Showing 213001 words to 216000 words out of 274096 words
Chapter 72 - DAULA BIYU Complet Document .txt
sabida duk cikin babu wacce ta taki sa'ar da na samu, dan haka babu wacce zata min iyayi ko kankanba. Ina fita na hango Rahil zaune shi dasu Shairah da Fudail sai Darda.
A hankali na isa gare su, sannan nayi musu bankwana. Ina lura da yadda jikin shi yayi sanyi musamman yadda na same su, suna hirar Mehran. A hankali muke tafiya yana me sauke ajiyar zuciya a kai a kai, ba zaka tab'a jin bai sauke tare da fitar numfashin sa ba, kuma yaki kallona, abinda na fahimta matsanancin kishi yake. Domin ina lura da yadda yake naushin hannun shi har muka isa gidan.
Saka kai nayi zan wuce masaukin mu naji ya riko hannuna, juyawa nayi tare da kallon shi.
"Me yasa baki da tausayi da jin kai? Me yasa ba zaki gane yadda nake kokarin kyautata miki ba? Kin fi son bare a kaina? Tun da kika shiga cikin gidan kika manta da batu na, sai yanzun kika tuna dani, gaskiya ina da zafin kishi da zafin rai idan na kuma ganin haka zan aikata abinda ba zai miki dadi ba."
Kasakai nayi ina kallon bawan Allah nan, wato sun mai dani sha tara, kowannen su buga ni yake kamar tamola, meye nayi musu haka da kowannen su yake jin zafi na? Nima cikin fushi na bar shi a tsaye,ban saurare shi ba,balle yayi tunanin zan bashi hakuri ko wani abu makamancin haka.
... A wannan daren mutane uku basu rintsa ba, gabaki dayan su kowanne da abinda yake ji, dan haka gari na wayewa. Mehran ya fara fitowa yana kallon masaukin da suke ciki. Har zuwa lokacin da aka fara fidda kayan Ikram, a lokacin Abrad ya shigo gidan. Babu shiri Mehran shima ya fita tare da nufar hanyar gidan.
Tare da wasu manyan dakarun shi suna dauke da manyan akwatin karfe, sai bayi mata da suke bin bayan Fudail dauke da tire a lullube da jan kyale. Tun safe Izmah da Nimra suke kallona,
"Toh wai meye suke nufi dake ne? Domin ga Abrad da Mehran suna Wajen sai Amir Rahil."
Zare tagumi nayi tare da cewa.
"Wallahi sun addabi rayuwata, musamman Abrad ya hana rayuwata sakat, Mehran kuwa bani da damuwa dashi. Sabida na gama zama dashi." Shiru nayi ina kallon su, kafin na cigaba da cewa.
"Amir nake tsoron kar Abrad yayi mishi renin hankalin da."
"Amirah ana jiran ki!"
A hankali na mike tare da hada abinda zan iya, sauran kuma su Izmah suka hada min, fitowa nayi na sami Sultanah Amrah, tana karyawa,zama nayi dan sam ban lura da falon dauke yake da mutane ba, sai da na zuba ruwan shayi, na tsinkayo Muryan Mehran.
"Ko zaki hada dani dan ban karya ba."
Caaaa suka min da ido, shi kuma yadda ya zauna tare da saka hannun shi ya kishingida kamar yana falon shi, d'ago kai nayi ina kallon shi. Kafin na mike tare da hada mishi jikina yana rawa, tasowa yayi tare da nufar inda nake hada shayin ya kai hannun shi zai rike ni.
"Har yanzun tana karkashin kulawata ce, idan ta fita daga Cikin SAMAIND ta shiga da'iran kulawar kowa, anan babu wanda ya isa ya tab'a ta a gaban D'an Abdus Samad."
Had'iye yawun nayi ina kallon Amir Rahil da yazo rike ni, sosai na kadu da yadda Fuskar Mehran ya sauya, dan haka kafin Amir Rahil ya rike ni, na kauce sannan na nufi inda Mehran da kofin ruwan zafin. Duk abinda yake faruwa Sultanah Amrah da Abrad suna kallon mu, sake shan kaina Amir Rahil yayi, ture shi Mehran yayi tare da kallon inda nake, ya mika min hannuna.
