuciyar shi take raya mishi ba kome bane kace Eh kome ta famjama famjam, amma ya kore tunanin haka ta hanyar amfani da hikima yace mishi.
"Haba ina babban kaya sai amale ai Ikram sai irinku saraki ba irin mu yardaddun ku ba, ai tafi karfina." Nawwas ya faɗa cikin girmamawa. Gyada kai yayi tare da kallon shi, sannan ya fashe da dariya yace mishi.
"Haba ai nasan kai ma wasa kake, manta da batun ta, muna zuba ido muga abinda ai faru".
~~~
SAMAIND
Yau kwana biyu da fara bawa Yan matan da suka zo gurin Mehran horo, a cikin su har da Jasrah da Mahlika. Yaran Gwamnonin Yankunan shi. Sosai suke daukar abinda ake musu.
Dan haka na maida hankali akan kaiwa da komowa duk abinda ake bukata daga gare shi, nice akan gaba.
"Ikram! Ana son magana dake a lambun tarihi"
"Ke Inam waye?"
Na tambaye ta kasa kasa,
"Wani ne wai Sarwat." Da sauri na juya baya na, tare da duba ko dakaru na biye dani.
Ajiyar zuciya na sauke tare da nufar Lambun tarihi. Da sauri.
Ina shiga na hango shi tsaye, yana me juya min baya.
"Sarwat! Kasan kasadar da ka kawo kanka kuwa? Ina Noman din yake?"
Juyawa yayi ya zuba min ido, hautsina kayan cikina yayi ban san lokacin da amai yazo min ba, na toshe baki na.
"Meehhh! meehhh!! meehraan!!!"
Rufe baki na, nayi da sauri tare da fashewa da kuka, na zube akan gwiwata.
Durkusawa yayi tare da d'ago kai na,
"Sabida bani da amfani shine kika manta da suna na! Noman Anwarulkharim! Shine cikekken sunan. Wakiliyar SULTAN Mehran. Nagode sosai, hakan ma Arziki ne. Ina kuma baki hakuri da abinda zan gaya miki, nazo ne mu koma gida.". Jan fasali yayi tare da kallona.
"Kiyi hakuri! Idan kin shirya ranar da zasu zab'e mishi matan shi, ranar zamu bar garin nan, sannan bazan miki dole ki bani ba, amma mahaifanki zan mai dake, dan kina da damar zama da Sultan Aamaan Mehran, ko zab'an zama da mutanen Gezira. Idan kuma na matsa miki, Kuma kiyi hakuri, nagode."
Rike hannun shi nayi tare da cewa.
"Ka rufa min asiri meye yasa kake bani hakuri, zan bika zan bika naga Airan. Zan bika naga gidan mu. Zan bika sabida kai ne kawai a zuciyata, wallahi babu ranar da rana zata fito ta fadi banyi kukan rashin ku ba, Noman ina kaunar ka, ko yau ka tashi mu tafi."
Girgiza kai yayi tare da cewa.
"Kiyi hakuri! Airan ta rasu."
Kukan ne ya tsaya min cak, baki na sake, wasu irin kwalla ne suke zuba min wannan bai sauka ba, wannan ya sauka, ban san lokacin da ya bar gurin ba, ina zaune baki a bude, na dimauce.
D'ago ni aka yi, tare da juyar dani, baki na a sake. Ina kallon shi tare da dakarun da aka baza ana niman Noman, saka kai na yayi a kirjin shi tare da rungume ni, sai lokacin na sami damar sake ajiyar zuciya, me tafe da kuka. Sosai nake yi. Tunda nayi wannan kukan har mukan shiga cikin gidan, ban kuma kuka ba, hawaye na ne ya kafe tare da saukar min da zazzaɓi, sosai na kwanta babu lafiya.
Tsawon kwana uku bana ko magana abin duniya Dame shi..idan na kalle shi tausayi yake bani, dan haka ranar da na fara magana abinda nace mishi.
"Karka ajiye ni a cikin abubuwa masu kyau, Ni bakar kaddara ce! Ba lallai bane na zame maka farar aniya. Ina baka hakuri domin Ni ba mazauniya bace.
Zanen Qaddara ta ce ta kawo ni daular ka, ko ina nan ko bani nan ka rike al'ummar ka, domin suna bukatar ka. Mehran mulki yana bukatar nutsuwa da fahimtar al'umma bai daya, sai kuma ina rokon ka, ka amshi addinin Musulunci kai ma zaka ji dadin a ranka. Amma babu dole domin mulkin adalci koda ba musulmi bane Allah yana mishi jagora, mulki musulmi idan babu adalci Allah yana rusata!"
Matsawa nayi jikin shi tare da riko hannun shi na saka a saman fuskana, tare da cewa.
"Mehran! Ina farin cikin zama da kai babu cuta babu cutarwa, Mehran kayi hakuri gaskiya ba ayi Ni domin nan ba, rayuwa ta da farin cikina suna wata duniyar na daban."
Kasa magana nayi sannan a hankali nake gaya mishi rasuwar kanwata, tare da kasa gaya mishi gaskiyar guduwa zanyin, domin har ga Allah yana bani tausayi,. Sannan na dauko wasu takardu da na hada bayanan da na samu a cikin fadar shi da almuddaha da ake a cikin masarautan shi na mika shi.
Sannan na mishi bayanin halin da Masarautan shi yake ciki, tare da saka hannun na jikin shi, ake zaluntar al'ummar shi. Zubawa juna ido muka yi sannan na fara dawo mishi da kalaman shi da muka yi lokacin da muka je madinatul Mah.
"Ni mace ce mara daraja, Ni kowani kare da doki yake bina, Mehran gashi kuma zan yi nisan zango, Mehran ka koya min yadda zan kare kai na, da lafiya ta. Sultan nagode sosai. Sultan nagode sosai."