A sanyayye na isa gare shi, rike hannuna Rahil yayi.
"Akwai baiko na akanta dan haka na fika iko akanta."
"Ni kuma baiwata ce, naga wanda ya isa ya min iko akanta."
"Wai kai waye ne? Meye nufinka da ita? Bilqisul Ikram Mustapha matar da zan aura ce! Dan haka baka isa ka tab'a min matar da zan aura ba."
Karb'an ruwan shayin yayi tare da ajiyewa, ya fisgo jikin shi.
"Aamaan ka sake min mata na" Amir Rahil ya daka mishi tsawa,
Tsakiyar su Abrad ya shiga tsakanin su, kallon Mehran yayi cikin nutsuwa da jin dadi, muryan shi kasa kasa, yace mishi.
"Fanko ce kake harzuka akanta, shima idan yasan wacece ita. Fasa auren ta zai yi. Karshe dai Ni ne dai zan karasa ab...."
Tass Mehran ya dauke shi da mari, tare da shake wuyar shi. Kamar mahaukaci ya rufe shi da duka, abun sai ya bamu tsoro da mamaki. Domin kuwa Amir Rahil ya kamata ya daka, amma ya bige da dukar Abrad dama yana cike dashi, kokarin shiga tsakanin su nayi amma Abrad ya riko ni, dai-dai Mehran yaja hannun shi zai naushe shi. Ganin yadda ya rungume ni yasa shi tsayawa cak.
" Sarkin Karfi gata a kirjina dake mu, nace ka dake mu. Ga Ikram din ta faɗa da bakin ta" da sauri na juya ina kallon shi tare da girgiza mishi kai.
"Karka tozarta ta! Na yarda kayi min kome amma karka wulakantatta a gaban jama'ar ta." Ya faɗa tare da sauke hannun shi. Kallon su nayi na ma kasa magana, hawaye Masu zafi suke zuba a cikin idanuna.
"Abrad meye nayi maka da zafi haƙa?"
Na tambaye shi bayan na kwace kai na, kallona yayi sannan ya fashe da dariya, bude baki yayi zai magana na kifa mishi mari, hawaye na zuba.
"Meye nayi maka da zafi? Meye na tsare maka da kake niman hanyar da zaka wulakantani? Ka gaya min meye nayi maka!"
"Zaki biya abinda kika aikata." Takowa yayi gaba na, tare da kallon fuskana yace min.
"Kina jin kunyar Kakarki ce? Ko kina tsoron kar kashe gimbiyar da tayi mu'amalanci wani namijin? Ko zaki iya tuna abinda wannan hannun yayi miki shekarun baya, da na tura shi."
Ji nayi kamar zan fadi,.dan wani irin jiri ne yake niman kayar dani, Lokaci guda Mehran da Rahil suka kawo min dauki, murmushi yayi sannan yace min.
"Sai na hanaki sukuni."
"Abrad wannan wani irin wawanci ne? Ikram din ce kake mata irin wannan haukar ka manta matsayinta ta ne a gurin Sariya? Yar Yayar matar ka ce fa. Wannan wacce irin hauka ce mara to ..."
"Kul! Idan kika yi wasa abinda zan fada sai ya saka yan majalisar ki sun sauke ki a kan mulkin ki, sannan kuma itama Ikram din Askandariya sai tayi mata wahalar shi, kai kuma Mehran kamar yadda na gaya mata haka kai ma. Kai sha-sha-sha bani da lokacin ka, sabida mutanen da suke da iko nake yi dasu. Abinda na sani baka isa ka auri Ikram ba. Amma zan baka damar niman taimako na yadda zaka aure ta. Idan ka shirya."
Yana gama abinda zai yi ya fita yana dariya wai shi yayi nasara. Sai da ya fita na sami damar fashewa da kuka. Kamar yadda naso yi. Mikewa Mehran yayi tare da barin gidan, Rahil kuwa kasa magana yayi. Kawai sai damke hannuna yayi tare da cewa.
"Ba zan tab'a barin ki cikin matsala ba matukar ina raye."
Sultanah kuwa kasa d'gowa tayi domin kuwa tana me jin kunya da bakin cikin abinda ya faru, ita da kanta ta kashe Zuri'ar ta, yau tayi abinda zai kaita ya baro ta.
Rike rigar shi nayi tare da fashewa da kuka, Abrad ya wulakantani, Mehran ya juya min baya, bani da zabin da ya wuce Rahil ko naki ko naso Rahil shine ya dace da rayuwata, ba zai tab'a bari na cikin kuncin rayuwa ba. Dan haka ya taimaka min na mike tare da kai ni har waje inda aka jibe mana kayan da Mehran ya kawo min yayi tafiyar shi.
Haka su Izmah da Nimra suka kwashe kayan aka zuba a saman rakumai, sannan na shiga keken dokin shi, su kuma suka shiga cikin na Sultanah Amratu. Muka bar masaukin bayan an hada mu da rakiyar dakarun Samaind kimanin dubu goma sha biyar, har Askandariya zasu rakani inji Sultan Mehran.
Tunda na shiga cikin keken nake kuka, wanda nasan ba na abinda Abrad yayi min bane, a'a zunzurutun rabuwa da Mehran ne da zanyi. Ji nake kamar na sauka nace musu bani tafiya ko ina zan zauna da Mehran. Tun kafin mu bar da'iran SAMAIND. Naji jikina yana bani tare dashi muke tafiya, dan haka na bude labulen jikin keken. Kurawa juna ido muka yi, sanya yake da kayan dakarun ƙasar. Hannun shi ya kai tare da riko hannuna. Sannan ya sake linzamin dokin shi ya saka min zoben da ya ciro daga aljuhun shi. Tare da sumbatar hannun.
"Ina tare dake har karshen rayuwata." Daga haka ya sake min hannuna. Ina gani muka yi ta tafiya muka bar shi a can baya. Hawayen da nake dannewa ne ya zubo min.
A hankali nace.
"Ina sonka!" Haka muka bar shi a gurin.
....... Hawayen da bai tab'a zaton zai zubda akan So ba yau ya zubda su. Rike d'an kunnenta yayi tare da kallon shi, ya tuna ranar da tazo amsar tayin shi take zata bude inda d'an kunnen yake ya hanata, kwallar shi ce ta sauka akan d'an kunnen. Ya damke a hankali. Tare da sumbatar shi, yace.
"Ina Sonki! Mara iyaka. Kece fitilar rayuwata."
Ya fada a hankali, kamar wani na jin shi. Tabbas sai yanzun ya kuma fahimtar shakuwar da take tsakanin su, bata wasa bane.
"Abrad!" Da sauri ya juya linzamin dokin shi ya nufi SAMAIND a guje tare da tuna ranar da ya fara ganin Ikram......
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
Littafi na uku
01
Tunda ya bar masaukin su Ikram ya sa aka hada musu nasu kayan suka bar gidan da suke, sai da suka kusan barin cikin garin SAMAIND. Yasa aka kama Nawwas.
Kallon juna suka yi kafin yacewa.
"Na sami labarin ka gayawa Fudail duk abinda ya faru, sai dai kayi kuskuren domin ba zan barka a raye ba, shi yasa nayi gaggawan barin SAMAIND domin wancan mahaukacin idan ya ritsani sai ta Allah."
Dariya Nawwas ya saka yana kallon Abrad, tare da nuna shi da yatsa kafin yace mishi.
"Kai tsaye ka mu'amalancin Ikram, Ni kuma a ruwan sanyi Mu'amalanci kanwarka tare da dauke abinda yake jikinta.
Bamu bar SAMAIND ba sai da na tabbatar da na kuma buɗe tsakanin kafarta na jefa linzamina. Yadda koda na mutu dole na bar baya da kura."
Dariya ya kuma fashewa da shi, yana mai maita abinda ya faru,, yana kuma gaya mishi abinda ya aikata da Kanwar shi. Babu abinda ya kai wannan abin tashin hankali. Idanun shi ne suka cika da kwalla. Wanda ya kasa jurewa har ya kai da ya zuba masa.
"Meye nayi maka Nawwas? Da kayi min yankan baya haka? Nawwas meye na tsare maka hakan da ka zab'i cilla rayuwar kanwata cikin tashin hankali? Nawwas me yasa baka yi a kaina ba."
"Hahaha... Hmmm, ka zata zan zuba ido ne ka tozarta Ikram? Ko ka zata zan zuba ido ne ka cigaba da abinda ranka yake so? Wannan shi ne kishi a tsakanin zubda jini. Idan kana tunanin ka zubda jinin Nu'man dan jin dadin ka da kuma cusgunawa Mehran dan Ikram ta tsane shi wannan kuskure ne babba karka manta kamar yadda ka mayarda da Ikram a shimfid'ar ka, hakan na mayar da Amirah Azizatul Nissah. Na maida ta kamar matar da na biya sadaki me daraja dan haka karka yi tunanin Mehran zai yarda da wata mace bayan Ikram! Kamar yadda kake da kwarin gwiwar rubutawa yan majalisar Masarautan SAMAIND haka nima na gayawa Mehran alakata da Kanwar ka, dan haka sai ka jira abinda zai biyo baya domin dai SAMAIND ba kanwan lasa bane.
Kayi kuskuren hadamme kome, Ni kuma nayi ƙoƙarin bayyanawa duniya waye kai, Ikram yanzun tayi maka nisa kanwarka zaka yi kokarin ganin ka fito da ita daga SAMAIND idan ba haka ba". Cikin wani irin fusata Abrad yaja takobi bai yi wata wata ba, ya sokawa Nawwas a kirjin shi sai da ya hudo bayan shi.
Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, ya kuma sake jan takobin ya soka mishi sai da jini ya fito ta bakin Nawwas. A lokacin ya tuna da Abinda Nu'man ya gaya mishi.
*Ban san meye muka yi ba kuka raba mana rayuwar mu! Sai dai nasan wata rana kai ma haka ce zata mamaye ka! Yadda kayi min haka kai ba za a maka*
Hawaye ne ya zubo mishi tare da kallon Abrad cikin tsannanin azaba.
"Ni nayi haka ne domin al'ummar Daular Umayyad! Nayi wannan aikin ne saboda Banu Umayyad. Sai dai kuma nayi imanin yadda na zubda jinin bawan Allah haka nima rawa jinin ya salwanta. Kai kuma Banu Umayyad za a shafe baki daya.
Sai kayi gudun da babu macecin ka. Abrad ni abokinka ne tun yaranta ka kashe ni da hannunka. Ba iya ni ne matsalar ba, rayuwar Kanwar ka anan zaka Fahimci muhimmancin rayuwar wanda kake so yaƙe"
Kasa magana yayi sakamakon jinin da ya cika mishi baki, mika mishi hannu yayi amma fir yaƙi amsar hannun. Juya baya Abrad yayi kwalla na zuba mishi. Bai san ta yadda zai taimakawa Azizah ba, babban tashin hankalin shi Azizatul Nissah. Juyawa yayi cikin tsannanin fushi ya sare kan Nawwas, ya fadi can jini yana zuba kamar da bakin kwarya.
Zama yayi tare da sake takobin ya fashe da kuka. Domin Nawwas ba kashin yarwa bane, ba kasafai ake samun irin shi ba. Nawwas abokin tarayya ne na kwarai. Mutum ne da ba a cika samun irin shi ba. Shi yasa yake kuka, sai kuma yadda Nawwas yaci Amanar shi yayi ta tarayya da Kanwar shi.
Sannan ya kwashi sirrin shi ya gayawa Mehran, "Me yasa Nawwas yaci amanata?" Ya tambaya da karfi cikin tsorata da yanayin shi duk suka ja baya, sai daga can asalin amintaccen bawan Nawwas yace mishi.
"Sabida shi ya fara son Ikram! Ya kaunace ta sama da kaunar da yakewa rayuwar shi! Ya bada rayuwar shi ne domin ita? Ya kuma saka duk wani matakin da zai bawa rayuwar ta taimako koda baya raye.
Sultan kayi hakuri amma kaunar Nawwas ga Ikram gaskiya ce. Soyayyar shi ga Ikram gaskiya ce, tabbas yaso ta tun daga ranar da muka sayo ta, har zuwa yau. Ya gaya maka gaskiya kamar yadda kowa ya kasa fahimtar da kai haka ne. Amma tabbas bayi kuskuren ba, samun masoyi irin shi ma sai an tuna."
Yana fadar haka ya shiga tattara gangan jikin Nawwas da kanshi yana zubda hawayen bakin ciki, da tausayin abinda ya faru. Ya tuna abinda Nawwas ya gaya mishi jiya.
"Karka sake ka gaya mishi gaskiya akan alakata da Azizatul Nissah! Zan gaya mishi abinda zai fusata shi. Domin ya bar Ikram ta rayu da Mehran, naso Mehran ya tsaya muyi tsayayya magana dashi amma fir yaki. Dan haka zan gayawa Fudail Insha Allah zai saurare ni. Amma kasan me? Hmm idan Abrad yaga zai rasa Ikram zai sauya tsarin gudanar da abinshi ka saka ido kayi kallo. Don Allah Rab ka kula min da Azizatul Nissah da abinda zata haifa."
A kidime ya kalle shi sannan yace mishi.
"Shugabana ka manta matsayinta ne a yanzun? Har kake batun abinda zata haifa"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Ba da ita ga Mehran ba shi yake nufin ita din mallakar shi bace, ita da abin cikin ta nawa ne, kuma mallakina ce, don Allah karka sake wani abu ya shiga cikin rayuwar su, fatana idan ka bar Oman kayi ƙoƙarin tsayawa Ikram, ka same ta da batun kome, kuma na roke ka don Allah ka tsaya a bayanta karka bari wani ya tab'ata. Ita kuma zata tsaya a gaban Azizatul Nissah."
Wani irin kuka ne ya kwace mishi me ƙarfi yana me kuma rungume kan Nawwas, tare da jin tashin hankali sama da farkon faruwan kome, kara rungume kan yayi yana faɗin.
"Me yasa kayi haka? Me yasa ka bada rayuwar ka domin wasu. Baka tuna bayanka ne? Me yasa kika zab'i zubda jini sama da kome ne?"
Ya faɗa da karfi, yana kuka tare da k'amk'ame kan Nawwas, juyawa Abrad yayi tare da zuba mishi ido, tabbas sun zabi zubda jini sama da kome akan mace! Akan Ikram, koma waye za a kashe! Akan Ikram koda kuwa rayuwar shi ce zai iya badawa, wani irin kwalla yake zubdawa tare da kallon gawan Nawwas, mutum na farko da ya fara ankarar dashi kuskuren abinda yake aikatawa ya kashe mutumin da bai hada shi da kome ba ya kashe mutumin da zunzurutun kaunar shi da shi ko barci yake sai ya tashi idan ya tura a kira shi ya kashe.
Ya kashe mutumin da yaso shi da gaskiya, ihu ya takarkara a cikin jirgin ruwan, sai da duk suka toshe kunnen su, ya kuma fashe da kuka yana faɗin.
"Jininki fansa ce ga jinin Aminina" ya faɗa yana kuka da bakin cikin abinda ya aikata , Rab yana jin shi, tabbas ya fara dauko haske akan abin da Nawwas ya gaya mishi.
Shiru cikin gurin yayi babu wanda ya kuma magana, mik'ewa yayi tare da cewa.
"Ku dauki gawan shi ku wurga